Baibul a cikin shekara guda Fabrairu 19Firistoci 9:1-241. A rana ta takwas, Musa ya kira Haruna da ’ya’yansa maza da kuma dattawan Isra’ila.2. Ya ce wa Haruna, “Ka ɗauki ɗan maraƙi domin hadayarka don zunubi da kuma ɗan rago domin hadaya ta ƙonawa, dukan biyu su kasance marar lahani, ka miƙa su a gaban Ubangiji.3. Sa’an nan ka ce wa Isra’ilawa, ‘Ku ɗauki bunsuru na yin hadaya don zunubi, da ɗan maraƙi bana ɗaya, da ɗan rago bana ɗaya marasa lahani, don hadaya ta ƙonawa,4. da bijimi da rago don hadayun salama, a yi hadaya da su ga Ubangiji, da hadaya ta gari da aka kwaɓa da mai, gama yau Ubangiji zai bayyana a gare ku.’ ”5. Suka ɗauki abubuwan da Musa ya umarta zuwa gaban Tentin Sujada, sai dukan jama’a suka zo kusa suka tsaya a gaban Ubangiji.6. Sa’an nan Musa ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya umarce ku ku yi, domin ɗaukakar Ubangiji za tă bayyana gare ku.”7. Musa ya ce wa Haruna, “Matsa kusa da bagaden, ka miƙa hadayarka don zunubi, da hadayarka ta ƙonawa, ka yi kafara don kanka da kuma don jama’a. Ka kuma kawo hadayar jama’a, ka yi kafara dominsu kamar yadda Ubangiji ya umarta.”8. Sai Haruna ya matsa kusa da bagaden, ya yanka ɗan maraƙi na yin hadaya don zunubi saboda kansa.9. ’Ya’yan Haruna maza suka kawo masa jinin, ya kuma tsoma yatsarsa a cikin jinin ya zuba cikin ƙahonin bagade; sauran jinin kuwa ya zuba a gindin bagaden.10. A kan bagaden, ya ƙone kitsen, ƙodojin, da abin da ya rufe hanta, daga hadaya don zunubi, yadda Ubangiji ya umarci Musa.11. Naman da fatar kuwa ya ƙone waje da sansanin.12. Sa’an nan ya yanka hadaya ta ƙonawa. ’Ya’yan Haruna maza suka miƙa masa jinin, ya kuwa yayyafa shi a kowane gefe na bagaden.13. Suka miƙa masa hadaya ta ƙonawa gunduwa-gunduwa, haɗe da kan, ya kuwa ƙone su a bisa bagaden.14. Sai ya wanke kayan ciki da ƙafafun, ya kuwa ƙone su tare da hadaya ta ƙonawa a kan bagade.15. Sa’an nan Haruna ya kawo hadayar da take domin mutane. Ya ɗauki akuya ta hadaya don zunubin mutane, ya yanka shi, ya miƙa shi domin hadaya don zunubi kamar yadda ya yi da na farko.16. Ya kawo hadaya ta ƙonawa ya kuma miƙa ta yadda aka tsara.17. Ya kuma kawo hadaya ta gari, ya ɗiba a tafi hannu ya ƙone a kan bagade tare da hadaya ta ƙonawa ta safe.18. Haruna ya yanka maraƙin da ragon a matsayin hadaya ta salama domin mutane. ’Ya’yansa maza suka miƙa masa jinin, ya kuwa yayyafa shi a kowane gefe na bagade.19. Amma sashen kitsen maraƙin da na ragon, da wutsiya mai kitse, da kitsen da yake rufe da kayan ciki, da ƙodoji da kuma kitsen da ya rufe hanta,20. suka shimfiɗa waɗannan a kan ƙirjin, sa’an nan Haruna ya ƙone kitsen a kan bagade.21. Sai Haruna ya kaɗa ƙirjin da kuma cinyar dama a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa, kamar yadda Musa ya umarta.22. Sa’an nan Haruna ya ɗaga hannuwansa wajen mutane ya sa musu albarka. Da yake ya miƙa hadaya don zunubi, hadaya ta ƙonawa da kuma hadaya ta salama, sai ya sauka.23. Sai Musa da Haruna suka shiga cikin Tentin Sujada. Da suka fita, sai suka sa wa mutane albarka; sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana ga dukan mutane.24. Sai wuta ta fito daga gaban Ubangiji ta cinye hadaya ta ƙonawa da sassan kitsen a kan bagaden. Sa’ad da dukan mutane suka ga haka, sai suka yi ihu suna farin ciki, suka fāɗi rubda ciki, suka yi sujada.Firistoci 10:1-201. ’Ya’yan Haruna maza, Nadab da Abihu suka ɗauki farantansu, suka sa wuta a ciki, suka zuba turare a kai; suka kuma miƙa haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji, ba irin wadda Ubangiji ya umarta ba.2. Sai wuta ta fito daga Ubangiji ta cinye su, suka kuma mutu a gaban Ubangiji.3. Sai Musa ya ce Haruna, “Ga abin da Ubangiji yake nufi sa’ad da ya ce, “ ‘A cikin waɗanda suka kusace ni za a tabbata ni mai tsarki ne; a fuskar dukan mutane za a kuwa girmama ni.’ ” Haruna ya yi shiru.4. Sai Musa ya kira Mishayel da Elzafan, ’ya’yan Uzziyel kawun Haruna, ya ce musu, “Ku zo nan; ku ɗauki ’yan’uwanku waje da sansani, daga gaban wuri mai tsarki.”5. Sai suka zo suka ɗauke su, suna nan cikin taguwoyinsu, zuwa waje da sansani yadda Musa ya umarta.6. Sa’an nan Musa ya ce wa Haruna da Eleyazar da Itamar ’ya’yansa maza, “Kada ku bar gashin kanku barkatai, kada kuma ku yage tufafinku, don kada ku mutu. Yin haka zai jawo fushin Ubangiji a kan dukan jama’a. Amma dangoginku, wato, dukan Isra’ilawa, suna iya kuka saboda waɗanda Ubangiji ya hallaka da wuta.7. Kada ku bar ƙofar Tentin Sujada ko kuwa ku mutu, domin man Shafan Ubangiji yana kanku.” Saboda haka suka yi kamar yadda Musa ya faɗa.8. Sa’an nan Ubangiji ya yi magana da Haruna ya ce,9. “Kai da ’ya’yanka maza, ba za ku sha ruwan inabi ko wani abu mai sa jiri ba a duk sa’ad da za ku shiga cikin Tentin Sujada, in ba haka ba za ku mutu. Wannan dawwammamiyar farilla ce wa tsararraki masu zuwa.10. Dole ku bambanta tsakanin mai tsarki da marar tsarki, tsakanin marar tsabta da mai tsabta,11. za ku kuma koyar da Isra’ilawa dukan farillan da Ubangiji ya ba su ta wurin Musa.”12. Musa ya ce wa Haruna da Eleyazar da Itamar ’ya’yansa maza da suka ragu, “Ku ɗauki ragowar hadaya ta gari wadda aka yi hadaya ta ƙonawa da ita ga Ubangiji ku ci ba tare da yisti ba, a gefen bagaden, gama tsattsarka ne.13. Ku ci shi a tsattsarkan wuri, gama rabonka ne da na ’ya’yanka daga cikin hadayun da akan ƙone da wuta ga Ubangiji; gama haka aka umarce ni.14. Amma kai da ’ya’yanka maza da mata za su iya ci ƙirjin da aka kaɗa, da kuma cinyar da aka miƙa. Ku ci su a wuri mai tsabta; an ba da su gare ku da kuma ’ya’yanku a matsayin rabo daga hadaya ta salama ta Isra’ilawa.15. Cinyar da aka miƙa da kuma ƙirjin da aka kaɗa, dole a kawo su tare da ɓangarori kitsen hadayun da aka yi ta wuri wuta, don a kaɗa a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa. Wannan zai zama na kullayaumi gare ka da ’ya’yanka, yadda Ubangiji ya umarta.”16. Sa’ad da Musa ya nemi sani game da akuyar hadaya don zunubi, ya kuwa gane cewa an ƙone shi, sai ya yi fushi da Eleyazar da kuma Itamar, ’ya’yan Haruna maza da suka ragu, ya kuma yi tambaya,17. “Me ya sa ba ku ci hadaya don zunubi a cikin wuri mai tsarki ba? Mafi tsaki ne; an ba ku ne don a ɗauke laifin jama’a ta wurin yin kafara saboda su a gaban Ubangiji.18. Da yake ba a kai jininsa cikin wuri mai tsarki ba, ya kamata ku ci akuyar a wuri mai tsarki, kamar yadda na umarta.”19. Sai Haruna ya amsa wa Musa, “Yau sun miƙa hadayarsu don zunubi da kuma hadayarsu ta ƙonawa a gaban Ubangiji, ga kuma irin waɗannan abubuwa da suka same ni, da a ce na ci hadaya don zunubi yau, da zai yi kyau ke nan a gaban Ubangiji?”20. Da Musa ya ji haka, sai ya gamsu.Zabura 25:1-71. A gare ka Ya Ubangiji, na miƙa raina.2. A gare ka na dogara, ya Allahna. Kada ka bari in sha kunya, ko ka bar abokan gābana su yi nasara a kaina.3. Ba wanda yake sa bege