Baibul a cikin shekara guda Fabrairu 20Firistoci 11:1-471. Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,2. “Ku ce wa Isra’ilawa, ‘Cikin dabbobin da suke a doron ƙasa, waɗannan ne za ku ci.3. Za ku iya cin dabbobin da suke da rababben kofato, waɗanda suke kuma tuƙa.4. “ ‘Akwai waɗanda suke tuƙa ko kuwa suna da rababben kofato kawai, duk da haka ba za ku ci su ba. Waɗannan kuwa su ne, raƙumi, ko da yake yana tuƙa, amma ba shi da rababben kofato; saboda haka cin namansa haram ne gare ku.5. Rema, ko da yake tana tuƙa, duk da haka ba ta da rababben kofato; saboda haka namanta haram ne gare ku.6. Zomo, ko da yake yana tuƙa, duk da haka ba shi da rababben kofato; saboda haka namansa haram ne gare ku.7. Alade, ko da yake yana da rababben kofato, amma ba ya tuƙa, saboda haka namansa haram ne gare ku.8. Ba za ku ci namansu ba, ko ku taɓa gawawwakinsu, gama haram ne gare ku.9. “ ‘Cikin dukan halittu masu rai da suke a cikin ruwan tekuna da rafuffuka, za ku iya cin kowane da yake da ƙege da kamɓori.10. Amma kowace halittar da take cikin tekuna da koguna da ba ta da ƙege da kamɓori, ko cikin dukan abubuwa masu rai a ruwa ko kuma sauran halittu a cikin ruwa za ku ɗauka su marasa tsaki ne gare ku.11. Da yake abubuwan ƙyama ne a gare ku, ba za ku ci namansu ba, kuma dole ku yi ƙyamar gawawwakinsu.12. Duk abin da yake a ruwa amma ba shi da ƙege ko kamɓori, za ku yi ƙyamarsa.13. “ ‘Waɗannan su ne tsuntsayen da za ku yi ƙyamarsu, ba za ku ci su ba domin sun zama abin ƙyama. Tsuntsayen kuwa su ne, gaggafa, ungulu, baƙin ungulu,14. shirwa, da duk wani irin baƙin shirwa,15. kowane irin hankaka,16. mujiya mai ƙaho, jimina, shaho, da kowane irin shaho,17. ƙaramin ƙururu, babba da jaka, zalɓe,18. kazar ruwa, kwasakwasa, da ungulu,19. shamuwa, kowane irin jinjimi, katutu da kuma jamage.20. “ ‘Dukan ƙwarin da suke da fikafikai masu tafiya da ƙafafu huɗu abin ƙyama ne gare ku.21. Sai dai akwai ƙwarin da suke da fikafikai masu tafiya da ƙafafu huɗu da za ku ci; waɗanda suke da cinyoyin da suke sa su iya tsalle.22. Za ku iya cin kowane irin fāra, gyare, ƙwanso da danginsu.23. Amma sauran ƙananan ƙwari duka masu fikafikai, suna kuma jan ciki, abin ƙyama ne a gare ku.24. “ ‘Duk wanda ya taɓa mushen waɗannan dabbobi, zai ƙazantu har fāɗuwar rana.25. Duk wanda ya ɗauki ɗaya daga cikin gawawwakinsu dole yă wanke rigunansa, zai kuma ƙazantu har zuwa yamma.26. “ ‘Kowace dabbar da ba ta da rababben kofato ko ba ta tuƙa, haram ce gare ku; duk wanda ya taɓa gawarsu zai ƙazantu.27. Duk abin da yake tafiya a kan dāginsa cikin dabbobin da suke da ƙafa huɗu, haram ne a gare ku. Duk wanda ya taɓa mushensu zai ƙazantu har zuwa yamma.28. Duk wanda ya ɗauki gawawwakinsu dole yă wanke rigunansa, zai kuma ƙazantu har yamma. Waɗannan dabbobi za su zama marasa tsabta a gare ku.29. “ ‘Waɗannan ƙananan dabbobi da suke rarrafe a ƙasa, haram ne a gare ku, wato, murɗiya, da ɓera, da gafiya da irinsa,30. da tsaka, da hawainiya, da ƙadangare, da guza, da damo.31. Dukan waɗanda suke rarrafe, za su zama marasa tsarki gare ku. Duk wanda ya taɓa su sa’ad da suka mutu, zai zama ƙazantacce har zuwa yamma.32. Duk abin da mushensu ya fāɗa a kai, zai ƙazantu. Ko a kan itace ne, ko a bisa tufafi, ko a fata, ko a buhu, ko cikin kowane irin abu da ake amfani da shi, to, tilas a sa shi cikin ruwa, zai zama ƙazantacce har zuwa yamma, sa’an nan zai tsarkaka.33. In waninsu ya fāɗi a cikin tukunyar laka, kome da yake a tukunyar zai ƙazantu, kuma dole a fashe tukunyar.34. Duk abincin da aka yarda a ci, wanda ya taɓa ruwa daga irin tukunyan nan zai zama marar tsabta, kuma duk ruwan da za a sha daga irin tukunyan nan ƙazantacce ne.35. Kowane irin abu da mushensu ya fāɗa a kai ya ƙazantu ke nan; ko a kan murhu, ko a tukunyar dahuwa, dole a farfashe