Baibul a cikin shekara guda Disamba 3Daniyel 9:1-271. A shekara ta fari da mulkin Dariyus ɗan Zerzes (wanda yake Bamediye), wanda aka mai da shi sarki a masarautar Babiloniyawa2. a shekara ta farko ta mulkinsa, ni, Daniyel na gane daga cikin littattafai, bisa ga maganar Ubangiji da aka faɗa wa annabi Irmiya, cewa zaman Urushalima kango zai kai shekara saba’in.3. Sai na juya wurin Ubangiji Allah na roƙe shi ta wurin addu’a da koke-koke, cikin azumi, ina saye da tsummoki, na kuma zauna a cikin toka.4. Na yi addu’a ga Ubangiji Allahna na furta laifina. “Ya Ubangiji, mai alfarma da kuma Allah mai banrazana, wanda yake cika alkawarinsa na ƙauna ga duk wanda ya ƙaunace shi ya kuma kiyaye dokokinsa,5. mun yi zunubi muka kuma yi ba daidai ba. Mu mugaye ne da kuma ’yan tawaye; mun juya wa umarninka da shari’unka baya.6. Ba mu saurari bayinka annabawa ba, waɗanda suka yi magana a sunanka ga sarakunanmu da masu mulkinmu da iyayenmu, da kuma dukan mutanen ƙasa.7. “Ubangiji, kai mai adalci ne, amma a yau kunya ta rufe mu, mutanen Yahuda da mutanen Urushalima da na dukan Isra’ila, waɗanda suke kusa da kuma nesa, a dukan ƙasashen da ka warwatsa mu saboda rashin amincinmu a gare ka.8. Ya Ubangiji, mu da sarakunanmu, da masu mulkinmu da iyayenmu kunya ta rufe mu saboda mun yi maka zunubi.9. Ubangiji Allahnmu mai jinƙai ne, mai gafartawa ne kuma, ko da yake mun yi masa tawaye;10. ba mu yi biyayya ga Ubangiji Allahnmu ba, ba mu kuma kiyaye shari’unsa da ya ba mu ta wuri bayinsa annabawa ba.11. Dukan Isra’ila sun karya dokokinka suka kuma juya maka baya, sun ƙi yi maka biyayya. “Saboda haka la’anoni da rantsuwar hukunce-hukuncen da suke a rubuce a cikin Dokar Musa, bawan Allah, sun kama mu domin mun yi maka zunubi.12. Ka cika kalmomin da ka yi a kanmu da kuma a kan masu mulkinmu ta wurin kawo mana babban bala’i. A duniya duka ba a taɓa yin wani abu kamar yadda aka yi wa Urushalima ba.13. Kamar yadda yake a rubuce cikin Dokar Musa, dukan wannan bala’i ya sauko a kanmu, duk da haka ba mu nemi tagomashin Ubangiji Allahnmu ta wurin barin aikatawa zunubanmu, mu kuma mai da hankali a kan gaskiyarka ba.14. Ubangiji bai yi wata-wata wajen kawo mana bala’i ba, domin Ubangiji Allahnmu mai adalci ne a cikin dukan abin da yake yi; duk da haka ba mu yi masa biyayya ba.15. “Yanzu, ya Ubangiji Allahnmu, wanda ya fito da mutanensa daga Masar ta hannu mai ƙarfi wanda kuma ya yi wa kansa sunan da ya dawwama har yă zuwa yau, mun yi zunubi, mun yi abin da ba daidai ba.16. Ya Ubangiji, ta wurin kiyaye dukan ayyukanka na adalci, ka huce daga fushinka da hukuncinka da ka yi a kan Urushalima, birninka, tudunka mai tsarki. Zunubinmu da laifofin iyayenmu sun mai da Urushalima da kuma mutanenka abin ba’a ga dukan waɗanda suke kewaye da mu.17. “Yanzu, ya Allahnmu, ka ji addu’o’i da koke-koken bayinka. Saboda sunanka, ya Ubangiji, ka duba da rahama wurinka mai tsarki da ya zama kango.18. Ka kasa kunne, ya Allah, ka kuma ji; ka buɗe idanunka ka kuma ga yadda birninka ya zama kango, birnin da yake ɗauke da Sunanka. Ba cewa muna roƙonka saboda mu masu adalci ba ne, amma saboda girman jinƙanka.19. Ya Ubangiji, ka saurara! Ya Ubangiji ka gafarta! Ya Ubangiji, ka ji ka kuma yi wani abu! Saboda sunanka, ya Allahna, kada ka yi jinkiri, domin da sunanka ake kiran