Baibul a cikin shekara guda Disamba 23Habakkuk 1:1-171. Saƙon da annabi Habakkuk ya karɓa.2. Har yaushe, ya Ubangiji, zan yi kukan neman taimako, amma ka ƙi ji? Ina kuka a gare ka saboda zalunci amma ba ka ce ufam ba.3. Me ya sa ka bari ina ta kallon rashin gaskiya? Me ya sa kake barin abin da ba daidai ba? Hallaka da tashin hankali suna a gabana; ga rashin jituwa da faɗa ko’ina.4. Saboda haka ba a bin doka, shari’a kuma ba ta aiki. Mugaye sun kewaye masu adalci don a hana gaskiya tă yi aiki.5. “Ka dubi al’ummai, ka gani, ka sha mamaki. Ga shi zan yi wani abu a kwanakinka, wanda ko ma an faɗa maka ba za ka gaskata ba.6. Zan tā da Babiloniyawa, waɗannan marasa hankali da kuma marasa tausayi; masu gajeren haƙuri, waɗanda suke ratsa ko’ina a duniya don su ƙwace wuraren zaman da ba nasu ba.7. Suna da bantsoro da firgitarwa; dokoki da ƙa’idodinsu ne kawai suka sani.8. Dawakansu sun fi damisoshi sauri, sun fi kyarketan yamma zafin rai. Mahayansu suna zuwa a guje; mahayansu daga nesa suka fito. Suna firiya kamar ungulu mai sauka da gaggawa don yă ci mushe;9. duk sukan zo da nufin tā-da-na-zaune-tsaye. Ana jin tsoronsu tun ma kafin su iso suna tattara bayi kamar yashi.10. Sukan yi wa sarakuna ba’a su kuma rena masu mulki. Sukan yi wa dukan birane masu mafaka dariya; sukan tara ƙasa su hau, su cinye abokan gābansu da yaƙi.11. Sa’an nan su wuce da sauri kamar iska, mutane ne masu laifi, waɗanda ƙarfinsu shi ne allahnsu.”12. Ya Ubangiji, ba tun fil azal kake ba? Ya Allahna, Mai Tsarkina, ba za mu mutu ba. Ya Ubangiji ka sanya su su tabbatar da hukunci; Ya Dutse, ka naɗa su don su yi hukunci.13. Idanunka masu tsarki ne da suka fi gaban duban mugunta; ba ka amince da abin da ke ba daidai ba. To, don me ka ƙyale munafukai suna cin karensu ba babbaka? Me ya sa kake shiru sa’ad da mugaye suke haɗiye adalai da suka fi su adalci?14. Ka mai da maza kamar kifin teku, kamar halittun tekun da ba su da shugaba.15. Mugu abokin gāba yakan kama su duka da ƙugiya, yă jawo su waje da abin kamun kifinsa, yă tattara su cikin ragarsa, ta haka yakan yi murna da farin ciki.16. Saboda haka yakan yi hadaya wa abin kamun kifinsa yă kuma ƙona turare wa ragarsa, domin ta wurin abin kamun kifinsa ne yake yin rayuwar jin daɗi yă kuma zaɓi irin abincin da yake so.17. Zai ci gaba da juye abin kamun kifinsu ke nan, suna hallaka al’ummai ba tausayi?Habakkuk 2:1-201. Zan tsaya wurin tsarona in kuma zauna a kan katanga; zan jira in ga abin da zai ce mini, da kuma wace amsa zan bayar ga wannan kuka.2. Sa’an nan Ubangiji ya amsa ya ce, “Ka rubuta wannan ru’uya ka bayyana ta a fili a kan alluna don mai shela yă ruga da ita, yă kai.3. Gama ru’uyar tana jiran ƙayyadadden lokaci; tana zancen ƙarshe kuma ba za tă zama ƙarya ba. Ko da ka ga kamar tana jinkiri, ka jira ta; lalle za tă zo, ba za tă makara ba.4. “Duba, abokin gāba ya cika da ɗaga