Baibul a cikin shekara guda Disamba 26Zakariya 1:1-211. A wata na bakwai na shekara ta biyu ta mulkin Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa annabi Zakariya ɗan Berekiya ɗan Iddo.2. “ Ubangiji ya yi fushi sosai da kakanninku.3. Saboda haka ka gaya wa mutanen, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ku komo gare ni,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki, ‘ni kuma zan komo gare ku,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.4. Kada ku zama kamar kakanninku, waɗanda annabawa na dā suka ce musu, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ku juya daga mugayen hanyoyinku da mugayen abubuwan da kuke yi.’ Amma ba su saurara ba, ko ma su kula da ni, in ji Ubangiji.5. Yanzu ina kakanninku suke? Annabawan kuma fa, sun rayu har abada ne?6. Amma maganata da dokokina da na umarta ta wurin bayina annabawa fa, ashe, ba su tabbata ba a kan kakanninku? “Sa’an nan suka tuba suka ce, ‘ Ubangiji Maɗaukaki ya yi mana daidai abin da hanyoyinmu suka cancanci mu samu, kamar dai yadda ya yi niyya yi.’ ”7. 7-8 A rana ta ashirin da huɗu ga watan goma sha ɗaya, wato, watan Shebat, a shekara ta biyu ta Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa annabi Zakariya ɗan Berekiya ɗan Iddo.8. Da dare, na ga wahayi, a gabana kuwa ga mutum a kan jan doki! Yana tsaye a cikin itatuwa masu furanni, a bayansa a cikin itatuwan ci-zaƙi, a bayansa kuwa akwai dawakai masu ruwan ja, ruwan ƙasa-ƙasa da kuma ruwan fari.9. Sai na yi tambaya na ce, “Mene ne waɗannan ranka yă daɗe?” Mala’ikan da yake magana da ni ya amsa ya ce, “Zan nuna maka mene ne su.”10. Sai mutumin da yake tsaye cikin itatuwan ci-zaƙin ya yi bayani cewa, “Su ne waɗanda Ubangiji ya aika ko’ina a duniya.”11. Sai suka ce wa mala’ikan da yake tsaye cikin itatuwan ci-zaƙin, “Mun ratsa ko’ina a duniya, sai muka ga duniya duka tana zaman lafiya.”12. Sa’an nan mala’ikan Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Maɗaukaki, har yaushe za ka ci gaba da ƙi nuna wa Urushalima da kuma garuruwan Yahuda jinƙai, waɗanda kake fushi da su shekarun nan saba’in?”13. Sai Ubangiji ya yi wa mala’ikan da ya yi magana da ni magana da kalmomi masu daɗi da kuma masu ta’azantarwa.14. Sai mala’ikan da yake magana da ni ya ce, “Ka yi shelar maganan nan, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ina kishi domin Urushalima da Sihiyona,15. amma ina fushi da ƙasashen da suke ji suna zaman lafiya, na ɗan yi fushina kawai, amma sai suka ƙara musu masifar.’16. “Saboda haka, ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Zan komo Urushalima da jinƙai, a can ne za a sāke gina gidana. Za a kuma miƙe ma’auni a bisa Urushalima,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.17. “Ci gaba da yin shela, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Garuruwana za su sāke kwarara da wadata, Ubangiji kuma zai sāke yi wa Sihiyona ta’aziyya, yă kuma zaɓi Urushalima.’ ”18. Sa’an nan na dubi sama a gabana kuwa sai ga ƙahoni huɗu!19. Na tambayi mala’ikan da yake mini magana, na ce, “Mene ne waɗannan?” Ya amsa mini ya ce, “Waɗannan su ne ƙahonin da suka watsar da Yahuda, Isra’ila da kuma Urushalima.”20. Sa’an nan Ubangiji ya nuna mini maƙera guda huɗu.21. Na yi tambaya na ce, “Mene ne waɗannan suke zuwa yi?” Ya amsa ya ce, “Waɗannan ne ƙahonin da suka watsar da Yahuda har ba wanda yake iya ɗaga kansa, amma maƙeran sun zo don su tsorata su su kuma saukar da ƙahonin ƙasashen nan waɗanda suka ɗaga ƙahoninsu gāba da ƙasar Yahuda don su warwatsa ta.”Zakariya 2:1-131. Sa’an nan na