Baibul a cikin shekara guda Nuwamba 18Ezekiyel 27:1-361. Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,2. “Ɗan mutum, ka yi makoki domin Taya.3. Ka ce wa Taya, wadda take zaune a hanyar shiga zuwa teku, kasuwar masu yawa mutane a bakin teku, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Kin ce, ya Taya, “Ni kyakkyawa ce cikakkiya.”4. Manyan tekuna ne wurin zamanki; maginanki sun sa kyanki ya zama cikakke.5. Sun yi dukan katakanki daga itatuwan fir daga Senir; sun kwaso itatuwan al’ul daga Lebanon don su yi miki jigon jirgin ruwa.6. Da oak daga Bashan suka yi sandunan tuƙan jirgin ruwa da itatuwan kasharina daga bakin tekun Saifurus suka yi daɓe jirgin ruwanki, suka kuma manne masa hauren giwa.7. Lilin mai kyau mai ado daga Masar ne filafilan jirgin ruwanki suka kuma zama tutarki; an yi tutarki da shuɗi da shunayya daga bakin tekun Elisha.8. Mutanen Sidon da Arfad su ne matuƙan jirgin ruwanki; gwanayenki, ya Taya, suna ciki a matsayi matuƙan jiragen ruwa.9. Masu hikima na Gebal suna ciki a matsayin masu tattoshe mahaɗan katakon jirginki. Dukan jiragen ruwa da matuƙansu sukan zo wurinki don kasuwanci.10. “ ‘Mutanen Farisa, Lidiya da Fut su ne suka zama sojoji a cikin mayaƙanki. Sun rataye garkuwoyinsu da hulunan kwano a katangarki, suna kawo miki daraja.11. Mutanen Arfad da Helek sun yi tsaron katangar a kowace gefe; mutanen Gammad su ne a hasumiyoyinki. Sun rataye garkuwoyinsu kewaye da katangarki; sun sa kyanki ya zama cikakke.12. “ ‘Tarshish ta yi ciniki da ke saboda yawan wadatar kayayyakinki; sun sayi kayan cinikinki da azurfa, ƙarfe, kuza da dalma.13. “ ‘Girka, Tubal da Meshek sun yi kasuwanci da ke; sun sayi kayanki suka biya da bayi da kuma abubuwan da aka yi da tagulla.14. “ ‘Mutanen Bet Togarma sun sayi kayan cinikinki da dawakai, dawakan yaƙi da alfadarai.15. “ ‘Mutanen Dedan sun yi kasuwanci da ke, bakin teku masu yawa abokan cinikinki ne; sun biya ki da hauren giwa da katakon kanya.16. “ ‘Mutanen Aram sun yi ciniki da ke saboda yawan kayanki; suka sayi kayan cinikinki da zumurrudu, da shunayya, da kayan ado, da lilin mai taushi, da murjani, da yakutu.17. “ ‘Yahuda da Isra’ila sun yi kasuwanci da ke; sun sayi kayanki da alkama da Minnit da alawa, da zuma, da mai, da ganyaye masu ƙanshi.18. “ ‘Mutanen Damaskus sun ga abin da za ki iya bayarwa sai suka yi ciniki da ke, ta sayi kayanki da ruwan inabi daga Helbon, da ulu daga Zahar.19. Wedan da Yaban kusa da Uzal, suka sayi kayanki; wato gyararren ƙarfe da kayan yaji.20. “ ‘Mutanen Dedan sun sayi kayanki da sirdin zama a kan dawakai.21. “ ‘Mutanen Arabiya da dukan sarakunan Kedar abokan cinikinki ne; sun yi ciniki da ke suka sayi kayanki da ’yan raguna, da raguna, da awaki.22. “ ‘’Yan kasuwan Sheba da Ra’ama sun yi ciniki da ke; suka sayi kayanki da kayan yaji mafi kyau iri-iri, da duwatsu masu daraja iri-iri, da zinariya.23. “ ‘Haran, Kanne da Eden da kuma ’yan kasuwan Sheba, Assuriya da Kilmad sun yi ciniki da ke.24. A kasuwarki sun yi ciniki da ke suka sayar miki tufafi masu tsada, da na shuɗi, da masu ado, da dardumai masu ƙyalƙyali da kirtani, da igiyoyi waɗanda aka tuƙa da kyau.25. “ ‘Jiragen ruwan Tarshish sun zama masu jigilar kayanki. Kin cika da kaya masu nauyi a tsakiyar teku.26. Matuƙan jiragenki sun kai ki can cikin