Baibul a cikin shekara guda Nuwamba 8Ezekiyel 7:1-271. Maganar Ubangiji ta zo gare ni cewa,2. “Ɗan mutum, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yake cewa wa ƙasar Isra’ila, “ ‘Ƙarshe ya zo! Ƙarshe ya zo a kan kusurwoyi huɗu na ƙasar.3. Ƙarshe yanzu yana a kanki. Zan fashe fushina a kanki. Zan shari’anta ki bisa ga halinki in sāka miki kuma saboda dukan ayyukan banƙyamar da kika yi.4. Ba zan dube ki da tausayi; ko in ƙyale ki ba. Tabbatacce zan sāka miki saboda halinki da kuma ayyukanki masu banƙyama a cikinki. Sa’an nan za ki san cewa ni ne Ubangiji.’5. “Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Masifa! Masifar da ba a taɓa gani ba tana zuwa.6. Ƙarshe ya zo! Ƙarshe ya zo! Ya farka a kanki. Ga shi, ya zo!7. Ƙaddara ta auko miki, ya ke wadda ke zama cikin ƙasar. Lokaci ya yi, rana ta gabato; akwai fargaba, ba farin ciki ba, a kan duwatsu.8. Ina gab da fasa hasalata a kanki in kuma aukar da fushina a kanki; zan shari’anta ke bisa ga halinki in kuma sāka miki saboda dukan ayyukanki masu banƙyama.9. Ba zan dube ki da tausayi ko in ƙyale ke ba; zan sāka miki bisa ga halinki da kuma ayyukan masu banƙyama a cikinki. Sa’an nan za ki san cewa ni ne Ubangiji wanda yake bugunki.10. “ ‘Ga shi ranar ta zo! Ta iso! Ƙaddararki ta keto, sandar ta yi toho, girman kai ya yi fure!11. Rikici ya yi girma ya zama sandar da za a hukunta mugunta; babu wani daga cikin mutanen da za a bari, babu wani dukiyarsu da za a bari, babu wani abin amfani.12. Lokaci ya yi! Ranar ta gabato! Kada mai saya ya yi farin ciki ko kuwa mai sayarwa ya yi baƙin ciki, gama hasala tana a kan dukan jama’a.13. Mai sayarwa ba zai mayar da ƙasar da ya sayar tuntuni ba muddin dukansu suna da rai, gama ba za a sauya wahayin da ya shafi dukan jama’a ba. Saboda zunubansu, babu ɗayansu da zai adana ransa.14. “ ‘Ko da yake suna busa ƙaho suna kuma shirya kome, ba wanda zai tafi yaƙi, gama hasalata tana a kan dukan jama’a.15. A waje takobi ne, a ciki annoba ne da yunwa; waɗanda suke fili za su mutu ta wurin takobi, waɗanda kuma suke cikin birni yunwa da annoba za su cinye su.16. Duk waɗanda suka tsira suka tsere za su kasance a cikin duwatsu, suna kuka kamar kurciyoyin kwaruruka, kowanne saboda zunubansa.17. Kowane hannu zai raunana, kowace gwiwa kuma za tă zama marar ƙarfi kamar ruwa.18. Za su sa tufafin makoki su kuma rufu da fargaba. Fuskokinsu kuma za su rufu da kunya a kuma aske kawunansu.19. “ ‘Za su zubar da azurfarsu a tituna, zinariyarsu kuma za tă zama ƙazantacciyar aba. Azurfarsu da zinariyarsu ba za su iya cetonsu a ranar hasalar Ubangiji ba. Ba za su ƙosar da yunwansu ko su cika cikinsu da shi ba, gama su ne sanadin tuntuɓensu cikin zunubi.20. Sun yi fariya kyan kayan adonsu suka kuma yi amfani da su don su yi gumakansu masu banƙyama, da ƙazantattun abubuwa.21. Zan ba da su duka kamar ganima ga baƙi da kuma kamar abin da aka washe ga mugayen duniya, za su kuma ƙazantar da su.22. Zan juye fuskata daga gare su, za su kuwa ƙazantar da wurina mai daraja; ’yan fashi za su shiga su kuma ƙazantar da shi.23. “ ‘Ka shirya sarƙoƙi, domin ƙasar ta cika da alhakin jini, birnin kuma ya cika da rikici.24. Zan kawo al’ummai mafi mugunta su mallaki gidajenku; zan kawo ƙarshen fariyar masu ƙarfi, Wurare Masu Tsarkinsu za su ƙazantu.25. Sa’ad da wahala ta zo, za su nemi salama, amma ba za su same ta ba.26. Masifa a kan masifa za su zo, jita-jita kuma a kan jita-jita. Za su yi ƙoƙarin samun wahayi daga annabi; koyarwar doka ta wurin firist za tă ɓace, kamar yadda shawarar dattawa za tă ɓace.27. Sarki zai yi makoki, yerima zai fid da zuciya, hannuwan mutanen ƙasar kuma za su yi rawa. Zan sāka musu bisa ga ayyukansu, zan kuma hukunta su bisa ga ma’auninsu. