Baibul a cikin shekara guda Disamba 28Zakariya 7:1-141. A shekara ta huɗu ta Sarki Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa Zakariya a rana ta huɗu ta watan tara, wato, watan Kisleb.2. Mutanen Betel sun aika Sharezer da Regem-Melek, tare da mutanensu su nemi tagomashin Ubangiji3. ta wurin tambayar firistocin da kuma annabawan gidan Ubangiji Maɗaukaki, “Ko ya kamata in yi makoki da azumi a wata na biyar, yadda na yi a shekaru masu yawa?”4. Sai maganar Ubangiji Maɗaukaki ta zo mini ta ce,5. “Ka tambayi dukan mutanen ƙasar da firistoci cewa, ‘Sa’ad da kuka yi makoki da azumi a wata na biyar da na bakwai dukan shekaru saba’in nan, a ainihi saboda ni kuka yi azumi?6. Kuma sa’ad da kuke ci kuke sha, ba kanku kuke yi wa shagali ba?7. Ashe, ba kalmomin da Ubangiji ya faɗi ke nan ta bakin annabawan farko ba sa’ad da Urushalima da garuruwan da suke kewaye da ita suke hutawa, suke cikin wadata, akwai kuma mutane a Negeb da yammancin gindin tuddai?’ ”8. Sai maganar Ubangiji ta sāke zuwa wa Zakariya cewa,9. “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ku yi shari’ar gaskiya; ku nuna jinƙai da tausayi ga juna.10. Kada ku danne gwauruwa ko maraya, baƙo ko talaka. A cikin zuciyarku kada ku yi mugun tunani game da juna.’11. “Amma suka ƙi su saurara; da taurinkai suka juya bayansu suka kuma toshe kunnuwansu.12. Suka taurare zukatansu kamar dutse, suka ƙi jin abin da doka ko kuma maganar Ubangiji Maɗaukaki take faɗi wadda ya aika ta wurin Ruhunsa ta wurin annabawan farko. Saboda haka Ubangiji Maɗaukaki ya ji fushi ƙwarai.13. “ ‘Sa’ad da na yi kira, ba su saurara ba; saboda haka sa’ad da suka kira, ba zan saurara ba,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.14. ‘Na warwatsar da su da guguwa a cikin dukan ƙasashe, inda suka zama baƙi. Aka bar ƙasar ta zama kango bayansu, da har ba mai shiga ko fita. Haka suka sa ƙasan nan mai daɗi ta zama kango.’ ”Zakariya 8:1-231. Maganar Ubangiji Maɗaukaki ta sāke zuwa gare ni.2. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Ina kishin Sihiyona ƙwarai; ina kuma cike da kishi dominta.”3. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Zan koma Sihiyona in zauna a Urushalima. Sa’an nan za a kira Urushalima Birnin Gaskiya, a kuma kira dutsen Ubangiji Maɗaukaki Dutse Mai Tsarki.”4. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Tsofaffi maza da mata za su sāke zauna a titunan Urushalima, kowanne da sanda a hannu saboda tsufa.5. Titunan birnin za su cika da samari da ’yan mata suna wasa.”6. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Mai yiwuwa ya zama da mamaki ga raguwar wannan mutanen da suke nan a lokacin, amma zai zama abin mamaki gare ni ne?” In ji Ubangiji Maɗaukaki.7. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Zan ceci mutanena daga ƙasashen gabas da yamma.8. Zan komo da su su zauna a Urushalima; za su zama mutanena, ni kuwa zan zama amintaccen Allahnsu mai adalci.”9. