Baibul a cikin shekara guda Fabrairu 24Firistoci 17:1-161. Ubangiji ya ce wa Musa,2. “Yi magana da Haruna da ’ya’yansa maza da kuma dukan Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji ya umarta.3. Duk mutumin Isra’ilan da ya yanka sa, ɗan rago ko akuya a sansani ko waje da shi4. a maimakon kawo shi a matsayin hadaya ga Ubangiji a gaban tabanakul na Ubangiji, za a ɗauki wannan mutum a matsayi mai laifin zub da jini, ya zub da jini, kuma dole a raba shi da mutanensa.5. Wannan ya zama haka saboda Isra’ilawa su kawo wa Ubangiji hadayun da suke yi a filaye. Dole su kawo su ga firist, wato, ga Ubangiji, a ƙofar Tentin Sujada, su miƙa su a matsayin hadayun salama.6. Firist zai yayyafa jinin a bagaden Ubangiji, a ƙofar Tentin Sujada, yă kuma ƙone kitsen kamar ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.7. Kada kuma su ƙara yin hadayunsu ga gumaka masu siffar bunsurai waɗanda suka bauta wa. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a gare su wa tsararraki masu zuwa.’8. “Faɗa musu, ‘Duk wani mutumin Isra’ila ko wani baƙon da yake zama a cikinsu wanda ya miƙa hadaya ta ƙonawa ko sadaka9. kuma bai kawo shi a ƙofar Tentin Sujada don yă miƙa shi ga Ubangiji ba, dole a raba wannan mutum da mutanensa.10. “ ‘Duk mutumin Isra’ila ko baƙon da yake zama a cikinsu wanda ya ci wani jini, zan yi gāba da wannan mutum wanda ya ci jinin, za a kuma raba shi da mutanensa.11. Gama ran halitta yana a cikin jinin, kuma na ba da shi gare ku don kafara a kan bagade, jini ne yake kafara saboda ran mutum.12. Saboda haka na ce wa Isra’ilawa, “Babu waninku da zai ci jini, babu wani baƙon da yake zama a cikinku da zai ci jini.”13. “ ‘Duk wani mutumin Isra’ila ko baƙon da yake zama a cikinku wanda ya ji wa wani dabba ko tsuntsu wanda ake ci ciwo, dole yă tsiyaye jinin yă rufe shi da ƙasa,14. domin ran kowace halitta yana cikin jini. Shi ya sa na ce wa Isra’ilawa, “Kada ku ci jinin wani halitta, domin ran kowace halitta yana cikin jinin; duk wanda ya ci shi dole a fid da shi.”15. “ ‘Kowa, ko haifaffe ɗan ƙasa ko baƙo, da ya ci wani abin da aka sami a mace, ko naman jeji ya yayyage, dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma; sa’an nan zai tsarkake.16. Amma in bai wanke rigunansa ya kuma yi wanka ba, alhaki zai kasance a kansa.’ ”Firistoci 18:1-301. Ubangiji ya ce wa Musa,2. “Yi wa Isra’ilawa magana ka kuma faɗa musu cewa, ‘Ni ne Ubangiji Allahnku.3. Kada ku yi yadda suke yi a Masar inda da kuke zama, kuma ba a ku yi kamar yadda suke yi a ƙasar Kan’ana inda nake kawo ku ba. Kada ku yi yadda suke yin abubuwa.4. Dole ku kiyaye dokokina kuma ku lura ku bi farillaina. Ni ne Ubangiji Allahnku.5. Ku kiyaye farillaina da dokokina, gama mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu. Ni ne Ubangiji.6. “ ‘Kada wani ya kusaci wani dangi na kusa don yă yi jima’i. Ni ne Ubangiji.7. “ ‘Kada ka ƙasƙantar da mahaifinka ta wurin kwana da mahaifiyarka. Ita mahaifiyarka ce; kada ka yi jima’i da ita.8. “ ‘Kada ka yi jima’i da matar mahaifinka, wannan zai ƙasƙantar da mahaifinka.9. “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar’uwarka, ko ’yar mahaifinka ko ’yar mahaifiyarka, ko an haife ta a gida ɗaya da kai ko kuwa a wani wuri dabam.10. “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar ɗanka ko ’yar ’yarka, wannan zai ƙasƙantar da kai.11. “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar matar mahaifinka wadda aka haifa wa mahaifinka; ita ’yar’uwarka ce.12. “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar’uwar mahaifinka, ita dangin mahaifinka ne na kusa.13. “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar’uwar mahaifiyarka, domin ita dangin mahaifiyarka ce na kusa.14. “ ‘Kada ka ƙasƙantar da ɗan’uwan mahaifinka ta wurin kusaci matarsa don ka yi jima’i da ita, ita bābarka ce.15. “ ‘Kada ka yi jima’i da matar ɗanka. Ita matar ɗanka ne; kada ka yi jima’i da ita.16. “ ‘Kada ka yi jima’i da matar ɗan’uwanka; wannan zai ƙasƙanta ɗan’uwanka.17. “ ‘Kada ka yi jima’i da mace da kuma ’yarta. Kada ka yi jima’i da ’yar ɗanta ko ’yar ’yarta; su danginta ne na kusa. Wannan mugun abu ne.18. “ ‘Kada ka auri ’yar’uwar matarka ta zama kishiyar matarka ka kuma yi jima’i da ita yayinda matarka tana da