Baibul a cikin shekara guda Fabrairu 15Firistoci 1:1-171. Ubangiji ya kira Musa ya yi masa magana daga cikin Tentin Sujada ya ce,2. “Yi magana da Isra’ilawa ka ce musu, ‘Duk sa’ad da waninku ya kawo hadaya ga Ubangiji, ku kawo hadayarku ta dabba daga garkenku ta shanu ko kuwa daga tumakinku.3. “ ‘In hadaya ta ƙonawar daga shanu ne, sai yă miƙa namiji marar lahani. Dole yă kawo shi a ƙofar Tentin Sujada don yă zama yardajje ga Ubangiji.4. Zai ɗibiya hannunsa a kan hadaya ta ƙonawar, za a kuwa karɓa a madadinsa don a yi kafara dominsa.5. Zai yanka ɗan bijimin a gaban Ubangiji, Haruna kuwa da ’ya’yansa maza firist, za su kawo jinin su kuma yafa shi a kan bagaden a kowane gefe a mashigin Tentin Sujada.6. Zai feɗe hadaya ta ƙonawar, yă yayyanka shi gunduwa-gunduwa.7. ’Ya’yan Haruna maza waɗanda suke firistoci za su hura wuta a bagade, su kuma shirya itace a kan wutar.8. Sa’an nan ’ya’yan Haruna maza waɗanda suke firistoci za su shirya gunduwa-gunduwar haɗe da kan da kuma kitsen a kan itace mai cin wuta wanda yake a kan bagaden.9. Zai wanke kayan cikin da kuma ƙafafun da ruwa, firist ɗin kuwa zai ƙone dukan waɗannan a kan bagade. Hadaya ce ta ƙonawa, hadaya ce kuma wadda aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.10. “ ‘In hadaya ta ƙonawar daga garke ne, ko na tumaki, ko na awaki, zai miƙa namiji ne marar lahani.11. Zai yanka shi a gefen arewa na bagaden a gaban Ubangiji, ’ya’yan Haruna firistoci kuwa za su yayyafa jinin dabbar a bagaden a kowane gefe.12. Zai yanka shi gunduwa-gunduwa, firist kuwa zai shirya su haɗe da kan, da kuma kitsen a kan itace mai cin wutar da yake a kan bagade.13. Zai wanke kayan cikin da kuma ƙafafun da ruwa, firist ɗin kuwa zai ƙone dukan waɗannan a kan bagade. Hadaya ce ta ƙonawa, hadaya ce kuma wadda aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.14. “ ‘In hadaya ga Ubangiji ɗin, hadaya ta ƙonawa ta tsuntsaye ce, zai miƙa kurciya ko ’yar tattabara.15. Firist zai kawo ta bagade, yă murɗe wuyan tsuntsun yă ƙone shi a kan bagade; zai tsiyaye jininsa tsuntsun a gefen bagaden.16. Amma zai ɗauki kayan cikin tsuntsun da gashin yă zubar da su a gefen bagaden a wajen gabas a wurin zuba toka.17. Zai tsaga shi biyu a tsaka, amma ba zai raba shi ba. Firist ɗin zai ɗibiya shi a bisa itacen da yake bisa bagaden, yă ƙone shi. Hadaya ce ta ƙonawa, hadaya ce kuma wadda aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.Firistoci 2:1-161. “ ‘Sa’ad da wani ya kawo hadaya ta gari ga Ubangiji, hadayarsa za tă zama gari mai laushi ne. Zai zuba mai a kai, yă sa turare a kansa2. yă kai wa ’ya’yan Haruna maza waɗanda suke firistoci. Firist zai ɗiba gari mai laushin a tafin hannu da kuma man, tare da dukan turaren, yă ƙone wannan a sashen tunawa a kan bagade, hadaya ce da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.3. Sauran hadaya ta garin zai zama na Haruna da ’ya’yansa; sashe mafi tsarki ne na hadayar da aka yi ga Ubangiji ta wuta.4. “ ‘In kuka kawo toyayyen hadayar gari da aka yi daga matoya, zai ƙunshi gari mai