Baibul a cikin shekara guda Fabrairu 11Fitowa 33:1-231. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka bar wannan wuri, kai da mutanen da ka fito da su daga Masar, ka haura zuwa ƙasar da na alkawarta da rantsuwa wa Ibrahim, Ishaku da Yaƙub cewa, ‘Zan ba zuriyarka.’2. Zan aika da mala’ika a gabanka in kuma kori Kan’aniyawa, Amoriyawa, Hittiyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa.3. Ka haura zuwa ƙasar da take zub da madara da zuma. Amma ba zan tafi tare da ku ba, saboda ku mutane ne masu taurinkai domin mai yiwuwa in hallaka ku a hanya.”4. Da mutane suka ji wannan mugun magana, sai suka fara makoki. Ba kuma wanda ya sa kayan ado.5. Gama Ubangiji ya riga ya ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Ku mutane ne masu taurinkai. In na yi tafiya da ku ko na ɗan lokaci, mai yiwuwa in hallaka ku. Yanzu sai ku tuɓe kayan adonku, zan kuwa yanke shawara a kan abin da zan yi da ku.’ ”6. Saboda haka Isra’ilawa suka tuttuɓe kayan adonsu a Dutsen Horeb.7. Musa fa ya saba ɗaukan tenti yă kafa shi a bayan sansani da ɗan nisa, yana kiransa “Tentin Sujada.” Duk wanda yake neman wani abu daga wurin Ubangiji sai yă tafi Tentin Sujada a bayan sansani.8. A sa’ad da kuma Musa ya fita zuwa Tentin, dukan mutanen sukan tashi su tsaya a ƙofofin tentinsu, suna kallon Musa, sai ya shiga tentin.9. Yayinda Musa ya shiga cikin tentin, sai al’amudin girgije yă sauko, yă tsaya a ƙofar yayinda Ubangiji yana magana da Musa.10. Lokacin da mutane suka ga al’amudin girgije a tsaye a ƙofar tentin, sai duk su miƙe tsaye su yi sujada, kowa a ƙofar tentinsa.11. Ubangiji yakan yi magana da Musa fuska da fuska, kamar yadda mutum yake magana da abokinsa. Sa’an nan Musa yă koma sansani, amma saurayin nan Yoshuwa ɗan Nun mai taimakonsa ba ya barin tentin.12. Musa ya ce wa Ubangiji, “Kana ta faɗa mini cewa, ‘Ka jagoranci mutane nan,’ amma ba ka faɗa mini wanda zai tafi tare da ni ba. Ga shi ka ƙara ce mini, ‘Na san ka, na san sunanka, ka kuma sami tagomashi a wurina.’13. In ka ji daɗina, ka koya mini hanyarka don in san ka, in kuma ci gaba da samun tagomashi daga gare ka. Ka tuna cewa wannan al’umma mutanenka ne.”14. Ubangiji ya amsa ya ce, “Zan tafi tare da kai, zan kuma rage maka nauyin kaya.”15. Musa kuwa ya ce masa, “In ba za tă tafi tare da mu ba, to, kada ka ɗaga mu daga nan.16. Yaya wani zai sani ko ka ji daɗina da kuma mutanenka, in ba ka tafi tare da mu ba? Mene ne kuma zai bambanta ni da mutanenka daga sauran jama’ar da suke a duniya?”17. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Zan yi yadda ka faɗa, gama ka sami tagomashi a wurina, na san ka, na kuma san sunanka.”18. Musa kuwa ya ce, “To, ka nuna mini ɗaukakarka.”19. Sai Ubangiji ya ce, “Zan wuce a gabanka, Ni Ubangiji zan yi shelar sunana a gabanka. Zan yi alheri ga duk wanda na so in yi masa alheri, zan nuna jinƙai ga duk wanda na so in yi masa jinƙai.20. Amma ya ce, ba za ka ga fuskata ba, don ba mutumin da zai gan ni yă rayu.”21. Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Ga wani wuri kusa da ni inda za ka tsaya bisa dutsen.22. A sa’ad da ɗaukakata tana wucewa, zan sa ka a cikin tsaguwar dutsen, in rufe ka da hannuna har sai na wuce.23. Sa’an nan zan ɗauke hannuna, ka kuwa ga bayana; amma fuskata, ba za ka gani ba.”Fitowa 34:1-351. Ubangiji ya ce wa Musa “Sassaƙa alluna biyu kamar na farko, ni kuwa in rubuta kalmomin da suke cikin alluna na farko da ka farfasa.2. Ka shirya da safe, ka hauro kan Dutsen Sinai. Ka gabatar da kanka a gare ni a can kan dutse.3. Ba wani da zai zo tare da kai, ko a gan shi ko’ina a kan dutsen, kada garkunan tumaki ko na shanu su yi kiwo kusa da dutsen.”4. Saboda haka Musa ya sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na fari, sai ya hau Dutsen Sinai da sassafe, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi, yana kuma ɗauke da alluna biyu na dutse a hannuwansa.5. Sa’an