Baibul a cikin shekara guda Fabrairu 14Fitowa 39:1-431. Daga zare mai ruwan shuɗi, da shuɗayya da kuma jan zare suka yi tsarkaken rigunan domin hidima a wuri mai tsarki. Suka kuma yi tsarkaken riguna don Haruna, yadda Ubangiji ya umarci Musa.2. Suka yi efod na zinariya, da shuɗi, da shunayya, da jan zare, da kuma lallausan lilin.3. Suka bubbuga zinariya ta zama falle, suka yayyanka ta zare-zare don su yi saƙa da ita, tare da zane na shuɗi, da na shunayya, da na jan zare, da na lallausan lilin, aikin gwani mai fasaha.4. Suka yi wa efod kafaɗu, sa’an nan suka haɗa su a gefenta biyu na sama, don a iya ɗaurawa.5. Gwanin mai saƙa ya saƙa abin ɗamarar efod. Da irin kayan da aka saƙa efod ne aka saƙa abin ɗamarar, wato, da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da jan zare, da zaren lallausan lilin, yadda Ubangiji ya umarci Musa.6. Suka shimfiɗa duwatsun onis, suka jera su cikin tsaiko na zinariya, suka kuma zāna sunayen ’ya’yan Isra’ila a kan duwatsun kamar yadda akan yi hatimi.7. Sa’an nan suka ɗaura su a ƙyallen kafaɗun efod a matsayin duwatsun tuni wa ’ya’yan Isra’ila, yadda Ubangiji ya umarci Musa.8. Suka yi ƙyallen maƙalawa a ƙirji, aikin gwani. Suka yi shi kamar efod, na zinariya, da na shuɗi, da na shunayya, da na jan zare, da kuma na lallausan lilin.9. Ƙyallen maƙalawa a ƙirjin murabba’i ne, aka ninka shi biyu, tsawonsa da fāɗinsa kamu ɗaya-ɗaya ne.10. Sa’an nan suka sa jeri huɗu na duwatsu masu daraja a bisansa. A jeri na farko akwai yakutu, da tofaz, da zumurrudu;11. a jeri na biyu akwai turkuwoyis, da saffaya, da daimon;12. a jeri na uku akwai yakinta, da idon mage, da ametis;13. a jeri na huɗu akwai beril, da onis, da yasfa. Aka sa su cikin tsaiko na zinariya.14. Aka zāna duwatsu goma sha biyu, ɗaya don kowane sunan ’ya’yan Isra’ila goma sha biyu, kamar yadda akan yi hatimi.15. Sai suka yi tuƙaƙƙun sarƙoƙi na zinariya zalla a kan ƙyallen maƙalawa a ƙirji.16. Suka yi tsaiko biyu na zinariya da zoban zinariya biyu, suka kuma ɗaura zoban a kusurwoyi biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji.17. Suka ɗaura sarƙoƙi biyu na zinariya da kusurwoyi na ƙyallen maƙalawa a ƙirji.18. Suka maƙala waɗancan bakin sarƙoƙin zinariya a tsaikon nan biyu, sa’an nan suka rataya su a kafaɗun efod daga gaba.19. Suka yi zobai biyu na zinariya suka haɗa, suka sa su a gefe biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji daga ciki kusa da efod.20. Sa’an nan suka yi waɗansu ƙarin zobai biyu na zinariya, suka maƙale su daga ƙasa a gaban kafaɗu biyu na efod kusa da mahaɗin a bisa abin ɗamarar efod.21. Suka ɗaura zoban ƙyallen maƙalawa a ƙirjin a zoban efod da shuɗiyar igiya don ƙyallen maƙalawa a ƙirji, ya kwanta lif a bisa kan abin ɗamarar efod don kada yă kunce daga efod, sun yi yadda Ubangiji ya umarci Musa.22. Suka kuma saƙa taguwa ta efod da shuɗi duka, aikin gwani mai saƙa,23. an yi wa taguwar wuyan wundi a tsakiya kamar sulke, aka daje wuyan don kada yă kece.24. Suka yi fasalin ’ya’yan rumman da shuɗi, da shunayya, da jan zare, da lallausan lilin kewaye da gefe-gefen taguwar.25. Suka yi ƙararrawa da zinariya zalla, suka sa su a tsakanin fasalin ’ya’yan rumman kewaye da gefe-gefen taguwa.26. Aka jera ƙararrawan da ’ya’yan rumman bi da bi. Haka aka jera