Baibul a cikin shekara guda Nuwamba 24Ezekiyel 39:1-291. “Ɗan mutum, ka yi annabci a kan Gog ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kai, ya Gog, babban sarkin Meshek da Tubal.2. Zan juya ka in kuma ja ka. Zan kawo ka daga can arewa in aike ka don ka fāɗa wa duwatsun Isra’ila.3. Sa’an nan zan karya bakan da take a hannun hagunka, in sa kibiyoyin da suke a hannun damanka su fāɗi.4. A kan duwatsun Isra’ila za ka fāɗi, kai da sojojinka da kuma al’ummai da suke tare da kai. Zan bayar da kai ka zama abinci ga tsuntsaye da namun jeji masu cin nama.5. Za ka mutu a fili, gama haka ni na faɗa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.6. Zan aika da wuta a kan Magog da kuma a kan waɗanda suke zama lafiya a bakin teku, za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji.7. “ ‘Zan sanar da sunana mai tsarki a cikin mutanena Isra’ila. Ba zan ƙara bari a ɓata sunana mai tsarki ba, kuma al’ummai za su san cewa Ni Ubangiji Mai Tsarki ne a cikin Isra’ila.8. Yana zuwa! Tabbatacce zai faru, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ranar da na yi magana ke nan.9. “ ‘Sa’an nan waɗanda suke zama a garuruwan Isra’ila za su fita su tattara makamai su hura wuta da su su kuma ƙone su, manya da ƙanana garkuwoyi, bakkuna da kibiyoyi, kulake da māsu. Shekara bakwai za su yi amfani da su don hura wuta.10. Ba za su yi wahalar zuwa jeji don neman itacen hura wuta ba, domin za su yi amfani da makamai don hura wuta. Za su kuma washe waɗanda suka washe su ganima, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.11. “ ‘A ranar zan yi wa Gog makabarta a cikin Isra’ila, a kwarin waɗanda suke tafiya wajen gabashin Teku. Za tă tare hanyar matafiya, domin za a binne Gog da dukan mutanensa a can. Ta haka za a kira wurin Kwarin Haman Gog.12. “ ‘Watanni bakwai gidan Isra’ila zai yi ta binne su don a tsarkake ƙasar.13. Dukan mutanen ƙasar za su binne su, kuma ranar da za a ɗaukaka ni za tă zama ranar tuni a gare su, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.14. “ ‘Za a ɗauki mutane kullum don tsabtacce ƙasar. Waɗansu za su ratsa ƙasar, ƙari da waɗannan, waɗansu za su binne gawawwakin da suka ragu a ƙasar. A ƙarshen watanni bakwai ɗin za su fara bincikensu.15. Yayinda suke ratsa ƙasar, in waninsu ya ga ƙashin mutum, zai kafa shi kamar alama a gefe sai masu haƙa kabari sun binne shi a Kwarin Haman Gog.16. Akwai wani garin da ake kira Hamona zai kasance a can. Ta haka za su tsabtacce ƙasar.’17. “Ɗan mutum, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ka gayyato kowane irin tsuntsu da dukan namun jeji, ‘Ku taru ku kuma zo wuri ɗaya daga ko’ina don hadayar da nake shirya muku, babbar hadaya a kan duwatsun Isra’ila. A can za ku ci nama ku kuma sha jini.18. Za ku ci naman manyan mutane ku kuma sha jinin sarakunan duniya sai ka ce an yanka raguna da ’yan tumaki, awaki da bijimai, dukansu turkakkun dabbobi daga Bashan.19. A hadayar da nake shirya muku, za ku ci kitse sai kun ƙoshi ku kuma sha jini sai kun bugu.20. A teburina za ku ci iya ƙoshiyarku da naman jama’a da kuma mahaya, manyan mutane da sojoji na kowane iri,’ in ji Ubangiji Mai Iko Duka.21. “Zan nuna ɗaukakata a cikin al’ummai, kuma dukan al’ummai za su ga hukuncin da zan yi da kuma hannu mai nauyin da zan ɗora a kansu.22. Daga wannan rana zuwa gaba gidan Isra’ila zai san cewa ni ne Ubangiji Allahnsu.23. Al’ummai kuma za su san cewa mutanen Isra’ila sun tafi zaman bauta saboda zunubinsu, domin sun yi rashin aminci gare ni. Saboda haka na kawar da fuskata daga gare su na miƙa su ga abokan gābansu, suka kuwa mutu ta takobi.24. Na yi da su gwargwadon rashin tsabtarsu da laifofinsu, na kuma kawar da fuskata daga gare su.25. “Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan komo da Yaƙub daga zaman bauta zan kuma yi wa dukan Isra’ila jinƙai, zan kuma yi kishi saboda sunana mai tsarki.26. Za su manta da kunyar da suka sha da dukan rashin amincin da suka nuna mini sa’ad da suke zama lafiya a ƙasarsu inda ba wanda zai tsorata su.27. Sa’ad da na komo da su daga al’ummai na kuma tattara su daga ƙasashen abokan gābansu, zan nuna kaina mai tsarki ta wurinsu a gaban al’ummai masu yawa.28. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji Allahnsu, gama ko da yake na tura su zaman bauta a cikin al’ummai, zan tattara su zuwa ƙasarsu, ba tare da barin wani a baya ba.29. Ba zan ƙara kawar da fuskata daga gare su, gama zan zuba Ruhuna a kan gidan Isra’ila, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”Ezekiyel 40:1-491. A shekara ta ashirin da biyar ta zaman bauta, a farkon shekara, a rana ta goma ga wata, a shekara ta goma sha huɗu bayan fāɗuwar birnin Urushalima, a wannan rana ikon Ubangiji ya sauko a kaina ya kuma iza ni.2. Cikin wahayin, Allah ya kai ni ƙasar Isra’ila ya sa ni a kan wani dutse mai tsayi ƙwarai, inda a gefen kudunsa akwai gine-ginen da suka yi kamar birni.3. A cikin wahayin ya kai ni can, na kuma ga mutum wanda kamanninsa ya yi kamar tagulla; yana tsaye a hanyar shiga yana riƙe da igiyar lilin da kuma karan awo a hannunsa.4. Mutumin ya ce mini, “Ɗan mutum, duba da idanunka, ka ji da kunnuwanka ka kuma lura da kowane abin da zan nuna maka, gama abin da ya sa na kawo ka nan ke nan. Ka faɗa wa gidan Isra’ila duk abin da ka gani.”5. Na ga katanga da ya kewaye filin haikali gaba ɗaya. Tsawon karan awon da yake a hannun mutumin kamu shida ne, sai ya auna kaurin katangar ya sami kamu shida, tsayinta kuma kamu shida.6. Sa’an nan ya tafi ƙofar da take fuskantar gabas. Ya hau matakanta ya auna madogarar ƙofa; zurfinta kamu shida ne.7. Tsawon kowane ɗakin matsara kamu shida ne, fāɗinsa kuma kamu shida, kaurin bangayen da suka raba ɗaki da ɗaki kamu biyar ne. Zurfin madogarar ƙofar da yake dab da shirayin da yake fuskantar haikalin kamu shida ne.8. Sa’an nan ya auna shirayin hanyar shiga;9. zurfinsa kamu takwas ne, kaurin kowane madogarar ƙofarsa kuwa kamu biyu ne. Shirayi hanyar shiga yana fuskantar haikalin.10. A cikin ƙofar gabas akwai ɗakuna uku a kowane gefe na hanyar shiga; dukan ukun girmansu ɗaya, bangayen da suke tsakani a kowane gefe girmansu ɗaya ne.11. Sa’an nan ya auna bakin hanyar shiga ya sami fāɗinsa kamu goma, tsawonsa kuma kamu goma sha uku.12. A gaban kowane