Baibul a cikin shekara guda Disamba 27Zakariya 4:1-131. Sai mala’ikan da ya yi magana da ni ya komo ya farkar da ni, kamar yadda ake farkar da mutum daga barcinsa.2. Ya tambaye ni ya ce, “Me ka gani?” Na amsa, na ce, “Na ga wurin ajiye fitilan zinariya da kwano a kai, da kuma fitilu bakwai a kansa, da butocin kai wa fitilu mai guda bakwai.3. Akwai kuma itatuwan zaitun guda biyu a gefensa, ɗaya a gefen dama na kwanon ɗaya kuma a gefen hagunsa.”4. Na tambayi mala’ikan da ya yi magana da ni na ce, “Mene ne waɗannan, ranka yă daɗe?”5. Sai ya amsa ya ce, “Ba ka san mene ne waɗannan ba?” Na amsa, na ce, “A’a, ranka yă daɗe.”6. Sai ya ce mini, “Wannan ce maganar Ubangiji ga Zerubbabel. ‘Ba ta wurin ƙarfi ba, ko ta wurin iko, sai dai ta wurin Ruhuna,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.7. “Kai mene ne, ya babban dutse? A gaban Zerubbabel za a rushe ka ka zama fili. Sa’an nan Zerubbabel yă kawo dutsen da ya fi kyau, a kuma yi ta sowa ana cewa, ‘Allah yă yi masa albarka! Allah yă yi masa albarka!’ ”8. Sai maganar Ubangiji ta zo mini,9. “Hannuwan Zerubbabel sun kafa harsashin haikalin nan; hannuwansa ne kuma za su gama ginin. Sa’an nan ne za ka san cewa Ubangiji Maɗaukaki ne ya aiko ni zuwa wurinka.10. “Wa ya rena ranar ƙananan abubuwa? Mutane za su yi murna sa’ad da suka ga igiyar gwaji a hannun Zerubbabel. “Waɗannan guda bakwai ɗin su ne idanun Ubangiji, masu jujjuyawa cikin dukan duniya.”11. Sai na tambaye shi na ce, “Mene ne waɗannan itatuwan zaitun guda biyu tsaye a hagu da kuma daman wurin ajiye fitilan fitilu?”12. Na sāke tambaye shi na ce, “Mene ne waɗannan rassa biyun nan na zaitun a gefen bututu biyu na zinariya da suke zuba man zinariya?”13. Ya amsa ya ce, “Ba ka san mene ne waɗannan ba?” Na ce, “A’a, ranka yă daɗe.”Zakariya 5:1-111. Na sāke dubawa sai ga naɗaɗɗen littafi mai firiya a gabana!2. Sai ya tambaye ni ya ce, “Me ka gani?” Sai na amsa na ce, “Na ga naɗaɗɗen littafi mai firiya, tsawonsa ƙafa talatin da fāɗinsa kuma ƙafa goma sha biyar.”3. Sai ya ce mini, “Wannan ce la’anar da za tă ratsa dukan ƙasar; gama bisa ga abin da ya ce a gefe ɗaya, za a kawar da kowane ɓarawo, kuma bisa ga abin da ya ce a ɗaya gefen za a kawar da duk mai rantsuwar ƙarya.4. Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Zan aika shi, zai shiga gidan ɓarawo, da gidan mai rantsuwar ƙarya da sunana. Zai kasance a gidansa yă hallaka gidan da katakon da duwatsun.’ ”5. Sai mala’ikan da yake mini magana ya zo gaba ya ce mini, “Duba ka gani ko mene ne wannan da yake fitowa.”6. Na tambaya na ce, “Mene ne?” Ya amsa ya ce, “Kwando ne na awo.” Ya ƙara da cewa, “Wannan shi ne laifin mutanen a duk fāɗin ƙasar.”7. Sa’an nan aka ɗaga murfin dalman, a ciki kuwa ga mace zaune!8. Ya ce, “Wannan mugunta ce,” ya kuma tura ta cikin kwandon ya rufe da murfin dalman, ya kuma danna da dutse.9. Na ɗaga idona sama, sai ga mata biyu a gabana, iska tana hura fikafikansu! Suna da fikafikai