Baibul a cikin shekara guda Disamba 22Nahum 1:1-151. Jawabi game da Ninebe a littafin wahayin Nahum, mutumin Elkosh.2. Ubangiji Allah mai kishi ne, mai sakayya kuma. Ubangiji Allah mai kishi ne, mai ɗaukar fansa kuma. Ubangiji yakan ɗauki fansa a kan maƙiyansa, yakan ci gaba da fushi a kan abokan gābansa.3. Ubangiji mai jinkirin fushi ne, mai iko duka kuma. Ubangiji ba zai bar masu zunubi babu horo ba. Hanyarsa tana cikin guguwa da kuma hadari, gizagizai kuwa su ne ƙurar ƙafafunsa.4. Yakan tsawata wa teku yă kuma busar da shi; yakan sa dukan koguna su kafe. Bashan da Karmel sun yi yaushi tohon Lebanon kuma ya koɗe.5. Duwatsu suna rawan jiki a gabansa tuddai kuma sun narke. Duniya da dukan abin da yake cikinta suna rawan jiki a gabansa.6. Wa zai iya tsaya wa fushinsa? Wa yake da ikon jimre wa zafin hasalarsa? Ana zuba fushinsa kamar wuta; aka kuma ragargaza duwatsu a gabansa.7. Ubangiji nagari ne, mafaka kuma a lokacin wahala. Yana kula da waɗanda suka dogara gare shi,8. amma da ambaliyar ruwa zai kawo Ninebe ga ƙarshe; zai fafari maƙiyansa zuwa cikin duhu.9. Dukan abin da suke ƙullawa game da Ubangiji zai kawo ga ƙarshe; wahala ba za tă sāke komowa ƙaro na biyu ba.10. Za su sarƙafe a ƙaya, za su kuma bugu da ruwan inabinsu; za a laƙume su kamar busasshiyar ciyawa.11. Daga cikinki, ya Ninebe wani ya fito wanda ya ƙulla wa Ubangiji makirci yana ba da mugayen shawarwari.12. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Ko da yake sun yi tarayya, suna kuma da yawa, za a yanke su, a kawar a su. Ko da yake na ba ki azaba, ya Yahuda, ba zan ƙara ba ki azaba ba.13. Yanzu zan karya karkiyarsu daga wuyanki in kuma tsittsinke sarƙar da suka ɗaura ki.”14. Ubangiji ya ba da umarni game da ke Ninebe, “Ba za ki sami zuriyar da za tă ci gaba da sunanki ba. Zan rurrushe siffofin da kuka sassaƙa da kuma gumakan da kuka ƙera gumakan da suke a cikin haikalin allolinku. Zan shirya kabarinki, domin ke muguwa ce.”15. Duba, can a bisa duwatsu, ga ƙafafu mai kawo labari mai daɗi, wanda yake shelar salama! Ki yi bukukkuwanki, ya Yahuda, ki kuma cika wa’adodinki. Mugaye ba za su ƙara mamaye ki ba; domin za a hallaka su ƙaƙaf.Nahum 2:1-131. Mai hari yana matsowa a kanki, Ninebe. Ki tsare mafaka, ki yi gadin hanya ki sha ɗamara ki tattaro dukan ƙarfinki!2. Ubangiji zai maido da darajar Yaƙub, kamar ta Isra’ila, ko da yake masu washewa sun washe su suka kuma lalatar da inabinsu.3. Garkuwoyin sojojinsa ja wur ne; jarumawansa suna sanye da kaya masu ruwan jan garura. Ƙarafan kekunan yaƙi suna walƙiya a ranar da aka shirya su; ana kaɗa māsu da bantsoro.4. Kekunan yaƙi sun zabura a tituna, suna kai da kawowa a dandali. Suna walƙiya kamar tocila suna sheƙawa a guje kamar walƙiya.5. Ninebe ta tattara rundunarta, duk da haka sun yi ta tuntuɓe a kan hanyarsu. Sun ruga zuwa katangan birnin, sun sanya garkuwar kāriya a inda ya kamata.6. An buɗe ƙofofin rafuffukan sai wurin ya rurrushe.7. An umarta cewa birnin za tă tafi bauta, za a kuma yi gaba da su. Bayi ’yan mata suna kuka kamar tattabaru suna buga ƙirjinsu.8. Ninebe tana kama da tafki, wanda ruwanta yana yoyo. Suna kuka suna cewa, “Ku tsaya! Ku tsaya,” amma ba wanda ya waiga.9. A washe azurfa; a washe zinariya; dukiyarsu ba ta da iyaka, arzikinsu