nan Ubangiji ya sauko a cikin girgije ya tsaya can tare da shi, ya kuma yi shelar sunansa.6. Sai Ubangiji ya wuce a gaban Musa, ya yi shela ya ce, “Ni ne Ubangiji Allah mai tausayi, mai alheri, mai jinkirin fushi, cike da ƙauna da aminci,7. nakan nuna ƙauna wa dubbai, nakan kuma gafarta mugunta, tawaye da zunubi. Amma ba na barin mai laifi, ba tare da na hore shi ba; nakan hukunta ’ya’ya da jikoki har tsara ta uku da ta huɗu saboda laifin iyaye.”8. Musa ya yi sauri ya rusuna har ƙasa, ya yi sujada.9. Ya ce, “Ya Ubangiji, in na sami tagomashi a idanunka, bari Ubangiji yă tafi tare da mu. Ko da yake wannan mutane masu taurinkai ne, ka gafarta muguntanmu da zunubanmu, ka kuma sāke sa mu zama abin gādonka.”10. Sai Ubangiji ya ce, “Ga shi na yi alkawari da kai. A gaban dukan mutanenka zan yi abubuwan banmamakin da ba a taɓa yinsa a cikin wata al’umma a duniya ba. Mutanen da kuke zaune cikinsu za su ga aikin bantsoro, da Ni Ubangiji zan yi muku.11. Ku yi biyayya da umarnin da na ba ka yau. Zan kora muku Amoriyawa, Kan’aniyawa, Hittiyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa.12. Ku kula, kada ku yi yarjejjeniya da waɗanda suke zaune a ƙasar da za ku tafi, in ba haka ba, za su zama muku tarko.13. Ku rurrushe bagadansu, ku farfashe keɓaɓɓun duwatsunsu, ku sassare ginshiƙan Asheransu.14. Kada ku bauta wa wani allah, gama Ubangiji, wanda sunansa Kishi, Allah ne mai kishi.15. “Ku kula, kada ku yi yarjejjeniya da mazaunan wannan ƙasa, don kada sa’ad da suke yi wa allolinsu sujada, suna miƙa musu hadaya, su gayyace ku, ku ci hadayar da suka miƙa wa allolinsu.16. Kada ku auro wa ’ya’yanku maza ’yan matansu, waɗanda suke yi wa alloli sujada, har su sa ’ya’yanku su bi allolinsu.17. “Kada ku yi alloli na zubi.18. “Sai ku yi Bikin Burodi Marar Yisti. Ku kuma ci burodi marar yisti har kwana bakwai, kamar yadda na umarce ku. Ku yi wannan a ƙayyadadden lokacinsa a watan Abib, gama a cikin watan ne kuka fita daga Masar.19. “Ɗan fari na kowane mutum zai zama nawa, har da ɗan farin na dabbobi, ko na garken shanu ko na tumaki.20. Ku fanshi ɗan farin jaki da na tunkiya, amma in ba ku fanshe shi ba, ku karya wuyansa. Ku fanshi duk ’ya’yan farinku maza. “Kada wani yă zo gabana hannu wofi.21. “Kwana shida za ku yi aiki, amma a rana ta bakwai za ku huta; ko da lokacin noma ne, ko lokacin girbi, sai ku huta.22. “Ku kiyaye Bikin Makoni wato, bikin girbin nunan fari na alkama, da Bikin Gama Tattara amfanin gonaki, a ƙarshen shekara.23. Sau uku a shekara, dukan mazanku za su bayyana a gaban Ubangiji Mai Iko Duka, Allah na Isra’ila.24. Zan kore al’umma daga gabanku, in fadada kan iyakarku, babu wanda zai yi ƙyashin ƙasarku a lokutan nan uku na shekara da kuka haura don ku bayyana a gaban Ubangiji, Allahnku.25. “Kada ku miƙa mini jinin hadaya tare da wani abin da yana da yisti, kada kuma ku bar kowace hadaya ta Bikin Ƙetarewa ta kwana.26. “Ku kawo nunan farin amfanin gonarku mafi kyau a gidan Ubangiji, Allahnku. “Kada ku dafa ɗan akuya a cikin madarar mahaifiyarsa.”27. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka rubuta waɗannan kalmomi, gama bisa ga kalmomin nan, na yi alkawari da kai da kuma Isra’ila.”28. Musa ya kasance tare da Ubangiji kwana arba’in da dare arba’in, bai ci ba, bai sha ba. Ya kuma rubuta kalmomin alkawari a kan alluna, wato, dokoki goma.29. Sa’ad da Musa ya sauko daga kan Dutsen Sinai tare da alluna biyu na Alkawari a hannuwansa, bai san cewa fuskarsa tana ƙyalli ba saboda zaman da ya yi a gaban Ubangiji.30. Da Haruna da dukan Isra’ila suka ga Musa, fuskarsa kuma tana ƙyalli, sai suka ji tsoron zuwa kusa da shi.31. Amma Musa ya kira su, sai Haruna da dukan shugabannin jama’ar suka zo wurinsa, ya kuwa yi musu magana.32. Daga baya sai dukan Isra’ilawa suka zo kusa da shi, ya kuma ba su dukan dokokin da Ubangiji ya ba shi a Dutsen Sinai.33. Da Musa ya gama magana da su, sai ya lulluɓe