Baibul a cikin shekara guda Fabrairu 9Fitowa 29:1-461. “Ga abin da za ka yi don ka keɓe su, don su yi mini hidima a matsayin firistoci. Ka ɗauki ɗan bijimi da raguna biyu marasa lahani.2. Daga garin alkama mai laushi marar yisti kuwa, ka yi burodi, da wainan da aka kwaɓa da mai, da ƙosai waɗanda an barbaɗa mai a kai.3. Ka sa waɗannan a cikin kwando. Sa’an nan ka miƙa su tare da ɗan bijimin da ragunan nan biyu.4. Bayan haka sai ka kawo Haruna da ’ya’yansa a ƙofar Tentin Sujada ka yi musu wanka.5. Ka ɗauki rigar ka sa wa Haruna, ka sa masa doguwar rigar, da rigar efod, da efod kanta, da ƙyallen maƙalawa a ƙirji. Ka ɗaura masa efod da ɗamarar da aka yi mata ado.6. Ka naɗa masa rawani a kai, ka kuma sa kambi mai tsarki a bisa rawanin.7. Ka ɗauki man shafewa ka shafe shi, ta wurin zuba man a kansa.8. Ka kawo ’ya’yansa, ka sa musu taguwoyi,9. ka kuma sa musu huluna a kansu. Sa’an nan ka ɗaura wa Haruna da ’ya’yansa abin ɗamara. Su kuwa da zuriyarsu, aikin firist kuwa zai zama nasu ta wurin dawwammamiyar farilla. “Ta haka za ka keɓe Haruna da ’ya’yansa maza.10. “Ka kuma kawo bijimin a gaban Tentin Sujada, sai Haruna da ’ya’yansa su ɗora hannuwansu a kansa.11. Ka yanka shi a gaban Ubangiji a ƙofar Tentin Sujada.12. Ka ɗibi jinin bijimin ka zuba a kan ƙahoni na bagade da yatsanka, sauran jinin kuwa ka zuba a gindin bagaden.13. Sa’an nan ka ɗauki dukan kitsen da ya rufe kayan ciki, da kitsen da yake manne da hanta, da ƙoda biyu da kuma kintsen da yake a kansu, ka ƙone su a kan bagade.14. Amma ka ƙone naman bijimin, da fatarsa, da kayan cikin, a bayan sansani. Hadaya ce ta zunubi.15. “Ka ɗauki ɗaya daga cikin ragunan, Haruna kuwa da ’ya’yan maza za su ɗora hannuwansa a kansa.16. Ka yanka ragon, ka ɗibi jinin, ka yayyafa shi kewaye da gefen bagaden.17. Ka yayyanka rago gunduwa-gunduwa, ka wanke kayan cikin, da ƙafafun, da kan, ka haɗa su da gunduwoyin.18. Sa’an nan ka ƙone ragon ɗungum a kan bagade. Hadaya ta ƙonawa ce ga Ubangiji, mai daɗin ƙanshi, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.19. “Ka ɗauki ɗayan ragon, sai Haruna da ’ya’yansa maza su ɗora hannuwansu a kansa.20. Ka yanka ragon, ka ɗibi jinin, ka shafa a bisa leɓen kunnen Haruna na dama, da bisa leɓen kunnuwan ’ya’yansa maza na dama, da kan manyan yatsotsin hannuwansu na dama, da kuma a kan manyan yatsotsin ƙafafunsu na dama. Sauran jinin kuwa, sai ka yayyafa shi kewaye da gefen bagaden.21. Ka ɗibi jinin da yake a kan bagade, da man shafewa, ka yafa a kan Haruna da rigunansa, da kuma a kan ’ya’yansa maza da rigunansu. Sa’an nan shi da ’ya’yansa maza da rigunansu za su tsarkake.22. “Ka ɗebi kitse daga wannan rago, ka yanke wutsiyarsa mai kitse, ka kuma ɗebi kitsen da ya rufe kayan ciki, da kitsen da yake bisa hanta, da ƙoda biyu da kitsen da yake kansu, da cinyar dama. (Gama rago ne don naɗi.)23. Daga kwandon burodi marar yisti, wanda yake gaban Ubangiji, ka ɗauki dunƙule ɗaya, da waina da aka yi da mai, da kuma ƙosai.24. Ka sa dukan waɗannan a hannun Haruna da ’ya’yansa maza, su kaɗa su a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa.25. Sa’an nan ka karɓe su daga hannuwansu, ka ƙone su a kan bagade tare da hadaya ta ƙonawa, domin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.26. Bayan haka, ka ɗauki ƙirjin ragon domin naɗin Haruna, ka kaɗa shi a gaban Ubangiji kamar hadaya ta