su kewaye da gefe-gefen taguwar aiki, yadda Ubangiji ya umarci Musa.27. Suka saƙa doguwar riga da lallausan lilin don Haruna da ’ya’yansa, aikin gwani mai saƙa,28. suka yi rawanin da lallausan lilin, da hulan lilin da rigunan ciki na lallausan lilin.29. Suka yi abin ɗamara da lallausan lilin da shuɗi, shunayya da jan zare, aikin gwanin mai ɗinki, yadda Ubangiji ya umarci Musa.30. Suka yi allo tsattsarka da zinariya tsantsa, suka zāna rubutu irin na hatimi a kansa haka, Mai tsarki ga Ubangiji.31. Sa’an nan suka ɗaura shi da shuɗiyar igiya a gaban rawanin, yadda Ubangiji ya umarci Musa.32. Ta haka aka gama dukan aikin tabanakul da Tentin Sujada. Isra’ilawa suka yi kome yadda Ubangiji ya umarci Musa.33. Sa’an nan suka kawo wa Musa tabanakul, tentin da dukan kayayyakinsa, ƙugiyoyinsa, katakansa, da sandunansa, da dogayen sandunansa da rammukansa;34. murfi na fatun rago wanda aka rina ja, da murfi na fatun shanun teku; da kuma laɓulen35. akwatin Alkawari da sandunansa da murfin kafara;36. tebur da dukan kayayyakinsa, da burodin Kasancewa;37. wurin ajiye fitilu na zinariya zalla, da jerin fitilunsa da dukan kayayyakinsa, da man fitila,38. bagade na zinariya, da man shafewa, da turare mai ƙanshi, da labulen ƙofar shiga tenti,39. bagade na tagulla na raga, da sandunansa da kayan aikinsa; da daro da wurin ajiyarsa,40. labulen filin, sandunansa da rammukansa, labulen ƙofar shiga filin; igiyoyi da ƙarafan kafa filin; dukan kayan aikin tabanakul da Tentin Sujada;41. da kuma saƙaƙƙun rigunan da ake sawa don hidima a wuri mai tsarki, duk da tsarkakan riguna na Haruna firist da rigunan ’ya’yansa maza, sa’ad da suke hidima a matsayin firistoci.42. Isra’ilawa suka yi dukan aikin nan yadda Ubangiji ya umarci Musa.43. Musa ya duba aikin, sai ya ga cewa sun yi shi daidai yadda Ubangiji ya umarta. Sai Musa ya sa musu albarka.Fitowa 40:1-381. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa,2. “Ka kafa tabanakul, da Tentin Sujada, a kan rana ta fari ga watan fari.3. Ka sa akwatin Alkawari a cikinsa, sa’an nan ka rufe shi da labule.4. Ka shigar da teburin ka shirya kayayyakin a kansa. Sa’an nan ka shigar da wurin ajiye fitilan ka kuma sa fitilunsa.5. Ka sa bagaden zinariya na ƙona turare a gaban akwatin Alkawari, ka kuma sa labule a ƙofar shiga tabanakul.6. “Ka ajiye bagade na yin hadaya ta ƙonawa a gaban ƙofar tabanakul, da Tentin Sujada;7. ka ajiye daron tsakanin Tentin Sujada da bagaden, ka kuma zuba ruwa a cikinsa.8. Ka yi fili kewaye da shi, ka kuma sa labule a ƙofar shiga filin.9. “Ka ɗauki man shafewa ka shafe tabanakul da duka abin da yake cikinsa; ka keɓe shi da dukan kayayyakinsa, zai zama tsarkake.10. Sa’an nan ka shafe bagaden hadaya ta ƙonawa da kayansa; ka keɓe bagaden, zai zama mai tsarki.11. Ka shafe daron da wurin ajiyarsa, ka kuma keɓe su.12. “Ka kawo Haruna da ’ya’yansa a ƙofar Tentin Sujada ka wanke su da ruwa.13. Sa’an nan ka sa wa Haruna tsarkakun riguna, ka shafe shi, ka kuma keɓe shi don yă yi mini hidima a matsayin firist.14. Ka kawo ’ya’yansa maza ka sa musu taguwoyi.15. Ka shafe su yadda ka shafe mahaifinsu, don su yi mini hidima a matsayin firistoci. Shafe musu man, zai sa su zama firistoci na ɗinɗinɗin, dukan zamanansu.”16. Musa ya aikata dukan kome yadda