Baibul a cikin shekara guda Fabrairu 3Fitowa 17:1-161. Dukan taron Isra’ilawa suka kama tafiya daga Hamadar Sin, suka yi ta tafiya suna sauka a wurare dabam-dabam bisa ga umarnin Ubangiji. A ƙarshe suka sauka a Refidim, suka zauna a can, amma ba ruwan da jama’a za su sha.2. Saboda haka suka yi wa Musa maganganun banza suka ce, “Ba mu ruwa mu sha.” Musa ya amsa ya ce, “Don me kuke mini maganganun banza? Don me kuke gwada Ubangiji?”3. Amma mutanen suka yi fama da ƙishirwa a can, suka yi gunaguni a kan Musa. Suka ce, “Don me ka fitar da mu daga Masar, ka sa mu da ’ya’yanmu da dabbobinmu, mu mutu da ƙishirwa?”4. Sai Musa ya yi kuka ga Ubangiji ya ce, “Me zan yi da wannan jama’a? Suna shiri su jajjefe ni da duwatsu.”5. Ubangiji amsa wa Musa, “Ka ɗauki sandan da ka bugi ruwan Nilu da shi. Ka kira waɗansu shugabannin Isra’ila, ku wuce a gaban jama’ar.6. Zan tsaya a can a gabanka, kusa da dutsen Horeb. Ka bugi dutsen, ruwa kuwa zai fito daga gare shi domin mutane su sha.” Sai Musa ya yi haka a idon dattawan Isra’ila.7. Sai suka ba wa wurin suna, Massa da Meriba, saboda Isra’ilawa sun yi jayayya, suka kuma gwada Ubangiji cewa, “ Ubangiji yana tsakaninmu ko babu?”8. Amalekawa suka zo, suka yaƙi Isra’ilawa a Refidim.9. Musa ya ce wa Yoshuwa, “Zaɓi waɗansu mazanmu, ka je ka yaƙi Amalekawa. Gobe zan tsaya a bisa tudu, da sandan Allah a hannuwana.”10. Sai Yoshuwa ya yaƙi Amalekawa kamar yadda Musa ya umarta, Musa, Haruna da Hur kuwa suka tafi bisa tudu.11. Muddin hannun Musa yana a miƙe, sai Isra’ilawa su yi ta cin nasara, amma da zarar hannunsa ya sauka, sai Amalekawa su yi ta cin nasara.12. Sa’ad da hannuwan Musa suka gaji, sai Haruna da Hur suka ɗauki dutse suka sa ya zauna a kai. Sa’an nan su kuma suka tsaya gefe da gefe, suna riƙe da hannuwansa har fāɗuwar rana.13. Sai Yoshuwa kuwa ya ci nasara a kan Amalekawa da takobi.14. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka rubuta wannan a cikin littafi, yă zama abin tuni, ka kuma faɗa wa Yoshuwa zan hallaka Amalekawa ƙaƙaf daga duniya.”15. Musa ya gina bagade, sai ya kira shi Ubangiji shi ne Tutata.16. Ya ce, “Gama an ɗaga hannuwa sama zuwa kursiyin Ubangiji, Ubangiji zai yaƙi Amalekawa daga tsara zuwa tsara.”Fitowa 18:1-271. Ana nan sai Yetro firist na Midiyan, kuma surukin Musa, ya ji duk abin da Allah ya yi wa Musa da mutanensa Isra’ila, da kuma yadda Ubangiji ya fitar da Isra’ila daga Masar.2. Bayan da Musa ya tura matarsa Ziffora gida, sai surukinsa Yetro ya karɓe ta3. da ’ya’yanta biyu maza. Ana kira ɗaya Gershom, domin Musa ya ce, “Na zama baƙo a baƙuwar ƙasa”;4. ɗayan kuma Eliyezer, domin ya ce, “Allah mahaifina ya taimake ni ya cece ni daga takobin Fir’auna.”5. Yetro surukin Musa tare da ’ya’yan Musa da matarsa suka zo wurin Musa a hamada, inda suka kafa sansani kusa da dutsen Allah6. Yetro ya riga ya aika wa Musa cewa, “Ni surukinka Yetro, ina zuwa wurinka tare da matarka da ’ya’yanka maza biyu.”7. Sai Musa ya tafi yă taryi surukinsa, ya sunkuya ya yi masa sumba. Suka gai da juna, sa’an nan suka shiga tenti.8. Musa kuwa ya faɗa wa surukinsa duk abubuwan da Ubangiji ya yi wa Fir’auna