su. Su haramtattu ne kuma dole ku ɗauke su haramtattu.36. Maɓuɓɓuga ko tafki na tarin ruwa zai ci gaba da zauna mai tsabta, amma duk wanda ya taɓa ɗaya daga cikin waɗannan gawawwakin ya haramtu.37. In gawa ta fāɗi a irin da za a shuka, irin zai ci gaba da zama mai tsabta.38. Amma in an sa ruwa a irin sai kuma gawar ta fāɗi a kai, to, irin ya zama haram gare ku.39. “ ‘In dabbar aka yarda a ci ta mutu, duk wanda ya taɓa gawarta zai ƙazantu har yamma.40. Duk wanda ya ci wani sashe na gawar dole yă wanke rigunansa, kuma zai ƙazantu har yamma. Duk wanda ya ɗauki gawar dole yă wanke rigunansa, zai kuwa ƙazantu har yamma.41. “ ‘Duk dabba mai rarrafe a ƙasa abin ƙyama ne; ba kuwa za a ci shi ba.42. Ba za ku ci wani halittar da take rarrafe a ƙasa, ko tana jan ciki, ko tana tafiya a kan ƙafafu huɗu, ko a kan ƙafafu da yawa ba; abin ƙyama ne.43. Kada ku ƙazantar da kanku ta wurin wani daga waɗannan halittu. Kada ku ƙazantar da kanku ta dalilinsu, ko a mai da ku haramtattu ta wurinsu.44. Ni ne Ubangiji Allahnku; ku tsarkake kanku ku kuma zama da tsarki, domin Ni mai tsarki ne. Kada ku ƙazantar da kanku ta wurin wani halittar da take rarrafe a ƙasa.45. Ni ne Ubangiji wanda ya fitar da ku daga Masar don in zama Allahnku; saboda haka ku zama da tsarki, domin Ni mai tsarki ne.46. “ ‘Waɗannan ne ƙa’idodi game da dabbobi, tsuntsaye, da kowane abu mai rai da yake motsi a cikin ruwa, da kowace halitta mai rarrafe a ƙasa.47. Dole ku bambanta tsakanin haramtacce da halaltacce, tsakanin halittu masu ran da za a iya ci da waɗanda ba za a iya ci ba.’ ”Firistoci 12:1-81. Ubangiji ya ce wa Musa,2. “Faɗa wa Isra’ilawa, ‘Macen da ta yi ciki ta kuma haihu ɗa namiji za tă ƙazantu kwana bakwai, kamar yadda takan ƙazantu a lokacin al’adarta.3. A rana ta takwas, za a yi wa yaron kaciya.4. Sa’an nan dole macen ta jira kwana talatin don a tsabtacce ta daga zub da jini. Ba za tă taɓa wani abu mai tsarki, ko ta je wuri mai tsarki ba sai kwanakin tsabtaccewarta sun cika.5. In ta haifi ’ya ta mace ce, makoni biyu macen za tă ƙazantu kamar yadda takan kasance a lokacin al’adarta. Sa’an nan dole tă jira kwana sittin don a tsabtacce ta daga zub da jininta.6. “ ‘Sa’ad da kwanakin tsabtaccewarta don ɗa namiji ko ’ya ta mace suka cika, sai ta kawo ɗan rago bana ɗaya wa firist a bakin ƙofar Tentin Sujada don hadaya ta ƙonawa da tattabara ko kurciya na hadaya don zunubi.7. Firist zai miƙa su a gaban Ubangiji don yă yi kafara dominta, sa’an nan tă tsabtacce daga zub da jininta. “ ‘Waɗannan su ne ƙa’idodi domin macen da ta haifi ɗa namiji ko ’ya ta mace.8. In ba za tă iya kawo ɗan rago ba, sai ta kawo kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu, ɗaya domin hadaya ta ƙonawa ɗayan kuma domin hadaya don zunubi. Ta haka firist zai yi kafara dominta, za tă kuwa zama tsabtacciya.’ ”Zabura 25:8-158. Ubangiji nagari da mai adalci ne; saboda haka yakan koyar da masu zunubi a hanyoyinsa.9. Yakan bi da masu tawali’u cikin abin da yake daidai ya kuma koyar da su hanyoyinsa.10. Dukan hanyoyin Ubangiji ƙaunatattu ne da kuma aminci ga waɗanda suke kiyaye abin da alkawari ya bukaci.11. Saboda sunanka, ya Ubangiji, ka gafarta laifina, ko da yake mai girma ne.12. To wane ne mai tsoron Ubangiji? Zai koyar da shi a hanyar da ya zaɓa masa.13. Zai ci kwanakinsa a wadace, kuma zuriyarsa za su gāji ƙasar.14. Ubangiji yakan amince da waɗanda suke tsoronsa; yakan sa su san alkawarinsa.15. Idanuna kullum suna a kan Ubangiji, gama shi ne kaɗai zai kuɓutar da ƙafafuna daga tarko.Karin Magana 10:1-31. Karin maganar Solomon. Ɗa mai hikima yakan kawo wa mahaifinsa farin ciki, amma wawan ɗa kan sa wa mahaifiyarsa baƙin ciki.2. Dukiyar da aka samu a hanyar da ba tă dace ba, ba ta da albarka, amma adalci kan ceci mutum daga mutuwa.3. Ubangiji ba ya barin mai adalci da yunwa amma yakan lalace burin mugu.Markus 2:1-281. Bayan ’yan kwanaki, da Yesu ya sāke shiga Kafarnahum, sai mutane suka ji labarin zuwansa gida.2. Mutane suka taru da yawa har ma babu wuri, ko a bakin ƙofa ma, sai ya yi musu wa’azin bishara.3. Waɗansu mutum huɗu suka zo wajensa ɗauke da wani shanyayye.4. Da ba su iya kai shi wurin Yesu ba, saboda taron, sai suka buɗe rufin gidan saman, bisa daidai inda Yesu yake. Bayan da suka huda rami, sai suka saukar da shanyayyen, kwance a kan tabarmarsa.5. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Saurayi, an gafarta zunubanka.”6. To, waɗansu malaman dokoki da suke zaune a wurin, suka yi tunani a zuciyarsu, suna cewa,7. “Me ya sa mutumin nan yake magana haka? Yana saɓo! Wane ne zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?”8. Nan da nan, Yesu ya gane a ruhunsa abin da suke tunani a zuciyarsu, sai ya ce musu, “Me ya sa kuke tunanin waɗannan abubuwa?9. Wanne ya fi sauƙi, a ce wa shanyayyen, ‘An gafarta zunubanka,’ ko a ce, ‘Tashi, ɗauki tabarmarka ka yi tafiya’?10. Amma don ku san cewa, Ɗan Mutum yana da iko a duniya yă gafarta zunubai.” Sai ya ce wa shanyayyen,11. “Ina ce maka, tashi, ɗauki tabarmarka, ka tafi gida.”12. Sai ya tashi, ya ɗauki tabarmarsa, ya yi tafiyarsa a gabansu duka. Wannan ya ba wa kowa mamaki, suka kuma ɗaukaka Allah suna cewa, “Ba mu taɓa ganin abu haka ba!”13. Yesu ya sāke tafiya bakin tafkin. Taro mai yawa ya zo wurinsa, sai ya fara koya musu.14. Yana cikin tafiya, sai ya ga Lawi, ɗan Alfayus zaune a inda ake karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.” Sai Lawi ya tashi, ya bi shi.15. Yayinda Yesu yake cin abinci a gidan Lawi, sai masu karɓar haraji da “masu zunubi” da yawa, suka zo suka ci tare da shi da almajiransa, gama akwai mutane da yawa da suka bi shi.16. Da malaman dokoki, waɗanda su ma Farisiyawa ne, suka ga yana ci tare da masu “zunubi” da masu karɓar haraji, sai suka tambayi almajiransa, suka ce, “Me ya sa yake ci tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?”17. Da jin wannan, Yesu ya ce musu, “Ai, masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya. Ban zo domin in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi.”18. To, almajiran Yohanna da na Farisiyawa suna azumi, sai waɗansu mutane suka zo suka tambayi Yesu, suka ce, “Yaya almajiran Yohanna da na Farisiyawa suna azumi, amma almajiranka ba sa yi?”19. Yesu ya amsa ya ce, “Yaya abokan ango za su yi azumi, sa’ad da yana tare da su? Ai, ba za su yi ba, muddin yana tare da su.20. Ai, lokaci yana zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa’an nan ne fa za su yi azumi.21. “Ba mai facin sabon ƙyalle a tsohuwar riga. In ya yi haka, sabon ƙyallen zai yage daga tsohuwar, yagewar kuwa za tă zama da muni.22. Ba wanda yakan zuba sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. In ya yi haka, ruwan inabin zai farfashe salkunan, yă yi hasarar ruwan inabin, salkunan kuma su lalace. A’a, yakan zuba sabon ruwan inabin a sababbin salkuna.”23. Wata ranar Asabbaci, Yesu yana ratsa gonakin hatsi, sai almajiransa da suke tafiya tare da shi, suka fara kakkarya waɗansu kan hatsi.24. Farisiyawa suka ce masa, “Duba, me ya sa suke yin abin da doka ta hana a yi, a ranar Asabbaci?”25. Ya amsa ya ce, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi ba, sa’ad da shi da abokan tafiyarsa suka ji yunwa, suna kuma cikin bukata?26. Ya shiga gidan Allah a zamanin Abiyatar babban firist, ya ci keɓaɓɓen burodin nan, ya kuma ba wa abokan tafiyarsa abin da firistoci kaɗai sukan ci bisa ga doka?”27. Sai ya ce musu, “An yi Asabbaci saboda mutum ne, ba mutum saboda Asabbaci ba.28. Don haka, Ɗan Mutum Ubangiji ne, har ma da na Asabbaci.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.