Baibul a cikin shekara guda Nuwamba 6Ezekiyel 3:1-271. Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ci abin da yake a gabanka, ka ci wannan littafi; sa’an nan ka tafi ka yi magana wa gidan Isra’ila.”2. Saboda haka na buɗe bakina, ya kuma ba ni littafin in ci.3. Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ci wannan littafin da nake ba ka, ka kuma cika cikinka da shi.” Sai na ci shi, ya kuma yi zaki kamar zuma a bakina.4. Sa’an nan ya ce mini, “Ɗan mutum, yanzu ka tafi gidan Isra’ila ka faɗa kalmomina gare su.5. Ba ina aikan ka wurin mutanen da suke da baƙon harshe da kuma yare mai wuya ba ne, amma zuwa ga gidan Isra’ila ne,6. ba ga mutane da yawa na baƙon harshe da yare mai wuya, waɗanda ba ka san kalmominsu ba. Tabbatacce da na aike ka wurin irinsu, da sun saurare ka.7. Amma gidan Isra’ila ba sa niyya su saurare ka domin ba sa niyya su saurare ni, gama dukan gidan Isra’ila sun taurare suna kuma kin ji.8. Amma zan sa ka zama mai taurinkai da taurin zuciya kamar su.9. Zan sa goshinka ya zama da tauri kamar dutse, da tauri fiye da dutsen ƙanƙara ƙarfi. Kada ka ji tsoronsu ko ka firgita ta wurinsu, ko da yake su gidan ’yan tawaye ne.”10. Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ji da kyau ka kuma lura da dukan kalmomin da nake maka magana.11. Ka tafi yanzu zuwa ga ’yan’uwanka waɗanda suke zaman bauta ka yi musu magana. Ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,’ ko ku ji, ko kada ku ji.”12. Sa’an nan Ruhu ya ɗaga ni sama, a bayana na ji wata karar babban motsi na cewa, Bari a yabi ɗaukakar Ubangiji a wurin zamansa!13. Karar fikafikan rayayyun halittun nan ne suke goge junansu da kuma karar da’irorin nan da suke kusa da su, ƙarar babban motsi.14. Sa’an nan Ruhu ya ɗaga ni sama ya kuma tafi da ni, na kuwa tafi da ɓacin rai da kuma fushin ruhuna, tare da hannu mai ƙarfi na Ubangiji a bisa na.15. Na zo wurin masu zaman bautan da suke zama a Tel Abib kusa da Kogin Kebar, A can kuwa, inda suke zama, na zauna a cikinsu kwana bakwai, ina mamaki.16. A ƙarshen kwana bakwai ɗin maganar Ubangiji ta zo mini cewa,17. “Ɗan mutum, na mai da kai mai tsaro don gidan Isra’ila; saboda haka ka ji maganar da zan yi ka kuma yi musu kashedin nan da ya fito daga gare ni.18. In na ce wa mugu, ‘Lalle za ka mutu,’ ba ka kuwa yi masa kashedi ko ka tsawata masa a kan mugayen hanyoyinsa don yă ceci ransa ba, wannan mugun zai mutu saboda zunubinsa, zan kuwa nemi hakkin jininsa a hannunka.19. Amma in ka yi wa mugun kashedi bai kuwa juya daga mugayen hanyoyinsa ba, zai mutu saboda zunubinsa; amma kai kam za ka kuɓuta.20. “Har yanzu, in mai adalci ya juya daga adalcinsa ya aikata mugunta, na kuma sa abin tuntuɓe a gabansa, zai mutu. Da yake ba ka yi masa kashedi ba, zai mutu saboda zunubinsa. Ba za a tuna da abin adalcin da ya yi ba, zan kuwa nemi hakkin jininsa a hannunka.21. Amma in ka yi wa mai adalcin kashedi kada yă yi zunubi bai kuwa yi zunubi ba, tabbatacce zai rayu saboda ya ji kashedin, kuma kai kam za ka kuɓuta.”22. Hannun Ubangiji ya kasance a kaina a can, ya kuma ce mini, “Tashi ka fita zuwa fili, a can kuwa zan yi maka