laushi, toyayye ba tare da yisti ba, gauraye kuma da mai, ko kuwa ƙosai da aka yi ba tare da yisti ba, aka kuma kwaɓa da mai.5. In an toya hadaya ta garinku a kasko, sai a yi shi da gari mai laushi haɗe da mai, ba kuwa da yisti ba.6. A gutsuttsura shi, a zuba mai a kansa, hadaya ce ta hatsi.7. In hadayarku ta hatsin da aka dafa ne a tukunya, sai a yi shi da gari mai laushi da kuma mai.8. A kawo hatsin da aka yi da waɗannan abubuwa ga Ubangiji; a ba wa firist wanda zai ɗauka yă kai bagade.9. Zai fid da sashen tunawa daga hadaya ta gari, yă ƙone shi a kan bagade kamar hadayar da ka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.10. Sauran hadaya ta garin za tă zama ta Haruna da ’ya’yansa; sashe mafi tsarki ne na hadayun da aka yi ga Ubangiji ta wuta.11. “ ‘Kowace hadaya ta garin da kuka kawo ga Ubangiji, dole a yi shi ba tare da yisti ba, gama ba za ku ƙone wani yisti, ko zuma a cikin hadayar da aka yi ga Ubangiji ta wuta ba.12. Za ku iya kawo su ga Ubangiji kamar hadaya ta ’ya’yan fari, amma ba za a miƙa su a bagade kamar turare mai ƙanshi ba.13. A sa gishiri a dukan hadayunku na hatsi. Kada a rasa sa gishirin alkawari na Allahnku a hadayunku na hatsi, a sa gishiri a dukan hadayunku.14. “ ‘In kuka kawo hadaya ta gari na ’ya’yan fari ga Ubangiji, sai ku miƙa ɓarzajjen kawunan sabon hatsin da aka gasa a wuta.15. A sa mai da turare a kansa, hadaya ce ta hatsi.16. Firist zai ƙone sashe na ɓarzajjen hatsin da kuma mai, tare da turare don tunawa, gama hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.Zabura 22:22-3122. Zan furta sunanka ga ’yan’uwana; cikin taron masu sujada zan yabe ka.23. Ku da kuke tsoron Ubangiji, ku yabe shi! Dukanku zuriyar Yaƙub, ku girmama shi! Ku girmama shi, dukanku zuriyar Isra’ila!24. Gama bai rena ko yă ƙyale wahalar masu shan wuya ba; bai ɓoye fuskarsa daga gare shi ba amma ya saurari kukansa na neman taimako.25. Daga gare ka yabona yake zuwa cikin babban taro; a gaban waɗanda suke tsoronka zan cika alkawarina.26. Matalauta za su ci su ƙoshi; su da suke neman Ubangiji za su yabe shi, bari zukatanku su rayu har abada!27. Dukan iyakokin duniya za su tuna su kuma juya ga Ubangiji, kuma dukan iyalan al’ummai za su rusuna a gabansa,28. gama mulki na Ubangiji ne kuma yana mulki a bisa al’ummai.29. Dukan attajiran duniya za su yi biki su kuma yi sujada; dukan waɗanda suka gangara zuwa ƙura za su durƙusa a gabansa, waɗanda ba za su iya bar kansu da rai ba.30. Zuriya masu zuwa za su yi masa hidima; za a faɗa wa zuriya na nan gaba game da Ubangiji.31. Za su yi shelar adalcinsa ga mutanen da ba a riga an haifa ba, gama ya aikata shi.Karin Magana 8:32-3632. “Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni; masu albarka ne waɗanda suke kiyaye hanyoyina.33. Ku saurari umarnina ku kuma zama masu hikima; kada ku ƙyale ta.34. Mai albarka ne wanda ya saurare ni; yana tsaro kullum a ƙofofina, yana jira a ƙofar shigata.35. Gama duk wanda ya same ni ya sami rai zai kuma sami tagomashi daga Ubangiji.36. Amma duk wanda ya kāsa samuna ya