Baibul a cikin shekara guda Nuwamba 28Ezekiyel 47:1-231. Mutumin ya komo da ni zuwa mashigin haikalin, sai na kuwa ga ruwa yana malalowa daga ƙarƙashin madogarar ƙofar haikalin wajen gabas (gama haikalin yana fuskantar gabas). Ruwan yana malalowa daga ƙarƙashin gefen kudun haikalin, kudu da bagaden.2. Sai ya fitar da ni ta ƙofar arewa ya kewaye da ni ta waje zuwa ƙofar da take waje mai fuskantar gabas, ruwan kuwa yana malalowa daga wajen kudu.3. Yayinda mutumin ya yi wajen gabas da karan awo a hannunsa, sai ya auna kamu dubu ya kuma bi da ni ta ruwan da zurfinsa ya kama ni a idon ƙafa.4. Ya auna wani kamu dubu ya kuma bi da ni a ruwan da zurfinsa ya kai ni gwiwa. Ya sāke auna kamu dubu ya kuma bi da ni a ruwan da zurfinsa kama ni a gindi.5. Ya auna wani kamu dubu, amma a yanzu ruwan ya zama kogin da ban iya hayewa ba, domin ruwan ya taso ya kuma yi zurfin da ya isa a yi iyo a ciki, kogin da ba za a iya hayewa ba.6. Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ga wannan?” Sa’an nan ya komo da ni zuwa bakin kogin.7. Sa’ad da na iso can, sai na ga itatuwa masu yawa a kowane gefen kogin.8. Sai ya ce mini, “Wannan ruwa yana malalowa zuwa yankin gabas ya kuma gangaro zuwa cikin Araba, inda zai shiga Teku. Sa’ad da ya shiga cikin Tekun sai ruwan a can ya zama mai daɗi.9. Tarin halittu masu rai za su rayu a duk inda ruwan ya malalo. Za a kasance da kifi masu yawa, domin wannan ruwa yana malalowa a can yana kuma mai da ruwan gishiri yă zama ruwa mai daɗi; saboda haka duk inda ruwan ya malalo, kome zai rayu.10. Masunta za su tsaya a gaɓar; daga En Gedi zuwa En Eglayim, za a kasance da wuraren jefa abin kamun kifi. Za a sami kifayen iri-iri, kamar kifaye Bahar Rum.11. Amma fadamun da tafkunan ba za su zama masu daɗi ba; za a bar su a gishirinsu.12. ’Ya’yan itatuwa na kowane iri za su yi girma a kowane gefen kogin. Ganyayensu ba su bushe ba, ba kuwa za su fasa yin ’ya’ya ba. Kowane wata za su ba da ’ya’ya domin ruwa daga wuri mai tsarki yana malalo musu. ’Ya’yansu za su zama abinci, ganyayensu kuma za su zama magani.”13. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “Waɗannan su ne iyakokin da za ku raba ƙasar gādo cikin kabilan Isra’ila goma sha biyu, da rabo biyu don Yusuf.14. Za ku raba ta daidai a cikinsu. Gama na ɗaga hannu na rantse zan ba da ita ga kakanninku, wannan ƙasa za tă zama gādonku.15. “Wannan ce za tă zama iyakar ƙasa. “A wajen arewa za tă fara daga Bahar Rum ta hanyar Hetlon ta wuce Lebo Hamat zuwa Zedad,16. Berota da Sibrayim (wadda take a iyaka tsakanin Damaskus da Hamat), har zuwa Hazer-Hattikon, wadda take a iyakar Hauran.17. Iyakar za tă miƙe daga teku zuwa Hazar-Enon, ta iyakar Damaskus, da iyakar Hamat a arewa. Wannan ita ce iyakar a wajen arewa.18. A wajen gabas iyakar za tă kama tsakanin Hauran da Damaskus, ta bi ta Urdun tsakanin Gileyad da ƙasar Isra’ila, zuwa tekun gabas har zuwa Tamar. Wannan ita ce iyakar a wajen gabas.19. A wajen kudu za tă fara daga Tamar har zuwa ruwan Meriba Kadesh, sa’an nan ta bi