kuma ba ya ƙarewa.10. Ta zama wofi, an washe ta, an tuɓe ta! Zukata sun narke, gwiwoyi suna kaɗuwa, jikuna suna rawa, fuskoki duk sun kwantsare!11. Ina kogon zakokin nan yake yanzu, inda suka ciyar da ’ya’yansu, inda zaki da zakanya sukan shiga, da ’ya’yansu, ba mai damunsu12. Zaki ya kashe abin da ya ishe ’ya’yansa ya kuma murɗe wuyan dabbobi ya cika wurin zamansa da abin da ya kama ya cika kogwanninsa da abin da ya kashe.13. “Ina gāba da ke,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan ƙone kekunan yaƙinki, takobi kuma zai fafare ’ya’yan zakokinki. Ba kuma zan bar miki namun jejin da za ki kashe a duniya ba. Ba kuwa za a ƙara jin muryar ’yan saƙonki ba.”Nahum 3:1-191. Kaiton birni mai zub da jini, wadda take cike da ƙarairayi, cike da ganima, wadda ba a rasa masu fāɗawa cikin wahala!2. Ku ji karar bulala da kwaramniyar ƙafafu, da sukuwar dawakai da girgizar kekunan yaƙi!3. Mahaya dawakai sun kunno kai, takuba suna walƙiya, māsu kuma suna ƙyali; ga ɗumbun da aka kashe ga tsibin matattu, gawawwaki ba iyaka, mutane suna tuntuɓe da gawawwaki,4. duk saboda yawan sha’awace-sha’awacen karuwa, mai daɗin baki, uwargidan maita, wadda ta ɓad da al’ummai ta wurin karuwancinta ta kuma ɓad da mutane ta wurin maitancinta.5. “Ina gāba da ke,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan kware fatarinki a idonki. Zan nuna wa al’ummai tsiraicinki, masarautai kuma kunyarki.6. Zan watsa miki ƙazanta, in yi miki wulaƙanci in kuma mai da ke abin reni.7. Duk wanda ya gan ki zai gudu daga gare ki yana cewa, ‘Ninebe ta lalace, wa zai yi makoki domin ta?’ Ina zan sami wani wanda zai yi miki ta’aziyya?”8. Kin fi Tebes ne da take a bakin Nilu, da ruwa yake kewaye da ita? Rafi shi ne kāriyarta, ruwanta kuma katanga.9. Kush da kuma Masar su ne ƙarfinta marar iyaka; Fut da Libiya suna cikin mataimakanta.10. Duk da haka an tafi da ita ta kuma tafi bauta. Aka fyaɗa ƙanananta da ƙasa aka yayyanka su gunduwa-gunduwa a kan kowane titi. Aka jefa ƙuri’a a kan manyan mutanenta, aka daure manyan mutanenta da sarƙoƙi.11. Ke ma za ki bugu, za ki ɓuya. Ki kuma nemi mafaka daga wurin abokin gāba.12. Dukan kagarunki suna kama da itatuwan ɓaure da ’ya’yansu da suka nuna. Da an girgiza, sai ɓaure su zuba a bakin mai sha.13. Dubi mayaƙanki, duk mata ne! Ƙofofin ƙasarki a buɗe suke ga abokan gābanki, wuta ta cinye madogaransu.14. Ki ja ruwa gama za a kewaye ki da yaƙi. Ki ƙara ƙarfin kagaranki! Ki kwaɓa laka, ki sassaƙa turmi ki gyara abin yin tubali!15. A can wuta za tă cinye ki; takobi zai sare ki, kuma kamar fāra, za a cinye ki. Ki riɓaɓɓanya kamar fāra, ki riɓaɓɓanya kamar fārin ɗango!16. Kin ƙara yawan masu kasuwancinki har sai da suka fi taurarin sama. Amma kamar fāra sun cinye ƙasar sa’an nan suka tashi, suka tafi.17. Masu tsaronki suna kama da fāri ɗango, shugabanninki sun yi cincirindo kamar fārin ɗango da suka sauka a kan bango a rana mai sanyi, amma da rana ta fito, duk za su tashi su tafi, ba kuma wanda ya san inda suka nufa.18. Ya sarkin Assuriya, makiyayanka sun yi barci; manyan mutanenka sun kwanta su huta. An watsar da mutanenka a cikin duwatsu, ba wanda zai tattaro su.19. Ba abin da zai warkar da rauninka; rauninka ya yi muni. Duk wanda ya ji labarinka zai tafa hannuwansa