Baibul a cikin shekara guda Disamba 5Hosiya 1:1-111. Maganar Ubangiji da ta zo wa Hosiya ɗan Beyeri a zamanin mulkin Uzziya, Yotam, Ahaz da Hezekiya, sarakunan Yahuda, da zamanin mulkin Yerobowam ɗan Yowash sarkin Isra’ila.2. Sa’ad da Ubangiji ya fara magana ta wurin Hosiya, Ubangiji ya ce masa, “Ka tafi, ka auro wa kanka mazinaciya da ’ya’yan da aka haifa ta hanyar rashin aminci, domin ƙasar tana da laifin mummunan zina ta wurin rabuwa da Ubangiji.”3. Saboda haka sai ya auri Gomer ’yar Dibilayim, ta kuwa yi ciki ta haifi ɗa namiji.4. Sai Ubangiji ya ce wa Hosiya, “Ka ba shi suna Yezireyel, domin ba da daɗewa ba zan hukunta gidan Yehu saboda kisan da aka yi a Yezireyel, zan kuma kawo ƙarshen mulkin Isra’ila.5. A wannan rana zan karye ƙarfin Isra’ila a Kwarin Yezireyel.”6. Gomer ta sāke ɗauki ciki ta kuma haifi ’ya mace. Sai Ubangiji ya ce wa Hosiya, “Ka ba ta suna, Lo-Ruhama, gama ba zan ƙara nuna wa gidan Isra’ila ƙauna ba, har da zan gafarta musu.7. Duk da haka zan nuna ƙauna ga gidan Yahuda; zan kuma cece su, ba da baka, takobi ko yaƙi ba, ko ta wurin dawakai, ko masu hawan dawakai ba, sai ko ta wurin Ubangiji Allahnsu.”8. Bayan ta yaye Lo-Ruhama, sai Gomer ta sāke haifi wani ɗa namiji.9. Sai Ubangiji ya ce, “Ka ba shi suna Lo-Ammi, gama ku ba mutanena ba ne, ni kuma ba Allahnku ba ne.10. “Duk da haka Isra’ilawa za su zama kamar yashi a bakin teku, da ba za a iya aunawa ko a ƙirga ba. A inda aka ce musu, ‘Ku ba mutanena ba ne,’ za a kira su ‘’ya’yan Allah mai rai.’11. Mutanen Yahuda da mutanen Isra’ila za su sāke haɗu su zama ɗaya, za su kuma naɗa shugaba guda su kuma fita daga ƙasar, gama ranar za tă zama mai girma wa Yezireyel.Hosiya 2:1-221. “Ka ce da ’yan’uwanka maza, ‘Mutanena,’ ka kuma ce da ’yan’uwanka mata, ‘Ƙaunatacciyata.’2. “Ka tsawata wa mahaifiyarka, ka tsawata mata, gama ita ba matata ba ce, ni kuma ba mijinta ba ne. Ku roƙe ta tă daina karuwancinta da kuma rashin aminci a tsakanin nononta.3. In ba haka ba zai tuɓe ta tsirara in bar ta kamar yadda take a ranar da aka haife ta; zan sa ta zama kamar hamada, in mayar da ita busasshiyar ƙasar, in kashe ta da ƙishirwa.4. Ba zan nuna wa ’ya’yanta ƙaunata ba, domin su ’ya’yan zina ne.5. Mahaifiyarsu ta yi rashin aminci ta kuma ɗauki cikinsu ta wurin yi abin kunya. Ta ce, ‘Zan bi kwartayena, waɗanda suke ba ni abinci da ruwa, ulu nawa da lilina, mai nawa da kuma abin sha na.’6. Saboda haka zai tare hanyarta da ƙaya; zan yi mata katanga don kada tă sami hanya.7. Za tă bi kwartayenta amma ba za tă kama su ba; za tă neme su amma ba za tă same su ba. Sa’an nan za tă ce, ‘Zan koma ga mijina na fari, gama dā ya fi mini yadda nake a yanzu.’8. Ba ta yarda cewa ni ne wanda ya ba ta hatsi, sabon ruwan inabi