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Ku da yanzu kuke jin maganan nan da annabawa suka faɗi, waɗanda suke a nan lokacin da aka kafa harsashin haikalin Ubangiji Maɗaukaki, bari hannuwanku su zama da ƙarfi don a gama gina haikalin.10. Kafin wannan lokaci babu albashi domin mutum ko dabba. Ba wanda yake iya sakewa yă yi hidimominsa saboda maƙiya, domin na sa kowa yă zama maƙiyi maƙwabcinsa.11. Amma yanzu ba zan yi da waɗanda raguwar mutane yadda na yi da na dā ba,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.12. “Iri zai yi girma da kyau, kuringa za tă ba da ’ya’yanta, ƙasa za tă ba da hatsi, sama kuma za tă ba da raɓa. Zan ba da duk waɗannan abubuwa su zama gādo ga raguwar mutanen nan.13. Kamar yadda kuka zama abin la’ana a ƙasashe, ya Yahuda da Isra’ila, haka zan cece ku, za ku kuma zama albarka. Kada ku ji tsoro, sai dai ku bar hannuwanku su zama da ƙarfi.”14. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Kamar dai yadda na yi niyyar kawo muku bala’i, in kuma ƙi jin tausayi sa’ad da kakanninku suka ba ni haushi,” in ji Ubangiji Maɗaukaki,15. kada ku ji tsoro “saboda a yanzu na yi niyya in sāke yi wa Urushalima da Yahuda abu mai kyau.16. Abubuwan da za ku yi ke nan. Ku gaya wa juna gaskiya, ku kuma dinga yin shari’ar gaskiya a ɗakunanku na shari’arku;17. kada ku ƙulla wa maƙwabtanku mugunta, kuma kada ku so yin rantsuwa ta ƙarya. Ina ƙyamar waɗannan duka,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.18. Maganar Ubangiji Maɗaukaki ta sāke zuwa wurina.19. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Azumin wata na huɗu, da na watan biyar, da na watan bakwai da na watan goma za su zama lokutan farin ciki da murna da kuma bukukkuwa na murna ga Yahuda. Saboda haka sai ku ƙaunaci gaskiya da salama.”20. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Mutane da yawa da kuma mazaunan birane da yawa har yanzu za su zo,21. mazaunan wani birni za su je wurin mazaunan wani birni su ce, ‘Bari mu je nan da nan mu roƙi Ubangiji mu kuma nemi Ubangiji Maɗaukaki. Ni kaina zan je.’22. Mutane da yawa kuma da al’ummai masu ƙarfi za su zo Urushalima su nemi Ubangiji Maɗaukaki su kuma roƙe shi.”23. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “A kwanakin nan, mutane goma daga kabilu da al’ummai za su riƙe rigar mutumin Yahuda guda su ce, ‘Bari mu tafi tare da kai, domin mun ji cewa Allah yana tare da ku.’ ”Zakariya 9:1-171. Annabci. Maganar Ubangiji tana gāba da ƙasar Hadrak za tă kuma sauko a kan Damaskus, gama idanun dukan mutane da na kabilan Isra’ila suna a kan Ubangiji,2. da kuma a kan Hamat ita ma, wadda ta yi iyaka da ita, da kuma a kan Taya da Sidon, ko da yake suna da hikima ƙwarai.3. Taya ta gina wa kanta mafaka mai ƙarfi; ta tara azurfa kamar ƙasa, zinariya kuma kamar tarin shara a tituna.4. Amma Ubangiji zai karɓe mallakarta, zai hallaka ikonta da take da shi a kan teku, wuta kuma za tă cinye ta.5. Ashkelon za tă ga haka ta ji tsoro; Gaza za tă yi birgima cikin azaba, haka Ekron ma, gama za tă fid da zuciya. Gaza za tă rasa sarkinta za a kuma gudu a bar Ashkelon.6. Baƙi za su mallaki Ashdod, kuma zan kawar da girman kan Filistiyawa.7. Zan kawar da jini daga bakinsu, zan kuma cire abincin da aka haramta daga tsakanin haƙoransu. Waɗanda za a bari za su zama na Allahnmu, su kuma zama shugabanni a Yahuda, Ekron kuma za tă zama kamar Yebusiyawa.8. Amma zan kāre gidana daga sojoji masu kai da kawowa. Azzalumi ba zai ƙara cin mutanena da yaƙi ba, gama yanzu ina tsaro.9. Ki yi murna ƙwarai, ya Diyar Urushalima! Ki yi sowa, Diyar Urushalima! Duba, ga sarkinki yana zuwa wurinki, mai adalci