Baibul a cikin shekara guda Nuwamba 19Ezekiyel 29:1-211. A shekara ta goma, a wata na goma, a rana ta goma sha biyu, maganar Ubangiji ta zo mini cewa,2. “Ɗan mutum, ka fuskanci Fir’auna sarkin Masar ka kuma yi annabci gāba da shi da dukan Masar.3. Yi masa magana ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Ina gāba da kai, Fir’auna sarkin Masar, kai babban mugun dodon ruwa kwance cikin rafuffukanka. Ka ce, “Nilu nawa ne; na yi shi wa kaina.”4. Amma zan sa ƙugiyoyi a muƙamuƙanka in sa kifin rafuffukanka su manne wa kamɓorinka. Zan jawo ka daga cikin tsakiyar rafuffukanka, da dukan kifayen rafuffukanka, waɗanda suka manne a ƙamborinka,5. Zan bar ka a cikin hamada, kai da dukan kifin rafuffukanka. Za ka fāɗi a fili ba kuwa za a tattara ka ko a kwashe ba. Zan ba da kai kamar abinci ga namun jeji na duniya da tsuntsayen sararin sama.6. Ta haka dukan waɗanda suke zama a Masar za su san cewa ni ne Ubangiji. “ ‘Ka zama sandan iwa domin gidan Isra’ila.7. Sa’ad da suka kama ka da hannuwansu, ka tsattsage, ka kuma buɗu a kafaɗunsu; sa’ad da suka jingina a kanka, sai ka karye, bayansu kuwa ya firgita.8. “ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan kawo takobi a kanka in kashe mutane da dabbobi.9. Masar za tă zama kufai. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji. “ ‘Domin ka ce, “Nilu nawa ne; ni na yi shi,”10. saboda haka ina gāba da kai da rafuffukanka, zan kuma maishe ƙasar Masar ta lalace ta kuma zama kango daga Migdol zuwa Aswan, har iyakar Kush.11. Ba ƙafar mutum ko ta dabbar da za tă ratsa ta; ba wanda zai zauna a can har shekaru arba’in.12. Zan mai da ƙasar Masar kufai a cikin ƙasashen da aka ragargaza, biranenta kuma za su zama kango har shekaru arba’in a cikin biranen da aka lalace. Zan watsar da Masarawa a cikin al’ummai in warwatsa su cikin ƙasashe.13. “ ‘Duk da haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ƙarshen shekaru arba’in ɗin zan tattara Masarawa daga al’ummai inda aka warwatsa su.14. Zan komo da su daga zaman bauta in mai da su zuwa Masar ta Bisa, ƙasarsu ta ainihi. A can za su zama masarauta marar ƙarfi.15. Za tă zama masarauta mafi rarrauna cikin masarautai, ba kuwa za tă ƙara ɗaga kanta a kan sauran al’ummai ba. Zan sa tă zama marar ƙarfi ƙwarai, har da ba za tă ƙara yin mulkin a kan al’ummai ba.16. Masar ba za tă ƙara zama abin dogara ga mutanen Isra’ila ba amma za tă zama abin tunin zunubinsu na juyawa gare ta don taimako. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”17. A shekara ta ashirin da bakwai, a wata na fari a rana ta farko, maganar Ubangiji ta zo mini cewa,18. “Ɗan mutum, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya sa sojojinsa su matsa wa Taya; kowane kai ya koɗe, kowace kafaɗa kuma ta goge. Duk da haka shi da sojojinsa ba su sami wani lada daga matsin da suka yi a kan Taya ba.19. Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan ba da Masar ga Nebukadnezzar sarkin Babilon, zai washe dukiyarta. Zai kwashe ya washe ƙasar ganima a matsayin abin biyan sojojinsa.20. Saboda haka na ba shi Masar a matsayin lada don ƙoƙarinsa domin shi da sojojinsa sun yi wannan domina ne, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.21. “A wannan rana zan sa ƙaho ya tsiro wa gidan Isra’ila, zan kuma buɗe bakinka a cikinsu. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.”Ezekiyel 30:1-261. Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,2. “Ɗan mutum, ka yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Yi kuka kana cewa, “Kaito saboda wannan rana!”3. Gama ranar ta yi kusa, ranar Ubangiji ta gabato, ranar gizagizai, lokacin hallaka wa al’ummai.4. Takobi zai zo a kan Masar, azaba za tă zo a kan Kush. Sa’ad da kisassu za su fāɗi a Masar, za a kwashe dukiyarta a tafi a rushe harsashinta.5. Kush da Fut, Lidiya da dukan Arabiya, Libiya da kuma mutanen ƙasar alkawari za su mutu ta wurin takobi tare da Masar.6. “ ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa, “ ‘Waɗanda suke goyon bayan Masar za su fāɗi ƙarfinta da take fariya da shi zai ƙare. Daga Migdol zuwa Aswan za su mutu ta wurin takobi a cikinta, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.7. Za su zama kango a cikin ƙasashen da suke kango, biranensu kuwa za su zama kufai a cikin biranen da suka lalace.8. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da suka ga na sa wuta wa Masar aka kuma ragargaza masu taimakonta.9. “ ‘A wannan rana manzanni za su fito daga wurina a jiragen ruwa don su tsorata Kush daga sake jikinta. Azaba za tă kama su a ranar hallakar Masar, gama tabbatacce za tă zo.10. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Zan kawo ƙarshen mutanen Masar ta hannun Nebukadnezzar sarkin Babilon.11. Shi da sojojinsa, mafi bantsoro cikin al’ummai, za a kawo don su hallaka ƙasar. Za su zāre takuba a kan Masar su kuma cika ƙasar da kisassu.12. Zan kafe rafuffukan Nilu in sayar da ƙasar ga mugayen mutane; ta hannun baƙi zan sa ƙasar ta lalace da kome da yake cikinta. Ni Ubangiji na faɗa.13. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Zan hallaka gumaka in kuma kawo ƙarshen siffofi a Memfis. Ba za a ƙara samun yerima a ƙasar Masar ba, zan kuma baza tsoro a duk fāɗin ƙasar.14. Zan lalace Masar ta Bisa in ƙuna wuta wa Zowan in zartar da hukunci a kan Tebes.15. Zan kwarara hasalata a kan Felusiyum, kagarar Masar, in kuma datse mutanen Tebes.16. Zan ƙuna wuta wa Masar; Felusiyum za tă sha azaba mai zafi. Za a tayar wa Tebes da hankali; Memfis za tă riƙa kasance cikin ɓacin rai.17. Samarin Heliyofolis da Bubastis za su mutu ta wurin takobi, biranen kansu za su tafi bauta.18. Duhu ne zai zama rana a Tafanes sa’ad da na karye ikon Masar; a can ƙarfin da take fariya zai ƙare. Za a rufe ta da gizagizai ƙauyukanta kuma za su tafi bauta.19. Ta haka zan zartar da hukunci a kan Masar, za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji.’ ”20. A shekara ta goma sha ɗaya, a wata na fari a rana ta goma sha bakwai, maganar Ubangiji ta zo mini cewa,21. “Ɗan mutum, na karye hannun Fir’auna sarkin Masar. Ba a daure shi don warkarwa ba ko a sa tsinke saboda kada yă zama da ƙarfi har ya riƙe takobi.22. Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da Fir’auna sarkin Masar. Zan karye hannuwansa biyu, hannun da yake da kyau da kuma wanda an riga an karya, in kuma sa takobi ya fāɗi daga hannunsa.23. Zan watsar da Masarawa a cikin al’ummai in warwatsa su cikin ƙasashe.24. Zan ƙarfafa hannuwan sarkin Babilon in kuma sa takobina a hannunsa, amma zan karya hannuwan Fir’auna, zai kuwa yi nishi a gabansa kamar mutumin da aka yi wa raunin mutuwa.25. Zan ƙarfafa hannuwan sarkin Babilon, amma hannuwan Fir’auna za su shanye. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na sa takobi a hannun sarkin Babilon na kuma miƙa shi a kan Masar.26. Zan watsar da Masarawa a cikin al’ummai in warwatsa su cikin ƙasashe. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.”Zabura 129:5-85. Bari dukan waɗanda suke ƙin Sihiyona a juye da su baya da kunya.6. Bari su zama kamar ciyawa a kan rufi, wadda takan bushe kafin tă yi girma;7. da ita mai girbi ba ya iya cika hannuwansa, balle wanda yake tarawa yă cika hannuwansa.8. Kada masu wuce su ce, “Albarkar Ubangiji ta kasance a kanku; muna sa muku albarka a cikin sunan Ubangiji.”Karin Magana 28:27-2727. Duk wanda yake bayarwa ga matalauta ba zai rasa kome ba, amma duk wanda bai kula da su ba yana samu la’ana masu yawa.Ibraniyawa 13:1-251. Ku ci gaba da ƙaunar juna kamar ’yan’uwa.2. Kada ku manta da yin alheri ga baƙi, gama ta yin haka ne waɗansu suka yi wa mala’iku hidima, ba da saninsu ba.3. Ku riƙa tunawa da waɗanda suke a kurkuku kamar tare kuke a kurkuku, da kuma waɗanda ake gwada musu azaba, kamar ku ake yi wa.4. Aure yă zama abin girmamawa ga kowa, a kuma kiyaye gadon aure da tsabta, gama Allah zai hukunta masu zina da kuma dukan masu fasikanci.5. Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce, “Ba zan taɓa bar ka ba; ba zan taɓa yashe ka ba.”6. Saboda haka muna iya fitowa gabagadi, mu ce, “Ubangiji ne mai taimakona; ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai iya yi mini?”7. Ku tuna da shugabanninku, waɗanda suka faɗa muku maganar Allah. Ku dubi irin rayuwar da suka yi ku kuma yi koyi da bangaskiyarsu.8. Yesu Kiristi ba ya sākewa, shi ne a jiya, shi ne a yau, shi ne kuma har abada.9. Kada a ɗauke muku hankali da sababbin koyarwa dabam-dabam. Yana da kyau zukatanmu su ƙarfafa ta wurin alheri, ba ta wurin abinci waɗanda ba su da amfani ga waɗanda suke cinsu.10. Muna da bagade inda firistocin da suka yi hidima a tabanakul ba su da izini su ci.11. Babban firist yakan ɗauki jinin dabbobi yă shiga cikin Wuri Mafi Tsarki a matsayin hadaya ta zunubi, amma jikunan dabbobin akan ƙone su a bayan sansani.12. Haka ma Yesu ya sha wahala a bayan gari don yă tsarkake mutane ta wurin jininsa.13. Saboda haka, sai mu fita mu je wajensa a bayan sansani, muna ɗaukar kunyar da ya sha.14. Gama a nan ba mu da dawwammamen birni, sai dai muna zuba ido a kan birnin nan mai zuwa.15. Saboda haka, ta wurin Yesu, bari mu ci gaba da miƙa hadaya ta yabo ga Allah, yabon leɓuna da yake shaidar sunansa.16. Kada kuma ku manta yin aikin nagari da kuma taimakon waɗansu, gama da irin waɗannan hadayu ne Allah yake jin daɗi.17. Ku yi wa shugabanninku biyayya ku kuma miƙa kanku ga ikonsu. Suna lura da ku kuma za su ba da lissafi a gaban Allah. Saboda haka kada ku sa su yi fushi saboda aikinsu, ku sa su yi farin ciki. In ba haka ba za su iya taimakonku ba ko kaɗan.18. Ku yi mana addu’a. Mun tabbata cewa muna da lamiri mai kyau, kuma muna da marmari mu yi rayuwa ta bangirma a ta kowace hanya.19. Ni musamman, ina roƙonku ku yi addu’a, don a komo da ni a gare ku ba da daɗewa ba.20. Bari Allah na salama, wanda ta wurin jinin madawwamin alkawari ya tā da Ubangijinmu Yesu daga matattu, wannan Makiyayin tumaki mai girma,21. yă kintsa ku da kowane abu mai kyau domin aikata nufinsa, bari kuma yă aikata abin da zai gamshe shi cikinmu, ta wurin Yesu Kiristi, a gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada. Amin.22. ’Yan’uwa, ina roƙonku ku yi haƙuri da wannan gargaɗi, don ba wata doguwar wasiƙa ce na rubuta muku ba.23. Ina so ku san cewa an saki ɗan’uwanmu Timoti. In ya iso da wuri, zan zo tare da shi in gan ku.24. Ku gai da dukan shugabanninku da kuma dukan mutanen Allah. Waɗanda suke Italiya suna gaishe ku.25. Alheri yă kasance da ku duka. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.