da Masarawa domin Isra’ila, da batun wahalolin da suka sha a hanya, da yadda Ubangiji ya cece su.9. Yetro ya yi murna da jin duk abubuwa masu kyau da Ubangiji ya yi wa Isra’ila, wajen cetonsu daga hannun Masarawa.10. “Yabo ga Ubangiji wanda ya cece ku daga hannun Masarawa da na Fir’auna, wanda kuma ya cece mutanensa daga hannun Masarawa.11. Yanzu na san cewa Ubangiji ya fi kowane allah, gama ya yi wannan ga masu girman kai da kuma waɗanda suka wulaƙanta Isra’ila.”12. Sa’an nan Yetro surukin Musa, ya kawo hadaya ta ƙonawa da waɗansu hadayu wa Allah, Haruna ya zo tare da dukan dattawan Isra’ila, suka ci abinci tare da surukin Musa a gaban Allah.13. Kashegari, Musa ya zauna domin yă yi wa mutane shari’a, sai suka tsaya kewaye da shi daga safe har yamma.14. Sa’ad da surukinsa ya lura da duk abin da Musa yake yi saboda mutane, sai ya ce, “Mene ne wannan da kake yi wa mutane? Don me kai kaɗai kake zama kana yin shari’a wa mutane, yayinda mutanen nan suke tsaya kewaye da kai daga safe har yamma?”15. Musa ya amsa ya ce, “Saboda mutanen suna zuwa wurina, don su nemi nufin Allah.16. Duk lokacin da suke da gardama, akan kawo su a wurina, ni kuma sai in raba tsakaninsu, in kuma koya musu dokokin Allah da farillansa.”17. Surukin Musa ya amsa ya ce, “Abin da kake yi ba daidai ba ne.18. Kai da dukan mutanen da suke zuwa wurinka za ku gajiyar da kanku. Aikin ya fi ƙarfinka; ba za ka iya yinsa kai kaɗai ba.19. Ka kasa kunne gare ni yanzu, zan ba ka shawara, Allah kuma yă kasance tare da kai. Kai za ka zama wakilin mutane a gaban Allah, ka kuma kawo gardamansu gare shi.20. Ka koya musu dokokinsa da farillarsa, ka kuma nuna musu hanyar rayuwa da ayyukan da za su yi.21. Amma ka zaɓi mutane masu iyawa daga dukan mutane, maza masu tsoron Allah, amintattu, masu ƙin rashawa, ka sanya su shugabanni na dubbai, ɗari-ɗari, hamsin-hamsin da goma-goma.22. Bari waɗannan mutane su sassanta mutane a kan ƙananan matsaloli, amma kowace babban matsala, ko bukata ta musamman, sai su kawo wurinka, ƙananan matsaloli kuma sai su yanke hukuncin da kansu. Ta haka ne za su taimaka wajen ɗaukan nauyin jama’a, don su sa aikin yă zama maka da sauƙi.23. In ka yi haka, Allah ya umarta za ka iya jimre gajiyar, kuma dukan mutanen nan za su koma gida da murna.”24. Musa ya kasa kunne ga surukinsa, ya kuma aikata duk abin da ya faɗa.25. Ya zaɓi mutane masu iyawa daga cikin dukan Isra’ila, ya naɗa su shugabannin mutane, shugabanni a kan dubbai, ɗari-ɗari, hamsin-hamsin da goma-goma.26. Suka yi hidimar alƙalanci na mutane a dukan lokaci. Gardandamin da suke da wuya, suka kawo wurin Musa, amma ƙananan batuttuwa, suka shari’anta a tsakaninsu.27. Sa’an nan Musa ya sallame surukinsa Yetro, ya kuwa koma ƙasarsa.Zabura 18:28-3628. Kai Ya Ubangiji, ka sa fitilata ta yi ta ci; Allahna ya mai da duhu ya zama haske.29. Da taimakonka zan iya fāɗa wa runduna; tare da Allahna zan iya rinjayi katanga.30. Game da Allah kuwa, hanyarsa cikakkiya ce; maganar Ubangiji marar kuskure ne. Shi garkuwa ne ga dukan waɗanda suke neman mafaka a gare shi.31. Gama wane ne Allah in ba Ubangiji ba? Wane ne kuwa Dutse in ba Allahnmu ba?32. Allah ne ya ƙarfafa ni da ƙarfi ya kuma sa hanyarta ta zama cikakkiya.33. Ya sa ƙafafuna kamar ƙafafun barewa; ya sa na iya tsaya a kan ƙwanƙoli.34. Ya horar da hannuwana don yaƙi; hannuwana za su iya tanƙware bakan tagulla.35. Ka ba ni garkuwar nasara, kuma hannunka na dama yana riƙe ni; ya sunkuya don ka mai da ni mai girma.36. Ka fadada hanyar da yake a ƙarƙashina, don kada ɗiɗɗigena yă juya.Karin Magana 6:16-1916. Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi, abubuwa bakwai da suke abin ƙyama gare shi,17. duban reni, harshe mai ƙarya, hannuwa masu zub da jinin marar laifi,18. zuciyar da take ƙulla mugayen dabaru, ƙafafun da suke sauri zuwa aikata mugunta,19. mai shaidar ƙarya wanda yake zuba ƙarairayi, da kuma mutumin da yake tā-da-na-zaune-tsaye a cikin ’yan’uwa.Mattiyu 22:1-221. Yesu ya sāke yin musu magana da misalai, yana cewa,2. “Mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya shirya bikin auren ɗansa.3. Sai ya aiki bayinsa su kira waɗanda aka gayyata zuwa bikin, amma waɗanda aka ce su zo bikin, suka ƙi zuwa.4. “Sai ya sāke aiken waɗansu bayi ya ce, ‘Ku ce wa waɗanda aka gayyata cewa na shirya abinci. An yanka bijimai da shanun da aka yi kiwo, kome a shirye yake. Ku zo bikin auren mana.’5. “Amma ba su kula ba, suka kama gabansu, ɗaya ya tafi gonarsa, ɗaya kuma ya tafi kasuwancinsa.6. Sauran suka kama bayinsa suka wulaƙanta su, suka kuma kashe su.7. Sai sarkin ya yi fushi. Ya aiki mayaƙansa suka karkashe masu kisankan nan, aka kuma ƙone birninsu.8. “Sa’an nan ya ce wa bayinsa, ‘Bikin aure fa ya shiryu, sai dai mutanen da na gayyata ba su dace ba.9. Ku bi titi-titi ku gayyato duk waɗanda kuka gani, su zo bikin.’10. Saboda haka bayin suka bi titi-titi, suka tattaro duk mutanen da suka samu, masu kirki da marasa kirki, zauren bikin ya cika makil da baƙi.11. “Amma da sarkin ya shigo don yă ga baƙin, sai ya ga wani can da ba ya sanye da kayan auren.12. Ya yi tambaya ya ce, ‘Aboki, yaya ka shigo nan ba tare da rigar aure ba?’ Mutumin ya rasa ta cewa.13. “Sai sarkin ya ce wa fadawa, ‘Ku daure shi hannu da ƙafa, ku jefar da shi waje, cikin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.’14. “Gama kirayayu da yawa, amma zaɓaɓɓu kaɗan ne zaɓaɓɓu.”15. Sai Farisiyawa suka yi waje, suka ƙulla yadda za su yi masa tarko cikin maganarsa.16. Suka aiki almajiransu tare da mutanen Hiridus wurinsa. Suka ce, “Malam, mun san kai mutum ne mai mutunci, kuma kana koyar da maganar Allah bisa gaskiya. Mutane ba sa ɗaukan hankalinka, domin ba ka kula ko su wane ne ba.17. To, ka gaya mana, a ra’ayinka? Ya dace a biya Kaisar haraji ko a’a?”18. Amma Yesu da yake ya san mugun nufinsu, sai ya ce, “Ku munafukai, don me kuke ƙoƙarin sa mini tarko?19. Ku nuna mini kuɗin da ake biyan haraji da shi.” Sai suka kawo masa dinari,20. sai ya tambaye su ya ce, “Hoton wane ne wannan? Kuma rubutun wane ne?”21. Suka amsa, “Na Kaisar ne.” Sai ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.”22. Da suka ji haka, sai suka yi mamaki. Saboda haka suka ƙyale shi, suka yi tafiyarsu. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.