magana.”23. Saboda haka na tashi da tafi fili. Ɗaukakar Ubangiji kuwa ta tsaya a can, kamar ɗaukakar da na gani kusa da Kogin Kebar, sai na fāɗi rubda ciki.24. Sai Ruhu ya sauko a kaina ya kuma ɗaga ni na tsaya a ƙafafuna. Ya yi mini magana ya ce, “Ka fita, ka rufe kanka a cikin gida.25. Kuma kai, ɗan mutum, za su ɗaura ka da igiyoyi; za a daure ka yadda ba za ka iya fita a cikin mutane ba.26. Zan sa harshenka ya manne wa dasashinka don ka yi shiru ka kuma kāsa tsawata musu, ko da yake su gidan ’yan tawaye ne.27. Amma sa’ad da na yi maka magana, zan buɗe bakinka za ka kuwa faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya faɗa.’ Duk mai ji ya ji, kuma duk wanda ya ƙi ji, ya ƙi ji; gama su gida ne na ’yan tawaye.Ezekiyel 4:1-171. “Yanzu, ɗan mutum, ka ɗauki tubalin yumɓu, ka ajiye shi a gabanka ka kuma zāna birnin Urushalima a kansa.2. Sa’an nan ka yi mata ƙawanya. Ka kafa mata katangar ƙawanya, ka gina katangar da ɗan tudu ka kewaye ta da dundurusai.3. Sa’an nan ka ɗauki kwanon ƙarfe, ka shirya shi kamar katangar ƙarfe tsakaninka da birnin ka kuma zuba mata ido. Za tă kasance a ƙarƙashin ƙawanya, kai kuwa za ka yi mata ƙawanya. Wannan zai zama alama ga gidan Isra’ila.4. “Sa’an nan ka kwanta a hagunka ka kuma sa zunubin gidan Isra’ila a kanka. Za ka ɗauki zunubinsu na waɗansu kwanakin da kake kwance a gefenka.5. Na ɗora maka kwanaki bisa ga shekarun zunubinsu. Saboda haka cikin kwana 390 za ka ɗauki zunubin gidan Isra’ila.6. “Bayan ka gama haka, ka sāke kwantawa, a wannan lokaci a gefen damarka, ka kuma ɗauki zunubin gidan Yahuda. Na ɗora maka kwanaki 40, kwana guda a madadin shekara guda.7. Ka juya fuskarka wajen ƙawanyar Urushalima da hannunka a buɗe ka yi annabci a kanta.8. Zan ɗaura ka da igiyoyi don kada ka juya daga wannan gefe zuwa wani gefe sai ka gama kwanakin ƙawanyarka.9. “Ka ɗauki alkama da sha’ir, wake da acca, gero da maiwa; ka sa su a tulun ajiya ka kuma yi amfani da su don yin burodi wa kanka. Za ka ci shi a kwanaki 390 da za ka kwanta a gefenka.10. Ka auna shekel ashirin na abinci don kowace rana ka kuma ci shi a ƙayyadadden lokaci.11. Haka ma ka auna kashi ɗaya bisa shida na garwan ruwa ka sha shi a ƙayyadadden lokaci.12. Ka ci abinci yadda za ka ci ƙosai sha’ir, ka gasa shi a gaban mutane, ka yi amfani da najasar mutane kamar itacen wuta.”13. Ubangiji ya ce, “Ta haka mutanen Isra’ila za su ci ƙazantaccen abinci a cikin al’ummai inda zan kore su in kai.”14. Sai na ce, “Ba haka ba ne, Ubangiji Mai Iko Duka! Ban taɓa ƙazantar da kaina ba. Daga ƙuruciyata har zuwa yanzu ban taɓa cin wani abin da aka samu ya mutu ko abin da namun jeji suka kashe ba. Ba nama marar tsabtan da ya taɓa shiga bakina.”15. Sai ya ce, “To da kyau, zan bari ka gasa burodin a kan kashin shanu a maimakon najasar mutane.”16. Sa’an nan ya ce mini, “Ɗan mutum, zan yanke tanadin abinci a Urushalima. Mutane za su auna abincin da za su ci da tsoro su kuma auna ruwan da za su sha cikin fargaba,17. domin abinci da ruwa za su kāsa. Za su damu da ganin juna za su kuma lalace saboda zunubinsu.Zabura 119:161-168161. Masu mulki suna tsananta mini ba dalili, amma