Baibul a cikin shekara guda Nuwamba 27Ezekiyel 45:1-251. “ ‘Sa’ad da kuka rarraba ƙasar gādo, ku miƙa wa Ubangiji rabon ƙasar ya zama yanki mai tsarki, tsawonsa ya zama kamu 25,000 fāɗinsa kuma ya zama 20,000, dukan ƙasar za tă zama mai tsarki.2. Daga cikin wannan, sashe guda da yake murabba’i mai tsawo kamu 500 zai zama don wuri mai tsarki, kamu 50 kewaye da shi zai zama fili.3. A cikin yanki mai tsarki, ka auna tsawo kamu 25,000 da kuma fāɗi kamu 10,000. A cikinsa wuri mai tsarki zai kasance, Wuri Mafi Tsarki.4. Zai zama tsattsarkan rabo na ƙasa domin firistoci, waɗanda za su yi hidima a cikin wuri mai tsarki da kuma waɗanda za su zo kusa don su yi hidima a gaban Ubangiji. Zai zama wuri don gidajensu ya kuma zama tsattsarkan wuri saboda wuri mai tsarki.5. Wani sashi kuma mai tsawo kamu 25,000 da fāɗi 10,000 zai zama na Lawiyawa, waɗanda suke hidima a cikin haikali, zai zama mallakarsu don su zauna a ciki.6. “ ‘Za ka ba wa birnin fāɗin mallakarsa kamu 5,000, tsawonsa kuma 25,000, haɗe da tsattsarkan rabo; zai kasance na gidan Isra’ila duka.7. “ ‘Sarki zai kasance da fili da ya yi iyaka da kowane gefe na yankin wuri mai tsarki da kuma mallakar birnin. Zai miƙe ya yi wajen yamma daga gefen yamma ya kuma yi wajen gabas daga gefen gabas, yana miƙewa a tsawo daga wajen yamma zuwa wajen gabashin iyaka don yă yi hannun riga da rabon kabilan.8. Wannan fili zai zama mallakarsa a Isra’ila. Kuma sarakunana ba za su ƙara zaluntar mutanena ba amma za su bar gidan Isra’ila ya mallaki ƙasar bisa ga kabilansu.9. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko na ce ku sarakunan Isra’ila, danniya da zaluncin da kuke yi sun isa! Ku yi shari’a bisa ga gaskiya da adalci, ku bar korar mutanena, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.10. Ku yi amfani da garwan da yake daidai, efa da yake daidai da kuma garwa da yake daidai.11. Efa da garwan su kasance girmansu ɗaya, garwan ya zama kashi ɗaya bisa goma na ganga efa kuma ya zama kashi ɗaya bisa goma na ganga; ganga fitaccen ma’auni na duka biyu.12. Shekel zai kasance da gera ashirin. Shekel ashirin a haɗa da shekel ashirin da biyar a haɗa da shekel goma sha biyar zai zama mina guda.13. “ ‘Wannan ita ce bayarwa ta musamman da za ku miƙa, kashi ɗaya bisa shida na efa daga kowace gangan alkama da kashi ɗaya bisa shida na efa daga kowace gangan sha’ir.14. Sashe na man da aka ƙayyade, da aka auna da garwa, kashi ɗaya bisa goma ne na garwa daga ganga (wanda yakan ci garwa goma, gama garwa goma suna daidai da ganga guda).15. A kuma ba da tunkiya daga kowane garke mai tumaki ɗari biyu daga makiyaya da aka yi masa banruwa sosai na Isra’ila. Za a yi amfani da waɗannan don hadayun gari, hadayun ƙonawa da hadayun salama don yin kafara saboda mutane, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.16. Dukan mutanen ƙasar za su yi wannan bayarwa ta musamman saboda amfanin sarki a Isra’ila.17. Zai zama hakkin sarki ne ya tanada hadayu na ƙonawa, hadayu na gari da hadayu na sha a bukukkuwa, Sabuwar Wata da Asabbatai, a duk ƙayyadaddun bukukkuwa na gidan Isra’ila. Zai tanada hadayu don zunubi, hadayu na gari, hadayu na ƙonawa da hadayu na salama don yin kafara saboda gidan Isra’ila.18. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a farkon wata a rana ta fari za ku ba da ɗan bijimi marar lahani a kuma tsarkake wuri mai tsarki.19. Firist zai ɗibi jinin hadaya don zunubi ya shafa a madogaran ƙofar haikali, a kusurwoyi huɗu na gefen bisa na bagade da kuma a kan madogaran ƙofar shiga na fili na can ciki.20. Za ku yi haka kuma a rana ta bakwai ga watan domin duk wanda ya yi zunubai ba da gangan ba ko ta wurin rashin sani; saboda haka sai ku yi kafara domin haikalin.21. “ ‘A wata na fari a rana ta goma sha huɗu za ku kiyaye Bikin Ƙetarewa, bikin da yakan ɗauki kwana bakwai, a lokacin ne za ku riƙa cin burodi marar yisti.22. A wannan rana sarki zai tanada bijimi a matsayin hadaya don zunubi domin kansa da kuma domin dukan mutanen ƙasar.23. Kowace rana a kwanaki bakwai na Bikin zai tanada bijimai guda bakwai da raguna bakwai marar lahani a matsayi hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, da kuma bunsuru saboda hadaya don zunubi.24. Zai tanada efa na gari don kowane bijimi da kuma efa don kowane rago, tare da kwalabar mai don kowane efa guda.25. “ ‘A lokacin kwana bakwai na Bikin, waɗanda za su fara a wata na bakwai a rana ta goma sha biyar, zai ba da abubuwan nan saboda hadayu don zunubi, hadayu na ƙonawa, hadayu na gari da kuma mai.Ezekiyel 46:1-241. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a rufe ƙofa ta fili na can cikin da take fuskantar gabas ranaku shida na aiki, amma a ranar Asabbaci da kuma a ranar ganin Sabuwar Wata a buɗe ta.2. Sarki zai shiga daga waje ta shirayin hanyar shiga yă tsaya a madogarar ƙofa. Firistoci za su miƙa hadayarsa ta ƙonawa da hadayunsa na salama. Zai yi sujada a madogarar ƙofar hanyar shiga sa’an nan ya fita, amma ba za a rufe ƙofar ba sai da yamma.3. A Asabbatai da kuma a Sabuwar Wata mutanen ƙasar za su yi sujada a gaban Ubangiji a mashigin wannan hanyar shiga.4. Hadaya ta ƙonawar da sarki ya kawo wa Ubangiji a ranar Asabbaci ’yan raguna shida ne da rago guda, dukansu marasa lahani.5. Hadayar garin da aka bayar tare da ragon efa guda ne, hadayar garin da ’yan ragunan yadda ya ga dama, tare da kwalabar mai don kowace efa.6. A ranar Sabuwar Wata zai miƙa ɗan bijimi, ’yan raguna guda shida da kuma rago guda, dukansu marasa lahani.7. Zai tanada a matsayin hadaya ta gari, efa guda tare da bijimi, efa guda tare da ’yan raguna, da kuma ’yan raguna yadda ya ga dama, tare da kwalabar mai don kowace efa.8. Sa’ad da sarki zai shiga, zai shiga ta shirayin hanyar shiga, zai kuma fita ta nan.9. “ ‘Sa’ad da mutanen ƙasar suka zo gaban Ubangiji a ƙayyadaddun bukukkuwa, duk wanda ya shiga ta ƙofar arewa don yă yi sujada sai ya fita ta ƙofar kudu; kuma duk wanda ya shiga ta ƙofar kudu sai ya fita ta ƙofar arewa. Ba wanda zai koma ta ƙofar da ya shiga, amma kowa zai fita a ƙofar ɗaura da wadda ya shiga.10. Sarki zai kasance a cikinsu, zai shiga sa’ad da suke shiga ya kuma fita sa’ad da suka fita.11. “ ‘A bukukkuwa da ƙayyadaddun bukukkuwa, hadaya ta gari zai zama efa tare da bijimi, efa