Baibul a cikin shekara guda Disamba 29Zakariya 10:1-121. Ku roƙi Ubangiji yă ba ku ruwa a lokacin bazara; Ubangiji ne yake yin gizagizan hadari. Shi ne yake ba wa mutane yayyafin ruwan sama yana kuma ba da tsire-tsire na fili ga kowa.2. Gumaka suna maganganun ruɗu, masu duba suna ganin wahayoyin ƙarya, suna faɗa mafarkan ƙarya suna ba da ta’aziyyar banza. Saboda haka mutane suna yawo kamar tumaki waɗanda suke shan wahala saboda rashin makiyayi.3. “Ina fushi da makiyayan, zan kuma hukunta shugabannin; gama Ubangiji Maɗaukaki zai lura da garkensa, wato, gidan Yahuda, zai kuma sa su zama kamar doki mai fariya cikin yaƙi.4. Daga Yahuda dutsen kusurwa zai fito, daga gare shi za a samu abin kafa tenti, daga gare shi za a sami bakan yaƙi, daga gare shi za a sami kowane mai mulki.5. Tare za su zama kamar mutane masu ƙarfi suna tattake lakar tituna a cikin yaƙi. Domin Ubangiji yana tare da su, za su yi faɗa su kuma yi nasara a kan masu yaƙi a kan dawakai.6. “Zan ƙarfafa gidan Yahuda in kuma ceci gidan Yusuf. Zan maido da su domin ina jin tausayinsu. Za su zama kamar ban taɓa ƙinsu ba, gama ni ne Ubangiji Allahnsu zan kuma amsa musu.7. Mutanen Efraim za su zama kamar mutane masu ƙarfi, zukatansu kuwa za su yi murna kamar sun sha ruwan inabi. ’Ya’yansu za su gani su yi murna; zuciyarsu za tă yi farin ciki a cikin Ubangiji.8. Zan ba da alama in kuma tattara su. Ba shakka zan fanshe su; za su yi yawa kamar yadda suke a dā.9. Ko da yake na warwatsa su cikin mutane, duk da haka a can ƙasashe masu nisa za su tuna da ni. Su da ’ya’yansu za su rayu, za su kuwa komo.10. Zan komo da su daga Masar in kuma tattara su daga Assuriya. Zan kawo su Gileyad da Lebanon, har wuri yă kāsa musu.11. Za su ratsa cikin tekun wahala; zan kwantar da raƙuman teku dukan zurfafan Nilu kuma za su bushe. Za a ƙasƙantar da Assuriya, sandar sarautar Masar kuma za tă rabu da ita.12. Zan ƙarfafa su a cikin Ubangiji kuma a cikin sunansa za su yi tafiya,” in ji Ubangiji.Zakariya 11:1-171. Buɗe ƙofofinki, ya Lebanon, don wuta ta cinye itatuwan al’ul naki.2. Yi kuka, ya itacen fir, gama itacen al’ul ya fāɗi; itatuwa masu daraja sun lalace! Ku yi kuka, ku itatuwan oak na Bashan; an sassare itatuwan babban kurmi!3. Ku ji kukan makiyaya; an ɓata musu wuraren kiwonsu masu ciyayi! Ku ji rurin zakoki; an lalatar da jejin Urdun!4. Ga abin da Ubangiji Allahna ya ce, “Yi kiwon garken tumakin da za a yanka.5. Masu sayensu sun yanyanka su, suka kuwa tafi ba hukunci. Masu sayar da su sun ce, ‘Yabi Ubangiji, na yi arziki!’ Makiyayansu ma ba su ji tausayinsu ba.6. Gama ba zan ƙara jin tausayin mutanen ƙasar ba,” in ji Ubangiji. “Zan ba da kowa ga maƙwabcinsa da kuma sarkinsa. Za su zalunci ƙasar, ba zan kuma cece su daga hannuwansu ba.”7. Saboda haka na yi kiwon garken da za a yanka, musamman garken da ake zalunta. Sai na ɗauki sanduna biyu na kira ɗaya Tagomashi, ɗaya kuma Haɗinkai, sai na yi kiwon garken.8. Cikin wata guda na kawar da makiyayan nan uku. Garken suka ƙi ni, na kuwa gaji da su9. na ce, “Ba zan zama makiyayinku ba. Bari masu mutuwa su mutu, masu hallaka kuma su hallaka. Bari waɗanda suka ragu su ci naman juna.”10. Sai na ɗauki sandana mai suna Tagomashi na karya shi, na janye alkawarin da na yi da dukan al’ummai.11. An janye shi a ranan nan, saboda haka garken da yake cikin wahala masu kallona sun san cewa maganar Ubangiji ce.12. Na faɗa musu cewa, “In kun ga ya fi kyau, ku biya ni; in kuwa ba haka ba, ku riƙe.” Saboda haka suka biya ni