da mai ba, wanda ya jibge mata azurfa da zinariya, waɗanda suka yi amfani wa Ba’al ba.9. “Saboda haka zan ƙwace hatsina sa’ad da ya nuna, da sabon ruwan inabina sa’ad da ya ƙosa. Zan karɓe ulu nawa da lilina, da take niyya ta rufe tsiraicinta.10. Saboda haka yanzu zan buɗe tsiraicinta a idanun kwartayenta; ba wani da zai ƙwace ta daga hannuwana.11. Zan tsayar da dukan bukukkuwarta, bukukkuwarta na shekara-shekara, da kuma kiyaye bikin Sababbin Wata nata, kwanakin Asabbacinta, dukan ƙayyadaddun bukukkuwarta.12. Zan lalatar da inabinta da kuma itatuwan ɓaurenta, waɗanda take cewa su ne abin da kwartayenta suka biya; zan mayar da su kurmi, namun jeji kuwa za su ci su.13. Zan hukunta ta saboda kwanakin da ta ƙone turare wa Ba’al; ta yi wa kanta ado da zobai da duwatsu masu daraja, ta bi kwartayenta, amma ta manta da ni,” in ji Ubangiji.14. “Saboda haka yanzu zan rarrashe ta; zan bishe ta zuwa hamada in kuma yi mata magana a hankali.15. A can zan mayar mata da gonakin inabinta, zan kuma sa Kwarin Akor yă zama ƙofar bege. A can za tă rera kamar a kwanakin ƙuruciyarta, kamar a lokacin da ta fita daga Masar.16. “A waccan rana,” in ji Ubangiji, “za ki ce da ni ‘mijina’; ba za ki ƙara ce ni ‘maigidana’ ba.17. Zan cire sunayen Ba’al daga leɓunanta; ba za a ƙara kira sunayensu ba.18. A waccan rana zan yi alkawari dominsu da namun jeji da kuma tsuntsayen sararin sama da dukan halittu masu rarrafe a ƙasa. Baka da takobi da yaƙi zan sa su ƙare a ƙasar, domin duk su zauna lafiya.19. Zan ɗaura aure da ke har abada; zan ɗaura aure da yake cikin adalci da gaskiya, cikin ƙauna da jinƙai.20. Zan ɗaura aure da yake cikin aminci za ki kuwa yarda cewa ni ne Ubangiji.21. “A waccan rana zan amsa,” in ji Ubangiji, “zan amsa wa sararin sama, za su kuwa amsa wa ƙasa;22. ƙasa kuma za tă amsa wa hatsi, sabon ruwan inabi da kuma mai, su kuma za su amsa wa Yezireyel.Zabura 138:4-64. Bari dukan sarakunan duniya su yabe ka, ya Ubangiji, sa’ad da suka ji maganganun bakinka.5. Bari su rera game da hanyoyin Ubangiji, gama ɗaukakar Ubangiji da girma take.6. Ko da yake Ubangiji yana bisa, yakan dubi kāsassu, amma tun da nesa ya san masu girman kai.Karin Magana 29:17-1717. Ka hori ɗanka, zai kuwa ba ka salama; zai ba ka farin cikin da kake so.1 Yohanna 3:1-241. Dubi irin ƙaunar da Uba ya ƙaunace mu da ita mana, har ana ce da mu ’ya’yan Allah! Haka kuwa muke! Dalilin da ya sa duniya ba tă san mu ba shi ne, don ba tă san shi ba.2. Abokaina ƙaunatattu, yanzu, mu ’ya’yan Allah ne, kuma abin da za mu zama nan gaba ba a riga an bayyana ba. Sai dai mun san cewa sa’ad da Kiristi ya bayyana, za mu zama kamar sa, domin za mu gan shi kamar yadda yake.3. Duk mai wannan bege a cikinsa yakan tsarkake kansa, kamar