Baibul a cikin shekara guda Nuwamba 13Ezekiyel 17:1-241. Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,2. “Ɗan mutum, ka shirya kacici-kacici ka faɗa wa gidan Isra’ila misali.3. Ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa babbar gaggafa mai manyan fikafikai, dogayen gasusuwa da gasusuwa da yawa masu launi iri-iri ta zo Lebanon. Ta cire kan al’ul,4. ta karya kan tohonsa da yake can bisansa ta kai ƙasar ciniki, inda ta shuka shi a birnin ’yan kasuwa.5. “ ‘Ta ɗebi waɗansu irin ƙasarku ta sa a ƙasa mai taƙi. Ta shuka shi kamar itacen wardi kusa da ruwa mai yawa,6. ya kuwa yi toho ya zama kuringa gajeruwa mai yaɗuwa. Rassanta suka tanƙwasa wajen gaggafar, amma saiwoyinta suka zauna a ƙarƙashinta. Ta haka ta zama kuringa, ta yi rassa ta kuma fid da ganyaye.7. “ ‘Akwai kuma wata babbar gaggafa mai manyan fikafikai da gashi mai yawa. Kuringan nan ta tanƙwasa saiwoyinta zuwa wajen wannan gaggafa daga inda aka shuka ta, ta kuma miƙe rassanta wajenta don gaggafar ta yi mata banruwa.8. An shuka ta a ƙasa mai kyau kusa da ruwa mai yawa don tă yi rassa masu yawa, ta ba da ’ya’ya ta kuma zama kuringa mai daraja.’9. “Ka gaya musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa wannan za tă ci gaba? Ba za a tumɓuke ta a kuma kakkaɓe ’ya’yanta don ta bushe ba? Dukan sababbin tohonta za su bushe. Ba sai da hannu mai ƙarfi, ko kuwa da yawan mutane za a tumɓuke ta daga saiwoyinta ba.10. Ko da an sāke shuka ta, za tă yi amfani ne? Ba za tă bushe gaba ɗaya sa’ad da iskar gabas ta hura ba, tă bushe a ƙasar da ta yi girma?’ ”11. Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa,12. “Ka faɗa wa gidan ’yan tawayen nan, ‘Ba ka san abin da waɗannan abubuwa suke nufi ba?’ Ka faɗa musu cewa, ‘Sarkin Babilon ya tafi Urushalima ya tafi da sarkinta da kuma manyan garinta, ya dawo da su Babilon.13. Sa’an nan ya ɗauki wani daga iyalin sarauta ya yi yarjejjeniya da shi, ya sa shi ya yi rantsuwa. Ya kuma tafi da shugabannin ƙasar,14. don a raunana masarautar, kada tă ƙara tashi, amma ta tsaya dai kan cika yarjejjeniyarsa.15. Amma sarkin nan ya yi tawaye a kan sarkin Babilon ta wurin aika jakadunsa zuwa Masar don a ba shi dawakai da sojoji masu yawa. Zai ci nasara? Shi da ya yi wannan abu zai tsira? Zai iya taka yarjejjeniya har ya tsere?16. “ ‘Muddin in raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, zai mutu a Babilon, a ƙasar sarkin nan da ya naɗa shi, domin bai cika rantsuwa da alkawarin da ya yi ba.17. Fir’auna da yawan sojojinsa da kuma yawan jama’arsa ba zai zama da taimako gare shi a yaƙi ba, sa’ad da sarkin Babilon zai gina mahaurai ya kuma yi ƙawanya don yă hallaka rayuka masu yawa.18. Bai cika rantsuwa ba ta wurin take alkawari. Domin sarkin Isra’ila ya ƙulla alkawari ya kuma aikata dukan waɗannan abubuwa, ba zai tsira ba.19. “ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce muddin ina raye, zan nemi hakkin rantsuwata da ya ƙi cikawa da kuma alkawarin da ya take.20. Zan kafa masa tarkona, zai kuma fāɗi a tarkona. Zan kawo shi a Babilon in kuma hukunta shi a can domin ya yi mini rashin aminci.21. Dukan sojojinsa zaɓaɓɓu za a kashe su da takobi, za a kuma watsar da waɗanda suka ragu ko’ina. Ta haka za ku san cewa Ni Ubangiji na faɗa.22. