Baibul a cikin shekara guda Fabrairu 29Firistoci 25:1-551. Ubangiji ya yi magana da Musa a kan Dutsen Sinai ya ce,2. “Yi wa Isra’ilawa magana, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar da zan ba ku, dole ƙasar kanta ta kiyaye Asabbaci ga Ubangiji.3. Shekara shida, za ku yi shuki, shekara shida kuma za ku aske gonakin inabinku, ku kuma tattara hatsinsu.4. Amma a shekara ta bakwai, ƙasar za tă sami hutun Asabbaci, Asabbaci ga Ubangiji. Kada ku yi shuki a gonakinku, ko kuwa ku aske gonakinku na inabi.5. Kada ku girbe abin da ya yi girma ba tare da ku kuka shuka ba, ko ku girbe inabin da ba ku aske ba. Ƙasar za tă kasance da shekarar hutu.6. Duk abin da gonar ta ba da amfani a shekara ta Asabbaci, zai zama abinci gare ku, wa kanku, bayinku maza da mata, da ma’aikatan da kuka ɗauka aiki, da kuma waɗanda ba zama ɗinɗinɗin suke yi tare da ku ba,7. haka ma zai zama abinci domin dabbobinku, da kuma namun jeji a ƙasarku. Duk abin da ƙasar ta bayar za a ci.8. “ ‘Ku ƙirga asabbatai bakwai na shekaru bakwai, sau bakwai. Gama asabbatai bakwai na shekaru bakwai za su yi daidai da shekaru arba’in da tara.9. Sa’an nan a busa ƙaho a ko’ina, a rana ta goma ga wata na bakwai; a Ranar Kafara, a busa ƙaho a dukan ƙasarku.10. Ku keɓe shekara ta hamsin ku kuma yi shelar ’yanci a dukan ƙasar ga mazaunanta. Za tă zama shekarar murna gare ku; kowannenku zai koma ga mallakar iyalinsa, kuma kowa ga danginsa.11. Shekara ta hamsin za tă zama ta murna a gare ku; kada ku yi shuki, kada kuma ku yi girbi abin da ya yi girma da kansa, ko ku girbe inabin da ba ku lura da shi ba.12. Gama shekara ce ta murna, za tă kuma zama mai tsarki a gare ku, ku dai ci abin da aka ɗauka kai tsaye daga gonaki.13. “ ‘A wannan Shekara ta Murna, kowa zai koma ga mallakarsa.14. “ ‘In ka sayar da gona wa wani daga mutanen ƙasarka, ko ka saya wata gona daga gare shi, kada ku cuci juna.15. Sa’ad da mutum ya sayi fili daga abokin zamansa, kuɗin zai kasance bisa ga yawan shekara hamsin ta murna da suka wuce, da kuma bisa ga yawan shekarun noma da suka rage kafin wata shekara hamsin ta murna.16. Idan shekarun suna da yawa, sai ku kara kuɗin filin, idan kuma shekarun ba su da yawa, sai ku rage kuɗin filin, gama ainihin abin da ake sayar maka shi ne yawan hatsin.17. Kada ku cuci juna, amma ku ji tsoron Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.18. “ ‘Ku bi farillaina, ku kuma yi hankali ga kiyaye dokokina, za ku kuwa zauna lafiya a ƙasar.19. Sa’an nan ƙasar za tă ba da amfaninta, za ku kuwa ci ku ƙoshi, ku kuma zauna lafiya.20. Mai yiwuwa ku ce, “Me za mu ci a shekara ta bakwai in ba mu yi shuki ko girbin hatsinmu ba?”21. Zan aika muku da irin albarka a shekara ta shida har da ƙasar za tă ba da amfani isashe na shekara uku.22. Yayinda kuke shuki a shekara ta takwas, za ku kasance da raguwa hatsi na shekarar da ta wuce, za ku kuma ci gaba da ci daga gare shi har girbin shekara ta tara yă shigo.23. “ ‘Kada a sayar da gona ɗinɗinɗin, gama ƙasar tawa ce, ku kuwa baƙi ne kawai, kuma ’yan haya nawa.24. Ko’ina a ƙasar da kuke da mallaka, dole ku tanadar da dama fansar ƙasar.25. “ ‘In ɗaya daga cikin mutanen ƙasarku ya talauta, ya kuma sayar da mallakarsa, sai danginsa na kusa yă je yă fanshi abin da mutumin ƙasarsa ya sayar.26. In mutumin ba shi da wanda zai fansa masa ita, shi kansa kuwa ya wadace, ya kuma sami isashen halin fansarta,27. sai yă lasafta yawan shekarun da aka yi tun da an sayar da filin. Kuɗin filin zai dangana ga yawan shekarun da suka rage kafin shekara hamsin ta murna da za tă zo; sa’an nan zai iya koma ga mallakarsa.28. Amma in bai sami halin sāke biyansa ba, abin nan da ya sayar zai ci gaba da