Baibul a cikin shekara guda Nuwamba 4Makoki 3:1-661. Ni ne mutumin da ya ga azaba ta wurin bulalar fushin Ubangiji.2. Ya kore ni, ya sa na yi tafiya a cikin duhu maimakon a cikin haske;3. ba shakka, ya juya mini baya, yana gāba da ni sau da sau, dukan yini.4. Ya sa fatar jikina da naman jikina sun tsufa ya kuma karya ƙasusuwana.5. Ya yi mini kwanton ɓauna ya kuma kewaye ni da baƙin ciki da kuma wahala.6. Ya sa na zauna a cikin duhu kamar waɗanda suka mutu da jimawa.7. Ya kewaye ni yadda ba zan iya gudu ba; Ya daure ni da sarƙa mai nauyi.8. Ko lokacin da nake kira don neman taimako, ba ya jin addu’ata.9. Ya tare hanyata da tubula na duwatsu; ya sa hanyata ta karkace.10. Kamar beyar da take a laɓe tana jira, kamar zaki a ɓoye,11. ya janye ni daga kan hanya ya ɓatar da ni ya bar ni ba taimako.12. Ya ja kwarinsa ya sa in zama abin baratarsa.13. Ya harbi zuciyata da kibiyoyin kwarinsa.14. Na zama abin dariya ga mutanena duka; suna yi mini ba’a cikin waƙa dukan yini.15. Ya cika ni da kayan ɗaci ya gundure ni da abinci mai ɗaci.16. Ya kakkarya haƙorana da tsakuwa; ya tattake ni cikin ƙura.17. An hana ni salama; na manta da ko mene ne ake kira wadata.18. Saboda haka na ce, “Darajata ta ƙare da kuma duk abin da nake begen samu daga wurin Ubangiji.”19. Na tuna da azabata da kuma sintiri, da na yi ta yi da ɗacin rai.20. Na tuna su sosai, sai kuma na ji ba daɗi a raina.21. Duk da haka na tuna da wannan na kuma sa bege ga nan gaba.22. Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba; gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.23. Sababbi ne kowace safiya; amincinka kuwa mai girma ne.24. Na ce wa kaina, “ Ubangiji shi ne nawa; saboda haka zan jira shi.”25. Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke da bege a cikinsa, ga kuma wanda yake neman shi;26. yana da kyau ka jira shiru domin samun ceton Ubangiji.27. Yana da kyau mutum yă sha wuya tun yana yaro.28. Bari yă zauna shiru shi kaɗai, gama haka Ubangiji ya sa yă yi.29. Bari yă ɓoye fuskarsa cikin ƙura kila akwai bege.30. Bari yă ba da kumatunsa a mare shi, yă kuma bari a ci masa mutunci.31. Gama Ubangiji ba ya yashe mutane har abada.32. Ko da ya kawo ɓacin rai, zai nuna tausayi sosai, ƙaunarsa tana da yawa.33. Gama ba haka kawai yake kawo wahala ko ɓacin rai ga ’yan adam ba.34. Bai yarda a tattake ’yan kurkuku a ƙasa ba,35. ko kuma a danne wa mutum hakkinsa a gaban Maɗaukaki,36. ko kuma a danne wa mutum shari’ar gaskiya ashe Ubangiji ba zai ga irin waɗannan abubuwa ba?37. Wane ne ya isa yă yi magana kuma ta cika in ba Ubangiji ne ya umarta ba?38. Ba daga bakin Maɗaukaki ne bala’i da abubuwa masu kyau suke fitowa ba?39. Don mene ne wani mai rai zai yi gunaguni sa’ad da aka ba shi horo domin zunubansa?40. Bari mu auna tafiyarmu mu gwada ta, sai mu kuma koma ga Ubangiji.41. Bari mu ɗaga zuciyarmu da hannuwanmu ga Allah na cikin sama, mu ce,42. “Mun yi zunubi mun yi tawaye ba ka kuwa gafarta ba.43. “Ka rufe kanka da fushi, ka fafare mu; ka karkashe mu ba tausayi.44. Ka rufe kanka da gajimare don kada addu’armu ta kai wurinka.45. Ka mai da mu tarkace da juji a