da rago, da kuma ’yan raguna da ya ga dama, haɗe da kwalabar mai.12. Sa’ad da sarki ya ba da hadaya ta yardar rai ga Ubangiji, ko hadaya ta ƙonawa ce ko hadayun salama ne, sai a buɗe masa ƙofar da take fuskantar gabas. Zai miƙa hadayarsa ta ƙonawa ko hadayarsa ta salama yadda yakan yi a ranar Asabbaci. Sa’an nan ya fita, bayan kuma ya fita, sai a rufe ƙofar.13. “ ‘Kullum za ku tanada ɗan rago bana ɗaya marar lahani don hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji; kowace safiya za ku tanada shi.14. Tare da shi za ku tanada hadaya ta gari kowace safiya, da ya haɗa da kashi ɗaya bisa shida na efa tare da kashi ɗaya bisa uku na mai ga garin da aka cuɗa. Miƙawar wannan hadaya ta gari ga Ubangiji dawwammamiyar farilla ce.15. Saboda haka za a tanada ɗan rago da hadaya ta gari da kuma mai kowace safiya don hadaya ta ƙonawa ta kullum.16. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa in sarkin ya ba wa ɗaya daga cikin ’ya’yansa kyauta daga gādonsa, zai kuwa zama na zuriyar; zai kuwa zama mallakarsu ta wurin gādo.17. In kuma ya ba wa ɗaya daga cikin bayinsa kyauta daga gadonsa, bawan zai iya riƙe shi sai shekarar ’yantarwa; sa’an nan ya mayar wa sarkin. Gādon sarki na ’ya’yansa maza ne kaɗai; na su ne.18. Kada sarki ya ƙwace gādon mutane, yana korinsu daga mallakarsu. Zai ba wa ’ya’yansa maza gādonsu daga cikin mallakarsa, don kada a raba wani daga mutanena da mallakarsa.’ ”19. Sa’an nan mutumin ya fitar da ni ta ƙofar shiga a gefen ƙofar zuwa tsarkakakkun ɗakuna waɗanda suke fuskantar arewa, waɗanda suke na firistoci, ya kuma nuna mini wani wuri daga can ƙurewar yamma.20. Ya ce mini, “Wannan shi ne wurin da firistoci za su dafa hadaya don laifi, da hadaya don zunubi, a nan ne kuma za su toya hadaya ta gari, domin kada su kai su a filin da yake waje, su tsarkake mutane.”21. Sa’an nan ya kawo ni filin da yake waje ya kuma bi da ni kewaye da kusurwoyi huɗunsa, na kuma ga kowace kusurwa na wani fili.22. A kusurwoyi huɗu na filin da yake waje akwai waɗansu filaye a haɗe, tsawonsu kamu arba’in fāɗinsu kuwa kamu talatin; kowane fili a kusurwoyi huɗun nan girmansu ɗaya ne.23. Kewaye da cikin kowane filin huɗun nan akwai ginin dutse, da murhu da aka gina a kewaye a ƙarƙashin ginin.24. Sai ya ce mini, “Waɗannan su ne ɗakunan dahuwa inda masu hidima a haikali za su dafa hadayun da jama’a.”Zabura 135:1-71. Yabi Ubangiji. Yabi sunan Ubangiji; yabe shi, ku bayin Ubangiji,2. ku waɗanda kuke hidima a gidan Ubangiji, cikin filayen gidan Allahnmu.3. Yabi Ubangiji, gama Ubangiji nagari ne; rera yabo ga sunansa, gama wannan yana da kyau.4. Gama Ubangiji ya zaɓi Yaƙub ya zama nasa, Isra’ila ya zama mallakarsa mai daraja.5. Na san cewa Ubangiji yana da girma, cewa shugabanmu ya fi dukan alloli girma.6. Ubangiji yana yin abin da ya ga dama, a sammai da kuma a duniya, cikin tekuna da kuma cikin dukan zurfafansu.7. Yakan sa gizagizai su taso daga iyakokin duniya; yakan aika da walƙiya tare da ruwan sama ya fito da iska daga ɗakunan ajiyarsa.Karin Magana 29:8-88. Masu ba’a kan kuta faɗa a birni, amma masu hikima sukan kwantar da fushi.1 