kaɗawa. Wannan ƙirji zai zama rabonka.27. “Ka tsarkake ƙirji na hadaya ta kaɗawa, da cinya ta hadaya ta ɗagawa, waɗanda za a kaɗa a kuma ɗaga na ragon naɗin, wanda yake na Haruna da kuma na ’ya’yansa maza.28. Wannan zai zama rabon Haruna da ’ya’yansa maza daga Isra’ilawa. Gama wannan hadaya ta ɗagawa ce daga cikin hadayu na salama da Isra’ilawa za su miƙa wa Ubangiji.29. “Keɓaɓɓun tufafin nan na Haruna za su zama na zuriyarsa bayan mutuwarsa. Da tufafin nan ne za a zuba musu mai, a keɓe su.30. Ɗan da ya gāje shi a matsayin firist, shi ne zai sa su har kwana bakwai, lokacin da ya shiga Tentin Sujada, don yă yi aiki a Wuri Mai Tsarki.31. “Ka ɗauki ragon naɗi, ka dafa naman a tsattsarkan wuri.32. A ƙofar Tentin Sujada, Haruna da ’ya’yansa maza za su ci wannan rago da burodin da yake cikin kwandon.33. Za su ci abubuwan nan da aka yi kafara da su a lokacin tsarkakewarsu da keɓewarsu. Ba wanda zai ci, sai su kaɗai, gama abubuwan nan tsarkaka ne.34. In naman ragon naɗi ko wani burodin ya ragu har safiya, a ƙone shi, kada a ci gama tsarkake ne.35. “Ka yi wa Haruna da ’ya’yansa maza duk abin da na umarce ka, ka ɗauki kwana bakwai don naɗinsu.36. Ka miƙa bijimi ɗaya kowace rana domin hadaya don zunubi ta yin kafara. Ka tsarkake bagade ta wuri yin kafara dominsa, ka shafe shi da mai don ka tsarkake shi.37. Kwana bakwai za ka yi kafara saboda bagaden, ka kuma tsarkake shi. Sa’an nan bagaden zai zama mafi tsarki, kuma duk abin da ya taɓa bagaden zai tsarkaka.38. “Ga abin da za ka miƙa a bisa bagaden kowace rana. ’Yan raguna biyu masu shekara ɗaya-ɗaya.39. Ka miƙa ɗaya da safe, ɗaya kuma da yamma.40. Haɗe da ɗan rago na farkon, ka miƙa mudun gari mai laushi wanda an gauraye da kwalaba ɗaya na tataccen mai zaitun, da kwalaba ɗaya na ruwan inabi don hadaya ta sha.41. Ka miƙa ɗaya ragon da yamma, tare da hadaya ta gari da hadaya ta sha kamar aka yi ta safe, mai daɗin ƙanshi, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.42. “Wannan za tă zama hadaya ta ƙonawar da za a dinga yi kowace rana, daga tsara zuwa tsara. Za a yi ta miƙa hadayar a ƙofar Tentin Sujada a gaban Ubangiji. A can zan sadu da kai, in yi magana da kai;43. a can kuma zan sadu da Isra’ilawa, in kuma tsarkake wurin da ɗaukakata.44. “Ta haka zan tsarkake Tentin Sujada da bagaden, in kuma tsarkake Haruna da ’ya’yansa maza su yi mini hidima a matsayin firistoci.45. Sa’an nan zan zauna a cikin Isra’ilawa, in kuma zama Allahnsu.46. Za su san cewa ni ne Ubangiji Allahnsu, wanda ya fitar da su daga Masar saboda in zauna a cikinsu. Ni ne Ubangiji Allahnsu.Fitowa 30:1-381. “Ka yi bagade da itacen ƙirya don ƙona turare.2. Zai zama murabba’i, tsawon zai zama kamu ɗaya, fāɗi kuma kamu ɗaya, amma tsayin yă zama kamu biyu, ƙahoninsa kuma su zama ɗaya da shi.3. Ka dalaye bisansa da kuma dukan gefe-gefensa da kuma ƙahoninsa da zinariya zalla, ka kuma yi zubi na zinariya kewaye da shi.4. Ka yi zobai biyu na zinariya domin bagade a ƙarƙashin zubin, biyu a gefe da gefe su fuskanci juna, don su riƙe sandunan da ake amfani da su don ɗaukarsa.5. Ka yi sandunan nan da itacen ƙirya, ka dalaye su da zinariya.6. Ka sa bagaden a gaban labulen da yake gaban akwatin alkawari, a gaba murfin kafara wanda yake bisa akwatin alkawari, inda zan sadu da kai.7. “Haruna zai ƙone turare a bisa bagaden kowace safiya, sa’ad da yake shirya fitilu.8. Dole Haruna yă ƙone turare sa’ad da ya ƙuna fitilu da yamma, ta haka za a riƙa ƙona turare a gaban Ubangiji, daga tsara zuwa tsara.9. Ba za a ƙona wani irin turare dabam a bisa wannan bagade ba, ba kuma za a miƙa hadaya ta ƙonawa, ko ta hatsi, ko ta sha a bisansa ba.10. Sau ɗaya a shekara, Haruna zai yi kafara a bisa ƙahoninsa. Dole a yi wannan kafara ta shekara-shekara da jinin kafara ta hadaya don zunubi daga tsara zuwa tsara. Gama bagaden mafi tsarki ne ga Ubangiji.”11. