Baibul a cikin shekara guda Nuwamba 21Ezekiyel 33:1-331. Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,2. “Ɗan mutum, yi magana da mutanen ƙasarka ka faɗa musu cewa, ‘Sa’ad da na kawo takobi a kan ƙasar, mutanen ƙasar kuwa suka zaɓi ɗaya daga cikin mutanensu suka mai da shi mai tsaro,3. ya kuma ga takobi yana zuwa a kan ƙasar ya kuwa busa ƙaho don yă faɗakar da mutane,4. in wani ya ji busar amma bai kula ba, takobin zai zo ya ɗauki ransa, jininsa kuwa zai zauna a kansa.5. Da yake ya ji ƙarar busar amma bai kula ba, jininsa zai zauna a kansa. Da a ce ya kula, da ya ceci kansa.6. Amma a ce mai tsaron ya ga takobi yana zuwa bai kuwa busa ƙaho don yă faɗakar da mutane ba sai takobi ya zo ya ɗauki ran waninsu, za a kawar da wannan mutum saboda zunubinsa, amma zan nemi hakkin jinin mutumin a kan mai tsaron.’7. “Ɗan mutum, na mai da kai mai tsaro bisa gidan Isra’ila; saboda haka ka ji abin da zan faɗa ka kuma gargaɗe su.8. Sa’ad da na ce wa mugu, ‘Ya mugun mutum, tabbatacce za ka mutu,’ kai kuma ba ka yi magana don ka juyar da shi daga hanyoyinsa ba, wannan mugun mutum zai mutu domin zunubinsa, zan kuma nemi hakkin jininsa a kanka.9. Amma in ka faɗakar da mugun mutumin don yă juye daga hanyoyinsa bai kuwa yi haka ba, zai mutu saboda zunubinsa, amma kai za ka kuɓutar da kanka.10. “Ɗan mutum, faɗa wa gidan Isra’ila, ‘Ga abin da kuke cewa, “Laifofinmu da zunubanmu suna nawaita mana, muna kuma lalacewa saboda su. Ta ƙaƙa za mu rayu?” ’11. Ka faɗa musu, ‘Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ba na jin daɗin mutuwar mugu, amma a maimako haka ya fi su juye daga hanyoyinsu su rayu. Ku juye! Ku juye daga mugayen hanyoyinku! Don me za ku mutu, ya gidan Isra’ila?’12. “Saboda haka, ɗan mutum, ka faɗa wa mutanen ƙasarka, ‘Adalcin adali ba zai cece shi sa’ad da ya ƙi yin biyayya ba, kuma muguntar mugu ba za tă sa ya fāɗi sa’ad da ya juya daga gare ta ba. Adali, in ya yi zunubi, ba za a bari yă rayu saboda adalcinsa na dā ba.’13. In na faɗa wa adali cewa tabbatacce zai rayu, amma sai ya dogara ga adalcinsa ya kuma aikata mugunta, babu ayyukan adalcinsa da za a tuna; zai mutu saboda muguntar da ya aikata.14. Kuma in na ce wa mugu, ‘Tabbatacce za ka mutu,’ amma sai ya juye daga zunubinsa ya kuma yi abin da yake gaskiya da kuma daidai,15. in ya mayar da jingina, ya mayar da abin da ya sata, ya kiyaye ƙa’idodin da suke ba da rai, ya daina yin mugunta, tabbatacce zai rayu; ba zai mutu ba.16. Babu wani zunubin da ya aikata da za a tuna da shi. Ya yi abin da yake gaskiya da kuma daidai; tabbatacce zai rayu.17. “Duk da haka mutanen ƙasarka sun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Alhali kuwa tasu ce ba daidai ba.18. In adali ya juye daga adalcinsa ya yi mugunta, zai mutu saboda haka.19. Kuma in mugu ya juye daga muguntarsa ya aikata abin da yake gaskiya da kuma daidai, zai rayu ta yin haka.20. Duk da haka, ya gidan Isra’ila kun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Amma zan hukunta kowane ɗayanku gwargwadon ayyukansa.”21. A shekara ta goma sha biyu ta zaman bautanmu, a wata na goma a rana ta biyar, wani mutumin da ya gudu daga Urushalima ya zo wurina ya ce, “Birnin ya fāɗi!”22. To a yamman da ya wuce kafin mutumin ya iso, hannun Ubangiji yana a kaina, ya kuma buɗe bakina kafin mutumin ya iso wurina da safe. Sai bakina ya buɗu ban kuma yi shiru ba.23. Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa,24. “Ɗan mutum, mutanen da suke zama a waɗannan kufai a ƙasar Isra’ila suna cewa, ‘Ibrahim mutum ɗaya ne kaɗai, duk da haka Ibrahim ya mallaki ƙasar. Amma mu da muke da yawa; lalle an ba mu ƙasar ta zama mallakarmu.’25. Saboda haka ka faɗa musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa da yake kun ci nama da jini a cikinsa kuka kuma bauta wa gumakanku kuka zub da jini, kuna gani za ku mallaki ƙasar?26. Kun dogara ga takobinku, kuka aikata abubuwan banƙyama, kowannenku kuma ya ƙazantar da matar maƙwabcinsa. Kuna gani za ku mallaki ƙasar?’27. “Ka faɗa musu wannan, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa muddin ina raye, waɗanda aka rage a kufai za su fāɗi ga takobi, waɗanda suke bayan gari kuwa namun jeji za su cinye su, waɗanda suke a mafaka da kogwannin duwatsu annoba za tă kashe su.28. Zan mai da ƙasar kango, kuma fariyar ƙarfinta zai ƙare, duwatsun Isra’ila za su zama kufai don kada wani ya ratsa su.29. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na mai da ƙasar kango saboda dukan abubuwan banƙyamar da suka yi.’30. “Game da kai kuma, ɗan mutum, mutanen ƙasarka suna magana da juna game da kai a katanga da kuma ƙofofin gidaje, suna ce wa juna, ‘Ku zo mu tafi mu ji maganar da ta zo daga wurin Ubangiji.’31. Mutanena sukan zo wurinka, yadda suka saba su zauna a gabanka don su saurari maganarka, amma ba sa aiki da abin da suka ji. Da bakunansu suna nuna ƙauna, amma zukatansu cike da haɗama suke don ƙazamar riba.32. Tabbatacce, gare su ba ka fi mai waƙar ƙauna da murya mai daɗi kana kuma yin kiɗa sosai ba, gama sukan ji maganarka amma ba sa amfani da ita.33. “Sa’ad da dukan wannan ya cika kuma zai cika ɗin, sa’an nan za su sani akwai annabi a tsakiyarsu.”Ezekiyel 34:1-311. Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,2. “Ɗan mutum, ka yi annabci a kan makiyayan Isra’ila; ka yi annabci ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa kaiton makiyayan Isra’ila waɗanda suke kula da kansu ne kawai! Ashe, bai kamata makiyaya ne su lura da tumaki ba?3. Kuna cin kitsensu, kuna yi wa kanku tufafi da gashinsu, kukan yanka turkakkun, amma ba ku yi kiwon tumakin ba.4. Ba ku ƙarfafa marasa ƙarfi ba, ko ku warkar da marasa lafiya ko ku ɗaura waɗanda suka ji rauni. Ba ku dawo da waɗanda suka yi makuwa ko ku nemi waɗanda suka ɓace ba. Amma sai kuka mallake su ƙarfi da yaji.5. Saboda haka suka warwatse domin babu makiyayi, kuma da suka warwatsu sai suka zama abincin namun jeji.6. Tumakina suna ta yawo a kan dukan duwatsu da kuma kowane tudu. Sun watsu a dukan duniya, kuma ba wanda ya neme su.7. “ ‘Saboda haka, ku makiyaya, ku ji maganar Ubangiji,8. Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, domin tumaki sun rasa makiyayi ta haka aka washe su suka kuma zama abincin dukan namun jeji, kuma domin makiyayana ba su nemi tumakina ba amma suka kula da kansu a maimakon tumakina,9. saboda haka, ya ku makiyaya, ku ji maganar Ubangiji,10. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da makiyaya kuma zan nemi hakkin tumakina daga gare su. Zan hana su yin kiwon tumakin don kada makiyayan su ƙara yin kiwon kansu. Zan ƙwace tumakina daga bakunansu, ba kuwa za su ƙara zama abincinsu.11. “ ‘Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ni kaina zan nemi tumakina.12. Kamar yadda makiyayi yakan lura da tumakinsa da suka watse sa’ad da yake tare da su, haka zan lura da tumakina. Zan cece su daga dukan wuraren da aka watsar da su a ranar gizagizai da baƙin duhu.13. Zan dawo da su daga al’ummai in kuma tattara su daga ƙasashe, zan kuma kawo su cikin ƙasarsu. Zan yi kiwonsu a kan duwatsun Isra’ila, a maɓulɓulai da kuma cikin wuraren zamansu a ƙasar.14. Zan kula da su a wurin kiwo mai kyau, kuma ƙwanƙolin duwatsun Isra’ila ne zai zama wurin kiwonsu. Za su kwanta a wurin kiwo mai kyau, a can kuma za su yi kiwo a wurin kiwo mai kyau a kan duwatsun Isra’ila.15. Ni kaina zan lura da tumakina in kuma sa su kwanta, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.16. Zan nemi ɓatattuna in kuma dawo da waɗanda suka yi makuwa. Zan ɗaura raunin waɗanda suka ji ciwo in kuma ƙarfafa marasa ƙarfi, amma zan hallaka ƙarfafa da kuma masu ƙiba. Zan yi kiwo tumaki da adalci.17. “ ‘Game da ku, tumakina, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan hukunta tsakanin tunkiya da tunkiya, da tsakanin raguna da awaki.18. Bai isa ba a ce kun yi kiwo a wuri mai kyau? Sai kun tattake sauran wurin kiwonku da ƙafafunku tukuna? Bai isa ba a ce kun sha ruwa mai tsabta? Sai kun kuma gurɓata sauran da ƙafafunku?19. Dole ne tumakina su ci abin da kuka tattake su kuma sha abin da kuka gurɓata da ƙafafunku?20. “ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce musu, duba, ni kaina zan hukunta tsakanin turkakkun tumaki da ramammun tumaki.21. Domin kun tunkuɗe marasa ƙarfi da kafaɗunku, kun kuma tunkuye su da ƙahoninku sai da suka gudu,22. zan cece tumakina ba za su ƙara zama ganima ba. Zan hukunta tsakanin tunkiya da tunkiya.23. Zan sa musu makiyaya guda, bawana Dawuda, zai kuwa lura da su; zai kula da su ya kuma zama makiyayinsu.24. Ni Ubangiji zan zama Allahnsu, bawana kuma Dawuda zai zama yerima a cikinsu. Ni Ubangiji na faɗa.25. “ ‘Zan yi alkawarin salama da su in kuma kawar wa ƙasar da namun jeji domin su zauna a hamada su kuma kwana a kurmi lafiya lau.26. Zan albarkace su in kuma sa tuduna kewaye da su. Zan zubo yayyafi a lokacinsa; za a kasance da yayyafin albarka.27. Itatuwan gona za su ba da ’ya’yansu, ƙasa kuma za tă ba da amfaninta; mutane za su zauna lafiya a ƙasarsu. Za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na karya karkiyarsu, na cece su daga hannun waɗanda suka bautar da su.28. Ba za su ƙara zama ganimar al’ummai ba, ba kuwa namun jeji za su cinye su ba. Za su zauna lafiya, kuma babu wani da zai sa su ji tsoro.29. Zan tanada musu ƙasar da aka sani don hatsinta, ba za su kuma ƙara zama abin da yunwa za tă fara musu a ƙasa ba ko su sha zargin sauran al’ummai.30. Sa’an nan za su san cewa ni, Ubangiji Allahnsu, ina tare da su kuma cewa su, gidan Isra’ila, mutanena ne, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.31. Ku tumakina, tumakin wurin kiwona, mutanena ne, ni kuwa Allahnku ne, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”Zabura 130:5-85. Zan jira Ubangiji, raina zai jira, kuma a cikin maganarsa na sa zuciyata.6. Raina na jiran Ubangiji fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya, fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya.7. Ya Isra’ila, sa zuciya ga Ubangiji, gama tare da Ubangiji akwai ƙauna marar ƙarewa kuma tare da shi akwai cikakkiyar fansa.8. Shi kansa zai fanshi Isra’ila daga dukan zunubansu.Karin Magana 29:1-11. Mutumin da ya ci gaba da taurinkai bayan an kwaɓe shi ba da daɗewa ba zai hallaka