birninka da jama’arka.”20. Yayinda da nake magana da addu’a, ina furta zunubina da zunubin mutanena Isra’ila ina miƙa koke-kokena ga Ubangiji Allahna saboda tudunsa mai tsarki,21. yayinda nake cikin addu’a, sai Jibra’ilu, mutumin nan da na gani a wahayin da ya wuce, ya zo wurina gaggauce wajen lokacin yin hadaya ta yamma.22. Ya umarce ni ya kuma ce mini, “Daniyel, yanzu na zo domin in ba ka hikima da ganewa.23. Da zarar ka fara addu’a, an amsa, wadda na zo in faɗa maka, gama ana ƙaunar ka sosai. Saboda haka, ka yi lura da saƙon ka kuma fahimci wahayin.24. “An ƙayyade wa jama’arka da tsattsarkan birninka shekara ɗari huɗu da tasa’in domin a kawo ƙarshen laifi da zunubi, domin a yi kafarar laifi, sa’an nan a shigo da adalci madawwami, a rufe wahayi da annabci, a tsarkake haikali.25. “Sai ka sani ka kuma fahimci wannan; Tun daga sa’ad da aka kafa doka don a maido a kuma sāke gina Urushalima har sai Shafaffen nan, mai mulki, ya zo, za a yi shekara arba’in da tara, da shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu. Za a sāke gina ta a yi mata tituna da mafaka.26. Bayan shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu, za a datse Shafaffen nan zai kuma kasance ba shi da kome. Mutanen mai mulkin za su zo su hallaka birnin da kuma wuri mai tsarki. Ƙarshen zai zo kamar rigyawa. Yaƙi zai ci gaba har ƙarshe, a kuma hallakar kamar yadda aka ƙaddara.27. Zai tabbatar da alkawari da mutane masu yawa har na shekara bakwai. A tsakiyar bakwai ɗin nan ɗaya zai kawo ƙarshen duk wata hadaya da baiko. Kuma a kusurwar haikali zai sa abin ƙyama mai kawo hallaka, har sai ƙarshen da aka ƙaddara ya auko wa wanda ya sa abin ƙyama.”Daniyel 10:1-211. A shekara ta uku ta Sairus sarkin Farisa, sai aka ba wa Daniyel (wanda ake kira Belteshazar) wahayi. Saƙon kuwa gaskiya ce wadda take tattare da babban yaƙi. Fahimtar saƙon ya zo masa a cikin wahayi.2. A wannan lokaci ni Daniyel na yi makoki har na sati uku.3. Ban ci abinci mai kyau ba; ba nama ko ruwa inabin da ya shiga bakina; kuma ba na amfani da man shafawa gaba ɗaya har sai da sati nan uku suka wuce.4. A rana ta ashirin da huɗu ga watan farko, a sa’ad da nake tsaye a bakin babban kogi, Tigris,5. na ɗaga kaina na duba sai ga wani mutum tsaye sanye da rigar lilin, ya yi ɗamara da zinariya zalla daga Ufaz kewaye da ƙugunsa.6. Jikinsa kamar lu’ulu’u yake, fuskarsa kuma kamar walƙiya, idanunsa kamar harshen wuta, hannuwansa da ƙafafunsa kamar gogaggiyar tagulla, muryarsa kuma kamar amon babban taron jama’a.7. Ni, Daniyel, kaɗai ne na ga wahayin; mutanen da suke tare da ni ba su gani ba, amma wata irin babbar razana ta auko musu har suka gudu suka ɓuya.8. Sai aka bar ni ni kaɗai, ina juyayi wannan babban wahayi, ba ni da sauran ƙarfi, fuskata ta yamutse kuma ba ni da sauran ƙarfi.9. Sai na ji yana magana, da ina sauraronsa, sai na shiga barci mai nauyi, na kuwa fāɗi rubda ciki.10. Sai hannu ya taɓa ni ya sa makyarkyata a hannuna da ƙafafuna.11. Sai ya ce, “Daniyel, kai ne wanda ake ƙauna sosai, ka yi lura da kyau game da kalmomin da zan yi maka magana a kansu, ka tashi yanzu, gama an aiko ni a gare ka.” Sa’ad da ya faɗa mini haka, sai na tashi a tsaye ina rawan jiki.12. Sai ya ci gaba da cewa, “Kada ka ji tsoro, Daniyel. Gama tun daga ran da ka fara sa zuciya ga neman