ɗaga kai sai na ga mutum a tsaye riƙe da ma’auni a hannunsa!2. Sai na yi tambaya, na ce, “Ina za ka?” Ya amsa mini ya ce, “Zan je in auna Urushalima, in ga yadda fāɗinta da tsawonta suke.”3. Sai mala’ikan da yake yi mini magana ya tafi, sai wani mala’ika ya zo ya same shi4. ya ce masa, “Yi gudu, gaya wa saurayin can cewa, ‘Urushalima za tă zama birni marar katanga domin mutane da dabbobi masu yawa ƙwarai za su kasance a cikinta.5. Ni da kaina ne zan zama katangar wuta kewaye da birnin, in kuma zama darajarta,’ in ji Ubangiji.6. “Zo! Zo! Ku gudu daga ƙasar arewa,” in ji Ubangiji, “gama na warwatsa ku a kusurwoyi huɗu na sama,” in ji Ubangiji.7. “Zo, ya ke Sihiyona! Ku tsere, ku masu zama a cikin Diyar Babilon!”8. Gama ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Bayan ya ɗaukaka ni, ya kuma aiko ni ga ƙasashen da suka washe ku gama duk wanda ya taɓa ku ya taɓa ƙwayar idonsa ne.9. Ba shakka zan tā da hannuna a kansu domin bayinsu su washe su. Sa’an nan za ku san cewa Ubangiji Maɗaukaki ne ya aiko ni.10. “Ki yi sowa ki yi murna, ya ke Diyar Sihiyona. Gama ina zuwa, zan zauna a cikinki,” in ji Ubangiji.11. “Ƙasashe da yawa za su haɗa kai da Ubangiji a ranan nan, za su kuma zama mutanena. Zan zauna a cikinku, za ku kuma san cewa Ubangiji Maɗaukaki ne ya aiko ni gare ku.12. Ubangiji zai gāji Yahuda a matsayin rabonsa a cikin ƙasa mai tsarki zai kuma sāke zaɓi Urushalima.13. Ku yi tsit a gaban Ubangiji, dukanku ’yan adam, gama ya taso daga wurin zamansa mai tsarki.”Zakariya 3:1-101. Sa’an nan ya nuna mini Yoshuwa babban firist a tsaye a gaban mala’ikan Ubangiji, Shaiɗan kuma yana tsaye a damansa don yă tuhume shi.2. Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “ Ubangiji ya tsawata maka, Shaiɗan! Ubangiji wanda ya zaɓi Urushalima, ya tsawata maka! Ashe, mutumin nan ba shi ne sandar da take ƙonewa da aka ciro daga cikin wuta ba?”3. Yanzu an sa wa Yoshuwa tufafi masu dauda sa’ad da yake tsaye a gaban mala’ikan.4. Mala’ikan ya ce wa waɗanda suke tsaye a gabansa, “Ku cire masa tufafinsa masu dauda.” Sai ya ce wa Yoshuwa, “Duba, na ɗauke zunubanka, zan sa maka tufafi masu tsada.”5. Sai na ce, “Sa masa rawani mai tsabta a kansa.” Aka sa masa rawani mai tsabta a kansa aka kuma sa masa tufafi yayinda mala’ikan Ubangiji yake tsaye a wurin.6. Mala’ikan Ubangiji ya yi wa Yoshuwa wannan gargaɗi.7. “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘In za ka yi tafiya a hanyoyina ka kuma kiyaye abubuwan da nake so, za ka zama shugaban haikalina, ka kuma lura da ɗakunan shari’ata, zan kuma ba ka wuri cikin waɗannan da suke tsaye a nan.8. “ ‘Ka saurara, ya babban firist Yoshuwa, kai da abokanka da suke zaune a gabanka, ku da kuke alamun abubuwan da za su zo. Zan kawo bawana, wanda yake Reshe.9. Dubi dutsen da na ajiye a gaban Yoshuwa! Akwai idanu bakwai a kan wannan dutse guda, zan kuma yi rubutu a kansa,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki, ‘zan kuma kawar da zunubin ƙasan nan a rana ɗaya.10. “ ‘A wannan rana kowannenku zai gayyaci maƙwabcinsa yă zauna a ƙarƙashin itacen inabi da kuma na ɓaure,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.”Zabura 147:12-2012. Ki ɗaukaka Ubangiji, ya Urushalima; ki yabi Allahnki, ya Sihiyona.13. Gama yana ƙarfafa ƙyamaren ƙofofinki yana kuma albarkace mutanenki a cikinki.14. Yana ba da salama ga iyakokinki yana kuma ƙosar da ke da alkama mafi kyau.15. Yana ba da umarninsa ga duniya; maganarsa tana tafiya da sauri.16. Yana shimfiɗa ƙanƙara kamar ulu yă kuma watsar da hazo kamar toka.17. Yana