manyan tekuna. Amma iskar gabas za tă farfasa ki kucu-kucu a tsakiyar teku.27. Dukiyarki, cinikinki da kayan kasuwarki, ma’aikatanki na jirgi, matuƙan jiragenki da masu tattoshe mahaɗan katakan jiragenki, ’yan kasuwarki da dukan sojojinki, da kuma kowa da yake cikin jirgi zai nutsa a tsakiyar teku a ranar da jirginki zai nutse.28. Ƙasashen bakin teku za su girgiza sa’ad da matuƙan jirginki suka yi kuka.29. Dukan waɗanda suke riƙe da matuƙi za su ƙyale jiragensu; ma’aikatan jirage da dukan matuƙan jirage za su tsaya a bakin teku.30. Za su tā da muryarsu su yi kuka mai zafi a kanki; za su yayyafa ƙura a kawunansu, su yi ta birgima a cikin toka.31. Za su aske kawunansu saboda ke za su kuma sa tufafin makoki. Za su yi kuka dominki su yi ɓacin rai da kuma kuka mai zafi.32. Yayinda suke kuka a kanki kuwa, za su yi makoki dominki suna cewa, “Wa ya taɓa yin shiru kamar Taya, kewaye da teku?”33. Sa’ad da kayan cinikinki suka tafi ƙasashen hayi, kin gamsar da al’ummai masu yawa; da dukiyarki masu yawa da kuma kayan cinikinki kin azurtar da sarakunan duniya.34. Yanzu teku ta farfashe ki cikin zurfafan ruwaye; kayan cinikinki da dukan kamfaninki sun nutse tare da ke.35. Dukan mazaunan bakin teku sun giggice saboda masifarki; sarakunansu sun tsorata ƙwarai fuskokinsu kuwa sun yamutse don tsoro.36. ’Yan kasuwa a cikin al’ummai suna yin miki tsaki; kin zo ga mummunar ƙarshe ba za ki ƙara kasancewa ba har abada.’ ”Ezekiyel 28:1-261. Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,2. “Ɗan mutum, ka faɗa wa mai mulkin Taya cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Cikin alfarmar zuciyarka ka ce, “Ni allah ne; ina zama a kan kursiyin allah a tsakiyar tekuna.” Amma kai mutum ne ba allah ba, ko da yake ka ɗauka kana da hikima kamar allah.3. Ka fi Daniyel hikima ne? Ba asirin da yake ɓoye a gare ka?4. Ta wurin hikimarka da ganewarka ka sami dukiya wa kanka ka kuma tara zinariya da azurfa cikin wuraren ajiyarka.5. Ta wurin dabararka mai girma cikin kasuwanci ka ƙara dukiyarka, kuma saboda dukiyarka zuciyarka ta cika da alfarma.6. “ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Domin ka ɗauka kai mai hikima ne, mai hikima kamar allah,7. zan kawo baƙi a kanka, waɗanda suka fi mugunta cikin sauran al’ummai; za su zāre takubansu a kan kyakkyawar hikimarka su kuma ɓarke darajarka mai walƙiya.8. Za su jefar da kai cikin rami, za ka kuwa yi muguwar mutuwa a tsakiyar tekuna.9. Za ka iya ce yanzu, “Ni allah ne,” a gaban waɗanda suka kashe ka? Za ka zama mutum kurum, ba allah ba, a hannuwan waɗanda suka kashe ka.10. Za ka yi mutuwar marar kaciya a hannuwan baƙi. Na faɗa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”11. Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,12. “Ɗan mutum, ka yi makoki domin sarkin Taya ka kuma ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Ka kasance hatimin cikakke, cike da hikima da cikakke a kyau.13. Ka kasance a Eden, a lambun Allah; aka yi maka ado da kowane dutse mai daraja, yakutu, tofaz, da zumurrudu, kirisolit, onis da yasfa, saffaya, turkuwoyis da beril. Tsare-tsare da shirye-shiryenka an yi su da zinariya ne; a ranar da aka halicce ka an shirya su.14. An shafe ka kamar kerub mai tsaro, gama haka na naɗa ka. Kana a tsattsarkan dutsen Allah; ka yi tafiya