cikin mutane.46. “Dukan maƙiyanmu suna ta yin mana magana marar daɗi.47. Muna cika da tsoro, da lalatarwa da hallakarwa.”48. Hawaye na kwararowa daga idanuna domin an hallaka mutanena.49. Idanuna za su ci gaba da kwararowa da hawaye, ba hutawa.50. Har sai in Ubangiji ya duba daga sama ya gani.51. Abin da nake gani yana kawo mini baƙin ciki domin dukan matan birnina.52. Maƙiyana suna farauta ta ba dalili kamar tsuntsu.53. Sun yi ƙoƙari su kashe ni a cikin rami suka kuma jajjefe ni da duwatsu;54. ruwaye suka rufe kaina, sai na yi tunani cewa na kusa mutuwa.55. Na yi kira ga sunanka, ya Ubangiji, daga rami mai zurfi.56. Ka ji roƙona, “Kada ka toshe kunnuwanka ka ƙi jin roƙona na neman taimako.”57. Ka zo kusa lokacin da na kira ka, kuma ka ce mini, “Kada ka ji tsoro.”58. Ya Ubangiji, ka goyi bayana; ka fanshi raina.59. Ya Ubangiji, ka ga inda aka yi mini ba daidai ba. Ka shari’anta, ka ba ni gaskiya!60. Ka ga zurfin ramakonsu, da duk mugun shirin da suke yi mini.61. Ya Ubangiji, ka ji zaginsu, da duka mugun shirin da suke yi mini62. Abin da maƙiyana suke yin raɗa a kai game da ni duk yini.63. Dube su! A zaune ko a tsaye, suna yi mini ba’a cikin waƙoƙinsu.64. Ka ba su abin da ya dace su samu, ya Ubangiji, domin abin da hannuwansu suka yi.65. Ka sa yana ta rufe zuciyarsu, kuma bari la’anarka ta bi su.66. Ka fafare su cikin fushi ka hallaka su daga cikin duniya ta Ubangiji.Makoki 4:1-221. Zinariya ta rasa kyanta, hasken zinariya ya dushe! An warwatsar da tsarkakakkun duwatsu masu daraja a kan tituna.2. Dubi samarin Sihiyona masu daraja, waɗanda a dā darajarsu ta isa nauyin zinariya, yanzu ana ɗaukar su a matsayin tukwanen ƙasa, aikin maginin tukwane!3. Ko diloli suna ba ’ya’yansu nono su sha, amma mutanena sun zama marasa zuciya kamar jiminai a cikin jeji.4. Domin ƙishirwa harshen jarirai ya manne a rufin bakinsu; yaran suna roƙo a ba su burodi, amma ba wanda ya ba su.5. Waɗanda a dā sukan ci abinci mai daɗi yanzu su ne masu bara a tituna. Waɗanda a dā suke sa kaya masu kyau yanzu suna kwance a kan tarin toka.6. Horon mutanena ya fi na Sodom girma, wadda aka hallaka farat ɗaya ba wani hannu da ya juya ya taimake ta.7. ’Ya’yan sarakunansu sun fi ƙanƙara haske sun kuma fi madara fari, jikunansu sun fi murjani ja, kyansu kamar shuɗin yakutu.8. Amma yanzu sun fi dare duhu; ba a iya gane su a tituna. Fatar jikinsu ta manne da ƙasusuwansu; sun bushe kamar itace.9. Gara waɗanda aka kashe su da takobi da waɗanda suke mutuwa da yunwa; sun rame domin rashin abinci a gona.10. Da hannuwansu mata masu tausayi sun dafa yaransu, suka zama masu abinci sa’ad da aka hallaka mutanena.11. Ubangiji ya saki fushinsa; ya zuba zafin fushinsa. Ya hura wuta a Sihiyona ta kuma cinye harsashin gininta.12. Sarakunan duniya ba su gaskata ba, haka ma mutanen duniya, cewa magabta da maƙiya za su iya shiga ƙofofin Urushalima.13. Amma ya faru domin zunuban annabawanta da muguntar firistocinta, waɗanda suka zub da jinin masu adalci a cikinsu.14. Yanzu suna yawo barkatai a tituna kamar makafi. Sun ƙazantu da jini yadda ba wanda zai kuskura ya taɓa rigunansu.15. “Ku