azurfa talatin.13. Sai Ubangiji ya ce mini, “Jefar da shi cikin ma’aji,” Lada mai kyau da aka yi cinikina ne! Saboda haka sai na ɗauki azurfa talatin ɗin na jefa su cikin gidan Ubangiji don a sa cikin ma’aji.14. Sai na karya sandana na biyu mai suna Haɗinkai, ta haka na karya ’yan’uwantakar da take tsakanin Yahuda da Isra’ila.15. Sai Ubangiji ya ce mini, “Ka sāke ɗaukar kayan aiki na wawan makiyayi.16. Gama zan tā da makiyayi a ƙasar wanda ba zai kula da ɓatattu, ko yă nemi ƙanana, ko yă warkar da waɗanda suka ji ciwo, ko kuma ciyar da masu lafiya ba, sai dai zai ci naman keɓaɓɓun tumaki, yă farfasa kofatonsu.17. “Kaito ga banzan makiyayin nan, wanda ya bar garken! Bari takobi yă sare hannunsa da idonsa na dama! Bari hannunsa yă shanye gaba ƙaf, idonsa na dama kuma yă makance sarai!”Zakariya 12:1-141. Annabci, maganar Ubangiji game da Isra’ila. Ubangiji, wanda ya shimfiɗa sammai, wanda ya kafa harsashin duniya, wanda kuma ya yi ruhun mutum a cikinsa ya ce,2. “Zan sa Urushalima ta zama kwaf mai sa mutanen da suke a dukan kewayenta, jiri. Yaƙi zai kewaye Urushalima har yă shafi Yahuda ma.3. A ranan nan, sa’ad da duk al’umman duniya za su tayar mata, zan sa Urushalima ta zama dutsen da ba a iya matsarwa ga dukan al’ummai. Duk waɗanda suka yi ƙoƙari su matsar da shi za su ji ciwo.4. A ranan nan zan sa kowane doki yă tsorata, mai hawan dokin kuma yă haukace,” in ji Ubangiji. “Zan sa idanuna in tsare gidan Yahuda, amma zan makantar da dukan dawakan al’ummai.5. Sa’an nan shugabannin Yahuda za su ce a cikin zukatansu, ‘Mutanen Urushalima suna da ƙarfi domin Ubangiji Maɗaukaki shi ne Allahnsu.’6. “A ranan nan zan sa shugabannin Yahuda su zama kamar tukunyar wuta a tarin itacen wuta; kamar harshen wuta a dammunan hatsi. Za su ƙone dukan mutanen da suke kewaye da su hagu da dama, amma babu abin da zai taɓa mutanen Urushalima.7. “ Ubangiji zai ceci wuraren zaman Yahuda da farko, don kada darajar gidan Dawuda da mazaunan Urushalima su fi na Yahuda daraja.8. A ranan nan Ubangiji zai kiyaye waɗanda suke zama a Urushalima, domin marasa ƙarfi a cikinsu su zama kamar Dawuda, gidan Dawuda kuma zai zama kamar Allah, kamar mala’ikan Ubangiji da yake tafiya a gabansu.9. A ranan nan zan fito don in hallaka dukan al’umman da suka yaƙi Urushalima.10. “Zan kuma zubo wa gidan Dawuda da mazaunan Urushalima ruhun alheri da na addu’a. Za su dube ni, wannan da suka soke shi, za su kuma yi makoki dominsa kamar yadda mutum yakan yi makokin mutuwar ɗansa tilo, su kuma yi baƙin ciki ƙwarai kamar yadda mutum yakan yi baƙin ciki don ɗan fari.11. A ranan nan kuka a Urushalima zai yi yawa kamar kukan Hadad Rimmon a filin Megiddo.12. Ƙasar za tă yi makoki, kowane iyali zai yi makoki a ware, tare da matansu su ma a ware, iyalin gidan Dawuda da matansu, iyalin gidan Natan da matansu,13. iyalin gidan Lawi da matansu, iyalin gidan Shimeyi da matansu,14. dukan sauran iyalan kuma da matansu.Zabura 149:1-41. Yabi Ubangiji. Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, yabonsa a cikin taron tsarkaka.2. Bari Isra’ila su yi farin ciki da Mahaliccinsu; bari mutanen Sihiyona su yi murna da Sarkinsu.3. Bari su yabi sunansa tare da rawa suna kuma yin kiɗi gare shi da ganga da garaya.4. Gama Ubangiji yana jin daɗin mutanensa; yakan darjanta masu sauƙinkai da ceto.Karin Magana 30:32-3332. “In ka yi wauta ka kuma ɗaukaka kanka, ko kuwa wani yana ƙulla maka mugunta, ka dāfa hannunka a bisa bakinka!33. Gama kamar yadda kaɗaɗɗen madara takan