a gare ka da zai taɓa shan kunya, amma za su sha kunya su da suke tayarwa babu dalili.4. Ka nuna mini hanyoyinka, ya Ubangiji, ka koya mini hanyoyinka;5. ka bi da ni cikin gaskiyarka ka kuma koya mini, gama kai ne Allah Mai cetona, kuma begena yana a kanka dukan yini.6. Ka tuna, ya Ubangiji da jinƙai da kuma ƙaunarka mai girma, gama suna nan tun dā.7. Kada ka tuna da zunuban ƙuruciyata da kuma hanyoyin tawayena; bisa ga ƙaunarka ka tuna da ni, gama kai nagari ne, ya Ubangiji.Karin Magana 9:13-1813. Wawancin mace a bayyane yake; ba ta da ɗa’a kuma ba ta da sani.14. Takan zauna a ƙofar gidanta, a wurin zama a wurin mafi tsayi na birni,15. tana kira ga masu wucewa, waɗanda suke tafiya kai tsaye a hanyarsu.16. “Bari dukan waɗanda suke marasa azanci su zo cikin nan!” Tana ce wa marasa hankali.17. “Ruwan da aka sata ya fi daɗi; abincin da aka ci a ɓoye ya fi daɗi!”18. Amma ba su san cewa matattu suna a can ba, cewa baƙinta suna a can cikin zurfin kabari ba.Markus 1:23-4523. Nan take, sai wani mutum mai mugun ruhu a majami’arsu, ya ɗaga murya ya ce,24. “Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai, Mai Tsarki nan na Allah!”25. Yesu ya tsawata masa ya ce, “Yi shiru! Fita daga cikinsa!”26. Sai mugun ruhun ya jijjiga mutumin da ƙarfi, ya fita daga jikinsa da ihu.27. Dukan mutane suka yi mamaki, suna tambayar juna suna cewa, “Mene ne haka? Tabɗi! Yau ga sabuwar koyarwa kuma da iko! Yana ma ba wa mugayen ruhohi umarni, suna kuma yin masa biyayya.”28. Labari game da shi ya bazu nan da nan ko’ina a dukan yankin Galili.29. Da suka bar majami’ar, sai suka tafi gidan su Siman da Andarawus, tare da Yaƙub da Yohanna.30. Surukar Siman tana kwance da zazzaɓi, sai suka gaya wa Yesu game da ita.31. Sai ya je wajenta, ya kama hannunta, ya ɗaga ta. Zazzaɓin kuwa ya sāke ta, ta kuma yi musu hidima.32. A wannan yamma, bayan fāɗuwar rana, mutane suka kawo wa Yesu dukan marasa lafiya, da masu aljanu.33. Duk garin ya taru a ƙofar gidan.34. Yesu kuwa ya warkar da marasa lafiya da yawa da suke da cututtuka iri-iri. Ya kuma fitar da aljanu da yawa, amma bai yarda aljanun suka yi magana ba, don sun san wane ne shi.35. Da sassafe, tun da sauran duhu, Yesu ya tashi, ya bar gida, ya tafi wani wurin da ba kowa, a can ya yi addu’a.36. Siman da abokansa suka fita nemansa.37. Da suka same shi, sai suka ce, “Kowa yana nemanka!”38. Yesu ya amsa ya ce, “Mu je wani wuri dabam, zuwa ƙauyukan da suke kusa, don in yi wa’azi a can ma. Wannan shi ne dalilin zuwana.”39. Sai ya tafi ko’ina a Galili, yana wa’azi a majami’unsu, yana kuma fitar da aljanu.40. Wani mutum mai kuturta ya zo wurinsa, ya durƙusa ya roƙe shi ya ce, “In kana so, za ka iya tsabtacce ni.”41. Cike da tausayi, sai Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin ya ce, “Na yarda, ka tsabtacce!”42. Nan da nan, sai kuturtar ta rabu da shi, ya kuma warke.43. Yesu ya sallame shi nan take, da gargaɗi mai ƙarfi cewa,44. “Ka lura kada ka gaya wa kowa wannan. Amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, ka kuma miƙa hadayun da Musa ya umarta saboda tsarkakewarka, don yă zama shaida gare su.”45. A maimakon haka, sai ya fita, ya fara magana a sake, yana baza labarin. Saboda haka, Yesu bai ƙara iya shiga cikin gari a fili ba, sai dai ya kasance a wuraren da ba kowa. Duk da haka, mutane suka yi ta zuwa wurinsa daga ko’ina. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.