Ubangiji ya umarce shi.17. Da haka aka kafa tabanakul, a rana ta fari ga wata na fari a shekara ta biyu.18. Sa’ad da Musa ya kafa tabanakul, ya sa rammuka a wurinsu, ya sa katakan, ya kuma sa sandunan, ya kakkafa dogayen sandunan.19. Sa’an nan ya shimfiɗa tentin a bisa tabanakul, ya kuma sa murfi a bisa tentin, yadda Ubangiji ya umarce shi.20. Ya ɗauki dokokin Alkawari ya sa a cikin akwatin, ya kuma zura sandunan a zoban akwatin, sa’an nan ya sa murfin kafara a bisansa.21. Sai ya kawo akwatin a cikin tabanakul, ya kuma rataye labulen rufewa ya tsare akwatin Alkawarin, yadda Ubangiji ya umarce shi.22. Musa ya sa teburin a Tentin Sujada, a gefen arewa na tabanakul waje da labulen.23. Ya shirya burodin a kai a gaban Ubangiji, yadda Ubangiji ya umarce shi.24. Ya sa wurin ajiye fitilan a Tentin Sujada ɗaura da teburin a gefen kudu na tabanakul25. ya kuma shirya fitilun a gaban Ubangiji, yadda Ubangiji ya umarce shi.26. Musa ya sa bagaden zinariya a cikin Tentin Sujada a gaban labulen27. ya ƙone turare mai ƙanshi a kai, yadda Ubangiji ya umarce shi.28. Sa’an nan ya sa labule a ƙofar shiga na tabanakul.29. Ya sa bagaden hadaya ta ƙonawa kusa da ƙofar tabanakul, Tentin Sujada, sa’an nan ya miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta gari a kansa, yadda Ubangiji ya umarce shi.30. Ya sa daro tsakanin Tentin Sujada da bagade, ya kuma zuba ruwa a cikinsa don wanki,31. a cikin kuwa Musa da Haruna da ’ya’yansa maza sukan wanke hannunsa da ƙafafunsu.32. Sukan yi wanka a duk sa’ad da suka shiga Tentin Sujada, ko in suka kusaci bagade, yadda Ubangiji ya umarci Musa.33. Sa’an nan Musa ya yi fili kewaye da tabanakul da kuma bagaden, ya rataye labule a ƙofar shiga filin. Da haka Musa ya gama aikin.34. Sa’an nan girgije ya rufe Tentin Sujada sai ɗaukakar Ubangiji ta cika tabanakul.35. Musa bai iya shiga Tentin Sujada ba domin girgije ya riga ya sauka a kansa, ɗaukakar Ubangiji kuwa ta cika tabanakul.36. Cikin tafiyar Isra’ilawa duka, sukan kama tafiyarsu ne a duk sa’ad da girgijen ya tashi daga kan tabanakul.37. Idan girgijen bai tashi ba, ba za su tashi ba, sai a ranar da ya tashi.38. Gama a cikin tafiyarsu duka, girgijen Ubangiji yana kan tabanakul da rana, da dare kuwa wuta yake cikinsa domin dukan Isra’ilawa su gani.Zabura 22:16-2116. Karnuka sun kewaye ni; ƙungiyar mugaye sun sa ni a tsaka, sun soki hannuwana da ƙafafuna.17. Zan iya ƙirga ƙasusuwana; mutane suna farin ciki a kaina.18. Sun raba rigunana a tsakaninsu suka kuma jefa ƙuri’a a kan rigunana.19. Amma kai, ya Ubangiji, kada ka yi nisa; Ya Ƙarfina zo da sauri don ka taimake ni.20. Ka ceci raina daga takobi, raina mai daraja daga ikon karnuka.21. Ka cece ni daga bakin zakoki; ka cece ni daga ƙahonin ɓauna.Karin Magana 8:22-3122. “ Ubangiji ya kawo ni a matsayi na farko na ayyukansa, kafin ayyukansa na tuntuni;23. an naɗa ni tun fil azal, daga farko, kafin duniya ta kasance.24. Sa’ad da babu tekuna, aka haife ni, sa’ad da babu maɓulɓulai masu ruwa;25. kafin a kafa duwatsu a wurarensu, kafin tuddai ma, an haife ni,26. kafin ya yi duniya ko gonaki ko wata ƙurar duniya.27. Ina nan sa’ad da ya kafa sammai a wurarensu, sa’ad da ya shata sararin sama a kan fuskar zurfafa,28. sa’ad da ya kafa gizagizai a bisa ya kuma kafa