ɗakin akwai bango mai tsayi kamu ɗaya, ɗakunan kuma kamu shida-shida ne a kowane gefe.13. Sa’an nan ya auna hanyar shiga daga saman bangon ɗaki a baya zuwa saman ɗakin da yake ɗaura da shi; nisansu kamu ashirin da biyar ne daga bango zuwa bango.14. Ya auna ɗakin bakin ƙofa na can ƙarshen hanyar shiga ya sami kamu sittin. Awon ya kai har zuwa shirayin da yake fuskantar filin.15. Nisan da take daga mashigin hanyar shiga zuwa can ƙarshen shirayin, kamu hamsin ne.16. Akwai ƙananan tagogi a ɗakunan da kuma a bangayen hanyar shiga, yadda suke a shirayin; tagogi a kewaye duka suna fuskantar ciki. An yi wa bangayen da suke waje ƙofar shiga ado da zāne-zāne siffofin itatuwan dabino.17. Sai mutumin ya bi da ni ta hanyar shiga zuwa filin waje, inda na ga ɗakuna talatin da aka gina kewaye a filin waje na filin. An gina waɗannan ɗakunan gefe a jikin bangon waje, a gabansu kuwa akwai daɓe kewaye da filin.18. Daɓen ya bi ta daidai gefen hanyoyin shiga, kuma faɗinsa ya yi daidai da tsawon ƙofofin shiga; wannan shi ne daɓen da yake ƙasa-ƙasa.19. Sa’an nan ya auna nisan da take daga hanyar shiga da take ƙasa-ƙasa daga ciki zuwa waje na filin ciki; ya kai kamu ɗari a gefen gabas haka ma yake a gefen arewa.20. Sa’an nan mutumin ya auna tsawo da fāɗin ƙofar da take fuskantar arewa, wadda take bi zuwa filin waje.21. Ƙofar shigar ma tana da ɗakuna uku-uku a kowane gefe. Girman bangayen da suka miƙe, da kuma shirayinta daidai suke da na ƙofa ta fari. Tsawonta kamu hamsin, fāɗinta kuwa kamu ashirin da biyar.22. Tagoginta, shirayinta da siffofin itatuwan dabinon da aka yi zāne-zānen adonta duk girmansu ɗaya ne da na ƙofar da take fuskantar gabas. Ɗakin shiga shi ma ya fuskanci filin yana kuma da matakai bakwai waɗanda suka bi zuwa ƙofar shiga, da shirayinta ɗaura da su.23. Akwai ƙofa zuwa filin ciki wadda take fuskantar ƙofar arewa, kamar dai yadda take a gabas. Ya auna daga ƙofa zuwa ƙofar da take ɗaura ta ita; ya sami kamu ɗari.24. Sa’an nan ya kai ni gefen kudu, na kuma ga ƙofa tana fuskantar kudu. Ya auna madogaranta da shirayinta, dukansu girmansu ɗaya ne kamar sauran ƙofofi biyun.25. Hanyar shiga da shirayinta suna da tagogi duk a kewaye, kamar tagogin sauran. Tsawonta kamu hamsin ne fāɗinta kuma kamu ashirin da biyar ne.26. Matakai bakwai sun haura zuwa ƙofar, da shirayi ɗaura da matakan; tana da zāne-zānen adon itatuwan dabino a bangayen a kowane gefe.27. Filin cikin ma yana da ƙofar da ta fuskanci kudu, sai ya auna daga wannan ƙofa zuwa ƙofar waje a gefen kudu; ya sami kamu ɗari.28. Sai ya kawo ni cikin filin ciki ta ƙofar kudu, ya kuma auna ƙofar kudu; ita ma tana da girma ɗaya da sauran ƙofofin shiga.29. Ɗakunanta na matsara, bangayenta duk suna da girma ɗaya da sauran. Hanyar shiga da shirayinta suna da tagogi duk a kewaye. Tsawonta kamu hamsin ne, fāɗinta kuma kamu ashirin da biyar ne.30. (Fāɗin shirayun hanyoyin shiga kewaye da filin ciki kamu ashirin da biyar ne, fāɗinsu kuma kamu biyar.)31. Shirayin ƙofar yana fuskantar filin waje; an yi zāne-zānen adon itatuwan dabino a madogarar bangayen hanyar shiga. Yana kuma da matakai takwas.32. Sai