Baibul a cikin shekara guda Disamba 24Zefaniya 1:1-181. Maganar Ubangiji da ta zo wa Zefaniya ɗan Kushi, ɗan Gedaliya, ɗan Amariya, ɗan Hezekiya, a zamanin Yosiya ɗan Amon sarkin Yahuda.2. “Zan hallaka kome a fuskar duniya,” in ji Ubangiji.3. “Zan hallaka mutane da dabbobi; zan kuma hallaka tsuntsayen sama da kifayen teku, da gumakan da suke sa mugaye su yi tuntuɓe.” “Sa’ad da zan kawar da mutum daga fuskar duniya,” in ji Ubangiji.4. “Zan miƙa hannuna gāba da Yahuda da kuma dukan mazaunan Urushalima. Zan datse raguwar Ba’al daga wannan wuri, da sunayen firistocin gumaka da na marasa sanin Allah,5. waɗanda suka rusuna a kan rufin ɗaki don su yi sujada ga rundunar taurari. Waɗanda suka rusuna suka kuma yi rantsuwa da sunan Ubangiji suke kuma rantsuwa da sunan Molek.6. Waɗanda suka juya daga bin Ubangiji, ba sa kuma neman Ubangiji ko su nemi nufinsa.”7. Ku yi shiru a gaban Ubangiji Mai Iko Duka, gama ranar Ubangiji ta yi kusa. Ubangiji ya shirya hadaya; ya kuma tsarkake waɗanda ya gayyato.8. “A ranar hadayar Ubangiji zan hukunta sarakuna da kuma ’ya’yan sarakuna da duk waɗanda suke sanye da rigunan ƙasashen waje.9. A wannan rana zan hukunta dukan waɗanda suke kauce taka madogarar ƙofa, waɗanda suke cika haikalin allolinsu da rikici da ruɗu.10. “A wannan rana,” in ji Ubangiji, “Za a ji kuka daga Ƙofar Kifi, kururuwa daga Sabon Mazauni, da kuma amo mai ƙarfi daga tuddai.11. Ku yi kururuwa, ku da kuke zaune a yankin kasuwa; za a hallaka dukan ’yan kasuwanku, dukan waɗanda suke kasuwanci da azurfa za su lalace.12. A wannan lokaci zan bincike Urushalima da fitilu in kuma hukunta waɗanda ba su kula ba, waɗanda suke kamar ruwan inabin da aka bar a ƙasan tukunya, waɗanda suke tsammani, ‘ Ubangiji ba zai yi kome ba nagari ko mummuna.’13. Za a washe dukiyarsu, a rurrushe gidajensu. Za su gina gidaje amma ba za su zauna a ciki ba; za su shuka inabi amma ba za su sha ruwansa ba.”14. Babbar ranar Ubangiji ta yi kusa, ta yi kusa kuma tana zuwa da sauri. Ku saurara! Kukan ranar Ubangiji za tă yi zafi, za a ji kururuwan jarumi a can.15. Ranan nan za tă zama ranar fushi, rana ce ta baƙin ciki da azaba, rana ce ta tashin hankali da lalacewa, ranar duhu baƙi ƙirin, ranar gizagizai da baƙin duhu,16. rana ce ta busa ƙaho da kururuwar yaƙi gāba da birane masu mafaka, da kuma kusurwar hasumiyoyi.17. “Zan kawo baƙin ciki a kan mutane za su kuma yi tafiya kamar makafi, domin sun yi wa Ubangiji zunubi. Za a zubar da jininsu kamar ƙura kayan cikinsu kuma kamar najasa.18. Azurfarsu ko zinariyarsu ba za su iya cetonsu ba a ranar fushin Ubangiji.” A cikin zafin kishinsa za a hallaka dukan duniya gama zai kawo ƙarshen dukan mazaunan duniya nan da nan.Zefaniya 2:1-151. Ku tattaru, ku tattaru, Ya ku al’umma marar kunya,2. kafin ƙayyadadden lokacin nan yă zo ranan nan kuma ta share ku kamar ƙaiƙayi kuma kafin fushi mai tsanani na Ubangiji yă auko muku, kafin ranar fushin Ubangiji ta auko muku.3. Ku nemi Ubangiji, dukanku ƙasashe masu tawali’u, ku da kuke