ganewa, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Allahnka, an ji addu’arka, amsar addu’arka ce ta kawo ni.13. Amma mai mulkin masarautar Farisa ya tsare ni har kwana ashirin da ɗaya. Sai da Mika’ilu, ɗaya daga cikin manya shugabanni, ya zo ya taimake ni, saboda an tsare ni a can tare da sarkin Farisa.14. Yanzu na zo domin in bayyana maka abin da zai faru da mutanenka nan gaba, gama wahayin ya shafi lokacin da bai riga ya zo ba ne.”15. Yayinda yake faɗin mini haka, sai na sunkuyar da kaina ƙasa shiru, ba magana.16. Sai wani wanda ya yi kama da mutum ya taɓa leɓunana, na kuma buɗe bakina sai na fara magana. Na ce wa wannan da yake tsaye a gabana, “Na cika da azaba saboda wannan wahayi, ranka yă daɗe, ina kuma neman taimako.17. Yaya ni bawanka zan iya magana da kai, ranka yă daɗe? Ƙarfina ya ƙare kuma ina numfashi da ƙyar.”18. Har yanzu wannan wanda yana kama da mutum ya taɓa ni ya kuma ba ni ƙarfi.19. Ya kuma ce, “Kada ka ji tsoro, ya kai mutumin da ake fahariya, salama a gare ka! Ka ƙarfafa yanzu; ka yi ƙarfin hali.” Sa’ad da ya yi magana da ni, sai na samu ƙarfi na ce, “Ka yi magana ranka yă daɗe, tun da yake ka sa na sami ƙarfi.”20. Sai ya ce mini, “Ka san abin da ya kawo ni gare ka? Ba da jimawa ba zan koma in yi yaƙi da mai mulkin Farisa, kuma idan na tafi, mai mulkin Hellenawa zai taso;21. amma da farko zan faɗa maka abin da aka rubuta a cikin Littafin Gaskiya (Babu wanda ya taimake ni yaƙi da waɗannan sai dai Mika’ilu, sarkinku.Zabura 137:7-97. Ka tuna, ya Ubangiji, abin da mutanen Edom suka yi a ranar da Urushalima ta fāɗi. Suka yi ihu suka ce, “A ragargaza ta, A ragargaza ta har tushenta!”8. Ya Diyar Babilon, an ƙaddara ke zuwa hallaka, mai farin ciki ne wanda ya sāka miki saboda abin da kika yi mana,9. shi da ya ƙwace jariranki ya fyaɗa su a kan duwatsu.Karin Magana 29:15-1515. Sandar gyara kan ba da hikima, amma yaron da aka bari ba horo kan jawo kunya ga mahaifiyarsa.1 Yohanna 1:1-101. Wannan da ya kasance tun farko, wanda muka ji, wanda muka gani da idanunmu, wanda muka duba, hannuwanmu kuma suka taɓa, wannan ne muke shela game da Kalman rai.2. Wannan Rai ya bayyana, muka kuwa gan shi, muka kuma shaida shi, muna kuwa yin muku shelar wannan rai madawwami, wanda dā yake tare da Uba, ya kuma bayyana a gare mu.3. Muna yin muku shelar abin da muka gani, muka kuma ji ne, domin ku ma ku yi zumunci tare da mu. Zumuncinmu kuwa yana tare da Uba da kuma Ɗansa, Yesu Kiristi.4. Muna rubuta wannan domin farin cikinmu yă zama cikakke.5. Wannan shi ne saƙon da muka ji daga wurinsa, muna kuma sanar da ku cewa Allah haske ne; a cikinsa kuwa babu duhu ko kaɗan.6. In muka ce muna zumunci da shi amma muna tafiya cikin duhu, ƙarya muke yi, kuma ba ma rayuwa bisa ga gaskiya.7. Amma in muna tafiya cikin haske, yadda yake cikin haske, muna da zumunci da juna ke nan, kuma jinin Yesu, Ɗansa, yana tsarkake mu daga dukan zunubi.8. In muka ce ba mu da zunubi, muna ruɗin kanmu ne, gaskiya kuwa ba ta cikinmu.9. In muka furta zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci kuma, zai gafarta mana zunubanmu, yă kuma tsarkake mu daga dukan rashin adalci.10. In muka ce ba mu yi zunubi ba, mun mai da shi maƙaryaci ke nan, maganarsa kuwa ba ta da wuri a cikinmu. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.