yana kuma da ceto, mai tawali’u yana kuma hawan jaki, yana a kan ɗan aholaki, a kan ’yar jaka.10. Zan ƙwace kekunan yaƙi daga Efraim, da kuma dawakan yaƙi daga Urushalima, za a kuma karya bakan yaƙi. Zai yi shelar salama ga al’ummai. Mulkinsa zai yaɗu daga teku zuwa teku, daga Kogi kuma zuwa ƙarshen duniya.11. Ke kuma, saboda jinin alkawarina da ke, zan ’yantar da ’yan kurkukunki daga rami marar ruwa.12. Ku koma maɓuya, ya ku ’yan kurkuku masu sa zuciya; ko yanzu ma na sanar cewa zan mayar muku ninki biyu.13. Zan lanƙwasa Yahuda yadda nake lanƙwasa bakana, in kuma cika ta da Efraim kamar kibiya. Zan tā da ’ya’yanki maza, ya Sihiyona, gāba da ’ya’yanki, ya Girka, in kuma mai da ke kamar takobin jarumin yaƙi.14. Sa’an nan Ubangiji zai bayyana a bisansu; kibiyarsa za tă wulga kamar walƙiya. Ubangiji Mai Iko Duka zai busa ƙaho; zai taho ta cikin guguwa daga kudu,15. Ubangiji Maɗaukaki kuma zai tsare su. Za su hallakar su kuma yi nasara da duwatsun majajjawa. Za su sha su yi kururuwa kamar sun sha ruwan inabi; za su cika kamar kwanon da ake amfani don a yayyafa jini a kusurwoyin bagade.16. Ubangiji Allahnsu zai cece su a wannan rana gama su mutanensa ne da kuma garkensa. Za su haska a cikin ƙasarsa kamar lu’ulu’u a rawani.17. Za su yi kyan gani da kuma bansha’awa! Hatsi zai sa samari su yi murna, sabon ruwan inabi kuma zai sa ’yan mata su yi farin ciki.Zabura 148:7-147. Yabi Ubangiji daga duniya, ku manyan halittun teku da kuma dukan zurfafan teku,8. walƙiya da ƙanƙara, dusar ƙanƙara da gizagizai, hadirin iskar da suke biyayya da umarnansa,9. ku duwatsu da dukan tuddai, itatuwa masu ’ya’ya da dukan al’ul,10. namun jeji da dukan dabbobin gida, ƙanana halittu da tsuntsaye masu firiya,11. sarakunan duniya da dukan al’ummai, ku sarakuna da dukan masu mulkin duniya,12. samari da ’yan mata, tsofaffi da yara.13. Bari su yabi sunan Ubangiji, gama sunansa ne kaɗai mafi ɗaukaka; darajarsa ta fi ƙarfin duniya da sammai.14. Ya tayar wa mutanensa ƙaho, yabon dukan tsarkakansa, na Isra’ila, mutanen da suke kurkusa da zuciyarsa. Yabi Ubangiji.Karin Magana 30:29-3129. “Akwai abubuwa uku da suke jan jiki da kuma taƙama a tafiyarsu abubuwa huɗu waɗanda suke kwarjini da taƙama a tafiyarsu,30. zaki mai ƙarfi a cikin namun jeji, wanda ba ya ratse wa kowa;31. zakara mai taƙama, da bunsuru, da kuma sarki mai sojoji kewaye da shi.Ruʼuya ta Yohanna 18:1-241. Bayan wannan sai na ga wani mala’ika yana saukowa daga sama. Yana da iko mai girma, aka haskaka duniya da darajarsa.2. Ya yi kira da babbar murya ya ce, “Ta fāɗi! Babilon Mai Girma ta fāɗi. Ta zama gidan aljanu da kuma wurin zaman kowace irin mugun ruhu, wurin zaman kowane irin tsuntsu marar tsabta da mai banƙyama.3. Gama dukan al’ummai sun sha ruwan inabin haukan zinace zinacenta. Sarakunan duniya sun yi zina tare da ita, attajiran duniya kuma sun arzuta da almubazzarancinta.”4. Sai na ji wata murya daga sama ta ce, “Ku fita daga cikinta, mutanena, don kada zunubanta su shafe ku, don kada wata annobarta ta same ku;5. gama zunubanta sun yi tsororuwa sun kai sama. Allah kuma ya tuna da laifofinta.6. Ku sāka mata kamar yadda ta sāka muku; ku sāka mata sau biyu na abin da ta yi. Ku dama mata sau biyu na abin da yake cikin kwaf nata.7. Ku ba ta isashen azaba da baƙin