zama mallakar mai sayan, sai Shekara ta Murna. Za a maido masa da ita a Shekara ta Murna, sa’an nan zai iya koma ga mallakarsa.29. “ ‘In mutum ya sayar da gida a birni mai katanga, yana da izini yă fanshe shi a ƙarshen shekara guda, bayan ya sayar da shi.30. In ba a fanshe shi a ƙarshen shekara ba, gidan da yake a birni mai katanga, zai zama mallakar na ɗinɗinɗin na mai sayan da kuma zuriyarsa. Ba za a mai da shi a Shekara ta Murna ba.31. Amma za a ɗauki gidaje a ƙauyuka marasa katanga kewaye da su daidai da gonaki. Za a iya fanshe su, a kuma mayar da su a Shekara ta Murna.32. “ ‘Kullum, Lawiyawa suna da izini su fanshi gidajensu a biranen Lawiyawa waɗanda suka mallaka.33. Saboda haka ana iya fansa mallakar Lawiyawa, wato, gidan da aka sayar a duk birnin da yake nasu, za a kuma mayar a Shekara ta Murna, gama gidaje a biranen Lawiyawa, mallakar Isra’ilawa ne.34. Amma kada a sayar da filayen kiwo na waɗannan birane; mallakarsu ce, ta ɗinɗinɗin.35. “ ‘In ɗaya daga ciki mutanen ƙasarku ya talauta, ba ya kuma iya tallafa wa kansa a cikinku, sai ku taimake shi kamar yadda za ku yi da baƙo a cikinku.36. Kada ku karɓi riba ta kowace iri daga gare shi, amma ku ji tsoron Allahnku, saboda mutumin ƙasarku yă ci gaba da zama a cikinku.37. Kada ku ba shi rancen kuɗi da ruwa, ko ku sayar masa abinci don samun riba.38. Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, don in ba ku ƙasar Kan’ana in kuma zama Allahnku.39. “ ‘In ɗaya daga cikin mutanen ƙasarku ya talauta a cikinku, ya kuma sayar da kansa gare ku, kada ku sa yă yi kamar bawa.40. Amma a ɗauke shi a matsayin ma’aikacin da aka ɗauka aiki, ko mazaunan da ba na ɗinɗinɗin ba a cikinku, sai yă yi muku aiki sai Shekara ta Murna.41. Sa’an nan a sake shi da ’ya’yansa, yă kuma koma ga danginsa da mallakar kakanninsa.42. Gama Isra’ilawa bayina ne, waɗanda na saya daga Masar, kada a sayar da su a matsayin bayi.43. Kada ku gwada musu azaba, amma ku ji tsoron Allahnku.44. “ ‘Bayinku maza da mata, za su zo daga al’ummai da suke kewaye da ku, daga gare su za ku iya saya bayi.45. Za ku iya saya waɗansu mutanen da ba sa zama ɗinɗinɗin a cikinku, da kuma membobin danginsu da aka haifa a ƙasarku.46. Za ku iya ba da su ga ’ya’yanku a matsayin kayan gādo, za ku kuma iya mai da su bayi dukan rayuwarsu, amma kada ku yi mulki a bisa ’yan’uwanku Isra’ilawa da tsanani.47. “ ‘In baƙo, ko wani da yake zama ba na ɗinɗinɗin ba a cikinku, ya wadace, ɗaya daga cikin mutanen ƙasarku kuwa ya talauta, ya kuma sayar da kansa ga baƙon da yake zama a cikinku, ko memba na dangin baƙon,48. yana da izini samun fansa, bayan ya sayar da kansa. Ɗaya daga cikin danginsa zai iya fansarsa.49. Kawu ko yaron ɗan’uwan mahaifin wannan mutum, ko kuwa wani dangi a cikin zuriyarsa, zai iya fanshe shi. Ko kuma in ya azurta, zai iya fansar kansa.50. Da shi da mai sayansa, za su ƙirga lokaci daga shekarar da ya sayar da kansa har zuwa Shekara ta Murna. Farashin sakinsa zai dangana a kuɗin da ake biyan ma’aikacin da aka ɗauka aiki, na yawan shekarun ne.51. In shekaru sun ragu, dole yă biya don fansarsa da kuɗi mai yawa fiye da wanda aka saye shi.52. In shekarun sun rage kaɗan ne kafin Shekara ta Murna, sai yă yi lissafin wannan, yă kuma biya fansarsa daidai wa daida.53. Sai a yi da shi kamar ma’aikacin da aka ɗauka aiki, daga shekara zuwa shekara; dole ku tabbata mai shi bai mallake shi da tsanani ba.54. “ ‘Ko ma ba a fanshe shi a ɗaya daga cikin waɗannan hanyoyi ba, sai a sake shi da ’ya’yansa a Shekara ta Murna,55. gama Isra’ilawa nawa ne a matsayin bayi. Su bayina ne waɗanda na saya daga Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.Zabura 28:6-96. Yabo ya tabbata ga