Baibul a cikin shekara guda Nuwamba 25Ezekiyel 41:1-261. Sai mutumin ya kawo ni wuri mai tsarki da yake waje ya kuma auna madogaransa; fāɗin gefe-gefen kamu shida ne a kowane gefe.2. Faɗin ƙofar shiga kamu goma ne, fāɗin bangaye a kowane madogararta kamu biyar-biyar ne. Ya kuma auna wuri mai tsarkin da yake waje; tsawonsa kamu arba’in fāɗinsa kuma kamu ashirin.3. Sa’an nan ya shiga wuri mai tsarki da yake can ciki ya auna madogarar ƙofar shigar; fāɗin kowanne kamu biyu ne. Faɗin ƙofar shigan kamu shida ne, fāɗin bangayen a kowane gefenta kamu bakwai-bakwai ne.4. Ya kuma auna tsawon wuri mai tsarki da yake can ciki; tsawon kamu ashirin ne, fāɗinsa kuma kamu ashirin daga ƙurewa wuri mai tsarki da yake waje. Ya ce mini, “Wannan shi ne Wuri Mafi Tsarki.”5. Sa’an nan ya auna bangon haikalin; kaurinsa kamu shida ne, kuma kowane ɗakin da yake a gefe kewaye da haikalin fāɗinsa kamu huɗu ne.6. Ɗakunan da suke gefe masu hawa uku ne, wani bisa wani, guda talatin a kowane hawa. Akwai katanga kewaye da bangayen haikalin don ta tokare ɗakunan, domin ba a so ɗakunan su jingina da bangon haikalin.7. Faɗin ɗakunan da suke gefe kewaye da haikalin ya yi ta ƙaruwa daga hawa zuwa hawa. Ginin da aka yi kewaye da haikalin ya yi ta ƙaruwa daga hawa zuwa hawa, don haka ɗakunan suka yi ta ƙara fāɗi yayinda suka ƙara bisa. Akwai mataki daga ɗaki na ƙasa zuwa ɗaki na bisa ta hanya hawa ɗaki na tsakiya.8. Na ga cewa haikalin yana da ɗagaggen tushe kewaye da shi, wanda ya zama harsashin ɗakunan da suke gefe. Tsawonsa kara guda ne mai tsawon kamu shida.9. Kaurin bangon waje na ɗakunan da suke gefe kamu biyar ne. Faɗin filin da yake tsakanin ɗakunan da suke gefen haikalin10. da ɗakunan firistoci kamu ashirin ne kewaye da haikalin.11. Akwai ƙofofin shiga daga fili, ɗaya a arewa ɗaya kuma a kudu; fāɗin tushen da ya yi kusa da filin kamu biyar ne kewaye.12. Faɗin ginin da yake fuskantar filin haikali a wajen yamma kamu saba’in ne. Kaurin bangon ginin kamu biyar ne kewaye, tsawonsa kuma kamu tasa’in ne.13. Sa’an nan ya auna haikalin; tsawonsa kamu ɗari ne, tsawon filin haikalin da ginin tare da bangayensa su ma kamu ɗari ne.14. Faɗin filin haikalin a wajen gabas, haɗe da gaban haikalin, kamu ɗari ne.15. Sa’an nan ya auna tsawon ginin da yake fuskantar filin a bayan haikalin, haɗe da rumfunansa a kowane gefe, kamu ɗari. Wuri mai tsarki da yake waje, wuri mai tsarki da yake can ciki da shirayin da yake fuskantar filin,16. da madogaran ƙofa da matsattsun tagogi da rumfuna kewaye da su ukun, har da kome da yake gaba haɗe da madogarar ƙofa, an rufe su da katako. An rufe bangon haikalin daga ƙasa har zuwa tagogi, tagogin kuwa an rufe su.17. A filin da yake bisan ƙofar shiga na waje zuwa wuri mai tsarki na can ciki da kuma a bangayen da aka daidaita tsakani kewaye da wuri mai tsarki na can ciki da kuma na can waje18. an zāna siffofin kerubobi da na itatuwan dabino. Zānen siffar itacen dabino yana a tsakanin kerub da kerub. Kowane kerub yana da fuska biyu,19. fuskar ɗaya kamar ta mutum tana fuskantar zānen siffar itacen dabino a wannan gefe, ɗaya fuskar kamar ta zaki tana fuskantar zānen siffar itacen dabino na wancan gefe. Haka aka zāna su dukan a jikin bangon haikalin kewaye.20. Daga ƙasa zuwa daurin ƙofa, an zāna siffofin kerubobi da na itatuwan dabino a waje na wuri mai tsarki.21. Wuri mai tsarki da yake waje yana da madogarar ƙofa murabba’i, haka ma wadda take a gaban Wuri Mafi Tsarki.22. Akwai bagaden katako mai tsayi kamu uku, fāɗinsa kamu biyu da kuma tsawonsa kamu biyu; kusurwansa, tushensa da kuma gefe-gefensa duk katako ne. Sai mutumin ya ce mini, “Wannan shi ne tebur da yake a gaban Ubangiji.”23. A wuri mai tsarki