Baibul a cikin shekara guda Fabrairu 13Fitowa 37:1-291. Bezalel ya yi akwatin alkawari da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kamu ɗaya da rabi.2. Ya dalaye shi da zinariya zalla, ciki da waje, ya kuma yi zubin zinariya kewaye da shi.3. Ya yi masa zubi huɗu na zoban zinariya, ya kuma ɗaura su a ƙafafunsa huɗu, zobai biyu a wannan gefe da kuma biyu a wancan.4. Sa’an nan ya yi sanduna na itacen ƙirya, ya dalaye shi da zinariya.5. Sai ya sa sandunan a cikin rammukan da suke gefen Akwatin don ɗaukarsa.6. Ya yi murfin jinƙai da zinariya zalla, wato, tsawonsa ƙafa biyu, fāɗinsa kuma ƙafa ɗaya da rabi.7. Sa’an nan ya yi kerubobi biyu da ƙeraren zinariya a ƙarshen murfin jinƙan.8. Ya yi kerub a iyakar gefe ɗaya, ya yi ɗayan kuma a wancan gefe; a iyakan nan biyu, ya yi su a haɗe da murfin.9. Kerubobin suka buɗe fikafikansu sama, suka inuwatar da murfin da fikafikansu. Kerubobin suna fuskantar juna, suna kuma kallon murfin.10. Suka yi tebur da itacen ƙirya, tsawonsa ƙafa biyu, fāɗinsa ƙafa ɗaya, tsayinsa kuma ƙafa ɗaya da rabi.11. Sa’an nan suka dalaye shi da zinariya zalla, suka kuma yi zubi na zinariya kewaye da shi.12. Suka kuma yi masa baki mai fāɗin tafi hannu, suka yi zubin zinariya a bisa bakin.13. Suka yi zubin zobai huɗu na zinariya don tebur ɗin, sai suka ɗaura su a kusurwoyi huɗu inda ƙafafu huɗun suke.14. Sa’an nan aka sa zoban kurkusa da bakin don riƙe sandunan da ake amfani da su wurin ɗaukan teburin.15. An yi sandunan da ake ɗaukan tebur da itacen ƙirya, aka kuma dalaye su da zinariya.16. Suka kuma yi duk kayayyakin teburin da zinariya zalla, farantansa, kwanonin tuya, kwanoninsa, da kuma butoci domin hadaya ta sha.17. Suka yi wurin ajiye fitila da zinariya zalla, suka yi gindinsa da kuma gorar jikinsa, da ƙerarriyar zinariya. Kwaf wurin ajiye fitila da mahaɗansa, da furanninsa, a haɗe aka yi su da wurin ajiye fitilan.18. Akwai rassa guda shida da suka miƙe daga gefe wurin ajiyar fitilar, uku a wannan gefe, uku kuma a wancan.19. A reshe guda na wurin ajiye fitilan, akwai kwaf uku masu kama da tohon almon, akwai kuma uku a reshe na biye, haka kuma suke a dukan rassa shida da suke daga wurin ajiye fitilan.20. A bisa wurin ajiye fitilan kuma akwai kwaf huɗu da aka yi su kamar furannin almon da toho da kuma mahaɗai.21. Toho ɗaya yana a ƙarƙashin rassa biyu waɗanda suke daga wurin ajiye fitilan, toho na biyu yana a ƙarƙashin rassa biyu na biye, toho na uku kuma yana a ƙarƙashin rassa biyu na uku, duka-duka rassa shida ne.22. An ƙera mahaɗai da rassa wurin ajiye fitila a haɗe. Da ƙerarriyar zinariya aka yi wurin ajiye fitilar da dukan komensa a haɗe.23. Da zinariya zalla suka yi fitilu bakwai, da hantsuka da farantansa.24. Daga talenti ɗaya na zinariya zalla suka yi wurin ajiye fitila da dukan kayayyakinsa.25. Suka yi bagaden ƙona turare da itacen ƙirya. Shi bagaden, murabba’i ne, tsawonsa kamu ɗaya, fāɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa kuma kamu biyu, ƙahoninsa kuwa