kamar na shamuwa, suka kuma ɗaga kwandon sama.10. Na tambayi mala’ikan da yake magana da ni na ce, “Ina za ku kai kwandon?”11. Ya amsa ya ce, “Zuwa ƙasar Babiloniya don a gina masa haikali. Sa’ad da aka gama ginin, za a ajiye shi a ciki.”Zakariya 6:1-151. Na sāke ɗaga kai sama, sai ga kekunan yaƙi guda huɗu a gabana suna fitowa tsakanin duwatsu guda biyu, duwatsun tagulla!2. Karusa ta farko tana da jajjayen dawakai, ta biyu kuma baƙaƙen dawakai,3. ta ukun farare dawakai, ta huɗu kuma dawakai masu ɗigo-ɗigo a dukan jikinsu, dukansu kuwa ƙarfafa.4. Sai na tambayi mala’ikan da yake magana da ni na ce, “Mene ne waɗannan, ranka yă daɗe?”5. Mala’ikan ya amsa mini ya ce, “Waɗannan su ne ruhohi huɗu na sama, waɗanda suka fito daga wurin Ubangiji na dukan duniya.6. Wannan mai baƙaƙen dawakai zai nufi wajen ƙasar arewa, mai fararen dawakai zai nufi wajen yamma, sai kuma mai dawakai masu ɗigo-ɗigo a jiki zai nufi wajen kudu.”7. Da ƙarfafa dawakan suka fito, sai suka yi marmari su ratsa dukan duniya. Sai ya ce, “Ku ratsa dukan duniya!” Saboda haka suka ratsa dukan duniya.8. Sai ya kira ni ya ce, “Duba, waɗanda suka nufi wajen ƙasar arewa sun ba wa Ruhuna hutu a ƙasar arewa.”9. Maganar Ubangiji ta zo mini, ta ce,10. “Ka karɓi azurfa da zinariya daga masu zaman bauta Heldai, Tobiya, Yedahiya, waɗanda suka iso daga Babilon. A ranar kuma ka je gidan Yosiya ɗan Zefaniya.11. Ka ɗauki azurfar da zinariyar ka yi rawani, ka ɗora shi a kan babban firist, Yoshuwa ɗan Yehozadak.12. Ka ce masa ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ga mutumin da sunansa ne Reshe, zai kuma ratse daga inda yake yă gina haikalin Ubangiji.13. Shi ne zai gina haikalin Ubangiji, za a kuma martaba shi da daraja, zai kuma zauna yă yi mulki a kan kursiyinsa. Zai zama firist a kan kursiyinsa. Kuma a tsakanin biyun za a sami zaman lafiya.’14. Za a ba Heldai, Tobiya, Yedahiya da kuma Hen ɗan Zefaniya kamar abin tunawa a cikin haikalin Ubangiji.15. Waɗanda suke nesa za su zo su taimaka gina haikalin Ubangiji, za ku kuma san cewa Ubangiji Maɗaukaki ne ya aiko ni gare ku. Wannan zai faru in kuka yi biyayya sosai ga Ubangiji Allahnku.”Zabura 148:1-61. Yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji daga sammai, yabe shi a bisa sammai.2. Yabe shi, dukanku mala’ikunsa, yabe shi, dukanku rundunarsa na sama.3. Yabe shi, rana da wata, yabe shi, dukanku taurari masu haskakawa.4. Yabe shi, ku bisa sammai da kuma ku ruwan bisa sarari.5. Bari su yabi sunan Ubangiji, gama ya umarta aka kuwa halicce su.6. Ya sa su a wurarensu har abada abadin; ya ba da umarnin da ba zai taɓa shuɗe ba.Karin Magana 30:24-2824. “Akwai abubuwa huɗu a duniya da suke ƙanana, duk da haka suna da hikima ƙwarai.25. Kyashi halittu ne da ba su da ƙarfi sosai, duk da haka suna ajiyar abincinsu da rani;26. remaye halittu ne da ba su da ƙarfi sosai, duk da haka sukan yi gidajensu a duwatsu;27. fāra ba su da sarki, duk da haka suna tafiya