ba makawa.Yaƙub 2:1-261. ’Yan’uwana, a matsayinmu cikin Ubangiji Yesu Kiristi maɗaukaki, kada ku nuna bambanci.2. A ce wani ya shigo cikin taronku saye da zoben zinariya da riguna masu tsada, wani matalauci kuma saye da tsummoki shi ma ya shigo,3. in kuka mai da hankali na musamman ga mutumin da yake da riguna masu tsadan nan kuka kuma ce, “Ga wurin zama mai kyau dominka,” amma kuka ce wa matalaucin nan, “Kai tsaya daga can,” ko kuwa, “Ka zauna a ƙasa kusa da ƙafafuna,”4. ashe, ba ku nuna bambanci a tsakaninku ke nan ba, kuka kuma zama alƙalai masu mugayen tunani?5. Ku saurara, ’yan’uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi waɗanda suke matalauta a idon duniya don su zama masu wadata cikin bangaskiya, su kuma gāji mulkin da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba?6. Ga shi kun wulaƙanta matalauta. Ashe, ba masu arziki ne suke cutarku ba? Ba su ba ne suke jan ku zuwa kotu?7. Ba su ba ne suke ɓata sunan nan mai martaba wanda aka san ku da shi ba?8. In fa kun kiyaye dokan nan ta mulki wadda take cikin Nassi mai cewa, “Ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” kun yi daidai.9. Amma in kuka nuna bambanci, kun yi zunubi ke nan shari’a kuma ta same ku da laifi a matsayin masu karya doka.10. Gama duk wanda ya kiyaye dukan doka amma ya yi tuntuɓe a kan abu ɗaya kaɗai, ya zama mai laifin karya dukansu ke nan.11. Gama shi da ya ce, “Kada ka yi zina,” shi ne kuma ya ce, “Kada ka yi kisankai.” In kuwa ba ka zina amma kana kisankai, ka zama mai karya doka ke nan.12. Ku yi magana ku kuma yi aiki kamar waɗanda za a yi musu shari’a bisa ga doka mai ba da ’yanci,13. gama za a yi wa duk wanda bai nuna jinƙai ba hukunci babu jinƙai. Jinƙai yakan yi nasara a kan hukunci!14. Wanda amfani ne, ’yan’uwana, a ce wani yă ce yana da bangaskiya, amma ba shi da ayyuka? Anya, wannan bangaskiya za tă iya cetonsa kuwa?15. A ce wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa ba shi da riguna ko abincin yini,16. sai waninku yă ce masa, “Sauka lafiya, Allah ya ba da ci da sha da kuma sutura,” amma bai yi wani abu game da bukatunsa na jiki ba, ina amfani?17. Haka ma bangaskiya ita kaɗai, in ba tare da ayyuka ba, matacciya ce.18. Amma wani zai ce, “Kai kana da bangaskiya; ni kuma ina da ayyuka.” Ka nuna mini bangaskiyarka ba tare da ayyuka ba, ni kuma zan nuna maka bangaskiyata ta wurin abin da nake yi.19. Ka gaskata cewa Allah ɗaya ne. To, da kyau! Ai, ko aljanu ma sun gaskata wannan, har da rawan jiki.20. Kai wawa, kana son tabbaci cewa bangaskiya marar ayyuka banza ce?21. Ashe, ba a mai da kakanmu Ibrahim mai adalci saboda abin da ya yi ba ne sa’ad da ya miƙa ɗansa Ishaku a bisa bagade?22. Ai, ka gani cewa bangaskiyarsa da ayyukansa sun yi aiki tare, bangaskiyarsa kuma ta zama cikakkiya ta wurin abin da ya yi.23. Aka kuma cika nassin nan da ya ce, “Ibrahim ya gaskata Allah, aka kuma lissafta wannan adalci ne gare shi,” aka kuma ce da shi abokin Allah.24. Kun ga cewa ashe mutum zai sami kuɓuta ta wurin abin da ya yi ne ba ta wurin bangaskiya kaɗai ba.25. Ta haka kuma ashe, Rahab karuwan nan ba a ɗauke ta mai adalci ce saboda abin da ta yi ba ne sa’ad da ta ba wa ’yan leƙen asirin nan masauƙi ta kuma sallame su suka tafi ta wata hanya dabam?26. Kamar yadda jikin da babu ruhu matacce ne, haka ma bangaskiyar da babu ayyuka matacciya ce. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.