kai; sha’awarsa ba daidai ba ce, amma mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiyarsa,5. ba shakka, ruwan inabi ya yaudare shi; yana fariya kuma ba ya hutu. Domin shi mai haɗama ne kamar kabari kuma kamar mutuwa, ba ya ƙoshi; yakan tattara dukan al’ummai wa kansa yana kuma kama dukan mutane su zama kamammu.6. “Dukansu ba za su yi masa tsiya, suna yin masa ba’a da dariya ba, suna cewa, “ ‘Kaito ga wannan wanda ya tara wa kansa kayan sata ya kuma wadatar da kansa da kayan ƙwace! Har yaushe wannan abu zai ci gaba?’7. Masu binka bashi ba za su taso maka nan da nan ba? Ba za su farka su sa ka fargaba ba? Ta haka ka zama ganima a gare su.8. Domin ka washe al’ummai masu yawa, mutanen da suka rage za su washe ka. Domin ka zub da jinin mutane; ka hallaka ƙasashe, da birane, da kuma kowa da yake cikinsu.9. “Kaito ga wanda ya gina masarautarsa da ƙazamar riba don yă kafa sheƙarsa can bisa, don yă tsere wa zama kango!10. Ka ƙulla lalacin mutane masu yawa, ta haka ka kunyatar da gidanka ka kuma hallaka ranka.11. Duwatsun katanga za su yi kuka, ginshiƙan katako kuma za su amsa.12. “Kaiton mutumin da ya gina birni da jinin da ya zubar ya kuma kafa gari ta wurin mugun aiki!13. Ba Ubangiji Maɗaukaki ne ya ƙudura cewa wahalar mutane ta zama mai kawai don wuta ba, cewa al’ummai su gajiyar da kansu a banza ba?14. Gama duniya za tă cika da sanin ɗaukakar Ubangiji, yadda ruwaye suka rufe teku.15. “Kaito wanda ya ba wa maƙwabtansa abin sha, yana ta zubawa daga salkan ruwan inabi har sai sun bugu, don dai yă ga tsiraicinsu.16. Za ka cika da kunya a maimakon ɗaukaka. Yanzu lokacinka ne! Kai ma ka sha, a kuma tone asirinka! Gama kwaf na hannun daman Ubangiji yana zuwa kewaye da kai, abin kunya kuma zai rufe darajarka.17. Ɓarnar da ka yi wa Lebanon zai komo kanka, kuma hallakar dabbobin da ka yi zai sa dabbobi su tsorata ka. Gama ka zub da jinin mutum; ka hallaka ƙasashe, da birane, da kuma kowa da yake cikinsu.18. “Ina amfanin gunki da mutum ne ya sassaƙa? Ko siffar da take koyar da ƙarya? Gama wanda ya yi shi yana dogara ne ga halittarsa; ya yi gumakan da ba sa magana.19. Kaito wanda ya ce da katako, ‘Rayu!’ Ko kuwa dutse marar rai, ‘Farka!’ Zai iya bishewa ne? An dalaye shi da zinariya da azurfa; ba numfashi a cikinsa.”20. Amma Ubangiji yana a cikin haikalinsa mai tsarki; bari dukan duniya tă yi shiru a gabansa.Habakkuk 3:1-191. Addu’ar annabi Habakkuk. A kan shigiyont.2. Ya Ubangiji, na ji irin shaharar da ka yi; na yi al’ajabi game da ayyukanka, ya Ubangiji. Ka maimaita su a kwanakinmu, ka sanar da su a lokacinmu; ka yi jinƙai ko a lokacin da kake fushi.3. Allah ya zo daga Teman, Mai Tsarkin nan daga Dutsen Faran. Ɗaukakarsa ta rufe sammai yabonsa kuma ya cika duniya.4. Darajarsa ta yi kamar fitowar rana; ƙyalƙyali ya wulga daga hannunsa, inda ikonsa yake a ɓoye.5. Annoba ta sha gabansa; cuta kuma tana