Baibul a cikin shekara guda Disamba 21Mika 6:1-161. Ku saurari abin da Ubangiji ya ce, “Tashi ku gabatar da ƙararku a gaban duwatsu; bari tuddai su ji abin da kuke so ku faɗa.2. “Ku saurara, ya ku duwatsu game da tuhumar da Ubangiji yake muku, ku ji, ku daɗaɗɗun tushin duniya. Gama Ubangiji yana da ƙara a kan mutanensa; yana tuhumar Isra’ila.3. “Ya ku mutanena, me na yi muku? Ta yaya na nawaita muku? Ku amsa mini.4. Na fito da ku daga ƙasar Masar na kuma ’yantar da ku daga ƙasar bauta. Na aika da Musa yă jagorance ku, haka ma Haruna da Miriyam.5. Ya ku mutanena, ku tuna abin da Balak sarkin Mowab ya ƙulla da kuma amsar da Bala’am ɗan Beyor ya bayar. Ku tuna da tafiyarku daga Shittim zuwa Gilgal, don ku san ayyukan adalcin Ubangiji.”6. Da me zan zo a gaban Ubangiji in rusuna a gaban Maɗaukaki Allah? Shin, zan zo ne a gabansa da hadaya ta ƙonawa, da ɗan maraƙi bana ɗaya?7. Ubangiji zai ji daɗin hadayar raguna dubbai da kuma rafuffukan mai dubbai goma? Zan ba da ɗan farina ne don laifina, ko ’ya’yan jikina domin zunubin raina?8. Ya nuna maka, ya mutum, abin da yake mai kyau. Me Ubangiji yake bukata daga gare ka kuwa shi ne ka yi gaskiya ka so aikata jinƙai ka kuma yi tafiya da tawali’u a gaban Allah.9. Ku saurara! Ubangiji yana kira ga birni, a ji tsoron sunana kuwa hikima ce, “Ku kasa kunne ga sandan nan da kuma wannan wanda ya naɗa.10. Har yanzu zan manta, ya muguwar gida da dukiyarki da kika samu a muguwar hanya zan kuma manta da bugaggen mudun awo wanda ake zargi?11. Zan kuɓutar da mutumin da yake da ma’auni na rashin gaskiya, da kuma buhun ma’aunan ƙarya?12. Attajiranta masu fitina ne; mutanenta kuma maƙaryata ne harsunansu kuwa suna yaudara.13. Saboda haka, zan hallaka ku in lalace ku saboda zunubanku.14. Za ku ci amma ba za ku ƙoshi ba, cikinku zai zama babu kome Za ku tattara amma ba za ku yi ajiyar kome ba, gama abin da kuka yi ajiya zan ba wa takobi.15. Za ku yi shuki amma ba za ku girba ba; za ku matse zaitun amma ba za ku yi amfani da mai wa kanku ba, za ku tattaka ’ya’yan inabi amma ba za ku sha ruwan inabin ba.16. Kuna kiyaye ƙa’idodin Omri da dukan ayyukan gidan Ahab kun kuma bi al’adunsu. Saboda haka, zan maishe ku kufai in mai da ku abin dariya a cikin mutane, za ku sha reni a wurin al’ummai.”Mika 7:1-201. Tawa ta ƙare! Ina kama da wanda yake tattara ’ya’yan itatuwa a lokacin kalar ’ya’yan inabi; babu sauran nonon inabin da za a tsinka a ci, babu kuma ’ya’yan ɓaure na farko-farkon da raina yake marmari.2. An kawar da masu tsoron Allah daga ƙasar; babu sauran mai adalcin da ya rage. Dukan mutane suna kwanto don su zub da jini; kowa yana farautar ɗan’uwansa da tarko.3. Dukan hannuwansu sun gwaninta wajen yin mugunta; shugabanni suna nema a ba su kyautai, alƙalai suna nema a ba su cin hanci, masu iko suna faɗar son zuciyarsu, duk suna ƙulla makirci tare.4. Mafi kyau a cikinsu yana kama da ƙaya, mafi gaskiyarsu ya fi shingen ƙaya muni. Ranar da Allah zai ziyarce ku ta zo, ranar da masu gadinku za su hura ƙaho. Yanzu