yin abin da ya umarta. Ku nemi adalci da tawali’u; mai yiwuwa ku sami mafaka a ranar fushin Ubangiji.4. Za a yashe Gaza a kuma bar Ashkelon kango. Da tsakar rana Ashdod za tă zama babu kowa a kuma tumɓuke Ekron.5. Taku ta ƙare ku da kuke zama a bakin teku, Ya ku mutanen Keretawa; maganar Ubangiji tana gāba da ke, Ya ke Kan’ana, ƙasar Filistiyawa. “Zan hallaka ki kuma babu abin da zai rage.”6. Ƙasar da take a bakin teku, inda Keretawa suke zaune, za tă zama wurin da makiyaya da ta garken tumaki.7. Za tă zama mallakar raguwar gidan Yahuda; a can za su sami wurin kiwo. Da yamma za su kwanta a gidajen Ashkelon. Ubangiji Allahnsu zai lura da su; zai maido musu da martabarsu.8. “Na ji irin zagin da Mowab take yi, da kuma ba’ar Ammonawa, waɗanda suka zagi mutanena suna kuma yi barazana a kan ƙasarsu.9. Saboda haka, muddin ina raye,” in ji Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, “tabbatacce Mowab za tă zama kamar Sodom, Ammonawa kuma kamar Gomorra, ƙasa mai ciyayi da rammukan gishiri, ƙasa marar amfani har abada. Raguwar mutanena za su washe su; waɗanda suka rage na al’ummata za su gāda ƙasarsu.”10. Wannan ne zai zama sakamakon girmankansu, saboda zagi da kuma ba’ar da suka yi wa mutanen Ubangiji Maɗaukaki.11. Ubangiji zai zama abin tsoro a gare su sa’ad da ya hallaka allolin ƙasar. Al’ummai a kowane bakin teku za su yi masa sujada, kowa a ƙasarsa.12. “Ku ma, ya Kushawa, za a kashe ku da takobina.”13. Zai kuma miƙa hannunsa gāba da arewa yă kuma hallaka Assuriya, zai mai da Ninebe kango gaba ɗaya ta kuma zama busasshiya kamar hamada.14. Garkuna za su kwanta a can, da kowace irin halitta, Mujiyar hamada da bushiya za su zauna a kan ginshiƙanta. Kukansu za tă ratsa tagogi, ɓuraguzai za su tare ƙofofin shiga, za a kware ginshiƙan al’ul.15. Birnin da yake harka ke nan da take zaune lafiya. Ta ce wa kanta, “Ni ce, kuma babu kamata.” Dubi irin kangon da ta zama mana, mazaunin namun jeji! Duk wanda ya wuce ta sai ya yi mata tsaki yana kaɗa kai.Zefaniya 3:1-191. Taki ta ƙare, ke birnin mai danniya, mai ’yan tawaye da kuma masu ƙazanta!2. Ba kya yi wa kowa biyayya, ba kya kuma yarda da kuskurenki. Ba kya dogara ga Ubangiji, ba kya kuma kusatowa kusa da Allahnki.3. Sarakunanki ruri ne na zakoki, shugabanninki kyarketan dare ne, waɗanda ba sa rage kome don safe.4. Annabawanki mahaukata ne mutanenki masu cin amana ne. Firistocinki suna ƙazantar da Wurin Mai Tsarki suna kuma keta dokoki.5. Ubangiji da yake cikinki mai adalci ne; ba ya yin abin da ba daidai ba. Kowace safiya yakan bayyana dokokinsa a fili, kowace sabuwar rana kuma ba ya kāsawa, duk da haka marasa adalci ba sa jin kunya.6. “Na daddatse al’ummai; an kuma rurrushe kagararsu. Na bar titunansu ba kowa, ba mai ratsawa a ciki. An ragargaza biranensu; ba wanda za a bari, babu ko ɗaya.7. Na ce wa birnin, ‘Tabbatacce za ki ji tsorona ki kuma yarda da gyara!’ Ta haka ba za a datse wurin zamanki ba, ba kuwa dukan hukuncena za su hau bisa kansu ba. Amma har yanzu suna marmari su yi rashin gaskiya a duk abin da suke yi.8. Saboda haka ku jira ni,” in ji Ubangiji; “a ranar da zan tsaya in ba da shaida, Na yanke shawara in tattara dukan al’ummai, in tattara mulkoki in kuma zuba fushina a kansu, da dukan zafin haushina. Za a mamaye dukan duniya da zafin fushina.9. “Sa’an nan zan tsarkake leɓunan mutanen, don dukansu su kira bisa ga sunan Ubangiji su kuma yi masa hidima kafaɗa da kafaɗa.10. Tun daga ƙetaren rafuffukan Kush masu yi mini sujada, mutanena da suke a warwatse, za su kawo mini hadayu.11. A wannan rana ba za ku sha kunya saboda laifofin da kuka yi mini, gama zan ɗauke wa wannan birni waɗanda suke farin ciki cikin girmankansu. Ba kuma za ka ƙara yin kallon reni a tuduna mai tsarki ba.12. Amma zan zauna a cikinki masu tawali’u da masu ƙasƙantar da kai, waɗanda suke dogara ga sunan Ubangiji.13. Raguwar Isra’ila ba za su ƙara aikata abin da ba daidai ba, ba za su faɗa ƙarya ba, ba kuwa za a sami ruɗu a bakunansu ba. Za su ci su kuma kwanta kuma babu wanda zai ba su tsoro.”14. Ki rera, ya Diyar Sihiyona; ki tā da murya, ya Isra’ila! Ki yi murna ki kuma yi farin ciki da dukan zuciyarki, Ya Diyar Urushalima!15. Ubangiji ya ɗauke hukuncinki, ya mai da abokan gābanki baya. Ubangiji, Sarkin Isra’ila, yana tare da ke; ba kuma za ki ƙara jin tsoron wani lahani ba.16. A wannan rana za su cewa Urushalima, “Kada ki ji tsoro, ya Sihiyona; kada ki bar hannuwanki su raunana.17. Ubangiji Allahnki yana tare da ke, mai iko ne don ceto. Zai yi matuƙar farin ciki da ke, zai rufe ki da ƙaunarsa, zai yi farin ciki da ke ta wurin rerawa.”18. “Zan cire taƙaici daga gare ki a ƙayyadaddun bukukkuwa; su kaya ne da kuma zargi a gare ki.19. A wannan lokaci zan jijji wa waɗanda suka danne ku; zan kuɓutar da guragu in kuma tattara waɗanda suke a warwatse. Zan sa a yabe su a kuma girmama su a kowace ƙasar da aka kunyatar da su.Zabura 147:1-61. Yabi Ubangiji. Yana da kyau a rera yabai ga Allahnmu, abu mai daɗi ne daidai ne kuma a yabe shi!2. Ubangiji ya gina Urushalima; ya tattara kamammu na Isra’ilan da aka kai bauta.3. Ya warkar da masu raunanar zuciya ya ɗaɗɗaura miyakunsu.4. Ya lissafta yawan taurari ya kuma kira kowannensu da suna.5. Shugabanmu mai girma ne mai iko duka; ganewarsa ba shi da iyaka.6. Ubangiji yana kula da masu sauƙinkai yakan yar da mugaye a ƙasa.Karin Magana 30:18-1918. “Akwai abubuwa uku da suke ba ni mamaki, abubuwa huɗu da ba na iya fahimtarsu,19. yadda gaggafa take firiya a sararin sama, yadda maciji yake tafiya a kan dutse, yadda jirgin ruwa yake tafiya a teku, da kuma sha’ani tsakanin namiji da ’ya mace.Ruʼuya ta Yohanna 14:1-201. Sai na duba, can a gabana kuwa ga Ɗan Rago, tsaye a kan Dutsen Sihiyona, tare da shi akwai kuma mutane 144,000 waɗanda suke da sunansa da sunan Ubansa a rubuce a goshinsu.2. Sai na ji ƙara daga sama kamar motsin ruwaye masu gudu, kamar kuma tsawa. Ƙarar da na ji ta yi kamar ta masu garaya da suke kiɗin garayarsu.3. Suka kuwa rera sabuwar waƙa a gaban kursiyin