Bitrus 3:1-221. Haka ma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, domin in waɗansunsu ba su gaskata maganar ba, wataƙila a shawo kansu ba tare da magana ba2. sa’ad da suka ga rayuwarku mai tsabta da kuma na ladabi.3. Kyanku bai kamata yă zama na adon jiki ba, kamar kitso da sa kayan ado na zinariya da kuma sa kaya masu tsada.4. Maimakon haka, kyanku ya kamata yă zama ainihi na halinku na ciki, kyan da ba ya koɗewa na tawali’u da kuma na natsattsen ruhu, wanda yake mai daraja a gaban Allah.5. Gama haka matan masu tsarki na dā waɗanda suka sa begensu ga Allah suka yi wa kansu ado. Sun yi wa mazansu biyayya,6. kamar Saratu, wadda ta yi biyayya ga Ibrahim, har ta kira shi maigidanta. Ku ’ya’yanta ne mata in kun aikata abin da yake daidai, ba ku kuma ba tsoro dama ba.7. Mazan aure, ku ma, ku yi zaman sanin ya kamata yayinda kuke zama da matanku, ku girmama su a matsayin abokan zama marasa ƙarfi da kuma a matsayin magādan kyautar rai na alheri tare da ku, don kada wani abu yă hana addu’o’inku.8. A ƙarshe, dukanku ku zauna lafiya da juna; ku zama masu juyayi, kuna ƙaunar juna kamar ’yan’uwa, ku zama masu tausayi da kuma tawali’u.9. Kada ku rama mugunta da mugunta ko zagi da zagi, sai dai ku sa albarka, gama ga wannan ne aka kira ku, ku kuma gāji albarka.10. Gama, “Duk wanda yake so yă ji daɗin rayuwa, yă kuma ga kwanaki masu kyau dole yă ƙame harshensa daga mugunta leɓunansa kuma daga maganar yaudara.11. Dole yă juye daga mugunta, ya aikata nagarta; dole yă nemi salama yă kuma bi ta.12. Gama idanun Ubangiji suna a kan masu adalci kunnuwansa kuma suna jin addu’arsu, amma fuskar Ubangiji tana gāba da masu mugunta.”13. Wa zai yi muku lahani in kun himmantu ga yin nagarta?14. Amma ko da za ku sha wahala saboda abin da yake daidai, ku masu albarka ne. “Kada ku ji tsoron abin da suke tsoro; kada kuma ku firgita.”15. Sai dai a cikin zukatanku ku keɓe Kiristi a matsayin Ubangiji. A kullum, ku kasance a shirye ku ba da amsa ga duk wanda yake neman ku ba da dalilin wannan begen da kuke da shi. Amma ku yi wannan cikin tawali’u da ladabi,16. tare da lamiri mai kyau, saboda waɗanda suke maganganun banza a kan kyawawan ayyukanku cikin Kiristi su ji kunya da irin ɓata suna da suke yi.17. Ya fi kyau, in nufin Allah ne, a sha wahala don yin nagarta fiye da yin mugunta.18. Gama Kiristi ya mutu domin zunubi sau ɗaya tak, mai adalci saboda marasa adalci, don yă kawo ku ga Allah. An kashe shi a cikin jiki, amma an rayar da shi a Ruhu,19. ta wurin wanda kuma ya tafi ya yi wa ruhohin da suke a kurkuku wa’azi20. waɗanda dā ba su yi biyayya ba sa’ad da Allah ya jira da haƙuri a kwanaki Nuhu yayinda ake sassaƙa jirgi. A cikinsa mutane kima ne kawai, su takwas, aka kuɓutar ta ruwa,21. ruwan nan kuwa kwatancin baftisma ne da yanzu ya cece ku ku ma, ba kawar da dauda daga jiki ba, sai dai yin alkawari na lamiri mai kyau ga Allah. Ya cece ku ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu,22. wanda ya tafi sama, yana kuma a hannun dama na Allah, mala’iku, mulkoki da kuma masu iko suna masa biyayya. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.