Rafin Masar zuwa Bahar Rum. Wannan ita ce iyakar a wajen kudu.20. A wajen yamma, Bahar Rum ne zai zama iyakar zuwa wani wuri ɗaura da Lebo Hamat. Wannan ita ce iyakar a wajen yamma.21. “Za ku rarraba wannan ƙasa a tsakaninku bisa ga kabilan Isra’ila.22. Za ku raba ta kamar gādo wa kanku da kuma wa baƙin da suka zauna a cikinku waɗanda suke da ’ya’ya. Za ku ɗauka su kamar ’yan ƙasa haifaffun Isra’ilawa; za su yi gādo tare da ku a cikin kabilan Isra’ila.23. A duk kabilar da baƙon yake zama, a can za ku ba shi gādonsa,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.Ezekiyel 48:1-351. “Ga kabilan, a jere bisa ga sunayensu. “A iyaka ta arewa, Dan zai sami rabo; zai bi hanyar Hetlon zuwa Lebo Hamat. Hazar-Enan da iyakar arewancin Damaskus kusa da Hamat za tă zama sashen iyakarsa a wajen gabas zuwa wajen yamma.2. Asher zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Dan daga gabas zuwa yamma.3. Naftali zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Asher daga gabas zuwa yamma.4. Manasse zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Naftali daga gabas zuwa yamma.5. Efraim zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Manasse daga gabas zuwa yamma.6. Ruben zai sami rabo; zai yi iyaka da Efraim daga gabas zuwa yamma.7. Yahuda zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Ruben daga gabas zuwa yamma.8. “Kusa da yankin Yahuda daga gabas zuwa yamma zai zama rabon da za ku bayar a matsayin kyauta ta musamman. Faɗinsa zai zama kamu 25,000, tsawonsa kuma zai zama daidai da tsawon yankunan kabilu daga gabas zuwa yamma; wuri mai tsarki zai kasance a tsakiyar wannan yanki.9. “Tsawon rabo na musamman da za ku bayar ga Ubangiji zai zama kamu 25,000, fāɗinsa kuma kamu 10,000.10. Wannan ne zai zama tsattsarkan rabo domin firistoci. Tsawon zai zama kamu 25,000 a wajen arewa, fāɗin kuma kamu 10,000 wajen yamma, kamu 10,000 zai zama fāɗinsa a wajen gabas, tsawonsa a wajen kudu zai zama kamu 25,000. A tsakiyarsa ne wuri mai tsarki na Ubangiji zai kasance.11. Wannan zai zama na keɓaɓɓun firistoci, zuriyar Zadok, waɗanda suka yi aminci cikin hidimata ba su kuwa karkata kamar yadda Lawiyawa suka yi sa’ad da Isra’ilawa suka karkace ba.12. Zai zama kyauta ta musamman a gare su daga tsattsarkan rabon ƙasar, kusa da yankin Lawiyawa.13. “Dab da yankin firistoci, Lawiyawa za su sami rabo mai tsawon kamu 25,000, fāɗin kuma kamu 10,000. Tsawonsa gaba ɗaya zai zama kamu 25,000, fāɗinsa kuma kamu 10,000.14. Ba za su sayar da shi ko su musayar da wani sashensa ba. Wannan shi ne mafi kyau na ƙasar ba kuma za a jinginar da ita ga wani ba, gama mai tsarki ce ga Ubangiji.15. “Sauran wurin da ya rage mai fāɗin kamu 5,000 da tsawon kamu 25,000 zai zama don amfanin kowa a birnin, don gidaje da wurin kiwo. Birnin zai kasance a tsakiyar wurin da ya ragen nan16. zai kuwa kasance da wannan awon, a wajen arewa kamu 45,000, wajen kudu kamu 45,000, wajen gabas kamu 45,000, wajen kudu kuma kamu 45,000.17. Wurin kiwo don birnin zai zama kamu 250 