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.’ ”Ezekiyel 8:1-181. A shekara ta shida, a wata shida a ranar ta biya, yayinda nake zaune a gidana dattawan Yahuda kuma suna zaune a gabana, hannun Ubangiji Mai Iko Duka ya zo a kaina a can.2. Na duba, sai na ga siffa kamar na mutum. Daga kwankwaso zuwa ƙasa ya yi kamar wuta, kuma daga kwankwaso zuwa sama kamanninsa ya yi haske yana ƙyalli kamar ƙarfe mai haske.3. Ya miƙa abin da ya yi kamar hannu ya kama a gashin kaina. Ruhu ya ɗaga ni tsakanin sama da ƙasa, a cikin wahayoyi kuma Allah ya ɗauke ni zuwa Urushalima, zuwa ƙofa zuwa gabas na cikin fili, inda gunki mai tsokanar kishi yake tsaye.4. A can gabana kuwa ga ɗaukakar Allah na Isra’ila, kamar a wahayin da na gani a fili.5. Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, duba waje arewa.” Sai na duba, a mashigin arewa na ƙofar bagaden kuwa na ga wannan gunki na tsokanar kishi.6. Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ga abin da suke yi, abubuwan banƙyamar da gidan Isra’ila ke yi a nan, abubuwan da za su kore ni daga wuri mai tsarkina? Amma za ka ga abubuwan da suka ma fi banƙyama.”7. Sa’an nan ya kawo ni mashigin filin. Na duba, na kuma ga rami a bango.8. Ya ce mini, “Ɗan mutum, yanzu ka haƙa cikin bangon.” Da na haƙa cikin bangon sai na ga ƙofar shiga a can.9. Sai ya ce mini, “Shiga ka ga mugaye da kuma abubuwa banƙyamar da suke yi a can.”10. Na kuwa shiga na duba, sai na ga zāne-zāne ko’ina a bangon na kowane irin abubuwa masu rarrafe da kuma dabbobi masu ƙazanta da dukan gumakan gidan Isra’ila.11. A gabansu ga dattawa saba’in na gidan Isra’ila tsaye a cikinsu, Ya’azaniya ɗan Shafan kuwa yana tsaye a cikinsu. Kowa yana da farantin ƙona turare a hannunsa, tulin hayaƙin turare mai ƙanshi ya tunnuƙe zuwa sama.12. Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ga abin da dattawan gidan Isra’ila suke yi a cikin duhu, kowa yana a ɗakin tsafin gunkinsa? Suna cewa, ‘ Ubangiji ba ya ganinmu; Ubangiji ya yashe ƙasar.’ ”13. Ya kuma ce, “Za ka gan su suna yin abubuwan da suka fi waɗannan banƙyama.”14. Sa’an nan ya kawo ni mashigin arewa na ƙofar gidan Ubangiji, sai na ga mata zaune a can, suna makokin Tammuz.15. Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ga wannan? Za ka ga abubuwan da suke masu banƙyama fiye da wannan.”16. Sa’an nan ya kawo ni cikin fili na cikin gidan Ubangiji, a can kuwa a ƙofar haikali, tsakanin shirayi da bagade, akwai kamar mutum ashirin da biyar. Suka ba haikalin Ubangiji baya suna fuskanta wajen gabas, suna rusuna wa rana a gabas.17. Ya ce mini, “Ka ga wannan, ɗan mutum? Ƙaramin abu ne gidan Yahuda su yi abubuwan banƙyamar da suke yi a nan? Dole ne su cika ƙasar da rikici su kuma ci gaba da tsokane ni in yi fushi? Dube su suna