a haɗe suke da shi.26. Suka dalaye saman da dukan gefe-gefen da kuma ƙahonin da zinariya zalla, suka kuma yi zubin zinariya kewaye da shi.27. Suka yi zobai biyu na zinariya a ƙarƙashin zubin, biyu-biyu ɗaura da juna, don su riƙe sandunan da za a ɗauka shi.28. Suka yi sandunan da itacen ƙirya, suka kuma dalaye su da zinariya.29. Suka kuma yi tsattsarkan mai na shafewa da kuma zalla turare mai ƙanshi, yadda mai yin turare yakan yi.Fitowa 38:1-311. Suka gina bagaden ƙona hadaya da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyar, fāɗinsa kamu biyar, murabba’i ke nan, tsayinsa kuwa kamu uku.2. Suka yi ƙahoni a kusurwansa huɗu, ƙahonin da bagade a haɗe suke, suka kuma dalaye bagaden da tagulla.3. Da tagulla kuma ya yi duk kayayyakin bagaden, da kwanoni, da babban cokali, da daruna, da cokula masu yatsotsi, da farantan wuta.4. Suka yi wa bagaden raga, tagulla kuma don yă sa shi a tsakiya.5. Suka yi zubin zoban tagulla don riƙe sanduna a kusurwoyi huɗu na ragar tagullar.6. Suka yi sanduna da itacen ƙirya, suka kuma dalaye su da tagulla.7. Suka sa sandunan a cikin zoban saboda su kasance a gefen bagade don ɗaukarsa, suka yi rami cikinsa.8. Suka yi daro da gammonsa da tagulla daga madubai na mata masu yin aiki a ƙofar Tentin Sujada.9. Suka kuma yi filin Tentin Sujada. Suka yi labulanta na gefen kudu da lallausan lilin, tsawonsu kamu ɗari,10. da sanduna ashirin da rammukan sandunan tagulla ashirin, da kuma ƙugiyoyin azurfa da maɗauri a kan sandunan.11. Tsawon labule na wajen gefen arewa kamu ɗari ne, yana kuma da sanduna guda ashirin da rammuka ashirin na tagulla, da ƙugiyoyin azurfa da maɗaurai a kan sandunan.12. Labule na gefen yamma kamu hamsin, da sanduna guda goma, da rammuka guda goma, da ƙugiyoyin azurfa da maɗaurai a kan sandunan.13. A ƙarshen gefen gabas, wajen fitowar rana, shi ma fāɗinsa kamu hamsin ne.14. Labule na gefe ɗaya na ƙofar, kamu goma sha biyar ne, da sanduna guda uku da rammukansu,15. akwai labule mai kamu goma sha biyar a ɗayan gefen ƙofar shiga zuwa filin Tentin Sujada, da sanduna uku da rammuka uku.16. An yi dukan labulan da suke kewaye da filin Tentin Sujada da lallausan zaren lilin.17. An yi rammukan sandunan da tagulla. An dalaye ƙugiyoyi da maɗauran da suke kan sandunan da azurfa; saboda haka dukan sandunan filin Tentin Sujada suna da maɗaurai na azurfa.18. Aka yi wa labulen ƙofar filin Tentin Sujada ado na ɗinki da na shuɗi, da na shunayya, da na jan zare, da na lallausan lilin, aikin gwaninta. Tsawonsa kamu ashirin, kuma kamar yadda labulen filin Tentin Sujada suke, tsayinsa kamu biyar ne,19. da sanduna guda huɗu da rammuka guda huɗu na tagulla. Ƙugiyoyinsu da maɗauransu na azurfa ne, aka kuma dalaye bisansu da azurfa.20. Aka yi dukan ƙarafan kafa tabanakul da kuma na kewayen filin Tentin Sujada da tagulla ne.21. Waɗannan su ne kayayyakin da aka yi amfani da su domin aikin tabanakul, da tabanakul na Shaida, waɗanda aka rubuta bisa ga umarnin Musa ta wurin Lawiyawa, a ƙarƙashin