ya kai ni filin da yake ciki a gefen gabas, ya kuma auna hanyar shiga; girmanta iri ɗaya ne kamar sauran.33. Ɗakunanta, bangayenta da shirayinta duk girmansu iri ɗaya ne kamar sauran. Hanyar shiga da shirayinta suna da tagogi duk a kewaye. Tsawon hanyar shiga kamu hamsin ne, fāɗinta kuma kamu ashirin da biyar.34. Shirayinta yana fuskantar filin da yake waje; tana da zāne-zānen adon itatuwan dabino a madogararta. Tana kuma da matakai takwas.35. Sa’an nan ya kawo ni ƙofar arewa ya kuma auna ta. Girmanta ɗaya ne da sauran,36. Haka ma ɗakunanta, bangayenta da shirayinta, ƙofar tana da tagogi duk a kewaye. Tsawonta kamu hamsin, fāɗinta kuma kamu ashirin da biyar.37. Shirayin ƙofar ta fuskanci filin waje; tana da zāne-zānen adon itatuwan dabino a madogaranta, matakai takwas kuwa sun haura zuwa wajenta.38. Ɗakin da hanya ta ratsa ciki yana kusa da shirayin a kowane hanyoyin shiga na ciki, inda a kan wanke hadayun ƙonawa.39. A shirayin hanyar shiga akwai tebur biyu a kowane gefe, inda ake yankan hadayun ƙonawa, hadayun zunubi da kuma hadayun laifi.40. Ta bangon waje na shirayin hanyar shiga, kusa da matakai a mashigin zuwa hanyar shiga da take arewa akwai tebur biyu, akwai kuma tebur biyu a gefe ɗaya na matakan.41. Duka dai akwai tebur huɗu a gefe ɗaya na hanyar shiga, huɗu kuma a ɗaya gefen, tebur takwas ke nan gaba ɗaya, inda a kan yanka hadayu a kai.42. Akwai kuma tebur huɗu da aka yi da sassaƙaƙƙun duwatsu don hadayun ƙonawa, tsawon kowanne kuwa kamu ɗaya da rabi ne, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kuma kamu ɗaya. A kansu ne a kan ajiye kayan yanka hadayun ƙonawa da kuma sauran hadayu.43. Aka kakkafa ƙugiyoyi kewaye a bangon, tsawon kowanne ya yi fāɗin tafin hannu. An yi amfani da teburin don a riƙa ajiye naman hadayu.44. Waje da ƙofar ciki, a cikin filin ciki, akwai ɗakuna biyu, ɗaya a gefen ƙofar arewa yana kuma fuskantar kudu, wani kuma a gefen ƙofar kudu yana fuskantar arewa.45. Sai mutumin ya ce mini, “Ɗakin da yake fuskantar kudu ne na firistocin da suke lura da haikali,46. ɗaya ɗakin kuma da yake fuskantar arewa ne na firistocin da suke lura da bagade. Waɗannan su ne ’ya’yan Zadok maza, waɗanda su ne kaɗai Lawiyawan da za su iya yin kusa da Ubangiji don su yi hidima a gabansa.”47. Sa’an nan ya auna filin, murabba’i ne, tsawonsa kamu ɗari, fāɗinsa kuma kamu ɗari. Bagaden kuwa yana a gaba a cikin haikalin.48. Sai ya kawo ni shirayin haikalin ya kuma auna madogaran shirayin; fāɗinsu a kowane gefe kamu biyar-biyar ne. Fāɗin mashigin kamu goma sha huɗu ne, bangayenta kuma kamu uku-uku ne a kowane gefe.49. Fāɗin shirayin kamu ashirin ne, kamu goma sha biyu kuma daga gaba zuwa baya. A kan kai samansa ta wurin hawan matakai, akwai kuma ginshiƙai a kowane gefe na madogaran.Zabura 132:10-1810. Saboda Dawuda bawanka, kada ka ƙi shafaffenka.11. Ubangiji ya rantse wa Dawuda tabbataccen rantsuwa cewa ba zai janye ba cewa, “Ɗaya daga cikin zuriyarka zan sa a kan kursiyinka,12. in ’ya’yanka maza za su kiyaye alkawari da farillan da na koya musu, to ’ya’yansu maza za su zauna a kan kursiyinka har abada abadin.”13. Gama