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ni kaina zan cire toho a kan itacen al’ul da yake can bisa in shuka; zan kuma karya ƙanƙanin reshe daga can bisan tohon in shuka a dutse mai tsayi.23. A ƙwanƙolin dutsen Isra’ila zan shuka shi; zai yi rassa yă ba da ’ya’ya yă kuma zama al’ul mai daraja. Tsuntsaye iri-iri za su yi sheƙa a cikinsa; za su sami mafaka a inuwar rassansa.24. Dukan itatuwan jeji za su san cewa Ni Ubangiji ne mai sa manyan itatuwa su zama ƙanana in kuma sa ƙananan itatuwa su zama manya. Nakan sa ɗanyen itace ya bushe, busasshen itace kuma ya zama ɗanye. “ ‘Ni Ubangiji na faɗa, zan kuma aikata.’ ”Ezekiyel 18:1-321. Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,2. “Me ku mutane kuke nufi da faɗar wannan karin magana a kan ƙasar Isra’ila cewa, “ ‘Ubanni sun ci ’ya’yan inabi masu tsami, haƙoran ’ya’ya kuwa sun mutu’?3. “Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ba za ku ƙara faɗar wannan karin magana a Isra’ila ba.4. Gama kowane mai rai nawa ne, mahaifi da ɗa, duk nawa ne. Mutumin da ya yi zunubi shi zai mutu.5. “A ce akwai mai adalci wanda yake aikata abin da yake daidai da kuma gaskiya;6. ba ya cin abinci a duwatsun tsafi ko ya dogara ga gumakan gidan Isra’ila. Ba ya ƙazantar da matar maƙwabcinsa ko ya kwana da mace lokacin al’adarta ba.7. Ba ya cin zalin wani, amma yakan mayar wa wanda ya ba shi jingina abin da ya jinginar masa. Ba ya yi fashi amma yakan ba wa mayunwata abinci ya kuma tanada wa marasa tufafi riga.8. Ba ya ba da bashi da ruwa ko ya karɓa ƙarin riba. Yakan janye hannunsa daga aikata mugunta yakan kuma yi shari’a cikin gaskiya tsakanin mutum da mutum.9. Yana bin ƙa’idodina yana kuma kiyaye dokokina da aminci. Wannan mutumin adali ne; tabbatacce zai rayu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.10. “A ce yana da ɗa wanda yana kisa ko yana yin ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa11. (ko da yake mahaifin bai yi ko ɗaya daga cikinsu ba). “Yakan ci abinci a duwatsun tsafi. Yakan ƙazantar da matar maƙwabci.12. Yakan ci zalin matalauta da mabukata. Yakan yi fashi. Ba ya mayar da abin da aka jinginar masa. Ya dogara ga gumaka. Yana aikata ayyukan banƙyama.13. Yakan ba da bashi da ruwa ya kuma karɓi riba mai yawa. Irin wannan mutum zai rayu? Ba zai rayu ba! Domin ya aikata dukan waɗannan abubuwa masu banƙyama, tabbatacce za a kashe shi, kuma hakkin jininsa zai zauna a kansa.14. “Amma a ce wannan ɗa yana da ɗa wanda ya ga dukan zunuban da mahaifinsa yake aikata, kuma ko da yake ya gan su, bai yi ko ɗaya daga cikin irin abubuwan nan ba, wato,15. “Bai ci abinci a duwatsun tsafi ba ko ya dogara ga gumakan gidan Isra’ila. Bai ƙazantar da matar maƙwabcinsa ba.16. Bai ci zalin wani ko ya karɓi jingina ba. Ba ya fashi amma yakan ba da abincinsa ga mayunwata ya tanada tufafi wa marasa tufafi.17. Yakan janye hannunsa daga zunubi ba ya kuma ba da bashi da ruwa ko karɓan riba da yawa. Yakan kiyaye dokokina ya kuma bi ƙa’idodina. Ba zai mutu saboda zunubin mahaifinsa ba; tabbatacce zai rayu.18. Amma mahaifinsa zai mutu saboda zunubinsa, domin ya yi ƙwace, ya yi wa ɗan’uwansa fashi ya kuma yi abin da ba daidai ba a cikin mutanensa.19. “Duk da haka kukan yi tambaya, ‘Me ya sa ɗan ba zai sami rabo a laifin mahaifinsa ba?’ Da yake ɗan ya yi abin da yake daidai da kuma gaskiya, ya kuma kiyaye dukan ƙa’idodina, tabbatacce zai rayu.20. Mutumin da ya yi zunubi shi zai mutu. Ɗa ba zai sami rabo a laifin mahaifi ba, mahaifi ba zai sami rabo a laifi ɗa ba. Adalcin adali zai zama nasa, muguntar mugu za tă koma kansa.21. “Amma in mugun mutum ya juya daga dukan zunubin da ya aikata ya kuma kiyaye dukan ƙa’idodina ya kuwa yi abin da yake daidai da kuma gaskiya, tabbatacce zai rayu; ba zai mutu ba.22. Babu laifin da ya yi da za a tuna da su. Saboda abubuwan adalcin da ya aikata, zai rayu.23. Ina jin daɗin mutuwar mugu ne? In ji Ubangiji Mai Iko Duka. A maimako, ban fi jin daɗi sa’ad da suka juyo daga hanyoyinsu suka rayu ba?24. “Amma in mai adalci ya juya daga adalcinsa ya yi zunubi ya kuma aikata abubuwa masu banƙyamar da mugun mutum ke aikatawa, zai rayu? Babu abubuwan adalcin da ya aikata da za a tuna da su. Saboda rashin amincinsa da kuma saboda zunubai da ya yi, zai mutu.25. “Duk da haka kun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Ka ji, ya gidan Isra’ila. Hanyata ba daidai ba ce?26. In mai adalci ya juye daga adalcinsa ya yi zunubi, zai mutu saboda wannan; saboda zunubin da ya yi, zai mutu.27. Amma in mugun mutum ya juye daga muguntarsa ya kuma yi abin da yake daidai da kuma gaskiya, zai ceci ransa.28. Domin ya lura da dukan laifofin da ya yi ya kuma juye daga gare su, tabbatacce zai rayu; ba zai mutu ba.29. Duk da haka mutanen Isra’ila sun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Hanyoyina ba daidai ba ne, ya gidan Isra’ila? Ba hanyoyinku ne ba daidai ba?30. “Saboda haka, ya gidan Isra’ila, zan hukunta ku, kowa bisa ga hanyarsa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ku tuba! Ku juye daga dukan laifofinku; sa’an nan zunubi ba zai zama sanadin fāɗuwarku ba.31. Ku raba kanku da dukan laifofin da kuka yi, ku sami sabuwar zuciya da sabon ruhu. Don me za ku mutu, ya gidan Isra’ila?32. Gama ba na jin daɗin mutuwar wani, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ku tuba don ku rayu!Zabura 124:1-81. Da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba, bari Isra’ila yă ce,2. da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba sa’ad da aka auka mana,3. sa’ad da fushinsu ya ƙuna a kanmu, ai, da sun haɗiye mu da rai;4. da rigyawa ta kwashe mu, da ambaliya ta rufe mu.5. Da ruwa mai hauka ya share mu ƙaf.6. Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda bai bari aka yayyage mu da haƙoransu ba.7. Mun tsira kamar tsuntsu daga tarkon mai farauta; an tsinke tarko, muka kuwa tsira.8. Taimakonmu yana a sunan Ubangiji, Wanda ya yi sama da ƙasa.Karin Magana 28:21-2121. Nuna sonkai ba shi da kyau, duk da haka mutum zai aikata abin da ba daidai ba saboda ’yar ƙaramar rashawa.Ibraniyawa 9:1-281. Alkawarin farko ya ƙunshi ƙa’idodi don sujada da kuma tsattsarkan wuri a duniya.2. An kafa tabanakul. A cikin ɗakinsa na farko akwai wurin ajiye fitila, tebur da kuma keɓaɓɓen burodi; an kira wannan Wuri Mai Tsarki.3. Sa’an nan akwai labule, kuma a bayan labulen akwai ɗaki na biyu da ake kira Wuri Mafi Tsarki,4. wanda yake da bagaden zinariya na turare da kuma akwatin alkawarin da aka dalaye da zinariya. A cikin akwatin alkawarin akwai tulun zinariya mai Manna a ciki, sandan Haruna wanda ya yi toho, da kuma allunan dutsen alkawari.5. A bisa akwatin alkawarin kuwa akwai kerubobi na Ɗaukaka, waɗanda suka inuwantar da murfin kafara da fikafikansu. Sai dai ba za mu tattauna waɗannan abubuwa dalla-dalla a yanzu ba.6. Sa’ad da aka shirya kome haka, sai firistoci suka shiga kullum cikin ɗaki na waje don su yi hidimarsu.7. Amma babban firist ne kaɗai yakan shiga ɗaki na ciki-ciki, sau ɗaya tak a