jagorancin Itamar ɗan Haruna, firist.22. (Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuda, ya yi dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa;23. tare da shi akwai Oholiyab ɗan Ahisamak, na kabilar Dan, shi gwani ne cikin aikin zāne-zāne, da ɗinki na shuɗi, da na shunayya, da na jan zare, da na lallausan lilin.)24. Jimillar zinariya daga hadaya ta kaɗawar da aka yi amfani da su domin aikin wuri mai tsarki ta kai talenti 29 da shekel 730, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri.25. Azurfar da aka samu daga ƙidayar taron jama’a, talenti 100 ne, da shekel 1,775, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri.26. Duk mutumin da ya shiga ƙirge daga mai shekaru ashirin zuwa gaba, ya ba da rabin shekel. Mazan da suka shiga ƙirge sun kai mutum 603,550.27. An yi amfani da azurfa talenti 100 don yin rammuka na wuri mai tsarki, da kuma rammukan labule, rammuka 100 daga talenti 100, talenti ɗaya don rami ɗaya.28. Suka yi amfani da shekel 1,775 don yin ƙugiyoyi saboda sanduna, suka dalaye bisan sandunan da maɗauransu.29. Tagullar da aka bayar daga hadaya ta kaɗawa ya kai talenti 70 da shekel 2,400.30. Suka yi amfani da shi don yin rammukan ƙofar Tentin Sujada, da bagaden tagulla tare da ragar tagulla da dukan kayayyakinsa,31. da rammukan sanduna don kewaye filin, da waɗanda suke ƙofarsa, da dukan ƙarafan kafa tenti don tabanakul, da kuma don kewaye filin.Zabura 22:9-159. Duk da haka ka fitar da ni daga ciki; ka sa na dogara gare ka, ko ma a ƙirjin mahaifiyata.10. Daga haihuwa an jefa ni a kanka; daga cikin mahaifiyata kai ne Allahna.11. Kada ka yi nesa da ni, gama wahala na kusa kuma babu wani da zai taimaka.12. Bijimai masu yawa sun kewaye ni; bijimai masu ƙarfi na Bashan sun sa ni a tsaka.13. Zakoki masu ruri suna yayyage abin da suka kama sun buɗe bakunansu a kaina.14. An zubar da ni kamar ruwa, kuma dukan ƙasusuwana sun fiffito daga mahaɗai. Zuciyata ta zama kaki; ta narke a cikina.15. Ƙarfina ya bushe kamar kasko, harshena kuma ya manne wa dasashina na sama; ka kwantar da ni a ƙurar mutuwa.Karin Magana 8:12-2112. “Ni, hikima, ina zama tare da hankali; ina da sani da iya rarrabewa.13. Jin tsoron Ubangiji shi ne ƙin mugunta; ina ƙin girman kai da fariya, halin mugunta da kuma muguwar magana.14. Shawara da yin tunani mai kyau nawa ne; ina da fahimi da kuma iko.15. Ta wurina sarakuna suke mulki masu mulki kuma suke yin dokokin da suke da adalci;16. ta wurina sarakuna suke mulki, da kuma dukan manyan mutanen da suke mulkin duniya.17. Ina ƙaunar waɗanda suke ƙaunata, kuma waɗanda suke nemana sukan same ni.18. Tare da ni akwai wadata da girmamawa, dukiya da wadata masu dawwama.19. ’Ya’yan itacena sun fi zinariya zalla; amfanin gonar da nake bayar ya fi azurfa mafi kyau.20. Ina tafiya a hanyar adalci, a kan hanyoyin gaskiya,21. ina ba da wadata ga waɗanda suke ƙaunata ina sa wuraren ajiyarsu su cika.Mattiyu 26:51-7551. Ganin haka, sai ɗaya daga cikin waɗanda suke tare da Yesu, ya