bin bayansa.6. Ya tsaya, ya kuwa girgiza duniya; ya duba, sai ya sa al’ummai suka yi rawan jiki. Tsofaffin duwatsu sun wargaje daɗaɗɗun tuddai kuma suka rurrushe. Hanyoyinsa dawwammamu ne.7. Na ga tentin Kushan cikin azaba; wuraren zaman Midiyan cikin damuwa.8. Ka ji haushin koguna ne, ya Ubangiji? Ko kuwa ka hasala da rafuffuka ne? Ko ka yi fushi da teku ne sa’ad da ka hau dawakanka da kuma kekunan yaƙinka masu nasara?9. Ka ja bakanka, ka nemi a ba ka kibiyoyi masu yawa. Ka raba duniya da koguna;10. duwatsu sun gan ka sai suka ƙame. Ruwaye masu hauka sun yi ta fantsamawa; zurfafa suka yi ruri suka tā da raƙuman ruwansu sama.11. Rana da wata suka tsaya cik a sammai da ganin kibiyoyinka masu wucewa fyu, da ganin hasken māshinka mai walƙiya.12. Cikin hasala ka ratsa duniya cikin fushi kuma ka tattake ƙasashe.13. Ka fito don ka fanshi mutanenka, don ceci shafaffenka. Ka ragargaza shugaban ƙasar mugaye, ka tuɓe shi daga kai har ƙafa.14. Da māshinsa ka soki kansa sa’ad da jarumawansa suka fito don su tarwatse mu, suna farin ciki sai ka ce masu shirin cinye matalautan da suke a ɓoye.15. Ka tattake teku da dawakanka, kana kaɗa manyan ruwaye.16. Na ji sai zuciyata ta buga, leɓunana sun yi rawa da jin murya; ƙasusuwana suka ruɓe, ƙafafuna kuma sun yi rawa. Duk da haka zan jira da haƙuri ga ranar bala’i ta zo a kan al’umman nan mai kawo mana hari.17. Ko da yake itace ɓaure bai tohu ba, ba kuma ’ya’ya a kuringar inabi, ko da yake zaitun bai ba da amfani ba, gonaki kuma ba su ba da abinci ba, ko da yake babu tumaki a garke, ba kuma shanu a turaku,18. duk da haka zan yi farin ciki da Ubangiji, zan yi murna da Allah Mai Cetona.19. Ubangiji Mai Iko Duka shi ne ƙarfina; yakan mai da ƙafafuna kamar na barewa, yakan sa in yi tafiya a wurare masu tsayi. Domin mai bi da kaɗe-kaɗe. A kan kayan kiɗi masu tsirkiyata.Zabura 146:1-101. Yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji, ya raina.2. Zan yabi Ubangiji dukan kwanakina; zan rera yabo ga Allahna muddin raina.3. Kada ka sa zuciyarka ga sarakuna, ga mutane masu mutuwa, waɗanda ba sa iya ceto.4. Sa’ad da numfashinsu ya rabu da su sai su koma ƙasa; a wannan rana shirye-shiryensu sun zama banza.5. Mai albarka ne wanda Allah na Yaƙub ne taimakonsa, wanda sa zuciyarsa yana a kan Ubangiji Allahnsa.6. Mahaliccin sama da ƙasa, teku, da kome da yake cikinsu, Ubangiji, wanda yake mai aminci har abada.7. Yakan biya bukatun mutanen da aka danne ya kuma ba da abinci ga mayunwata. Ubangiji yakan ’yantar da ’yan kurkuku,8. Ubangiji yakan ba wa makafi ido, Ubangiji yakan ɗaga waɗanda aka rusunar da su ƙasa, Ubangiji yana ƙaunar masu adalci.9. Ubangiji yana tsaron baƙi yana kuma lura da marayu da kuma gwauruwa, amma yakan lalatar da hanyoyin mugaye.10. Ubangiji yana mulki har abada, Allahnki, ya Sihiyona, daga zamani zuwa zamani. Yabi Ubangiji.Karin Magana 30:17-1717. “Idon