ciki kamar daraja da kuma jin daɗin da ta ba wa kanta. A zuciyarta takan yi taƙama, ta ce, ‘Ina zama kamar sarauniya; ni ba gwauruwa ba ce, kuma ba zan taɓa yin makoki ba.’8. Saboda haka a rana ɗaya annobarta za su cim mata, mutuwa, makoki da kuma yunwa. Wuta zai cinye ta, gama Ubangiji Allah mai girma ne, wanda yake shari’anta ta.9. “Sa’ad da sarakunan duniya da suka yi zina da ita suka kuma yi tarayya cikin jin daɗinta suka ga hayaƙin ƙunarta, za su yi kuka da makoki saboda ita.10. Don tsoron ganin azabarta za su tsaya daga nesa, su yi kuka suna cewa, “ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma. Ya ke Babilon, birni mai iko! Cikin sa’a guda hallakarki ta zo!’11. “Attajiran duniya za su yi kuka su kuma yi makoki a kanta, domin ba wanda yake ƙara sayen kayayyakinsu12. kayayyakin zinariya, azurfa, duwatsu masu daraja da lu’ulu’ai; lallausan lilin, tufa masu ruwan shunayya, siliki da jan tufa; da kowane irin katakai masu ƙanshi da kayayyaki na kowane iri da aka yi da hauren giwa, katakai masu tsada, tagulla, baƙin ƙarfe da dutse mai sheƙi;13. kayayyakin sinnamon da kayan yaji, na turaren wuta, mur da turare, na ruwan inabi da man zaitun, na gari mai laushi da alkama; shanu da tumaki; dawakai da kekunan doki, da jikuna da kuma rayukan mutane.14. “Za su ce, ‘Amfanin da kike marmari ya kuɓuce. Dukan arzikinki da darajarki sun ɓace, ba kuwa za a ƙara samunsu ba.’15. Attajiran da suka sayar da waɗannan kayayyaki suka kuma sami arzikinsu daga gare ta za su tsaya daga nesa, cike da tsoron ganin azabarta. Za su yi kuka da makoki16. su ce, “ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma, saye da lallausan lilin, shunayya da kuma ja, mai walƙiya da zinariya, duwatsu masu daraja da kuma lu’ulu’ai!17. Cikin sa’a guda irin wannan dukiya mai yawa ta hallaka!’ “Duk matuƙan jirgin ruwa, da dukan waɗanda suke tafiya a jirgin ruwa, ma’aikatanta, da duk masu samun abin zama gari daga teku za su tsaya daga nesa.18. Sa’ad da suka ga hayaƙin ƙunarta, za su yi ihu su ce, ‘An taɓa samun birni kamar wannan babban birnin kuwa?’19. Za su zuba ƙura a kawunansu, da kuka da makoki za su yi ta kururuwa, “ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma, inda dukan waɗanda suke da jiragen ruwa a teku suka arzuta da ɗumbun dukiyarsa! Cikin sa’a ɗaya ta hallaka!’20. “Ki yi murna a kanta, ya sama! Ku yi murna, ku tsarkaka! Ku yi murna, ku manzanni da annabawa! Allah ya hukunta shi saboda abin da ya yi muku.”21. Sa’an nan wani mala’ika mai ƙarfi ya ɗauki dutse kamar girman babban dutsen niƙa ya jefa cikin teku ya ce, “Da wannan irin giggitawa za a jefar da birnin Babilon mai girma ƙasa, ba za a ƙara ganin ta ba.22. Ba za a ƙara jin ƙarar kiɗin masu garaya da muryar mawaƙa, da na masu bushe-bushe, da na masu busan ƙaho a cikinki ba. Ba za a ƙara samun ma’aikaci na kowace irin sana’a a cikinki kuma ba. Ba za a ƙara jin ƙarar dutsen niƙa a cikinki kuma ba.23. Hasken fitila ba zai ƙara haskakawa a cikinki ba. Ba za a ƙara jin muryar ango da amarya a cikinki ba. Attajiranki, dā su ne manyan mutanen duniya. Ta wurin sihirinki, dukan ƙasashe sun kauce.24. A cikinta aka sami jinin annabawa, da na tsarkaka, da kuma na dukan waɗanda aka kashe a duniya.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.