zuba ƙanƙara kamar ƙananan duwatsu. Wa zai iya jure wa sanyin da ya aiko?18. Yakan aiki maganarsa ta kuwa narkar da su; yakan tā da iskarsa, ruwaye kuwa su gudu.19. Ya bayyana maganarsa ga Yaƙub, dokokinsa da ƙa’idodinsa ga Isra’ila.20. Bai yi wannan ga wata al’umma ba; ba su san dokokinsa ba. Yabi Ubangiji.Karin Magana 30:21-2321. “Akwai abubuwa uku da duniya kan yi rawan jiki, abubuwa huɗu da ba ta iya jurewa,22. bawan da ya zama sarki, wawan da ya ƙoshi da abinci,23. macen da ba a ƙauna wadda ta sami miji, da kuma baiwar da ta ɗauki matsayin uwargijiyarta.Ruʼuya ta Yohanna 16:1-211. Sai na ji wata babbar murya daga haikalin tana ce wa mala’iku bakwai nan, “Ku tafi ku zuba kwanoni bakwai nan na fushin Allah a kan duniya.”2. Mala’ika na fari ya je ya juye kwanonsa a bisan ƙasa, sai munanan gyambuna masu zafi suka fito a jikin mutanen da suke da alamar dabbar suka kuma yi wa siffarta sujada.3. Mala’ika na biyu ya juye kwanonsa a bisan teku, sai tekun ya zama jini kamar na mataccen mutum, kuma kowane abu mai rai da yake cikin tekun ya mutu.4. Mala’ika na uku ya juye kwanonsa a bisan koguna da maɓulɓulan ruwa, sai suka zama jini.5. Sa’an nan na ji mala’ikan da yake lura da ruwaye ya ce, “Kai mai adalci ne cikin waɗannan hukuntai, kai da kake yanzu, kake kuma a dā, Mai Tsarki, saboda yadda ka yi hukuncin nan;6. gama sun zub da jinin tsarkakanka da kuma annabawanka, ka kuwa ba su jini su sha, yadda ya dace da su.”7. Na kuma ji bagaden ya amsa, “I, Ubangiji Allah, Maɗaukaki, hukuntanka daidai yake na adalci ne kuma.”8. Mala’ika na huɗu ya juye kwanonsa a bisan rana, sai aka ba wa rana iko ta ƙona mutane da wuta.9. Aka ƙone su da zafin wuta mai tsanani suka kuwa la’anci sunan Allah wanda yake da iko a kan waɗannan annoban, amma suka ƙi su tuba su kuma ɗaukaka shi.10. Mala’ika na biyar ya juye kwanonsa a bisan gadon sarautar dabbar, mulkinta kuwa ya zama duhu. Mutane suka yi ta cizon bakinsu saboda azaba11. suka kuma la’anci Allah na sama saboda zafinsu, da kuma saboda gyambunansu, amma suka ƙi su tuba daga abin da suka riga suka yi.12. Mala’ika na shida ya juye kwanonsa a bisan babban kogin Yuferites, sai ruwansa ya shanye don a shirya hanya saboda sarakuna daga Gabas.13. Sa’an nan na ga mugayen ruhohi guda uku da suka yi kamar kwaɗi; suka fito daga bakin macijin nan, da kuma daga bakin dabbar, da kuma daga bakin annabin ƙaryan nan.14. Su ruhohin aljanu ne da suke aikata abubuwan banmamaki, sukan je wurin sarakunan dukan duniya, don su tattara su don yaƙi a babbar ranar Allah Maɗaukaki.15. “Ga shi, ina zuwa kamar ɓarawo! Mai albarka ne wanda yake zama a faɗake yana kuma saye da tufafinsa, don kada yă yi tafiya tsirara a kuma kunyata shi.”16. Sa’an nan aka tattara sarakuna zuwa wurin da a Ibraniyanci ake kira Armageddon.17. Mala’ika na bakwai ya juye kwanonsa cikin iska, daga haikalin kuwa sai aka ji wata babbar murya daga kursiyin, tana cewa, “An gama!”18. Sai ga walƙiya, ƙararraki, tsawa da kuma matsananciyar girgizar ƙasa. Ba a taɓa yin irin wannan girgizar ƙasar ba, tun kasancewar mutum a duniya, girgizar ƙasar kuwa gawurtacciya ce.19. Babban birnin ya rabu kashi uku, biranen al’ummai kuma suka rurrushe. Allah ya tuna da Babilon Mai Girma ya kuma ba ta kwaf cike da ruwan inabin fushinsa.20. Kowane tsibiri ya gudu ba a kuwa ƙara ganin duwatsu ba.21. Daga sararin sama manyan ƙanƙara masu nauyin gaske suka fāɗo a kan mutane. Suka kuma la’anci Allah saboda annobar ƙanƙarar, domin annobar ta yi muni ƙwarai. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.