a tsakiyar duwatsun wuta.15. Ka kasance marar laifi cikin dukan hanyoyinka daga ranar da aka halicce ka sai da aka sami mugunta a cikinka.16. Ta wurin yawan kasuwancinka ka cika da rikici, ka kuma yi zunubi. Saboda haka na kore ka da kunya daga dutsen Allah, na kore ka, ya kerub mai tsaro, daga cikin duwatsun wuta.17. Zuciyarka ta cika da alfarma saboda kyanka, ka kuma lalace hikimarka saboda darajarka. Saboda haka na jefar da kai zuwa ƙasa; na sa ka zama abin kallo a gaban sarakuna.18. Ta wurin yawan zunubanka da kasuwancinka na cuta ka ƙazantar da wuri mai tsarkinka. Saboda haka na sa wuta ta fito daga cikinka, ta cinye ka, na maishe ka toka a bisa ƙasa a kan idon dukan waɗanda suke kallonka.19. Dukan al’umman da suka san ka sun giggice saboda masifar da ta auko maka; ka zo ga mummunar ƙarshe ba za ka ƙara kasancewa ba har abada.’ ”20. Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,21. “Ɗan mutum, ka fuskanci Sidon; ka yi annabci a kanta22. ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Ina gāba da ke, ya Sidon, zan sami ɗaukaka a cikinki. Za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na zartar da hukunci a kanta na kuma nuna kaina mai tsarki a cikinta.23. Zan aika da annoba a kanta in kuma sa jini ya zuba a titunanta. Kisassu za su fāɗi a cikinta, da takobi yana gāba da ita a kowane gefe. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.24. “ ‘Mutanen Isra’ila ba za su ƙara kasance da mugayen maƙwabta waɗanda za su zama sarƙaƙƙiya masu zafi da ƙaya mai tsini ba. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.25. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa sa’ad da na tattara mutanen Isra’ila daga al’ummai inda suke a warwatse, zan nuna kaina mai tsarki a cikinsu a idon al’ummai. Sa’an nan za su zauna a ƙasarsu, wadda na ba wa bawana Yaƙub.26. Za su zauna a can lafiya su kuma gina gidaje su nome gonakin inabi; za su zauna lafiya sa’ad da zan zartar da hukunci a kan dukan maƙwabtansu da suka wulaƙanta su. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji Allahnsu.’ ”Zabura 129:1-41. Sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami, bari Isra’ila yă ce,2. sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami, amma ba su yi nasara a kaina ba.3. Manoma sun nome bayana suka yi kunyoyinsu da tsayi.4. Amma Ubangiji mai adalci ne; ya ’yantar da ni daga igiyoyin mugaye.Karin Magana 28:26-2626. Duk mai dogara ga kansa wawa ne, amma duk wanda yake tafiya da hikima zai zauna lafiya.Ibraniyawa 12:1-291. Saboda haka, da yake muna kewaye da irin wannan taron shaidu mai girma, sai mu yar da duk abin da yake hana mu da kuma zunubin da yake saurin daure mu, mu kuma yi tseren da aka sa a gabanmu da nacewa.2. Bari mu kafa idanunmu a kan Yesu, tushe da kuma kammalar bangaskiyarmu, wanda ya jure kunyar gicciye da aka yi masa, domin ya san cewa daga baya zai yi farin ciki ya yi haka. Yanzu kuma yana zaune a hannun dama na kursiyin Allah.3. Ku lura da wannan wanda ya jure da irin hamayyan nan daga masu zunubi, don kada ku gaji, har ku fid da zuciya.4. Cikin famanku da zunubi, ba ku yi tsayayya har ga zub da jininku ba tukuna.5. Kun kuma manta da kalmar ƙarfafawan nan da tana ce da ku ’ya’ya, “Ɗana kada ka rena horon Ubangiji, kada kuma ka fid da zuciya sa’ad