zuciyata na rawan jiki game da maganarka.162. Ina farin ciki da alkawarinka kamar yadda wani kan sami ganima mai girma.163. Na ƙi ina kuma ƙyamar ƙarya amma ina ƙaunar dokarka.164. Sau bakwai a rana ina yabonka saboda dokokinka masu adalci.165. Waɗanda suke ƙaunar dokarka suna da babban salama, kuma babu abin da zai sa su yi tuntuɓe.166. Ina jiran cetonka, ya Ubangiji, ina kuma bin umarnanka.167. Ina biyayya da farillanka, gama ina ƙaunarsu ƙwarai.168. Ina biyayya da farillanka da kuma koyarwarka, gama dukan hanyoyina sanannu ne gare ka.Karin Magana 28:13-1313. Duk wanda ya ɓoye zunubansa ba ya taɓa cin nasara, amma duk wanda ya furta ya kuma ƙi su yakan sami jinƙai.Ibraniyawa 2:1-181. Dole mu ƙara mai da hankali sosai ga abubuwan da muka ji, don kada mu kauce.2. Gama in saƙon da aka faɗi ta bakin mala’iku ya zama tabbatacce, kuma kowane ƙeta umarni da rashin biyayya suka karɓi sakamakonsu da ya dace,3. yaya za mu tsira in muka ƙyale irin wannan babban ceto? Wannan ceto, wanda Ubangiji ne ya fara sanar, aka kuma tabbatar mana ta bakin waɗanda suka ji shi.4. Allah shi ma ya shaida ta wurin alamu, abubuwan banmamaki da mu’ujizai iri-iri, da kuma baye-bayen Ruhu Mai Tsarki da aka rarraba bisa ga nufinsa.5. Ba ga mala’iku ba ne ya sa su yi mulkin duniya mai zuwa, wanda muke magana a kai ba.6. Amma akwai wani wurin da wani ya shaida cewa, “Mene ne mutum, da kake tuna da shi, ɗan mutum da kake kula da shi?7. Ka sa shi ƙasa kaɗan da darajar mala’iku; ka naɗa shi da ɗaukaka da girma,8. ka kuma sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa.” Ta wurin sa kome a ƙarƙashinsa, Allah bai bar wani abu da bai sa a ƙarƙashinsa ba. Duk da haka a yanzu ba mu ga kowane abu a ƙarƙashinsa ba.9. Sai dai muna ganin Yesu, wanda aka mai da shi ƙasa kaɗan da darajar mala’iku, yanzu kuwa an naɗa shi da ɗaukaka da girma domin yă sha wahalar mutuwa, domin ta wurin alherin Allah yă ɗanɗana mutuwa saboda kowa.10. Ta wurin kawo ’ya’ya masu yawa zuwa ga ɗaukaka, ya dace cewa Allah, wanda dominsa da kuma ta wurinsa ne kome yake kasancewa, ya sa tushen cetonsu yă zama cikakke ta wurin shan wahala.11. Da shi wanda yake tsarkake mutane da kuma su waɗanda ake tsarkakewa duk ’yan iyali ɗaya ne. Saboda haka Yesu ba ya kunyan kiransu ’yan’uwansa.12. Ya ce, “Zan sanar da sunanka ga ’yan’uwana; a gaban jama’a zan rera yabonka.”13. Har wa yau ya ce, “Zan dogara gare shi.” Ya kuma ce, “Ga ni, da ’ya’yan da Allah ya ba ni.”14. Da yake ’ya’yan suna da nama da jini, shi ma sai ya ɗauki kamanninsu na mutum domin ta wurin mutuwarsa yă hallaka wanda yake riƙe da ikon mutuwa, wato, Iblis15. ya kuma ’yantar da waɗanda dukan rayuwarsu tsoron mutuwa ya riƙe su cikin bauta.16. Gama tabbatacce ba mala’iku ne ya taimaka ba, sai dai zuriyar Ibrahim.17. Saboda wannan dole a mai da shi kamar ’yan’uwansa ta kowace hanya, domin yă zama babban firist mai aminci da mai jinƙai cikin hidima ga Allah, yă kuma miƙa hadayar sulhu saboda zunuban mutane.18. Domin shi kansa ya sha wahala sa’ad da aka gwada shi, yana iya taimakon waɗanda ake yi wa gwaji. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.