a wajen arewa, kamu 250 a wajen kudu, kamu 250 a wajen gabas da kuma kamu 250 a wajen yamma.18. Tsawon abin da ya rage a wurin, dab da tsattsarkan rabo, zai zama kamu 10,000 wajen gabas, kamu 10,000 kuma wajen yamma. Amfanin da zai bayar zai tanada abinci don ma’aikatan birnin.19. Masu aiki daga birnin waɗanda suka nome ta za su fito daga dukan kabilan Isra’ila.20. Dukan rabon zai zama murabba’i, kamu 25,000 kowane gefe. A matsayin kyauta ta musamman za ku keɓe tsattsarkan rabo, haka ma za ku yi da mallakar birnin.21. “Abin da ya rage a kowane gefe na wurin zai zama tsattsarkan rabo kuma mallakar birnin za tă zama ta sarki. Zai miƙe wajen gabas daga kamu 25,000 na tsattsarkan rabo zuwa iyakar da take wajen gabashin iyaka, da kuma a wajen yamma kamu 25,000 zuwa iyakar da take a wajen yamma. Dukan wuraren nan da suke hannun riga da rabon kabilan zai zama na sarki, tsattsarkan rabon tare da wuri mai tsarkin za su kasance a tsakiyarsu.22. Ta haka mallakar Lawiyawa da mallakar birnin za su kasance a tsakiyar wurin da yake na sarki. Wurin da yake na sarki zai kasance tsakanin iyakar Yahuda da iyakar Benyamin.23. “Game da sauran kabilun kuwa, “Benyamin zai sami rabo; zai miƙe daga wajen gabas zuwa wajen yamma.24. Simeyon zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Benyamin daga gabas zuwa yamma.25. Issakar zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Simeyon daga gabas zuwa yamma.26. Zebulun zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Issakar daga gabas zuwa yamma.27. Gad zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Zebulun daga gabas zuwa yamma.28. Iyakar kudu ta Gad za tă miƙe kudu daga Tamar zuwa ruwan Meriba Kadesh, sa’an nan ta bi Rafin Masar zuwa Bahar Rum.29. “Wannan ce ƙasar da za ku raba gādo ga kabilan Isra’ila, kuma wannan ne zai zama rabonsu,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.30. “Waɗannan za su zama ƙofofin birnin. “Farawa da gefen arewa, wanda yake da tsawon kamu 4,50031. za a ba wa ƙofofin birnin sunaye kabilan Isra’ila. Ƙofofi uku a gefen arewa za su zama ƙofar Ruben, ƙofar Yahuda da ƙofar Lawi.32. A gefen gabas, wanda yake da tsawon kamu 4,500 zai kasance da ƙofofi uku, ƙofar Yusuf, ƙofar Benyamin da ƙofar Dan.33. A gefen kudu, wanda yake da tsawon kamu 4,500, zai kasance da ƙofofi uku, ƙofar Simeyon, ƙofar Issakar da ƙofar Zebulun.34. A gefen yamma, wanda yake da tsawon kamun 4,500, zai kasance da ƙofofi uku, ƙofar Gad, ƙofar Asher da kuma ƙofar Naftali.35. “Duk nisan wurare kewaye da birnin zai zama kamu 18,000 ne. “Sunan birnin kuwa daga wannan lokaci zai zama, ‘ Ubangiji yana a nan.’ ”Zabura 135:8-148. Ya kashe ’ya’yan fari na Masar, ’ya’yan fari na mutane da na dabbobi.9. Ya aiko da alamu da abubuwan banmamaki a tsirkiyarku, ya Masar, a kan Fir’auna da kuma dukan bayinsa.10. Ya bugi al’ummai masu yawa ya kuma karkashe manyan sarakuna,11. Sihon sarkin Amoriyawa, Og sarkin Bashan da kuma dukan sarakunan Kan’ana,12. ya kuma ba da ƙasarsa kamar abin gādo, abin gādo ga mutanensa Isra’ila.13. Sunanka, ya Ubangiji, dawwammame ne har abada, sanin da aka yi maka, ya Ubangiji, yana nan cikin dukan zamanai.14. Gama Ubangiji zai nuna cewa mutanensa ba su da laifi ya kuma ji tausayin bayinsa.Karin Magana 29:9-99. In mai hikima ya je wurin shari’a da wawa, wawa kan yi ta fushi yana ta dariya, ba kuwa za a sami salama ba.1 Bitrus 4:1-191. Saboda haka, da yake Kiristi ya sha wahala a jikinsa, sai ku ma ku yi wa kanku ɗamara da irin wannan hali, gama wanda ya sha wahala a jikinsa ya gama da zunubi ke nan.2. Ta haka, ba ya sauran rayuwarsa a kan mugayen sha’awace-sha’awacen jiki, sai dai nufin Allah.3. Gama kun ɓata lokaci sosai a dā kuna yin abubuwan da masu bauta gumaka suka zaɓa su yi, kuna rayuwa cikin lalata, sha’awace-sha’awace, buguwa, shashanci, shaye-shaye da kuma bautar gumaka masu banƙyama.4. Sun yi mamaki da ba kwa haɗa kai da su a yanzu, da ba kwa kutsa kai tare da su cikin irin rayuwar banzan nan, har suna zaginku.5. Amma dole su ba da lissafi gare shi wanda yake a shirye yă shari’anta masu rai da matattu.6. Dalilin ke nan da ya sa aka yi wa’azin bishara har ga waɗanda yanzu suke mutattu, don ko da yake an hukunta su a matsayin mutane a batun jiki, amma su rayu ga Allah a batun ruhu.7. Ƙarshen abubuwa duka ya yi kusa. Saboda haka ku kasance masu tunani mai kyau da masu kamunkai don ku iya yin addu’a.8. Fiye da kome, ku ƙaunaci juna sosai, domin ƙauna tana rufe zunubai masu ɗumbun yawa.9. Ku riƙa karɓar juna ba da gunaguni ba.10. Kowa yă yi amfani da kowace baiwar da ya samu don kyautata wa waɗansu, cikin aminci yana aikata alherin Allah a hanyoyi dabam-dabam.11. In wani ya yi magana, ya kamata yă yi ta a matsayin wanda yake magana ainihin kalmomin Allah. In wani yana yin hidima, ya kamata yă yi ta da ƙarfin da Allah ya tanadar, domin a cikin kome a yabi Allah ta wurin Yesu Kiristi. A gare shi ɗaukaka da iko sun tabbata har abada abadin. Amin.12. Abokaina ƙaunatattu, kada ku yi mamakin gwaji mai tsananin da kuke sha, sai ka ce wani baƙon abu ne yake faruwa da ku.13. Sai dai ku yi murna cewa kuna tarayya cikin shan wahalolin Kiristi, domin ku kai ga farin ciki mai yawa sa’ad da aka bayyana ɗaukakarsa.14. In an zage ku saboda sunan Kiristi, ku masu albarka ne, gama Ruhun ɗaukaka da kuma na Allah yana bisanku.15. In kuna shan wahala, kada yă zama don ku masu kisankai ne ko ɓarayi ko masu wani irin laifi ko kuma masu shisshigi.16. Amma fa, in kuka sha wahala a matsayin ku Kirista ne, kada ku ji kunya, sai dai ku yabi Allah cewa kuna amsa wannan suna.17. Gama lokaci ya yi da za a fara yi wa iyalin Allah shari’a; in kuwa ya fara da mu, to, me zai faru da waɗanda ba sa biyayya da bisharar Allah?18. Kuma, “In da ƙyar masu adalci su kuɓuta, me zai faru da marasa tsoron Allah da kuma masu zunubi?”19. Saboda haka, waɗanda suke shan wahala bisa ga nufin Allah ya kamata su danƙa kansu ga Mahaliccinsu mai aminci, su kuma ci gaba da aikata abin da yake daidai. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.