da yake waje da kuma Wuri Mafi Tsarki suna da ƙofa biyu a haɗe.24. Kowace ƙofa tana da murfi biyu masu buɗewa ciki da waje.25. A ƙofofin wuri mai tsarki da yake waje an zāna siffofin kerubobi da na itatuwan dabino kamar yadda aka zāna a bangayen, akwai kuma rumfar da aka yi da itace a gaban shirayin.26. A bangayen da suke gefen shirayin akwai matsattsun tagogi da aka zāna siffar itatuwan dabino a kowane gefe. Gefe-gefen ɗakunan haikalin ma suna da rumfuna.Ezekiyel 42:1-201. Sai mutumin ya kai ni wajen arewa zuwa cikin filin da yake waje ya kuma kawo ni ɗakunan da suke ɗaura da filin haikalin da yake a gefen arewa.2. Tsawon ginin da yake fuskantar arewa kamu ɗari ne fāɗinsa kuma kamu hamsin.3. A gaban kamu ashirin na filin da yake can ciki da kuma a gaban daɓen filin da yake waje, akwai rumfuna a jere waɗanda suke fuskantar juna hawa uku-uku.4. A gaban ɗakunan akwai hanya a can ciki mai fāɗin kamu goma, tsawonta kuma kamu ɗari. Ƙofofinsu suna wajen arewa.5. Ɗakunan da suke bisa ba su da fāɗi, gama mataki hawan benen ya cinye wuri fiye da a ɗakunan da suke a hawa na ƙasa da na tsakiya.6. Ɗakunan da suke a hawa na uku ba su da ginshiƙai, yadda filayen suka kasance da su, saboda haka suka matsu fiye da waɗanda suke a hawa na ƙasa da na tsakiya.7. Akwai katanga wadda take waje, wadda ta yi hannun riga da ɗakunan filin waje; ta miƙe a gaban ɗakunan, tsawonta kamu hamsin ne.8. Yayinda tsawon jerin ɗakunan da suke a gefe kusa da filin da yake waje kamu hamsin ne, tsawon jerin ɗakunan da suke a gefen da yake kurkusa da wuri mai tsarki kamu ɗari ne.9. Ɗakunan da suke can ƙasa suna da ƙofar shiga a wajen gabas in za a shiga cikinsu daga filin da yake waje.10. A wajen kudu a ta katangar filin da yake waje, kusa da filin haikali da yake ɗaura da katangar waje, akwai ɗakuna11. da hanya a gabansu. Waɗannan sun yi kama da ɗakunan da suke wajen arewa; tsawonsu da fāɗinsu duk iri ɗaya ne, da irin mafita ɗaya da kuma yadda aka shirya su. Sun yi kama da ƙofofin da suke wajen arewa12. haka ma ƙofofin ɗakunan a wajen kudu. Akwai ƙofa a farkon hanyar da ta yi hannun riga da ɗayan katangar da ta miƙe wajen gabas, inda za a iya shiga ɗakunan.13. Sai ya ce mini, “Ɗakunan arewa da na kudu waɗanda suke fuskantar filin haikali ɗakunan firistoci ne, inda firistocin da suke kusaci Ubangiji za su ci hadayu mafi tsarki. A can za su ajiye hadayu mafi tsarki, hadayu na gari, hadayu na zunubi da hadayu na laifi, gama wuri mai tsarki ne.14. Da zarar firistoci suka shiga wuri mai tsarki, ba za su fita zuwa filin da yake waje ba sai sun tuɓe rigunan da suka yi hidima da su, gama waɗannan masu tsarki ne. Za su sa waɗansu riguna kafin su kusaci wuraren da mutane suke.”15. Da ya gama auna filin da yake cikin haikali, sai ya fitar da ni ta ƙofar gabas ya auna dukan filin kewaye.16. Ya auna gefen gabas da karan awo; ya samu kamu ɗari biyar.17. Ya auna gefen arewa da karan awon; ya samu kamu ɗari biyar.18. Ya auna gefen kudu da karan awon; ya samu kamu ɗari biyar.19. Sa’an nan ya juya zuwa gefen yamma ya auna shi da karan awon, ya samu kamu ɗari biya.20. Ta haka ya auna dukan kusurwoyi huɗu. Filin yana da katanga kewaye da shi, tsawon kamu ɗari biyar, fāɗin kuma kamu ɗari biyar don yă raba wuri mai tsarki daga wuri marar tsarki.Zabura 133:1-31. Abu mai kyau ne, mai daɗi kuma sa’ad da ’yan’uwa suna zaman lafiya!2. Yana kamar mai mai darajar da aka zuba a kai, yana gangarawa a gemu, yana gangarawa a gemun Haruna, har zuwa wuyan rigunansa.3. Yana kamar raɓar Hermon da take zubowa a kan Dutsen Sihiyona. Gama a can Ubangiji ya tabbatar da albarkarsa, har ma rai na har abada.Karin Magana 29:6-66. Mugun mutum tarko ne ta wurin zunubinsa, amma mai adalci zai iya rera ya kuma yi murna.1 Bitrus 1:1-251. Bitrus, manzon Yesu Kiristi, Zuwa ga zaɓaɓɓu na Allah, baƙi a duniya, da suke a warwatse ko’ina a Fontus, Galatiya, Kaffadokiya, Asiya da kuma Bitiniya,2. waɗanda aka zaɓa bisa ga rigyasanin Allah Uba, ta wurin aikin tsarkakewar Ruhu, don biyayya ga Yesu Kiristi, su kuma sami yayyafan jininsa. Alheri da salama su zama naku a yalwace.3. Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi! Cikin jinƙansa mai girma ya ba mu sabuwar haihuwa cikin bege mai rai ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu,4. da kuma cikin gādon da ba zai taɓa lalacewa, ɓacewa ko koɗewa ba, ajiyayye a sama dominku,5. ku waɗanda ta wurin bangaskiya ake kiyayewa ta wurin ikon Allah har yă zuwa ceton da yake a shirye da za a bayyana a ƙarshen lokaci.6. A kan wannan kuke cike da farin ciki ƙwarai, ko da yake yanzu na ɗan lokaci kuna fuskantar baƙin ciki daga gwaje-gwaje iri-iri.7. Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne, wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan gwada ta da wuta, domin bangaskiyan nan taku ta jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Kiristi.8. Ko da yake ba ku taɓa ganinsa ba, kuna ƙaunarsa; kuma ko da yake ba kwa ganinsa yanzu, kun gaskata shi, kun kuma cika da farin ciki ƙwarai, wanda ya fi gaban faɗi,9. gama kuna samun sakamakon bangaskiyarku, ceton rayukanku ke nan.10. Game da ceton nan, annabawa, waɗanda suka yi maganar alherin da za tă zo gare ku, sun yi bincike mai zurfi, a natse,11. suna ƙoƙari su san lokaci da kuma yanayin da Ruhun Kiristi da yake cikinsu yana nunawa sa’ad da ya yi faɗi a kan wahalolin Kiristi da kuma ɗaukaka da za tă bi.12. Aka bayyana musu cewa ba kansu ne suke bauta wa ba sai ku, sa’ad da suka yi maganar abubuwan da aka faɗa muku ta wurin waɗanda suka yi muku wa’azin bishara, ta wurin Ruhu Mai Tsarki wanda aka aika daga sama. Ko mala’iku ma suna marmari su ga waɗannan abubuwa.13. Saboda haka, ku shirya kanku don aiki; ku zama masu kamunkai; ku kafa begenku duka a kan alherin da za a ba ku sa’ad da aka bayyana Yesu Kiristi.14. Kamar ’ya’ya masu biyayya, kada ku bi mugayen sha’awace-sha’awacen da dā kuke da su sa’ad da kuke rayuwa a cikin jahilci.15. Amma kamar yadda wanda ya kira ku yake mai tsarki, haka ku ma sai ku kasance masu tsarki cikin dukan abubuwan da kuke yi;16. gama a rubuce yake cewa, “Ku zama masu tsarki, domin ni mai tsarki ne.”17. Tun da yake kuna kira ga Uba wanda yake yin wa kowane mutum shari’a bisa ga ayyukansa ba bambanci, sai ku yi rayuwarku a nan kamar baƙi cikin tsoro mai bangirma.18. Gama kun san cewa ba da abubuwa masu lalacewa kamar azurfa ko zinariya ce aka fanshe ku daga rayuwar banza da kuka karɓa daga kakanni-kakanninku ba,19. sai dai an fanshe ku da jini mai daraja na Kiristi, ɗan rago marar aibi ko lahani.20. An zaɓe shi kafin halittar duniya, amma an bayyana shi a zamanin ƙarshe saboda ku.21. Ta gare shi ne kuka gaskata da Allah, wanda ya tā da shi daga matattu, aka kuma ɗaukaka shi, ta haka bari bangaskiyarku da begenku su kasance ga Allah.22. Yanzu da kuka tsarkake kanku ta wurin yin biyayya ga gaskiyan nan, don ku kasance da ƙauna mai gaskiya wa ’yan’uwanku, sai ku ƙaunaci juna ƙwarai, daga zuciya.23. Gama an sāke haihuwarku, ba da iri da yake lalacewa ba, sai dai marar lalacewa, ta wurin rayayyiya da kuma madawwamiyar maganar Allah.24. Gama, “Dukan mutane kamar ciyawa suke, darajarsu kuma kamar furannin jeji ne; ciyawa takan yanƙwane furannin kuma su kakkaɓe,25. amma maganar Ubangiji tana nan har abada.” Wannan kuwa ita ce kalmar da aka yi muku wa’azi. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.