shekara, kuma sai da jini, wanda yakan miƙa domin zunubansa da kuma domin zunuban da mutane suka yi a cikin rashin sani.8. Ta haka Ruhu Mai Tsarki ya nuna cewa ba a riga an bayyana hanyar shiga Wuri Mafi Tsarki ba tukuna, muddin tabanakul na fari yana nan tsaye.9. Wannan ma yana da ma’ana wa mutane a yau. Ya nuna cewa ba za mu iya wanke lamirinmu ta wurin miƙa baye-baye da hadayu ba.10. Waɗannan ƙa’idodi sun shafi sha’anin abinci da abin sha ne kawai da kuma ƙa’idodi tsarkake kanmu. Dokoki game da abubuwa na waje da ake amfani da su za su kasance ne sai lokacin ya yi da za a kawo abu mafi kyau.11. Sa’ad da Kiristi ya zo a matsayin babban firist na kyawawan abubuwan da suka riga suka kasance a nan, ya bi ta cikin tabanakul mafi girma da kuma mafi cikakke wanda ba mutum ne ya yi ba, wato, ba na wannan halitta ba.12. Bai shiga ta wurin jinin awaki da na maruƙa ba; amma ya shiga Wuri Mafi Tsarki sau ɗaya tak ta wurin jininsa, bayan ya samo madawwamiyar fansa.13. In har akan yayyafa jinin awaki da na bijimai da kuma tokar karsanar a kan waɗanda suke marasa tsabta bisa ga al’ada, a tsarkake su yadda za su zama masu tsabta a waje,14. balle jinin Kiristi, wanda ta wurin Ruhu madawwami ya miƙa kansa marar aibi ga Allah, ai, zai tsabtacce lamirinmu daga ayyukan da suke kai ga mutuwa, don mu bauta wa Allah mai rai!15. Saboda haka Kiristi shi ne matsakancin sabon alkawari, don waɗanda aka kira su sami madawwamin gādon da aka yi alkawari, yanzu da ya mutu a matsayin mai fansa don yă ’yantar da su daga zunuban da aka aikata a ƙarƙashin alkawari na farko.16. Sa’ad da wani ya yi alkawari game da gādonsa, dole a tabbatar da mutuwar wanda ya yi ta,17. domin alkawarin gādo yana aiki ne kawai bayan mai yinsa ya mutu, ba ya taɓa aiki yayinda mai yinsa yana da rai.18. Shi ya sa alkawari na farko bai fara aiki ba sai da aka zub da jini.19. Sa’ad da Musa ya sanar wa dukan mutane kowane umarni na doka, sai ya ɗauki jinin maruƙa tare da ruwa, jan ulu da kuma rassan hizzob, ya yayyafa a kan naɗaɗɗen littafin da kuma a kan dukan mutanen.20. Ya ce, “Wannan shi ne jinin alkawarin da Allah ya umarce ku ku kiyaye.”21. Ta haka ya yayyafa jinin a kan tabanakul da kuma a kan dukan kayayyakin da ake amfani da su don yin hidima.22. Tabbatacce, doka ta bukaci a tsabtacce kusa kowane abu da jini, kuma in ba tare da zub da jini ba babu gafara.23. Waɗannan abubuwa hotuna ne kawai na abin da yake a sama, dole kuma a tsarkake su ta wurin waɗannan ƙa’idodi. Amma dole a tsarkake ainihin abubuwa na sama da wani abu mafi kyau.24. Gama Kiristi bai shiga wani wuri tsattsarka da mutum ya yi ba, wanda yake hoto ne kawai na gaskataccen, a’a sama kanta ya shiga, domin yă bayyana a gaban zatin Allah a yanzu saboda mu.25. Bai kuwa shiga sama domin yă yi ta miƙa kansa a kai a kai, yadda babban firist yake shiga Wuri Mafi Tsarki kowace shekara da jinin da ba nasa ba.26. Da a ce haka ne, ai, da Kiristi ya sha wahala sau da yawa tun halittar duniya. Amma yanzu ya bayyana sau ɗaya tak a ƙarshen zamanai domin yă kawar da zunubi ta wurin miƙa kansa hadaya.27. Kamar dai yadda aka ƙaddara wa mutum yă mutu sau ɗaya, bayan haka kuma sai shari’a,28. haka aka miƙa Kiristi hadaya sau ɗaya domin yă ɗauke zunuban mutane masu yawa; zai kuma bayyana sau na biyu, ba don yă ɗauki zunubi ba, sai dai don yă kawo ceto ga waɗanda suke jiransa. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.