cuci kansa; dukan waɗanda suke ƙina suna ƙaunar mutuwa ke nan.”Mattiyu 27:27-5427. Sai sojojin gwamna suka ɗauki Yesu suka kai shi Fadar mai mulki, sa’an nan suka tara dukan kamfanin sojoji kewaye da shi.28. Suka tuɓe shi, suka yafa masa wata jar riga.29. Suka kuma tuƙa wani rawanin ƙaya, suka sa masa a kā. Suka sa sanda a hannun damansa. Suka durƙusa a gabansa, suka yi masa ba’a, suna cewa, “Ranka yă daɗe sarkin Yahudawa!”30. Suka tattofa masa miyau, suka karɓe sandan, suka yi ta ƙwala masa shi a kai.31. Bayan sun yi masa ba’a, sai suka tuɓe masa rigar, suka sa masa nasa tufafin. Sai suka tafi da shi, domin su gicciye shi.32. Suna fitowa ke nan, sai suka sadu da wani mutumin Sairin, mai suna Siman. Sai suka tilasta shi ya ɗauki gicciyen.33. Sai suka iso wani wurin da ake kira Golgota (wanda yake nufin Wurin Ƙoƙon Kai).34. A can, suka ba shi ruwan inabi gauraye da wani abu mai ɗaci yă sha. Amma da ya ɗanɗana, sai ya ƙi sha.35. Bayan da suka gicciye shi, sai suka raba tufafinsa a tsakaninsu ta wurin jefa ƙuri’a.36. Sa’an nan suka zauna suna tsaronsa.37. Bisa da kansa kuwa, an kafa rubutun zargin da aka yi masa, da ya ce, Wannan shi ne Yesu Sarkin Yahudawa.38. An gicciye ’yan fashi biyu tare da shi, ɗaya a damansa, ɗaya kuma a hagunsa.39. Masu wucewa, suka zazzage shi, suna kaɗa kai,40. suna cewa, “Kai da za ka rushe haikali, ka kuma gina shi cikin kwana uku, ceci kanka mana! In kai Ɗan Allah ne, ka sauka daga gicciyen!”41. Haka ma, manyan firistoci da malaman dokoki da kuma dattawa, suka yi ta yin masa ba’a, suna cewa,42. “Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa! In shi ne Sarkin Isra’ila! To, yă sauko daga kan gicciyen nan, mu kuwa mu gaskata shi.43. Ya dogara ga Allah. Bari Allah yă cece shi yanzu, in yana sonsa, domin ya ce, ‘Ni Ɗan Allah ne.’ ”44. Haka ma, ’yan fashin da aka gicciye tare da shi, suka zazzage shi.45. Daga sa’a ta shida, har zuwa sa’a ta tara, duhu ya rufe ƙasa duka.46. Wajen sa’a ta tara, Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani?” (Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?” ).47. Sa’ad da waɗanda suke tsattsaye a wurin suka ji haka, sai suka ce, “Yana kiran Iliya.”48. Nan da nan, ɗaya daga cikinsu ya ruga, ya sami soso, ya jiƙa shi da ruwan tsami, ya sa a sanda, ya miƙa wa Yesu, yă sha.49. Sauran kuwa suka ce, “Ƙyale shi mu ga, ko Iliya zai zo yă cece shi.”50. Da Yesu ya sāke ɗaga murya da ƙarfi, sai ya saki ruhunsa.51. A daidai wannan lokaci, sai labulen haikali ya tsage gida biyu, daga sama har ƙasa. Ƙasa ta jijjiga, duwatsu kuma suka farfashe.52. Kaburbura suka bubbuɗe, jikunan tsarkaka da yawa kuwa cikin waɗanda da suka mutu, suka tashi.53. Suka firfito daga kaburbura, sa’an nan bayan tashin Yesu daga matattu, suka shiga birni mai tsarki, suka bayyana ga mutane da yawa.54. Da jarumin nan tare da waɗanda suke tsaron Yesu, suka ga girgizar ƙasa, da kuma abin da ya faru, sai tsoro ya kama su, suka kuma ce, “Gaskiya, wannan Ɗan Allah ne!” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.