da kuma a gaban halittu huɗun nan masu rai, da kuma a gaban dattawa. Ba wanda ya iya koyon waƙar sai mutanen nan 144,000 da aka fansa daga duniya.4. Waɗannan su ne waɗanda ba su ƙazantar da kansu da mata ba, gama sun kiyaye kansu da tsarki. Suna bin Ɗan Ragon duk inda ya tafi. Su ne aka saya daga cikin mutane aka kuwa miƙa su kamar ’ya’yan fari ga Allah da kuma Ɗan Ragon.5. Ba a sami ƙarya a bakunansu ba; su kuma marasa aibi ne.6. Sai na ga wani mala’ika yana tashi sama a tsakiyar sararin sama, yana kuma da madawwamiyar bishara wadda zai yi shela ga waɗanda suke zama a duniya, ga kowace al’umma, kabila, harshe, da kuma jama’a.7. Ya ce da babbar murya, “Ku ji tsoron Allah ku kuma ɗaukaka shi, domin sa’ar hukuncinsa ya yi. Ku yi wa wannan da ya halicci sammai, ƙasa, teku, da maɓulɓulan ruwa sujada.”8. Mala’ika na biyu ya biyo yana cewa, “Ta fāɗi! Babilon Mai Girma ta fāɗi, wadda ta sa dukan al’ummai suka sha ruwan inabin hauka na zinanta.”9. Mala’ika na uku ya biyo su ya ce da babbar murya, “Duk wanda ya yi wa dabban nan da siffarta sujada ya kuma sami alamarta a goshi ko a hannu,10. shi ma zai sha ruwan inabin fushin Allah, wanda aka zuba da duk ƙarfinsa a kwaf fushinsa. Za a ba shi azaba da farar wuta mai ci a gaban tsarkakan mala’iku da na Ɗan Ragon.11. Hayaƙin azabarsu kuwa zai dinga tashi har abada abadin. Kuma babu hutu dare ko rana wa waɗanda suke wa dabbar da siffarta sujada, ko kuwa ga duk wanda ya sami alamar sunanta.”12. Wannan yana bukata haƙuri, a gefen tsarkakan da suke biyayya da umarnan Allah suka kuma kasance da aminci ga Yesu.13. Sai na ji murya daga sama ta ce, “Rubuta, Masu albarka ne matattun da suka mutu cikin Ubangiji daga yanzu zuwa gaba.” “I, za su huta daga faman aikinsu, gama ayyukansu za su bi su,” in ji Ruhu.14. Na duba, can gabana kuwa ga farin girgije, zaune kuma a kan girgijen kuwa ga wani da ya yi kamar “ɗan mutum” tare da rawanin zinariya a kansa da kuma lauje mai kaifi a hannunsa.15. Sai wani mala’ika ya fito daga haikali ya kuma yi kira da babbar murya ga wannan mai zaune a kan girgijen ya ce, “Ɗauki laujenka ka yi girbi, domin lokacin girbi ya yi, gama amfanin da yake duniya ya nuna.”16. Sai wannan mai zaune a girgijen ya wurga laujensa a duniya, sai aka kuwa girbe duniya.17. Wani mala’ika kuma ya fito daga haikali a sama, shi ma yana da lauje mai kaifi.18. Har yanzu, wani mala’ika mai lura da wuta, ya fito daga bagaden ya yi kira da babbar murya ga wannan wanda yake da lauje mai kaifi ya ce, “Ɗauki laujenka mai kaifi ka tattara kawunan ’ya’yan inabi daga kuringar inabin duniya, domin ’ya’yan inabin sun nuna.”19. Mala’ikan ya wurga laujensa a duniya, ya tattara ’ya’yan inabin, ya kuma zuba su cikin babbar wurin matsewar inabin fushin Allah.20. Aka tattake su a wurin matsin inabi a bayan gari, jini kuwa ya yi ta gudana daga wurin matsin inabi tsayinsa ya kai kamar tsawon linzami a bakin doki, nisansa kuma ya kai wajen kilomita 300. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.