ne lokacin ruɗewarku.5. Kada ka yarda da maƙwabci; kada ka sa begenka ga abokai. Ko ma wadda take kwance a ƙirjinka, ka yi hankali da kalmominka.6. Gama ɗa yakan ce wannan ba mahaifinsa ba ne, diya kuma takan tayar wa mahaifiyarta, matar ɗa takan yi gāba da uwar mijinta, abokan gāban mutum su ne iyalin cikin gidansa.7. Amma game da ni, zan sa bege ga Ubangiji, ina sauraron Allah Mai Cetona; Allahna kuwa zai ji ni.8. Kada ku yi farin ciki, ku maƙiyana! Ko da yake na fāɗi, zan tashi. Ko da yake na zauna a cikin duhu, Ubangiji zai zama haskena.9. Domin na yi masa zunubi, zan fuskanci fushin Ubangiji, har sai ya dubi batuna ya kuma tabbatar da ’yancina. Zai kawo ni zuwa wurin haske; zan ga adalcinsa.10. Sa’an nan maƙiyina zai gani yă kuma sha kunya, shi da yake ce da ni “Ina Ubangiji Allahnka?” Zai gani, yă kuma ji kunya. Ko yanzu ma za a tattake shi kamar taɓo a tituna.11. Ranar gina katangarka tana zuwa, a ranar za a fadada iyakokinka.12. A wannan rana mutane za su zo gare ka daga Assuriya da kuma biranen Masar, daga Masar ma har zuwa Yuferites daga teku zuwa teku, kuma daga dutse zuwa dutse.13. Duniya za tă zama kufai saboda mazaunanta, saboda ayyukansu.14. Ka yi kiwon mutanenka da sandarka, garken gādonka, wanda yake zaune shi kaɗai a kurmi, a ƙasa mai kyau ta kiwo, bari su yi kiwo a Bashan da Gileyad kamar a kwanakin dā.15. “Kamar a kwanakin da kuka fito daga Masar, zan nuna musu al’ajabaina.”16. Al’ummai za su gani su kuma ji kunya, za a kuma ƙwace musu dukan ikonsu. Za su kama bakinsu kunnuwansu kuma za su zama kurame.17. Za su lashi ƙura kamar maciji, kamar dabbobi masu rarrafe a ƙasa. Za su fito daga maɓuyarsu da rawan jiki, za su juya cikin tsoro ga Ubangiji Allahnmu su kuma ji tsoronku.18. Wane ne Allah kamar ka, wanda yake yafe zunubi yă kuma gafarta laifofin mutanensa da suka ragu? Ba ka zama mai fushi har abada amma kana marmari ka nuna jinƙai.19. Za ka sāke jin tausayinmu; za ka tattake zunubanmu a ƙarƙashin sawunka ka kuma tura dukan kurakuranmu zuwa cikin zurfafan teku.20. Za ka yi wa Yaƙub aminci, ka kuma nuna jinƙai ga Ibrahim, kamar yadda ka yi alkawari da rantsuwa ga kakanninmu tun a kwanankin dā.Zabura 145:10-1610. Dukan abubuwan da ka yi za su yabe ka, ya Ubangiji; tsarkakanka za su ɗaukaka ka.11. Za su yi maganar ɗaukakar mulkinka za su kuma yi zancen ikonka,12. saboda dukan mutane su san manyan ayyukanka da ɗaukakar darajar mulkinka.13. Mulkinka madawwamin mulki ne, sarautarka kuma za tă dawwama cikin dukan zamanai. Ubangiji mai aminci ne ga dukan alkawuransa mai ƙauna kuma ga dukan abubuwan da ya yi.14. Ubangiji yana riƙe da dukan waɗanda suka faɗi yana kuma ɗaga dukan waɗanda aka rusunar da su ƙasa.15. Idanun kowa yana dogara gare ka, kana kuma ba su abincinsu a lokacin da ya dace.16. Ka buɗe hannunka ka kuma ƙosar da sha’awar kowane abu mai rai.Karin Magana 30:15-1515. “Matsattsaku tana da ’ya’ya mata biyu. Suna kuka suna cewa, ‘Ba ni! Ba ni!’ “Akwai abubuwa uku da ba sa taɓa ƙoshi, guda huɗu ba sa taɓa cewa, ‘Ya isa!’Ruʼuya ta Yohanna 11:1-191. Aka ba ni ƙara kamar sandan awo aka kuma ce mini, “Tafi ka auna haikalin Allah da bagaden, ka kuma ƙirga waɗanda suke sujada a can.2. Sai dai kada ka haɗa da harabar waje; kada ka auna ta, domin an ba da ita ga Al’ummai. Za su tattaka birni mai tsarki har watanni 42.3. Zan kuma ba wa shaiduna nan biyu iko, za su kuwa yi annabci na kwanaki 1,260, saye da gwadon makoki.”4. Waɗannan su ne itatuwan zaitun biyu da kuma alkukai biyu da suke tsaye a gaban Ubangijin duniya.5. Duk wanda ya yi ƙoƙari yin musu lahani, wuta za tă fito daga bakunansu ta cinye abokan gābansu. Haka ne duk mai niyyar yin musu lahani zai mutu.6. Waɗannan mutane suna da iko su kulle sararin sama don kada a yi ruwan sama a lokacin da suke annabci; suna kuma da iko su juye ruwaye su zama jini su kuma bugi duniya da kowace irin annoba a duk lokacin da suke so.7. To, da suka gama shaidarsu, dabbar da takan fito daga Abis za tă kai musu hari, tă kuwa sha ƙarfinsu tă kuma kashe su.8. Gawawwakinsu za su kasance a kwance a titin babban birni, wanda a misalce ake kira Sodom da Masar, inda kuma aka gicciye Ubangijinsu.9. Kwana uku da rabi mutane daga kowace jama’a, kabila, harshe da kuma al’umma za su yi ta kallon gawawwakinsu su kuma ƙi binne su.10. Mazaunan duniya za su ƙyaface su kuma yi biki ta wurin aika kyautai wa juna, domin waɗannan annabawan nan biyu ne suka azabtar da mazaunan duniya.11. Amma bayan kwana uku da rabi ɗin numfashin rai daga Allah ya shige su, suka kuwa tashi tsaye, tsoro kuma ya kama waɗanda suka gan su.12. Sai suka ji wata babbar murya daga sama tana ce musu, “Ku hauro nan.” Suka kuwa haura zuwa sama cikin girgije, yayinda abokan gābansu suna kallo.13. A wannan sa’a aka yi wata babbar girgizar ƙasa kashi ɗaya bisa goma kuma na birnin ya rushe. Aka kashe mutane dubu bakwai a girgizar ƙasar, waɗanda suka tsira kuwa suka ji tsoro suka ɗaukaka Allah na sama.14. Kaito na biyu ya wuce; kaito na uku yana zuwa ba da daɗewa ba.15. Mala’ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji muryoyi masu ƙarfi a sama da suka ce, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Kiristinsa, zai kuwa yi mulki har abada abadin.”16. Sai dattawan nan ashirin da huɗu da suke zaune a kursiyoyinsu a gaban Allah, suka fāɗi da fuskokinsu a ƙasa suka kuma yi wa Allah sujada,17. suna cewa, “Muna maka godiya ya Ubangiji Allah, Maɗaukaki, wanda yake a yanzu, shi ne kuma a dā, domin ka karɓi ikonka mai girma ka kuma fara mulki.18. Al’ummai suka yi fushi; fushinka kuwa ya zo. Lokaci ya yi don a shari’anta matattu, da kuma don sākawa wa bayinka annabawa da tsarkakanka da kuma su waɗanda suke girmama sunanka, ƙarami da babba, don kuma hallakar da waɗanda suka hallaka duniya.”19. Sa’an nan aka buɗe haikalin Allah da yake a sama, kuma a cikin haikalinsa aka ga akwatin alkawarinsa. Sai kuwa ga walƙiya, ƙararraki, tsawa, girgizar ƙasa, da kuma ƙanƙara masu girma. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.