da ya kwaɓe ka,6. domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna, yakan kuma hori duk wanda yakan karɓa a matsayin ɗa.”7. Ku jimre shan wahala a matsayin horo; Allah yana yi da ku kamar ’ya’ya. Gama wane ɗa ne mahaifinsa ba ya horonsa?8. In ba a hore ku ba (kowa kuwa yakan sami horo), to, ku shegu ne ba ’ya’yan gida ba.9. Ban da haka ma, dukanmu mun kasance da ubannin jiki waɗanda suka hore mu muka kuma yi musu ladabi. Ashe, bai kamata mu yi wa Uban ruhohinmu biyayya mu kuwa rayu ba!10. Ubanninmu sun hore mu na ɗan lokaci yadda suka ga ya fi kyau; amma Allah yakan hore mu don amfaninmu, domin mu sami rabo cikin tsarkinsa.11. Babu horon da yake da daɗi a lokacin da ake yinsa, sai dai zafi. Amma daga baya waɗanda suka horu ta haka sukan sami kwanciyar rai wadda aikin adalci yake bayarwa.12. Saboda haka, sai ku ƙarfafa raunanan hannuwanku da gwiwoyinku marasa ƙarfi!13. “Ku shirya hanyoyi marasa gargaɗa saboda ƙafafunku,” don kada guragu su daɗa gurguntawa, sai dai su warke.14. Ku yi iyakacin ƙoƙari ku yi zaman lafiya da kowa, ku kuma zama masu tsarki; gama in ban da tsarki ba babu wanda zai ga Ubangiji.15. Ku lura fa kada wani yă kāsa samun alherin Allah, kada kuma wani tushen ɗacin rai yă tsira har yă kawo rikici, yă kuma ƙazantar da mutane da yawa.16. Ku lura kada wani yă zama mai fasikanci, ko marar tsoron Allah kamar Isuwa, wanda saboda ƙwaryar abinci ɗaya tak ya sayar da gādonsa na ɗan fari.17. Daga baya, kamar yadda kuka sani, sa’ad da ya nemi yă gāji wannan albarka, aka ƙi shi. Bai sami zarafin tuba ba, ko da yake ya nemi albarkan nan da hawaye.18. Ba ku zo ga Dutsen Sinai wanda ana iya taɓawa ba, ko ga wuta mai ci sosai, ko ga duhu baƙi ƙirin, ko19. ko busar ƙaho, ko ga irin wata murya mai magana da kalmomin da masu jinta suka yi roƙo kada su ƙara ji,20. domin ba su iya jimrewa da abin da aka umarta cewa, “Ko da ma dabba ce ta taɓa dutsen, dole a jajjefe ta da duwatsu.”21. Ganin wannan abu da matuƙar bantsoro yake, har Musa ya ce, “Ina rawar jiki don tsoro.”22. Sai dai kun zo ne ga Dutsen Sihiyona, ga Urushalima ta sama, birnin Allah mai rai. Kun zo ga dubu dubban mala’ikun da suke cikin taron farin ciki,23. kun zo ga ikkilisiyar ɗan fari, waɗanda sunayensu suna a rubuce a sama. Kun zo ga Allah, alƙalin dukan mutane, kun kuma zo ga ruhohin mutane masu adalci da aka mai da su cikakku.24. Kun zo ga Yesu, mai yin sulhu na sabon alkawari, da kuma ga jinin da aka yayyafa wanda yake magana mafi kyau fiye da jinin Habila.25. Ku lura fa kada ku ƙi wanda yake magana. Gama in su ba su tsira sa’ad da suka ƙi wanda ya gargaɗe su a wannan duniya ba, to, ƙaƙa mu za mu tsira, in mun ƙi jin wannan da yake yi mana gargaɗi daga Sama?26. A lokacin nan muryarsa ta jijjiga duniya, amma yanzu ya yi alkawari cewa, “Har wa yau sau ɗaya tak zan ƙara jijjiga ba duniya kaɗai ba, amma har ma da sammai.”27. Wannan magana “sau ɗayan nan” sun nuna, kawar da abin da za a iya jijjigawa, wato, ƙirƙiro abubuwa, saboda abubuwan da ba a iya jijjigawa, su kasance.28. Saboda haka, da yake muna karɓar mulkin da ba ya jijjiguwa, sai mu yi godiya, ta haka kuwa mu yi wa Allah sujada yadda ya kamata, tare da bangirma da kuma tsoro,29. gama “Allahnmu wuta ne mai cinyewa.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.