yadda shi Kiristi yake da tsabta.4. Duk mai yin zunubi yana karya doka ne; tabbatacce, zunubi, karya doka ne.5. Sai dai kun san cewa Kiristi ya bayyana ne domin yă ɗauke zunubanmu. A cikinsa kuwa babu zunubi.6. Ba mai rayuwa a cikinsa da yake cin gaba da yin zunubi. Kowa da yake aikata zunubi, bai taɓa ganinsa ba, bai ma san shi ba.7. ’Ya’yana ƙaunatattu, kada ku yarda wani yă ruɗe ku. Duk mai yin abin da yake daidai mai adalci ne, yadda Kiristi yake mai adalci.8. Duk mai aikata abin da yake zunubi shi na Iblis ne, domin Iblis mai aikata zunubi ne tun farko. Dalilin da ya sa Ɗan Allah ya bayyana kuwa shi ne don yă rushe aikin Iblis.9. Babu haifaffe na Allah da zai ci gaba da yin zunubi, domin iri na Allah yana a cikinsa; ba zai iya ci gaba da yin zunubi ba, domin haifaffe ne na Allah.10. Ta haka muka san waɗanda suke ’ya’yan Allah da kuma waɗanda suke ’ya’yan Iblis. Duk wanda ba ya yin abin da yake daidai, ba ɗan Allah ba ne; haka ma wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa.11. Wannan shi ne saƙon da kuka ji tun farko. Ya kamata mu ƙaunaci juna.12. Kada ku zama kamar Kayinu, wanda ya zama na mugun nan, ya kuma kashe ɗan’uwansa. Me ya sa ya kashe shi? Domin ayyukansa mugaye ne, na ɗan’uwansa kuma na adalci ne.13. Kada ku yi mamaki ’yan’uwana, in duniya ta ƙi ku.14. Mun san cewa mun riga mun ratsa daga mutuwa zuwa rai, domin muna ƙaunar ’yan’uwanmu. Duk wanda ba ya ƙauna matacce ne har yanzu.15. Duk mai ƙin ɗan’uwansa mai kisankai ne, kun kuma san cewa ba mai kisankan da yake da rai madawwami a cikinsa.16. Yadda muka san ƙauna ke nan, wato, Yesu Kiristi ya ba da ransa dominmu. Ya kamata mu ma mu ba da rayukanmu domin ’yan’uwanmu.17. In wani yana da arziki, ya kuma ga ɗan’uwansa cikin rashi, bai kuwa taimake shi ba, anya, ƙaunar Allah tana a cikinsa kuwa?18. ’Ya’yana ƙaunatattu, kada mu yi ƙauna da fatar baki kawai, sai dai mu nuna ta ta wurin aikatawa da kuma gaskiya.19. Ta haka muka san cewa mu na gaskiya ne, kuma za mu iya tsaya a gaban Allah ba tare da rawar jiki ba.20. Idan zuciyarmu ta nuna mana muna da laifi, mun san cewa Allah ya fi zuciyarmu, ya kuma san dukan kome.21. Abokaina ƙaunatattu, in zukatanmu ba su ba mu laifi ba, muna da ƙarfin halin tsayawa a gaban Allah ke nan.22. Muna kuma samun dukan abin da muka roƙa daga gare shi, domin muna biyayya da umarnansa, muna kuma yin abin da ya gamshe shi.23. Umarninsa kuwa shi ne, mu gaskata da sunan Ɗansa, Yesu Kiristi, mu kuma ƙaunaci juna kamar yadda ya umarce mu.24. Waɗanda suke biyayya da umarnansa kuwa suna rayuwa a cikinsa, shi kuma a cikinsu. Ta haka muka san cewa yana raye a cikinmu. Mun san haka ta wurin Ruhun da ya ba mu. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.