zaro takobinsa ya kai wa bawan babban firist sara, ya fille masa kunne.52. Sai Yesu ya ce, masa, “Mai da takobinka kube, gama duk masu zare takobi, a takobi za su mutu.53. Kuna tsammani ba zan iya kira Ubana, nan take kuwa yă aiko mini fiye da rundunar mala’iku goma sha biyu ba?54. Amma ta yaya za a cika Nassin da ya ce dole haka yă faru?”55. A wannan lokaci sai Yesu ya ce wa taron, “Ina jagoran wani tawaye ne, da kuka fito da takuba da kuma sanduna domin ku kama ni? Kowace rana ina zama a filin haikali ina koyarwa, ba ku kuwa kama ni ba.56. Amma wannan duka ya faru ne don a cika rubuce-rubucen annabawa.” Sa’an nan dukan almajiran suka yashe shi suka gudu.57. Waɗanda suka kama Yesu kuwa suka kai shi wurin Kayifas, babban firist, inda malaman dokoki da dattawa suka taru.58. Amma Bitrus ya bi daga nesa, har zuwa cikin filin gidan babban firist. Ya shiga, ya zauna tare da masu gadi, don yă ga ƙarshen abin.59. Sai manyan firistoci da ’yan majalisa duka suka yi ta neman shaidar ƙarya a kan Yesu, don su sami dama su kashe shi.60. Amma ba su sami ko ɗaya ba, ko da yake masu shaidar ƙarya da yawa sun firfito. A ƙarshe, biyu suka zo gaba,61. suka furta cewa, “Wannan mutum ya ce, ‘Ina iya rushe haikalin Allah, in sāke gina shi cikin kwana uku.’ ”62. Sa’an nan babban firist ya miƙe tsaye, ya ce wa Yesu, “Ba ka da wata amsa? Shaidar da mutanen nan suke yi a kanka fa?”63. Amma Yesu ya yi shiru. Sai babban firist ya ce masa, “Na haɗa ka da Allah mai rai. Faɗa mana in kai ne Kiristi, Ɗan Allah.”64. Sai Yesu ya amsa ya ce, “I, haka yake yadda ka faɗa. Sai dai ina gaya muku duka, nan gaba, za ku ga Ɗan Mutum zaune a hannun dama na Mai Iko, yana kuma zuwa a kan gizagizan sama.”65. Sa’an nan babban firist ya yage tufafinsa ya ce, “Ya yi saɓo! Don me muke bukatar ƙarin shaidu? Ga shi, yanzu kun dai ji saɓon.66. Me kuka gani?” Suka amsa, suka ce, “Ya cancanci mutuwa.”67. Sai suka tottofa masa miyau a fuskarsa, suka kuma bubbuge shi da hannuwansu. Waɗansu kuma suka mammare shi68. suka ce, “Yi mana annabci, Kiristi. Wa ya buge ka?”69. To, Bitrus yana nan zaune a filin, sai wata yarinya baiwa, ta zo wurinsa. Ta ce, “Kai ma kana tare da Yesu mutumin Galili.”70. Amma ya yi mūsu a gabansu duka. Ya ce, “Ban san abin da kike magana ba.”71. Sa’an nan ya fito zuwa hanyar shiga, inda wata yarinya kuma ta gan shi, ta ce wa mutanen da suke can, “Wannan mutum ma yana tare da Yesu Banazare.”72. Ya sāke mūsu har da rantsuwa, yana cewa, “Ban ma san mutumin nan ba!”73. Bayan ɗan lokaci, sai na tsattsaye a wurin, suka hauro wurin Bitrus, suka ce, “Tabbatacce, kai ɗayansu ne, don harshen maganarka, ya tone ka.”74. Sai ya fara la’antar kansa, yana ta rantsuwa yana ce musu, “Ban ma san mutumin nan ba!” Nan da take, sai zakara ya yi cara.75. Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi cewa, “Kafin zakara yă yi cara, za ka yi mūsun sani na sau uku.” Sai ya fita waje, ya yi ta kuka. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.