rai.19. “ ‘Kada ka kusaci mace don ka yi jima’i da ita a lokacin ƙazantar al’adarta.20. “ ‘Kada ka yi jima’i da matar maƙwabcinka ka ƙazantar da kanka tare da ita.21. “ ‘Kada ku ba da wani daga cikin ’ya’yanku don a yi hadaya wa Molek, gama ba za ku ƙasƙantar da sunan Allahnku ba. Ni ne Ubangiji.22. “ ‘Kada ka kwana da namiji kamar yadda namiji yakan kwana da ta mace, wannan abin ƙyama ne.23. “ ‘Kada ka yi jima’i da dabba ka ƙazantar da kanka. Mace ba za tă ba da kanta ga dabba don yă yi jima’i da ita ba; wannan abin ƙyama ne.24. “ ‘Kada ku ƙazantar da kanku da wani daga cikin waɗannan, domin haka al’umman da zan kora a gabanku suka ƙazantu.25. Har ƙasar ma ta ƙazantu, saboda haka na hukunta ta saboda zunubinta, ƙasar kuwa ta amayar da mazaunanta.26. Amma dole ku kiyaye farillaina da kuma dokokina. Kada haifaffe ɗan ƙasa da baƙin da suke zama a cikinku yă yi wani daga cikin waɗannan abubuwa banƙyama,27. gama mutanen da suka zauna a wannan ƙasa kafin ku sun aikata dukan waɗannan abubuwa, suka kuma ƙazantu.28. Kuma in kuka ƙazantar da ƙasar, za tă amayar da ku kamar yadda ta amayar da al’umman da suka riga ku.29. “ ‘Duk wanda ya yi wani daga cikin waɗannan abubuwa banƙyama, dole a fid da mutumin daga cikin mutanensa.30. Ku kiyaye umarnaina kuma kada yi ku wata al’ada mai banƙyamar da aka yi kafin ku zo kuma kada ku ƙazantar da kanku da su. Ni ne Ubangiji Allahnku.’ ”Zabura 27:1-31. Ubangiji ne haskena da cetona, wa zan ji tsoro? Ubangiji ne mafakar raina, wane ne zan ji tsoro?2. Sa’ad da mugaye suka tasar mini don su cinye ni, sa’ad da abokan gābana da maƙiyina suka kawo mini hari, sun yi tuntuɓe suka fāɗi.3. Ko da yake mayaƙa sun kewaye ni, zuciyata ba za tă ji tsoro ba; ko da yake ya ɓarke a kaina, duk da haka zan ƙarfafa.Karin Magana 10:9-99. Mai mutunci yana tafiya lafiya, amma shi da yake tafiya a karkatattun hanyoyi za a kama shi.Markus 4:21-4121. Sai ya ce musu, “Ko kukan kawo fitila ku rufe ta da murfi ko kuma ku sa ta a ƙarƙashin gado ne? Ba kukan sa ta a kan wurin ajiye fitila ba?22. Duk abin da yake a ɓoye, dole za a fallasa shi. Duk abin da kuma yake a rufe, dole za a fitar da shi a fili.23. Duk mai kunnen ji, bari yă ji.”24. Ya ci gaba da cewa, “Ku lura da abin da kuke ji da kyau. Mudun da ka auna da shi, da shi za a auna maka, har ma a ƙara.25. Duk wanda yake da shi, za a ƙara masa, duk wanda kuma ba shi da shi, ko abin da yake da shi ma, za a karɓe daga gare shi.”26. Ya sāke cewa, “Mulkin Allah yana kama da haka. Wani mutum ya yafa iri a gona.27. A kwana a tashi har irin yă tsiro, yă yi girma, bai kuwa santa yadda aka yi ba.28. Ƙasar da kanta takan ba da ƙwaya, da farko takan fid da ƙara, sa’an nan ta fid da kai, sa’an nan kan yă fid da ƙwaya.29. Da ƙwayan ya nuna, sai yă sa lauje yă yanka, domin lokacin girbi ya yi.”30. Ya kuma ce, “Da me za mu kwatanta mulkin Allah, ko kuwa da wane misali za mu bayyana shi?31. Yana kama da ƙwayar mustad, wadda ita ce ƙwaya mafi ƙanƙanta da akan shuka a gona.32. Duk da haka, in aka shuka ƙwayar, sai tă yi girma, tă zama mafi girma a itatuwan lambu. Har itacen yă kasance da manyan rassa, inda tsuntsayen sararin sama sukan iya huta a inuwarsa.”33. Da misalai da yawa irin waɗannan, Yesu ya yi magana da su, daidai yadda za su iya fahimta.34. Ba abin da ya faɗa musu, da ba da misali ba. Amma lokacin da yake shi kaɗai tare da almajiransa, sai yă bayyana kome.35. A wannan rana, da yamma, sai ya ce wa almajiransa, “Mu ƙetare zuwa wancan hayi.”36. Da suka bar taron, sai suka tafi tare da shi yadda yake, a cikin jirgin ruwa. Akwai waɗansu jiragen ruwa kuma tare da shi.37. Sai babban hadari mai iska ya tashi, raƙuman ruwa suna ta bugun jirgin ruwan, har jirgin ruwan ya kusa yă cika da ruwa.38. Yesu kuwa yana can baya, yana barci a kan katifa. Sai almajiran suka tashe shi suka ce masa, “Malam, ba ka kula ba ko mu nutse?”39. Sai ya farka ya tsawata wa iskar, ya ce wa raƙuman ruwan, “Shiru! Ku natsu!” Sai iskar ta kwanta, kome kuma ya yi tsit.40. Sai ya ce wa almajiransa, “Don me kuke tsoro haka? Har yanzu ba ku da bangaskiya ne?”41. Suka tsorata, suka ce wa juna, “Wane ne wannan? Har iska da raƙuman ruwa ma suna masa biyayya!” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.