fuskarsa.34. Amma duk sa’ad da ya je gaban Ubangiji don yă yi magana da shi, sai yă tuɓe lulluɓin har sai ya fito. Kuma duk sa’ad da ya fito yă faɗa wa Isra’ilawa abin da aka umarce shi,35. sai su ga fuskarsa tana ƙyalli. Sa’an nan Musa yă sāke lulluɓe fuskarsa, har sai ya shiga don yă yi magana da Ubangiji.Zabura 21:8-138. Hannunka zai kakkama dukan abokan gābanka; hannunka na dama zai kakkama masu ƙinka.9. A lokacin bayyanarka za ka sa su zama kamar wutar matoya. Cikin fushinsa Ubangiji zai haɗiye su, kuma wutarsa za tă cinye su.10. Za ka hallaka ’ya’yansu daga duniya, zuriyarsu kuma daga ’yan adam.11. Ko da yake suna shirya maka mugunta suna kuma ƙirƙiro mugayen dabaru, ba za su yi nasara ba;12. gama za ka sa su juye bayansu sa’ad da ka auna su da bakan da ka ja.13. Ka sami ɗaukaka, ya Ubangiji cikin ƙarfinka; za mu rera mu kuma yabi ikonka.Karin Magana 8:1-51. Hikima ba ta yin kira ne? Fahimi ba ya tā da muryarsa ne?2. A ƙwanƙoli a kan hanya, inda hanyoyi suka haɗu, ta ɗauki matsayinta;3. kusa da ƙofofin shiga cikin birni, a mashigai, ta tā da murya,4. “Gare ku, ya mutane, nake kira; na tā da muryata ga dukan ’yan adam.5. Ku da kuke marasa azanci, ku yi hankali; ku da kuke wawaye, ku nemi fahimi.Mattiyu 26:1-251. Sa’ad da Yesu ya gama faɗin dukan waɗannan abubuwa, sai ya ce wa almajiransa,2. “Kamar yadda kuka sani, Bikin Ƙetarewa sauran kwana biyu, za a kuma ba da Ɗan Mutum don a gicciye shi.”3. Sai manyan firistoci da dattawan mutane, suka taru a fadan babban firist, mai suna Kayifas,4. suka ƙulla shawara su kama Yesu da makirci, su kuma kashe shi.5. Suka ce, “Amma ba a lokacin Biki ba, don kada mutane su tā da rikici.”6. Yayinda Yesu yake a Betani, a gidan wani mutumin da ake kira Siman Kuturu,7. wata mace ta zo wurinsa da wani ɗan tulun alabasta na turaren mai tsada sosai, wanda ta zuba a kansa a lokacin da yake cin abinci.8. Sa’ad da almajiransa suka ga wannan, sai suka yi fushi. Suka ce, “Wannan almubazzaranci fa!9. Wannan turare ai, da an sayar da shi da kuɗi mai yawa a ba matalauta kuɗin.”10. Sane da wannan, Yesu ya ce musu, “Me ya sa kuke damun macen nan? Ta yi mini abu mai kyau ne.11. Matalauta za su kasance tare da ku kullum, amma ni ba zan kasance tare da ku kullum ba.12. Sa’ad da ta zuba turaren nan a jikina, ta shirya ni ne don jana’izata.13. Gaskiya nake gaya muku, duk inda aka yi wa’azin bisharan nan a duniya duka, abin da matan nan ta yi, za a riƙa faɗarsa don tunawa da ita.”14. Sai ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, wanda ake kira Yahuda Iskariyot, ya je wurin manyan firistoci15. ya ce, “Me za ku ba ni, in na bashe shi gare ku?” Sai suka ƙirga masa kuɗi azurfa talatin.16. Daga wannan lokaci, Yahuda ya yi ta neman zarafin da zai miƙa shi.17. A rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, sai almajiran suka zo wurin Yesu suka yi tambaya suka ce, “Ina kake so mu je mu shirya maka wurin da za ka ci Bikin Ƙetarewa?”18. Ya amsa ya ce, “Ku shiga gari wurin wāne, ku ce masa, ‘Malam ya ce, lokacina ya yi kusa. Zan ci Bikin Ƙetarewa tare da almajiraina a gidanka.’ ”19. Saboda haka almajiran suka yi yadda Yesu ya umarce su, suka kuwa shirya Bikin Ƙetarewa.20. Da yamma ta yi, sai Yesu ya zauna don cin abinci tare da Sha Biyun.21. Yayinda suke cin abinci, sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”22. Suka yi baƙin ciki ƙwarai, suka fara ce masa da ɗaya-ɗaya, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”23. Yesu ya amsa ya ce, “Wanda ya sa hannunsa a kwano tare da ni ne, zai bashe ni.24. Ɗan Mutum zai tafi kamar yadda aka rubuta game da shi. Amma kaiton mutumin da zai bashe Ɗan Mutum! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da ya fi masa.”25. Sa’an nan Yahuda, wanda zai bashe shi ya ce, “Tabbatacce ba ni ba ne, ko, Rabbi?” Yesu ya amsa ya ce, “I, kai ma ka fada.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.