da yake yi wa mahaifi ba’a, wanda yake wa mahaifiya dariyar rashin biyayya, hankakin kwari za su ƙwaƙule masa ido, ungulai za su cinye su.Ruʼuya ta Yohanna 13:1-181. Macijin kuwa ya tsaya a bakin teku. Sai na ga wata dabba tana fitowa daga teku. Tana da ƙahoni goma da kawuna bakwai, da kuma rawani goma a ƙahoninta, a kowane kai kuwa akwai sunan saɓo.2. Dabbar da na gani ta yi kamar damisa, amma tana da ƙafafu kamar na beyar, bakinta kuma ya yi kamar na zaki. Macijin nan ya ba wa dabbar ƙarfinsa da gadon sarautarsa da kuma ikonsa mai girma.3. Ɗaya daga cikin kawunan dabbar ya yi kamar yana da raunin da zai iya kashe shi, amma raunin nan da zai iya kashe shi ya riga ya warke. Dukan duniya ta yi mamaki ta kuma bi dabbar.4. Mutane suka yi wa macijin sujada domin ya ba wa dabbar ikonsa, suka yi wa dabbar sujada, suka kuma yi tambaya cewa, “Wane ne yake kama da dabban nan? Wa zai iya yaƙe ta?”5. Aka ba wa dabbar baki don ta faɗi kalmomin girman kai da na saɓo ta kuma yi amfani da ikonta har watanni arba’in da biyu.6. Ta buɗe bakinta don tă yi wa Allah saɓo, ta kuma ɓata sunansa da kuma mazauninsa da na waɗanda suke zama a sama.7. Aka ba ta iko tă yaƙi tsarkaka tă kuma ci nasara a kansu. Aka kuma ba ta iko bisa kowace kabila, jama’a, harshe da kuma al’umma.8. Dukan mazaunan duniya za su yi wa dabbar sujada, dukan waɗanda ba a rubuta sunayensu a cikin littafin ran da yake na Ɗan Ragon da aka yanka tun kafin halittar duniya ba.9. Duk mai kunne ji, bari yă ji.10. Duk wanda aka ƙaddara ga bauta, ga bauta zai tafi. Duk wanda aka ƙaddara za a kashe da takobi, da takobin za a kashe shi. Wannan yana bukata haƙuri da aminci a gefen tsarkaka.11. Sai na ga wata dabba tana fitowa daga ƙasa. Tana da ƙahoni biyu kamar ɗan rago, amma ta yi magana kamar maciji.12. Ta mori dukan ikon dabban nan ta fari a madadinta, ta sa duniya da mazaunanta su yi wa dabba ta farin nan sujada, wadda aka warkar mata da raunin nan da zai iya kashe ta.13. Ta kuma yi manyan ayyuka da kuma alamu masu banmamaki, har ta sa wuta ta sauko daga sama zuwa ƙasa a gaban idon mutane.14. Saboda alamun nan da aka ba ta iko tă yi a madadin dabban nan ta fari, sai ta ruɗi mazaunan duniya. Ta umarce su su kafa siffa don girmama dabbar da aka ji mata rauni da takobi duk da haka ta rayu.15. Aka ba ta iko tă ba da numfashi ga siffar dabban nan ta fari, don tă yi magana tă kuma sa a kashe duk waɗanda suka ƙi yi wa siffar sujada.16. Ta kuma tilasta wa kowa, manya da yara, mawadata da matalauta, ’yantattu da bayi, don a yi musu alama a hannun dama ko a goshi,17. don kada kowa yă saya ko yă sayar, sai dai yana da alamar, wadda take sunan dabbar ko kuma lambar sunanta.18. Wannan yana bukata hikima. Duk mai hankali, sai yă lissafta lambar dabbar, gama lamban nan ta mutum ne. Lambarta kuwa ita ce 666. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.