kawo mai, murɗa hanci kuma takan sa a yi haɓo, haka tsokanar fushi takan kawo faɗa.”Ruʼuya ta Yohanna 19:1-211. Bayan wannan sai na ji abin da ya yi kamar ƙasaitaccen taron mutane a sama, suna cewa, “Halleluya! Ceto da ɗaukaka da iko sun tabbata ga Allahnmu,2. gama hukuncinsa daidai ne, mai adalci kuma. Ya hukunta babbar karuwan nan wadda ta ɓata duniya da zinace zinacenta. Ya rama jinin bayinsa a kanta.”3. Suka sāke tā da murya suka ce, “Halleluya! Hayaƙin yake fitowa daga wurinta ya yi ta tashi sama har abada abadin.”4. Dattawan nan ashirin da huɗu da halittu huɗun nan masu rai suka fāɗi suka yi wa Allah sujada, wannan da yake zaune a kursiyi. Suka tā da murya suka ce, “Amin, Halleluya!”5. Sa’an nan wata murya ta fito daga kursiyin, tana cewa, “Ku yabi Allahnmu, dukanku da kuke bayinsa, ku da kuke tsoronsa, babba da yaro!”6. Sai na ji wani abu mai ƙara kamar ƙasaitaccen taron mutane, kamar rurin ruwaye masu gudu da kuma kamar bugun tsawa mai ƙarfi, suna tā da murya suna cewa, “Halleluya! Gama Ubangiji Allahnmu Maɗaukaki ne yake mulki.7. Bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna mu kuma ɗaukaka shi! Domin lokacin auren Ɗan Ragon ya yi, amaryarsa kuwa ta shirya kanta.8. Aka ba ta lallausan lilin, mai haske da tsabta ta sanya.” (Lallausan lilin yana misalta ayyukan adalci na tsarkaka.)9. Sai mala’ikan ya ce mini, “Rubuta, ‘Masu albarka ne waɗanda aka gayyace su zuwa bikin auren Ɗan Ragon!’ ” Sai ya ƙara da cewa, “Waɗannan su ne kalmomin Allah da gaske.”10. Da wannan sai na fāɗi a gabansa, don in yi masa sujada. Amma ya ce mini, “Kada ka yi haka! Ni ma abokin bauta ne da kai da kuma ’yan’uwanka waɗanda suke riƙe da shaidar Yesu. Ka yi wa Allah sujada! Domin shaidar Yesu ita ce ruhun annabci.”11. Sai na ga sama a buɗe can kuwa a gabana ga farin doki, sunan mahayinsa Mai Aminci da Mai Gaskiya ne. Da adalci yake shari’a yake kuma yaƙi.12. Idanunsa sun yi kamar harshen wuta, a kansa kuwa akwai rawani masu yawa. Yana da suna rubuce a kansa da babu wanda ya sani sai dai shi.13. Yana saye da rigar da aka tsoma a jini, sunansa kuwa Kalman Allah ne.14. Mayaƙan sama suna biye da shi, suna hawan fararen dawakai, saye da fararen tufafi masu tsabta na lallausan lilin.15. Daga bakinsa takobi mai kaifi ya fito. Da shi zai karkashe al’ummai. “Zai yi mulkinsu da sandan sarautar ƙarfe.” Yana tattake wurin matsin ruwan inabi na fushin Allah Maɗaukaki.16. A rigarsa da kuma a cinyarsa akwai wannan suna a rubuce, Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji.17. Na kuma ga wani mala’ika tsaye a cikin rana, wanda ya yi kira da babbar murya ga dukan tsuntsaye da suke tashi sama a tsakiyar sararin sama cewa, “Ku zo, ku taru don babban bikin nan na Allah,18. don ku ci naman sarakuna, jarumawa, da kuma manyan mutane, na dawakai da mahayansu, da kuma naman dukan mutane, ’yantacce da bawa, babba da yaro.”19. Sa’an nan na ga dabbar da sarakunan duniya da mayaƙansu sun taru don su yi yaƙi da wannan wanda yake kan farin dokin da kuma mayaƙansa.20. Amma aka kama dabbar tare da annabin ƙaryan nan wanda ya aikata alamu masu banmamaki a madadinta. Da waɗannan alamun ne ya ruɗe waɗanda suka sami alamar dabbar suka kuma bauta wa siffarta. Aka jefa dukansu biyu da rai cikin tafkin wuta ta da farar wuta mai ci.21. Sauran kuma aka kashe su da takobin da ya fito daga bakin wannan wanda yake kan dokin. Dukan tsuntsaye kuwa suka ci namansu iyakar iyawarsu. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.