Ubangiji ya zaɓi Sihiyona, ya so ta zama mazauninsa,14. “Wannan shi ne wurin hutuna har abada abadin; a nan zan zauna ina mulki gama ina son ta,15. zan albarkace ta da tanade-tanade masu yawa; matalautanta za su ƙoshi da abinci.16. Zan suturta firistocinta da ceto, tsarkakanta kuma kullum za su rera don farin ciki.17. “A nan zan sa ƙaho ya yi girma wa Dawuda in kuma kafa fitila saboda shafaffena.18. Zan suturta abokan gābansa da kunya, amma rawanin da yake a kansa zai yi ta walƙiya.”Karin Magana 29:5-55. Duk wanda yake wa maƙwabcinsa daɗin baki yana sa wa ƙafafunsa tarko ne.Yaƙub 5:1-201. Yanzu fa sai ku saurara, ku masu arziki, ku yi kuka da ihu, saboda azabar da take zuwa a kanku.2. Arzikinku ya ruɓa, asu kuma sun cinye tufafinku.3. Zinariyarku da azurfarku sun yi tsatsa. Tsatsarsu kuwa za tă zama shaida a kanku, ta kuma ci namar jikinku kamar wuta. Kun ɓoye dukiya a kwanakin ƙarshe.4. Ga shi! Zaluncin da kuka yi na hakkin ma’aikatan gonakinku yana ta ƙara. Kukan masu girbi ya kai kunnuwan Ubangiji Maɗaukaki.5. Kun yi rayuwar jin daɗi a duniya kuna ci kuna sha na ganin dama. Kun ciyar da kanku kun yi ƙiba don ranar yanka.6. Kun hukunta kun kuma kashe mutane marasa laifi, waɗanda ba su yi gāba da ku ba.7. Saboda haka ’yan’uwa, sai ku yi haƙuri har dawowar Ubangiji. Ku dubi yadda manomi yakan jira gona ta ba da amfaninta mai kyau, da kuma yadda yake haƙurin jiran ruwan sama na damina da na kaka.8. Haka ku ma, ku yi haƙuri, ku tsaya da ƙarfi, gama dawowar Ubangiji ya yi kusa.9. ’Yan’uwa, kada ku yi gunaguni da juna, don kada a hukunta ku. Alƙalin yana tsaye a bakin ƙofa!10. ’Yan’uwa, ku ɗauki annabawa da suka yi magana a cikin sunan Ubangiji, a matsayin gurbi na haƙuri a cikin shan wahala.11. Kamar yadda kuka sani, mukan ce da waɗanda suka jure, masu albarka ne. Kun ji daurewar Ayuba, kuka kuma ga abin da Ubangiji ya yi a ƙarshe. Ubangiji yana cike da tausayi da jinƙai.12. ’Yan’uwana, fiye da kome, kada ku yi rantsuwa ko da sama, ko da ƙasa ko da wani abu dabam. Bari “I” naku yă zama “I”. “A’a” naku kuma yă zama “A’a”, don kada a hukunta ku.13. Akwai waninku da yake shan wahala? Ya kamata yă yi addu’a. Akwai wani mai murna? Sai yă rera waƙoƙin yabo.14. Akwai waninku da yake ciwo? Ya kamata yă kira dattawan ikkilisiya su yi masa addu’a, su kuma shafa masa mai cikin sunan Ubangiji.15. Addu’ar da aka yi cikin bangaskiya, za tă warkar da marar lafiya, Ubangiji zai tashe shi. In ya yi zunubi kuwa za a gafarta masa.16. Saboda haka, ku furta wa juna zunubanku, ku yi addu’a saboda juna, domin ku sami warkarwa. Addu’ar mai adalci tana da iko da kuma amfani.17. Iliya mutum ne kamar mu. Ya yi addu’a da gaske don kada a yi ruwan sama, ba a kuma yi ruwan sama a ƙasar ba har shekaru uku da rabi.18. Ya sāke yin addu’a, sai sammai suka ba da ruwan sama, ƙasa kuma ta ba da amfaninta.19. ’Yan’uwana, in waninku ya kauce daga gaskiya, wani kuma ya komo da shi,20. sai yă tuna da wannan. Duk wanda ya komo da mai zunubi daga kaucewarsa, zai cece shi daga mutuwa, yă kuma rufe zunubai masu ɗumbun yawa. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.