Baibul a cikin shekara guda Disamba 14Amos 4:1-131. Ku kasa kunne ga wannan, ya ku shanun Bashan a kan Dutsen Samariya, ku matan da kuke cin zalin matalauta, kuke kuma danne matalauta, kuna kuma ce wa mazanku, “Ku kawo mana abin sha!”2. Ubangiji Mai Iko Duka ya rantse da tsarkinsa. “Tabbatacce lokaci yana zuwa da za a jawo ku da ƙugiyoyi, na ƙarshenku za a kama da ƙugiyar kifi.3. Dukanku za ku wuce ta kai tsaye ta inda katangar ta tsage, za a jefar da ku a Harmon,” in ji Ubangiji.4. “Ku tafi Betel ku yi ta aikata zunubi; ku je Gilgal ku ƙara yin zunubi. Ku kawo hadayunku kowace safiya, zakkarku kowace shekara uku.5. Ku ƙona burodinku mai yisti kamar hadaya ta godiya, ku yi fariya game da hadayunku na yarda rai, ku yi taƙama game da su, ya ku Isra’ilawa, gama abin da kuke jin daɗin aikata ke nan,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.6. “Na bar ku da yunwa a kowace birni, da kuma rashin abinci a kowane gari, duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” in ji Ubangiji.7. “Na kuma hana muku ruwan sama tun shuke-shuken suna wata uku kafin lokacin girbi. Na sa aka yi ruwan sama a wani gari, sai na hana a yi a wani gari. Wata gona ta sami ruwan sama; wata gona kuma ta bushe.8. Mutane suna tangaɗi daga gari zuwa gari suna neman ruwa amma ba su sami isashen ruwan sha ba, duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” in ji Ubangiji.9. “Sau da yawa na ɓata gonakinku da fumfuna da kuma cuta. Fāri suka cinye itatuwanku na inabi da na ɓaure, da na zaitun duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” in ji Ubangiji.10. “Na aiko muku annoba yadda na yi a Masar. Na karkashe samarinku da takobi, tare da kamammun dawakanku. Na cika hancinku da warin sansaninku, duk da haka ba ku juyo gare ni ba” in ji Ubangiji.11. “Na hallaka waɗansunku kamar yadda na hallaka Sodom da Gomorra. Kuna kama da itace mai cin wutar da na cire daga cikin wuta, duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” in ji Ubangiji.12. “Saboda haka ga abin da zan yi da ku, ya Isra’ila, don kuwa zan yi muku haka, sai ku yi shirin gamuwa da Allahnku, ya Isra’ila.”13. Shi wanda ya yi duwatsu, ya halicci iska, ya kuma bayyana wa mutum tunaninsa, shi wanda ya juya safiya ta zama duhu yana takawa a wurare masu tsawo na duniya, Ubangiji Allah Maɗaukaki ne sunansa.Amos 5:1-271. Ku ji wannan magana, ya gidan Isra’ila, ina makokin nan dominku.2. “Budurwa Isra’ila ta fāɗi, ba za tă ƙara tashi ba, an yashe ta a ƙasarta, ba wanda zai ɗaga ta.”3. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “Birnin da ta fitar da masu ƙarfi dubbai don Isra’ila guda ɗari kaɗai za su dawo; garin da ya fitar da masu ƙarfi ɗari kuwa goma kaɗai za su dawo.”4. Ga abin da Ubangiji ya ce wa gidan Isra’ila. “Ku neme ni ku rayu;5. kada ku nemi Betel, kada ku je Gilgal, kada ku yi tafiya zuwa Beyersheba. Gama ba shakka Gilgal za tă tafi bauta, za a kuwa mai da Betel ba kome ba.”6. Ku nemi Ubangiji ku kuma rayu, ko kuwa zai ratsa yă share gidan Yusuf kamar wuta; zai cinye Betel kuwa ba zai sami wanda zai kashe ta ba.7. Ku ne masu mai da gaskiya ta koma ɗaci ku kuma zubar da adalci.8. (Shi wanda ya yi Taurarin nan da ake ce Kaza da ’Ya’yanta da kuma Mai Farauta da Kare, wanda ya mai da duhu ya zama haske ya kuma baƙanta rana ta zama dare, yakan kwashe ruwan teku ya zubar a ƙasa, Ubangiji ne sunansa,9. yakan kawo hallaka a mafaka mai ƙarfi yakan kuma mai da birnin mai katanga ya zama kufai).10. Ba ku son mai yin gaskiya a ɗakin shari’a kuna ƙin mai faɗar gaskiya.11. Kuna matsa wa matalauta kuna sa su dole su ba ku hatsi. Saboda haka, ko da yake kun gina gidajen duwatsu, ba za ku zauna a cikinsu ba; ko da yake kun nome gonaki masu kyau, ba za ku sha ruwan inabinsu ba.12. Gama na san yawan laifofinku da kuma girman zunubanku. Kuna danne masu adalci kuna kuma cin hanci kuna kuma hana a yi wa matalauta shari’ar adalci a majalisa.13. Saboda haka mai hankali yakan yi shiru a lokuta kamar haka, gama lokutan mugaye ne.14. Ku yi nagarta, ba mugunta ba; don ku rayu sa’an nan Ubangiji Allah Maɗaukaki zai kasance da ku, kamar yadda kuka ce zai yi.15. Ku ƙi mugunta, ku ƙaunaci nagarta; ku dinga yin shari’ar gaskiya a ɗakunan shari’a. Mai yiwuwa Ubangiji Allah Maɗaukaki zai ji tausayin raguwar Yusuf.16. Saboda haka