Baibul a cikin shekara guda Fabrairu 16Firistoci 3:1-171. “ ‘In hadayar wani mutum, hadaya ta salama ce, ya kuma miƙa ’yar dabba daga garke, ko namiji ko ta mace ce, sai yă miƙa dabbar da ba ta da lahani a gaban Ubangiji.2. Yă kuma ɗibiya hannunsa bisa kan hadayarsa, yă yanka ta a mashigin Tentin Sujada. Sa’an nan ’ya’yan Haruna waɗanda suke firistoci za su yayyafa jinin a kan bagade a kowane gefe.3. Daga hadaya ta zumuncin da zai kawo, sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji a wuta; wato, dukan kitsen da ya rufe kayan ciki ko kuwa da sun shafe su,4. da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta waɗanda zai cire tare da ƙodoji.5. ’Ya’yan Haruna za su ƙone shi a kan bagade a bisa hadaya ta ƙonawa wadda take a kan itacen da yake cin wuta, kamar hadayar da ka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.6. “ ‘In ya miƙa dabba ce daga garke a matsayin hadaya ta salama ga Ubangiji, zai miƙa namiji ko ta mace marar lahani.7. In ya miƙa ɗan rago ne, zai kawo shi a gaban Ubangiji.8. Zai ɗibiya hannu a kan hadayarsa, yă yanka shi a gaban Tentin Sujada. Sa’an nan ’ya’yan Haruna maza za su yayyafa jinin dabbar a kowane gefe na bagade.9. Daga hadaya ta zumuncin zai kawo, sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji a wuta, wato, kitsen, ƙibabbiya wutsiyar gaba ɗaya da ya yanka gab da ƙashin gadon baya, dukan kitsen da ya rufe kayan ciki, ko kuwa da suka shafe su,10. da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta waɗanda zai cire tare da ƙodoji.11. Firist zai ƙone su a kan bagade kamar hadayar abinci, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.12. “ ‘In yana miƙa akuya ce, zai kawo ta a gaban Ubangiji.13. Zai ɗibiya hannunsa a kanta yă kuma yanka ta a gaban Tentin Sujada. Sa’an nan ’ya’yan Haruna maza za su yayyafa jininta a kowane gefe na bagade.14. Daga abin da zai miƙa sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji a wuta, wato, dukan kitsen da ya rufe kayan cikin, ko kuwa da suka shafe su,15. da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta waɗanda zai cire tare da ƙodoji.16. Firist zai ƙone su a kan bagade kamar abinci, hadaya ce da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi. Dukan kitsen na Ubangiji ne.17. “ ‘Wannan dawwammamiyar farilla ce ga tsararraki masu zuwa, a inda za ku zauna. Ba za ku ci wani kitse ko wani jini ba.’ ”Firistoci 4:1-351. Ubangiji ya ce wa Musa,2. “Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘Sa’ad da wani ya yi zunubi ba da gangan ba, har ya karya ɗaya daga cikin dokokin Ubangiji,3. “ ‘In shafaffen firist ya yi zunubi, ya jawo wa jama’a laifi, dole yă kawo wa Ubangiji ɗan bijimi marar lahani a matsayin hadaya don zunubi saboda zunubin da ya yi.4. Zai kawo bijimin a ƙofar Tentin Sujada a gaban Ubangiji. Zai ɗibiya hannunsa a kan bijimin, yă kuma yanka shi a gaban Ubangiji.5. Sa’an nan shafaffen firist zai ɗiba jinin bijimin yă kai cikin Tentin Sujada.6. Yă tsoma yatsarsa a cikin jinin, yă kuma yafa sau bakwai a gaban Ubangiji, a gaban labulen wuri mai tsarki.7. Sa’an nan firist ɗin zai zuba jinin a ƙahonin bagaden turare masu ƙanshi da suke a gaban Ubangiji a Tentin Sujada. Sauran