saboda farin cikin fāɗuwarka, gama wane ne bai ji jiki a hannunka ba?Zabura 145:17-2117. Ubangiji mai adalci ne cikin dukan hanyoyinsa yana kuma nuna ƙauna ga dukan abubuwan da ya yi.18. Ubangiji yana kusa da kowa da ya kira gare shi, ga duk wanda ya kira gare shi cikin gaskiya.19. Yakan cika sha’awar waɗanda suke tsoronsa; yakan ji kukansu yă kuma cece su.20. Ubangiji yakan lura da dukan waɗanda suke ƙaunarsa, amma dukan mugaye zai hallaka su.21. Bakina zai yi magana cikin yabon Ubangiji. Bari kowace halitta ta yabi sunansa mai tsarki har abada abadin.Karin Magana 30:16-1616. Kabari, mahaifar da ba ta haihuwa, ƙasa, wadda ba ta taɓa ƙoshi da ruwa, da kuma wuta, wadda ba ta taɓa cewa ‘Ya isa!’Ruʼuya ta Yohanna 12:1-171. Babbar alama mai banmamaki ta bayyana a sama, mace tana lulluɓe da rana, da kuma wata a ƙarƙashin sawunta, akwai kuma rawani mai taurari goma sha biyu a kanta.2. Tana da ciki ta kuma yi kuka mai zafi yayinda take gab da haihuwa.3. Sai wata alama ta bayyana a sama, wani babban jan maciji mai kawuna bakwai da ƙahoni goma da rawani bakwai a kan kawunansa.4. Wutsiyarsa ta share kashi ɗaya bisa uku na taurari daga sararin sama ta kuma zubar da su ƙasa. Ƙaton jan macijin ya tsaya a gaban macen wadda take gab da haihuwa, don yă cinye ɗanta nan take bayan an haife shi.5. Ta haifi ɗa, namiji, wanda zai yi mulkin dukan al’ummai da sandar ƙarfe. Aka fyauce ɗanta zuwa wurin Allah da kuma kursiyinsa.6. Sai macen ta gudu zuwa hamada zuwa inda Allah ya shirya dominta, inda za a lura da ita har kwana 1,260.7. Aka kuwa yi yaƙi a sama. Mika’ilu da mala’ikunsa yaƙi macijin, maciji da mala’ikunsa su ma suka mai da martani.8. Amma macijin nan ba shi da isashen ƙarfi, har suka rasa matsayinsu a sama.9. Aka jefar da ƙaton jan macijin ƙasa, tsohon maciji nan da ake kira Iblis, ko Shaiɗan, wanda ya ɓad da dukan duniya. Aka jefar da shi ƙasa, tare da mala’ikunsa a duniya.10. Sa’an nan na ji babbar murya daga sama tana cewa, “Yanzu ceto da iko da mulkin Allahnmu, da kuma ikon Kiristinsa. Gama mai zargin ’yan’uwanmu, wanda yake zarginsu a gaban Allahnmu dare da rana, an jefar da shi ƙasa.11. Sun ci nasara a kansa ta wurin jinin Ɗan Ragon da ta wurin kalmar shaidarsu; ba su ƙaunaci rayukansu sosai har da za su ja da baya daga mutuwa.12. Saboda haka ku yi farin ciki, ku sammai, da ku da kuke zaune a cikinsu! Amma kaiton duniya da kuma teku, gama Iblis ya sauko gare ku! Ya cika da fushi, domin ya san cewa lokacinsa ya rage kaɗan.”13. Sa’ad da macijin ya ga an jefar da shi a duniya, sai ya fafari macen nan da ta haifi ɗa namiji.14. Sai aka ba wa macen fikafikai biyu na babban gaggafa, don ta tashi sama zuwa inda aka shirya mata a hamada, inda za a lura da ita na ɗan lokaci, lokuta da rabin lokaci, inda macijin ba zai iya kaiwa ba.15. Sa’an nan daga bakinsa macijin ya kwarara ruwa kamar kogi, don ruwan ya cimma matan yă kuma kwashe ta tare da ambaliya.16. Amma ƙasa ta taimaki macen ta wurin buɗe bakinta ta kuma shanye ruwan kogin da macijin ya kwarara daga bakinsa.17. Sai macijin ya yi fushi da macen ya kuma koma wajen sauran zuriyarta don yă yaƙe su waɗannan waɗanda suke biyayya da umarnan Allah suke kuma riƙe da shaidar Yesu. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.