tafi! Ba ku da tsabta!” Haka mutane suke ihu suke ce musu. “Ku tashi daga nan! Ku tashi daga nan! Kada ku taɓa mu!” Sa’ad da suka gudu suna yawo, mutanen waɗansu ƙasashe suka ce, “Ba za su ci gaba da zama a nan ba.”16. Ubangiji kansa ya warwatsa su; ya daina duban su. Ba a ba firistoci girma, ba su ba dattawa gata.17. Idanunmu sun gaji, suna ta dubawa ko taimako zai zo; mu sa ido ko za mu ga ƙasar da za tă iya taimakon mu.18. Ana bin sawunmu, ba za mu iya tafiya kan tituna ba. Ƙarshenmu ya kusa, kwanakinmu sun ƙare, gama ƙarshenmu ya zo.19. Masu fafarar mu sun fi gaggafa mai firiya a sararin sama sauri; sun fafare mu a kan duwatsu suna fakon mu a jeji.20. Shafaffe na Ubangiji, numfashin ranmu, ya fāɗi cikin tarkonsu. Muna tunani cewa za mu iya rayuwa cikin sauran mutane a ƙarƙashin inuwarsa.21. Ku yi murna da farin ciki, ya Diyar Edom, ke mai zama a ƙasar Uz. Amma ke ma za a ba ki kwaf; za ki bugu ki zama tsirara.22. Ya Diyar Sihiyona, hukuncinki zai ƙare; ba zai sa zaman bautarki yă yi tsayi ba. Amma ya Diyar Edom, zai hukunta zunubinki yă tona tsiraicinki.Makoki 5:1-221. Ka tuna, ya Ubangiji, abin da ya faru da mu; duba, ka ga kunyar da muka sha.2. An ba wa baƙi gādonmu, gidajenmu kuma aka ba bare.3. Mun zama marayu marasa ubanni, uwayenmu kamar gwauraye.4. Dole mu sayi ruwan da muke sha; sai mun biya mu sami itace.5. Masu fafararmu sun kusa kama mu; mun gaji kuma ba dama mu huta.6. Mun miƙa kanmu ga Masar da Assuriya don mu sami isashen abinci.7. Kakanninmu sun yi zunubi kuma ba sa nan yanzu, mu ne aka bari muna shan hukuncinsu.8. Bayi suna mulki a kanmu, kuma ba wanda zai ’yantar da mu daga hannuwansu.9. Muna samun burodi a bakin rayukanmu domin takobin da yake a jeji.10. Fatar jikinmu ta yi zafi kamar murhu, muna jin zazzaɓi domin yunwa.11. An yi wa mata fyaɗe a cikin Sihiyona, da kuma budurwai a cikin garuruwan Yahuda.12. An rataye ’ya’yan sarakuna da hannuwansu; ba a ba wa dattawa girma.13. Samari suna faman yin niƙa; yara kuma suna fama da ƙyar da nauyin kayan itace.14. Dattawan sun bar ƙofar birnin, samari sun daina rera waƙa.15. Farin ciki ya rabu da zuciyarmu; rayuwarmu ta zama makoki.16. Rawani ya fāɗi daga kanmu. Kaiton mu gama mun yi zunubi!17. Domin wannan zuciyarmu ta yi sanyi; domin waɗannan abubuwa idanunmu sun dushe18. gama Tudun Sihiyona ya zama kufai, sai diloli ke yawo a wurin.19. Ya Ubangiji, kai ne mai iko har abada; kursiyinka ya dawwama cikin dukan zamani.20. Don mene ne kake mantawa da mu koyaushe? Me ya sa ka yashe mu da jimawa?21. Ka sāke jawo mu gare ka, ya Ubangiji, don mu komo; ka sabunta kwanakinmu su zama kamar yadda suke a dā22. sai dai in ka ƙi mu gaba ɗaya kana fushi da mu fiye da yadda za a iya aunawa.Zabura 119:145-152145. Na yi kira da dukan zuciyata; ka amsa mini, ya Ubangiji, zan kuwa yi biyayya da ƙa’idodinka.146. Na yi kira gare ka; ka cece ni zan kuwa kiyaye farillanka.147. Na tashi kafin fitowar rana na kuma yi kukan neman taimako; na sa zuciyata a maganarka.148. Ban rufe idanuna ba dukan dare, don in yi tunani a kan alkawuranka.149. Ka ji muryata bisa ga ƙaunarka; ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga dokokinka.150. Waɗanda suke ƙirƙiro mugayen dabaru suna nan kusa, amma suna nesa da dokarka.151. Duk da haka kana kusa, ya Ubangiji, kuma dukan umarnanka gaskiya ne.152. Tun tuni na koyi daga farillanka cewa ka kafa su su kasance har abada.Karin Magana 28:11-1111. Mai arziki zai yi zato shi mai hikima ne a ganinsa, amma matalauci mai basira ya fi shi sanin abin da yake daidai.Filemon 1:1-251. Bulus, ɗan kurkuku saboda Kiristi Yesu, da kuma Timoti ɗan’uwanmu, Zuwa ga Filemon ƙaunataccen abokinmu da kuma abokin aikinmu,2. zuwa kuma ga Affiya ’yar’uwarmu, zuwa kuma ga Arkiffus abokin famarmu, da zuwa kuma ga ikkilisiyar da take taruwa a gidanka.3. Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.4. Kullum nakan gode wa Allahna sa’ad da nake tuna da kai cikin addu’o’ina,5. domin ina jin labari bangaskiyarka cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunarka da kake yi saboda dukan tsarkaka.6. Ina addu’a ka zama mai ƙwazo cikin shaida bangaskiyarka, domin ka sami cikakken fahimta ta kowane abin da yake nagarin da muke da shi cikin Kiristi.7. Ƙaunarka ta sa ni farin ciki ƙwarai ta kuma ƙarfafa ni, domin kai, ɗan’uwa, ka wartsake zukatan tsarkaka.8. Saboda haka, ko da yake cikin Kiristi ina iya yin ƙarfin hali in umarce ka ka yi abin da ya kamata,9. duk da haka ina roƙonka saboda ƙauna, na fi so in roƙe ka, ni Bulus tsoho, a yanzu kuma ga ni ɗan sarƙa saboda Kiristi Yesu.10. Ina roƙonka saboda ɗana Onesimus, wanda ya zama ɗana yayinda nake cikin sarƙoƙi.11. Dā kam, ba shi da amfani a gare ka, amma yanzu ya zama da amfani a gare ka da kuma gare ni.12. Ina aike shi yă koma gare ka, shi da yake zuciyata.13. Na so in riƙe shi a wurina a madadinka domin yă taimake ni yayinda nake cikin sarƙoƙi saboda bishara.14. Sai dai ban so in yi kome ban da yardarka ba, domin kowane alherin da za ka yi, yă fito daga zuciyarka, ba na tilas ba.15. Wataƙila abin da ya sa aka raba ka da shi na ɗan lokaci ƙanƙani shi ne don ka same shi da amfani16. ba kamar bawa kuma ba, sai dai fiye da bawa, a matsayin ƙaunataccen ɗan’uwa. Shi ƙaunatacce ne sosai a gare ni amma a gare ka ya ma fi zama ƙaunatacce, kamar mutum da kuma kamar ɗan’uwa a cikin Ubangiji.17. Saboda haka in ka ɗauke ni a kan ni abokin tarayya ne, sai ka marabce shi kamar yadda za ka marabce ni.18. In ya yi maka wani laifi ko kuma yana riƙe maka wani bashi, sai ka mai da shi a kaina.19. Ni, Bulus, nake rubuta wannan da hannuna. Zan biya ka, kada ma a yi zancen ranka da kake riƙe mini bashi.20. Ina fata, ɗan’uwa, zan sami amfani daga gare ka cikin Ubangiji; ka wartsake zuciyata cikin Kiristi.21. Da tabbacin biyayyarka, ina rubuta maka, da sanin za ka yi fiye da abin da na ce.22. Abu guda ya rage, ka shirya mini masauƙi, domin ina bege za a mayar da ni gare ku albarkacin addu’o’inku.23. Efafaras, abokin tarayyata a kurkuku cikin Kiristi Yesu, yana gaishe ka.24. Haka kuma Markus, Aristarkus, Demas da kuma Luka, abokan aikina.25. Alherin Ubangiji Yesu Kiristi yă kasance da ruhunku. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.