tsokanata!18. Saboda haka zan hukunta su cikin fushi; Ba zan dube su da tausayi ko kuwa in ƙyale su ba. Ko da yake suna ihu a kunnuwana, ba zan saurare su ba.”Zabura 120:1-71. Na yi kira ga Ubangiji cikin damuwata, ya kuwa amsa mini.2. Ka cece ni, ya Ubangiji, daga leɓuna masu ƙarya da kuma daga harsuna masu yaudara.3. Me zai yi maka, me kuma ya fi, ya kai harshe mai yaudara?4. Zai hukunta ku da kibiyoyi masu tsini na jarumi, tare da garwashin wuta na itacen tsintsiya.5. Kaitona da nake zama a Meshek, da nake zama a ciki tentunan Kedar!6. Da daɗewa na zauna a cikin waɗanda suke ƙin salama.7. Ni mutum ne mai salama; amma sa’ad da na yi magana, su sai su yi ta yaƙi.Karin Magana 28:15-1515. Kamar rurin zaki ko sanɗar beyar haka mugun mutum mai mulki a kan mutane marasa ƙarfi yake.Ibraniyawa 4:1-161. Saboda haka, da yake alkawarin shiga hutunsa yana nan har yanzu, sai mu yi hankali kada waninku yă kāsa shiga.2. Gama mu ma mun ji an yi mana wa’azin bishara, kamar yadda su ma suka ji; sai dai saƙon da suka ji ba tă amfane su ba, domin waɗanda suka ji ba su karɓe shi da bangaskiya ba.3. Mu kam da muka gaskata mu ne muka shiga wannan hutu, kamar yadda Allah ya ce, “Saboda haka na yi rantsuwa cikin fushina, ‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ” Allah ya faɗa haka ko da yake ya riga ya kammala aikinsa tun halittar duniya.4. Gama a wani wuri ya yi magana a kan rana ta bakwai cikin waɗannan kalmomi, “A rana ta bakwai kuwa Allah ya huta daga dukan aikinsa.”5. Haka kuma a nassin nan ya ce, “Ba za su taɓa shiga hutuna ba.”6. Har yanzu dai da sauran dama domin waɗansu su shiga, su kuwa waɗanda aka fara yi wa albishirin nan sun kāsa shiga saboda rashin biyayya.7. Saboda haka Allah ya sāke sa wata rana, yana kiranta Yau, bayan wani dogon lokaci Allah ya yi magana ta bakin Dawuda, yadda aka riga aka faɗa, “Yau, in kuka ji muryarsa, kada ku taurare zukatanku.”8. Gama da a ce Yoshuwa ya ba su hutu, da Allah bai yi magana daga baya a kan wata rana dabam ba.9. Har yanzu, akwai wani hutun Asabbacin da ya rage domin mutanen Allah;10. gama duk wanda ya shiga hutun Allah, shi ma yakan huta daga nasa aiki, kamar yadda Allah ya huta daga nasa.11. Saboda haka, bari mu yi iyakacin ƙoƙarinmu mu shiga wannan hutu, don kada wani yă kāsa ta wurin bin gurbinsu na rashin biyayya.12. Maganar Allah tana da rai, tana kuma da ƙarfin aiki. Ta fi kowane takobi mai baki biyu kaifi. Maganarsa takan ratsa har ciki-ciki, tana raba rai da ruhu, gaɓoɓi da kuma ɓargon ƙashi; har sai ta tone ainihi wane ne muke.13. Babu wani abu cikin dukan halittar da yake ɓoye daga fuskar Allah. Kowane abu a buɗe yake yana kuma a shimfiɗe a idanun wanda dole mu ba da lissafi a gare shi.14. Saboda haka, da yake muna da babban firist mai girma wanda ya ratsa sama, Yesu Ɗan Allah, bari mu riƙe bangaskiyan nan wadda muke shaidawa da ƙarfi.15. Gama babban firist da muke da shi ba marar juyayin kāsawarmu ba ne, amma muna da wanda aka gwada ta kowace hanya, kamar dai yadda akan yi mana, duk da haka bai yi zunubi ba.16. Saboda haka sai mu matso kusa da kursiyin alheri da ƙarfi zuciya, don mu sami jinƙai mu kuma sami alherin da zai taimake mu a lokacin bukata. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.