Ubangiji, gama ya ji kukata na neman jinƙai.7. Ubangiji shi ne ƙarfina da garkuwata; zuciyata ta amince da shi, kuma na sami taimako. Zuciyata ta yi tsalle don farin ciki zan kuwa yi godiya gare shi cikin waƙa.8. Ubangiji shi ne ƙarfin mutanensa, kagarar ceto domin shafaffensa.9. Ka cece mutanenka ka kuma albarkace gādonka; ka zama mai kiwonsu ka kuma riƙe su har abada.Karin Magana 10:19-2119. Sa’ad da magana ta yi yawa, ba a rasa zunubi a ciki, amma shi da ya ƙame harshensa mai hikima ne.20. Harshen adali azurfa ce zalla, amma zuciyar mugu ba ta da wani amfani.21. Leɓunan adalai kan amfane yawanci, amma wawa kan mutu saboda rashin azanci.Markus 6:30-5630. Manzannin suka taru kewaye da Yesu, suka ba shi rahoton duk abin da suka yi, da kuma suka koyar.31. To, saboda mutane da yawa suna kai da kawowa, har ma ba su sami damar cin abinci ba, sai ya ce musu, “Ku zo mu kaɗaita inda ba kowa don ku ɗan huta.”32. Sai suka tafi a jirgin ruwa su kaɗai, inda ba kowa.33. Amma mutane da yawa waɗanda suka ga tashinsu, sun gane su, sai suka ruga da gudu a ƙafa daga dukan birane, suka riga su kaiwa can.34. Da Yesu ya sauka, ya ga taro mai yawa, sai ya ji tausayinsu, gama kamar tumaki suke waɗanda ba su da makiyayi. Sai ya fara koya musu abubuwa da yawa.35. A lokacin nan yamma ta yi, sai almajiransa suka zo wurinsa suka ce masa, “Wurin nan ƙauye ne, ga shi kuma lokaci ya ƙure.36. Ka sallami mutanen su shiga ƙauyukan da suke kurkusa, su sayi wa kansu wani abu, su ci.”37. Sai ya amsa ya ce, “Ku, ku ba su wani abu su ci.” Suka ce masa, “Ai, wannan zai ɗauki albashin wata takwas na mutum! Mu je mu kashe yawan kuɗin nan a burodi mu ba su su ci?”38. Sai ya yi tambaya ya ce, “Burodi nawa kuke da su? Je ku duba.” Da suka duba, sai suka ce, “Biyar da kifi biyu.”39. Sa’an nan Yesu ya umarce su su sa dukan mutanen su zazzauna ƙungiya-ƙungiya a kan ɗanyar ciyawa.40. Haka suka zazzauna a ƙungiyar ɗari-ɗari, da kuma hamsin-hamsin.41. Ya ɗauki burodi guda biyar da kifin nan biyu, ya ɗaga kai sama, ya yi godiya, ya kakkarya burodin. Sai ya ba wa almajiransa su rarraba wa mutane. Ya kuma rarraba kifi biyun a tsakaninsu duka.42. Kowa ya ci, ya ƙoshi,43. almajiran suka kwashe gutsattsarin burodin da na kifin cike da kwanduna goma sha biyu.44. Yawan mutanen da suka ci kuwa maza dubu biyar ne.45. Nan da nan Yesu ya sa almajiransa su shiga jirgin ruwa, su sha gabansa zuwa Betsaida, shi kuma yă sallami taron.46. Bayan ya bar su, sai ya hau kan dutse don yă yi addu’a.47. Da yamma ta yi, jirgin ruwan yana tsakiyar tafkin, Yesu kuma yana can a ƙasa shi kaɗai.48. Ya ga almajiran suna fama da tuƙi saboda iska tana gāba da su. Wajen tsara ta huɗu na dare, sai ya tafi wurinsu, yana takawa a kan tafkin. Ya yi kamar zai wuce su,49. amma da suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai suka yi tsammani fatalwa ce. Sai suka yi ihu,50. domin dukansu sun gan shi, suka kuma tsorata. Nan da nan ya yi magana da su ya ce, “Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro.”51. Sai ya shiga jirgin ruwan tare da su, iskar kuma ta kwanta. Dukansu suka yi mamaki,52. gama ba su fahimci al’amarin burodin nan ba, don zuciyarsu ta taurare.53. Da suka haye, sai suka sauka a Gennesaret, suka daure jirgin a ƙugiya.54. Da fitowarsu daga jirgin, sai mutane suka gane Yesu.55. Suka gama yankin da gudu, suna ɗaukan marasa lafiya a kan tabarmai zuwa duk inda suka ji yake.56. Duk inda ya shiga, cikin ƙauyuka, birane ko karkara, sai su kwantar da marasa lafiya a bakin kasuwa. Suka roƙe shi yă bari su taɓa gefen rigarsa kawai, kuma duk waɗanda suka taɓa shi kuwa, suka warke. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.