tare bisa ga girma;28. ana iya kama ƙadangare da hannu, duk da haka akan same shi a fadodin sarakuna.Ruʼuya ta Yohanna 17:1-181. Ɗaya daga cikin mala’iku bakwai masu ɗauke da kwanoni bakwai nan, ya zo ya ce mini, “Zo, zan nuna maka hukuncin babbar karuwan nan da take zaune a bisan ruwaye masu yawa.2. Da ita ce sarakunan duniya suka yi zina mazaunan duniya kuma suka bugu da ruwan inabin zinace zinacenta.”3. Sa’an nan mala’ikan ya ɗauke ni cikin Ruhu zuwa hamada. A can na ga mace zaune a kan wata jan dabbar da aka rufe da sunayen saɓo tana kuma da kawuna bakwai da ƙahoni goma.4. Macen tana saye da tufafi masu ruwan ja da shunayya, tana ƙyalli da zinariya, duwatsu masu daraja da kuma lu’ulu’ai. Tana riƙe da kwaf na zinariya a hannunta, cike da abubuwa masu banƙyama da kuma ƙazantar zinace zinacenta.5. Sunan da aka rubuta a goshinta asiri ne, Babilon mai girma mahaifiyar karuwai da kuma na abubuwa masu banƙyama na duniya.6. Na ga cewa macen ta bugu da jinin tsarkaka, jinin waɗanda suka shaida Yesu. Da na gan ta, sai na yi mamaki ƙwarai.7. Sa’an nan mala’ikan ya ce mini, “Don me kake mamaki? Zan bayyana maka asirin macen nan da dabbar da take hawa, wadda take da kawuna bakwai da ƙahoni goma.8. Dabbar da ka gani, a dā ta taɓa kasancewa, a yanzu, ba ta, za tă kuma fito daga Abis zuwa ga hallakarta. Mazaunan duniya waɗanda ba a rubuta sunayensu a littafin rai tun kafin halittar duniya ba za su yi mamaki sa’ad da suka ga dabbar, domin a dā ta taɓa kasancewa, yanzu kuwa ba ta, duk da haka za tă dawo.9. “Wannan yana bukata hankali da kuma hikima. Kawuna bakwai nan tuddai bakwai ne da macen take zama a kai.10. Sarakuna bakwai ne kuma. Biyar sun fāɗi, ɗaya yana nan, ɗayan kuma bai zo ba tukuna; amma sa’ad da ya zo, zai kasance na ɗan lokaci.11. Dabbar da a dā ta taɓa kasancewa, amma yanzu ba ta, ita ce sarki na takwas. Ita ɗaya ce cikin bakwai ɗin, kuma tana tafiya zuwa ga hallakarta.12. “Ƙahonin nan goma da ka gani sarakuna goma ne da ba su riga sun karɓi mulki ba, amma waɗanda na sa’a guda za su karɓi iko a matsayin sarakuna tare da dabbar.13. Suna da manufa guda za su kuma ba wa dabbar ikonsu da kuma sarautarsu.14. Za su yi yaƙi da Ɗan Ragon, sai dai Ɗan Ragon zai ci nasara a bisansu domin shi ne Ubangijin iyayengiji, Sarkin sarakuna, tare da shi kuwa kirayayunsa, zaɓaɓɓunsa da kuma amintattu masu binsa za su kasance.”15. Sa’an nan mala’ikan ya ce mini, “Ruwayen da ka gani, inda karuwan take zama, jama’a ce, taro masu yawa, al’ummai da kuma harsuna.16. Dabbar da kuma ƙahoni goma da ka gani za su ƙi jinin karuwar. Za su kai ta ga hallaka su kuma bar ta tsirara; za su ci namanta su kuma ƙone ta da wuta.17. Gama Allah ya sa a zukatansu su cika nufinsa ta wurin yarda su ba wa dabbar ikonsu tă yi mulki, sai lokacin da kalmomin Allah sun cika.18. Macen da ka gani ita ce babban birnin da yake mulki a bisan sarakunan duniya.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.