jinin bijimin zai zuba a gindin bagaden hadaya ta ƙonawa a ƙofar zuwa Tentin Sujada.8. Zai cire dukan kitsen daga bijimin hadaya don zunubi, kitsen da ya rufe kayan cikin, ko kuwa da suka shafe su,9. da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta, waɗanda zai cire tare da ƙodoji.10. Zai cire su daidai kamar yadda akan cire na bijimin hadaya ta salama. Sai firist ɗin yă ƙone su a kan bagaden ƙona hadaya.11. Amma fatar ɗan bijimin, da namansa, da kansa, da ƙafafunsa, da kayan cikinsa, da hanjinsa,12. wato, dukan sauran bijimi, dole yă ɗauke su zuwa waje da sansani zuwa wani wuri mai tsabta inda ake zub da toka, yă ƙone shi a itacen da yake cin wuta a tarin toka.13. “ ‘In dukan jama’ar Isra’ilawa suka yi zunubi ba da gangan ba, har suka aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, ko da yake jama’ar ba su san batun ba, duk da haka sun yi laifi.14. Sa’ad da suka gane da zunubin da suka aikata, dole taron su kawo ɗan bijimi a matsayin hadaya don zunubi, su kawo shi a gaban Tentin Sujada.15. Dattawan jama’a za su ɗibiya hannuwansu a kan bijimin a gaban Ubangiji, sai a yanka bijimin a gaban Ubangiji.16. Sa’an nan shafaffen firist zai ɗibi jinin bijimi zuwa cikin Tentin Sujada.17. Zai tsoma yatsarsa cikin jini yă kuma yayyafa shi a gaban Ubangiji sau bakwai a gaban labule.18. Zai zuba jinin a ƙahonin bagaden da suke gaban Ubangiji a cikin Tentin Sujada. Zai zuba sauran jinin a gindin bagaden hadaya ta ƙonawa a ƙofar zuwa Tentin Sujada.19. Zai cire dukan kitsen daga gare shi yă ƙone a kan bagade,20. yă kuma yi da wannan bijimi kamar yadda ya yi da bijimi na hadaya don zunubi. Ta haka firist zai yi kafara dominsu, za a kuwa gafarta musu.21. Sa’an nan zai ɗauki bijimin waje da sansani yă ƙone shi kamar yadda ya ƙone bijimi na fari. Wannan ita ce hadaya don zunubi domin jama’a.22. “ ‘Sa’ad da shugaba ya yi zunubi ba da gangan ba, har ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji Allahnsa ya umarta, to, ya yi laifi.23. Sa’ad da aka sanar da shi game da zunubin da ya yi, dole yă kawo bunsuru marar lahani a matsayin hadayarsa.24. Zai ɗibiya hannunsa a kan bunsurun yă kuma yanka shi a inda ake yankan hadayar ƙonawa a gaban Ubangiji. Hadaya ce ta zunubi.25. Sa’an nan firist zai ɗibi jinin hadaya don zunubi da yatsarsa yă sa a ƙahonin bagaden hadayar ƙonawa, yă kuma zuba sauran jinin a gindin bagade.26. Zai ƙone dukan kitse a kan bagade kamar yadda ya ƙone kitsen hadaya ta salama. Ta haka firist zai yi kafara saboda zunubin mutumin, za a kuwa gafarta masa.27. “ ‘In wani memba a cikin jama’a ya yi zunubi ba da gangan ba, ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, to, ya yi laifi.28. Sa’ad da aka sanar da shi game da zunubin da ya yi, dole yă kawo akuya marar lahani a matsayin hadayarsa domin zunubin da ya yi.29. Zai ɗibiya hannunsa a kan hadaya don zunubin yă kuma yanka ta a inda ake hadaya ta ƙonawa.30. Sa’an nan firist zai ɗibi jinin da yatsarsa yă zuba a ƙahoni a bagaden hadaya ta ƙonawa, yă kuma zuba sauran jinin a ƙasan bagade.31. Za a ɗebe kitsenta duka kamar yadda akan ɗebe kitsen hadaya ta salama. Firist zai ƙona shi a kan bagaden don ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Ta haka firist zai yi kafara dominsa, za a kuwa gafarta masa.32. “ ‘Idan kuwa daga cikin ’yan tumaki zai ba da hadayarsa, sai ya kawo ’yar tunkiya marar lahani.33. Zai ɗibiya hannunsa a kanta yă kuma yanka ta hadaya don zunubi a inda ake yankan hadayar ƙonawa.34. Sa’an nan firist zai ɗibi jinin hadaya don zunubin da yatsarsa yă zuba a ƙahonin bagaden hadayar ƙonawa, yă kuma zuba sauran jinin a gindin bagade.35. Zai kuma ɗebe kitsenta duka kamar yadda a kan ɗebe na ragon hadaya ta salama. Firist zai ƙone shi a bisa bagaden a bisa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Ta haka firist ɗin zai yi kafara dominsa saboda zunubin da ya yi, za a kuwa gafarta masa.Zabura 23:1-61. Ubangiji ne yake kiwona, ba zan rasa kome ba,2. Yakan sa in kwanta a makiyaya mai ɗanyar ciyawa, yakan bi da ni kusa da ruwaye marar hayaniya,3. yakan maido da raina. Yakan bi da ni a hanyoyin adalci saboda sunansa.4. Ko da na yi tafiya ta kwari na inuwar mutuwa, ba zan ji tsoron mugu ba, gama kana tare da ni; bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya, za su yi mini ta’aziyya.5. Ka shirya mini tebur a gaban abokan gābana. Ka shafe kaina da mai; kwaf nawa ya cika har yana zuba.6. Tabbatacce alheri da ƙauna za su bi dukan kwanakin raina, zan kuwa zauna a gidan Ubangiji har abada.Karin Magana 9:1-61. Hikima ta gina gidanta; ta yi ginshiƙansa bakwai.2. Ta shirya abincinta gauraye da ruwan inabinta; ta kuma shirya teburinta.3. Ta aiki bayinta mata, tana kuma kira daga wurare masu tsayi na birnin.4. “Bari dukan waɗanda suke marasa azanci su zo nan ciki!” Tana faɗa wa marasa hankali.5. “Ku zo, ku ci abincina da ruwan inabin da na gauraye.6. Ku bar hanyoyinku marasa hankali za ku kuwa rayu; yi tafiya a hanyar fahimi.Mattiyu 27:55-6655. Akwai mata da yawa a can, suna kallo daga nesa. Sun bi Yesu tun daga Galili, suna masa hidima.56. A cikinsu, akwai Maryamu Magdalin, da Maryamu uwar Yaƙub da Yoses, da kuma uwar ’ya’yan Zebedi.57. Da yamma ta yi, sai ga wani mutum mai arziki daga Arimateya, sunansa Yusuf, wanda shi da kansa almajirin Yesu ne.58. Ya je wurin Bilatus, ya roƙe shi yă ba shi jikin Yesu. Sai Bilatus ya umarta a ba shi.59. Yusuf ya ɗauki jikin ya nannaɗe shi da zanen lilin mai tsabta.60. Sa’an nan ya sa shi a sabon kabarinsa, wanda ya haƙa a dutse. Bayan ya gungura wani babban dutse ya rufe bakin kabarin, sai ya tafi abinsa.61. Maryamu Magdalin da ɗayan Maryamun, suna zaune a wurin, ɗaura da kabarin.62. Kashegari, wato, bayan Ranar Shirye-shirye, sai manyan firistoci da Farisiyawa, suka je wurin Bilatus.63. Suka ce, “Ranka yă daɗe, mun tuna, mai ruɗin nan tun yana da rai ya ce, ‘Bayan kwana uku, zan tashi daga matattu.’64. Saboda haka, ka ba da umarni, a tsare kabarin sai rana ta uku ɗin. In ba haka ba, almajiransa za su iya zuwa su sace jikin, sa’an nan su faɗa wa mutane cewa, an tashe shi daga matattu. Ruɗin ƙarshen nan fa, sai yă fi na farkon muni.”65. Sai Bilatus ya ce, “Shi ke nan, ku ɗebi soja, ku je ku tsare kabarin iya ƙoƙarinku.”66. Sai suka je suka tsare kabarin ta wurin buga masa hatimi, suka kuma sa masu gadi. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.