ga abin da Ubangiji, Ubangiji Allah Maɗaukaki yana cewa, “Za a yi kururuwa a dukan tituna a kuma yi kuka don azaba a dukan wuraren da jama’a sukan taru. Za a yi kira ga manoma su yi kuka masu makoki kuma su yi kuka.17. Za a yi kuka a dukan gonakin inabi, gama zan ratsa a cikinku,” in ji Ubangiji.18. Kaitonku masu son ganin ranar Ubangiji! Don me kuke son ganin ranar Ubangiji? Za a duhunta ranan nan, ba haske ba.19. Za ku zama kamar mutanen da suka guje wa zaki sai suka fāɗa a hannun beyar, ko kuma kamar wanda ya shiga gida ya dāfa hannu a bango sai maciji ya sare shi.20. Ashe, ranar Ubangiji ba duhu ba ce, a maimakon haske, duhu wuluk, ba tare da ko ɗan haske ba.21. “Na ƙi, ina kuma ƙyamar bukukkuwanku na addini; ba na son ganin tarurrukanku.22. Ko da kun kawo mini hadayu na ƙonawa da kuma hadayu na hatsi, ba zan karɓa ba. Ko da kun kawo zaɓaɓɓun hadayu na zumunta, ba zan ɗauke su a bakin kome ba.23. Ku tashi daga nan da surutan waƙoƙinku! Ba zan saurari kaɗe-kaɗe da bushe bushenku ba.24. Amma bari gaskiya ta kwararo kamar kogi, adalci kuma kamar rafin da ba ya taɓa bushewa!25. “Kun kawo mini hadayu da sadakoki shekaru arba’in a cikin jeji, ya ku gidan Isra’ila?26. Kun ɗaga masujadar sarkinku, siffofin gumakanku, tauraron allahnku, wanda kuka yi wa kanku.27. Saboda haka zan tura ku zaman bauta gaba da Damaskus,” in ji Ubangiji, wanda sunansa ne Allah Mai Iko.Zabura 141:5-105. Bari mutum mai adalci yă buge ni, alheri ne; bar shi yă tsawata mini, mai ne a kaina. Kaina ba zai ƙi shi ba, duk da haka addu’ata kullum tana gāba da mugayen ayyuka.6. Za a jefar da masu mulkinsu ƙasa daga ƙwanƙolin dutse, mugaye kuwa za su san cewa maganata daidai ne.7. Za su ce, “Kamar yadda mutum kan yi huda yă tsage ƙasa, haka aka watsar da ƙasusuwanmu a bakin kabari.”8. Amma na kafa idanuna a kanka, ya Ubangiji Mai Iko Duka; a cikinka ina neman mafaka, kada ka miƙa ni ga mutuwa.9. Ka kiyaye ni daga tarkon da aka sa mini, daga tarkon da mugaye suka sa.10. Bari mugaye su fāɗa a cikin ragarsu, amma bari ni in zo in wuce lafiya.Karin Magana 29:26-2626. Mutane sukan nemi samun farin jini daga wurin sarki, amma daga wurin Ubangiji ne mutum kan sami adalci.Ruʼuya ta Yohanna 4:1-111. Bayan wannan sai na duba, a can kuma a gabana ga ƙofa a buɗe a sama. Sai muryar da na ji da fari da take magana da ni mai kama da busar ƙaho ta ce, “Hauro nan, zan kuma nuna maka abin da lalle zai faru bayan wannan.”2. Nan da nan sai ga ni cikin Ruhu, a can a gabana kuwa ga kursiyi a cikin sama da wani zaune a kansa.3. Wannan mai zama a can kuwa yana da kamannin dutsen yasfa da karneliya. Bakan gizo, mai kama da zumurrudu, ya kewaye kursiyin.4. Kewaye da kursiyin kuwa akwai waɗansu kursiyoyi ashirin da huɗu, zaune a kansu kuwa dattawa ashirin da huɗu ne. Suna saye da fararen tufafi suna kuma da rawanin zinariya a kawunansu.5. Daga kursiyin hasken walƙiya yana ta fitowa, da ƙararraki da kuma tsawa. A gaban kursiyin, fitilu bakwai suna ci. Waɗannan ne ruhohi bakwai na Allah.6. Haka kuma a gaban kursiyin akwai wani abu mai kama da tekun gilashi, yana ƙyalli kamar madubi. A tsakiya kuwa, kewaye da kursiyin, akwai halittu huɗu masu rai, cike kuma suna da idanu gaba da baya.7. Halitta ta fari tana kama da zaki, ta biyun kuwa tana kama da bijimi, ta ukun kuma tana da fuska kamar ta mutum, ta huɗun kuma tana kama da gaggafa mai tashi sama.8. Kowace a cikin halittu huɗu masu rai ɗin nan tana da fikafikai guda shida, tana kuma cike da idanu a ko’ina, har ma ƙarƙashin fikafikanta. Dare da rana ba sa fasa cewa, “ ‘Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki shi ne Ubangiji Allah Maɗaukaki,’ wanda yake a dā, wanda yake a yanzu, wanda kuma yake nan gaba.”9. Duk lokacin da halittu masu ran nan suka rera ɗaukaka, girma da kuma godiya ga wannan wanda yake zaune a kan kursiyin da kuma wanda yake mai rai har abada abadin,10. sai dattawa ashirin da huɗun nan su fāɗi a ƙasa a gaban wannan wanda yake zaune a kursiyin, su yi sujada wa wannan wanda yake da rai har abada abadin. Sukan ajiye rawaninsu a gaban kursiyin suna cewa,11. “Ya Ubangijinmu da Allahnmu, ka cancanci ɗaukaka da girma da iko, domin ka halicci dukan abubuwa, kuma ta wurin nufinka aka halicce su suka kuma kasance.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.