maɓulɓulan zurfafa daram,29. sa’ad da ya ba wa teku iyakarsa domin kada ruwaye su zarce umarninsa, da kuma sa’ad da ya shata tussan duniya.30. A lokacin ni ne mai tsara abubuwa a gefensa. Na cika da murna kowace rana, kullum ina farin ciki a gabansa,31. ina farin ciki da dukan duniyarsa ina murna da ’yan adam.Mattiyu 27:1-261. Da wayewar gari, sai dukan manyan firistoci da dattawan mutane suka yanke shawara su kashe Yesu.2. Suka daure shi, suka tafi da shi, suka ba da shi ga gwamna Bilatus.3. Sa’ad da Yahuda, wanda ya bashe Yesu, ya ga an yanke wa Yesu hukuncin kisa, sai ya yi “da na sani.” Ya je mayar wa manyan firistoci da dattawan kuɗin azurfa talatin ɗin.4. Ya ce, “Na yi zunubi da na ci amanar marar laifi.” Suka ce masa, “Ina ruwanmu da wannan? Wannan dai ruwanka ne.”5. Sai Yahuda ya zubar da kuɗin a cikin haikalin ya tafi. Sa’an nan ya je ya rataye kansa.6. Manyan firistoci suka ɗauki kuɗin, suka ce, “Doka ta hana a sa kuɗin a cikin ma’aji, da yake kuɗin jini ne.”7. Saboda haka, sai suka yanke shawara su yi amfani da kuɗin suka sayi filin mai yin tukwane, saboda binne baƙi.8. Shi ya sa ake kiran filin, Filin Jini har yă zuwa yau.9. Sai abin da aka faɗa ta bakin annabi Irmiya ya cika cewa, “Suka ɗauki azurfa talatin, kuɗin da mutanen Isra’ila suka sa a kansa,10. suka kuma yi amfani da su, suka sayi filin mai yin tukwane, kamar yadda Ubangiji ya umarce ni.”11. Ana cikin haka, Yesu kuwa yana tsaye a gaban gwamna, sai gwamnan ya tambaye shi, “Kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya ce, “I, haka ne, kamar yadda ka faɗa.”12. Da manyan firistoci da dattawa suka zarge shi, bai ba da amsa ba.13. Sai Bilatus ya tambaye shi ya ce, “Ba ka jin shaidar da suke kawowa a kanka?”14. Amma Yesu bai ce uffam game da ko ɗaya daga cikin zargin da suka yi masa ba. Har gwamna ya yi mamaki ƙwarai.15. A wannan irin Biki, gwamna yana da wata al’ada, ta sakin ɗan kurkuku guda wanda taron suka zaɓa.16. To, a wannan lokaci kuwa suna da wani shahararren ɗan kurkuku da ake kira Barabbas.17. Saboda haka da taron suka taru, sai Bilatus ya tambaye su ya ce, “Wane ne a cikinsu kuke so in sakar muku. Barabbas ko Yesu wanda ake kira Kiristi?”18. Don ya san saboda sonkai ne suka ba da Yesu a gare shi.19. Yayinda Bilatus yake zaune a kan kujerar shari’a, sai matarsa ta aika masa da wannan saƙo cewa, “Kada ka sa hannunka a kan marar laifin nan, domin na sha wahala ƙwarai, a cikin mafarki yau game da shi.”20. Amma manyan firistoci da dattawa suka shawo kan taron, su ce, a ba su Barabbas, amma a kashe Yesu.21. Gwamna ya yi tambaya ya ce, “Wane ne cikin biyun nan, kuke so in sakar muku?” Suka ce, “Barabbas.”22. Bilatus ya yi tambaya, “To, me zan yi da Yesu wanda ake kira Kiristi?” Duka suka ce, “A gicciye shi!”23. Bilatus ya ce, “Don me? Wane laifi ya yi?” Amma suka ƙara tā da ihu, suna cewa, “A gicciye shi!”24. Da Bilatus ya ga cewa ba ya kaiwa ko’ina, sai ma hargitsi ne yake so yă tashi, sai ya ɗibi ruwa, ya wanke hannuwansa a gaban taron ya ce, “Ni kam, ba ruwana da alhakin jinin mutumin nan. Wannan ruwanku ne!”25. Sai dukan mutane suka amsa, suka ce, “Bari alhakin jininsa yă zauna a kanmu da ’ya’yanmu!”26. Sai ya sakar musu Barabbas. Amma ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.