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa,12. “Sa’ad da za ku ƙidaya Isra’ilawa, dole kowanne yă biya domin yă fanshe kansa ga Ubangiji a lokacin da aka ƙidaya shi. Ta haka babu wata annobar da za tă buge su sa’ad da kuke ƙidaya su.13. Kowannen da ya ƙetare zuwa wurin waɗanda aka riga aka ƙidaya, dole yă ba da rabin shekel, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, wanda nauyinsa garwa ashirin ne. Wannan rabin shekel hadaya ce ga Ubangiji.14. Duk waɗanda suka ƙetare, waɗanda shekarunsu ya kai ashirin ko fiye, za su ba da hadaya ga Ubangiji.15. Masu arziki ba za su bayar fiye da rabin shekel ba, talakawa kuma ba za su bayar ƙasa da haka ba, sa’ad da za ku yi hadaya ga Ubangiji don kafara rayukanku.16. Ku karɓi kuɗin kafara daga hannun Isra’ilawa, ku yi amfani da shi domin hidimar Tentin Sujada. Zai zama abin tunawa ga Isra’ilawa a gaban Ubangiji, don su yi kafarar rayukansu.”17. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa,18. “Ka yi daro na tagulla, ka yi masa ƙafafun da za a ajiye shi da tagulla don wanki. Ka ajiye shi tsakanin Tentin Sujada da bagade, ka zuba ruwa a ciki.19. Haruna da ’ya’yansa maza za su wanke hannuwansu da ƙafafunsu da ruwan da yake cikinsa.20. Duk lokacin da suka shiga Tentin Sujada, za su yi wanka, don kada su mutu. Duk lokacin da suka yi kusa da bagade don hidima ta miƙa hadayar da aka yi wa Ubangiji da wuta,21. za su wanke hannuwansu da ƙafafunsu, don kada su mutu. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla domin Haruna da zuriyarsa daga tsara zuwa tsara.”22. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa,23. “Ka ɗauki waɗannan kayan yaji masu kyau, shekel 500 na ruwan mur, rabin turaren sinnamon mai daɗin ƙanshi shekel 250, shekel 250 na turaren wuta mai ƙanshi,24. shekel 500 na kashiya, duk bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, da moɗa na man zaitun.25. Da waɗannan za ka yi man shafewa mai tsarki, yadda mai yin turare yake yi. Zai zama man shafewa mai tsarki.26. Sa’an nan ka yi amfani da shi don shafa wa Tentin Sujada, da akwatin alkawari,27. da tebur da kuma dukan kayansa, da wurin ajiye fitila da dukan kayansa, da bagaden ƙona turare,28. bagaden hadaya ta ƙonawa da dukan kayansa, da daro da mazauninsa.29. Za ka tsarkake su don su zama mafi tsarki, kuma duk abin da ya taɓa su, zai zama mai tsarki.30. “Ka shafe Haruna da ’ya’yansa maza, ka kuma tsarkake su don su yi mini hidima a matsayin firistoci.31. Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Wannan mai, zai zama mai tsarki ne a gare ni don shafewa, daga tsara zuwa tsara.32. Kada a zuba a jikunan mutane, kada kuma a yi wani mai irinsa. Wannan mai, mai tsarki ne, za ku kuma ɗauke shi a matsayi mai tsarki.33. Duk wanda ya yi irin wannan mai, duk wanda kuma ya shafa shi a kan wani wanda yake ba firist ba, za a ware shi daga mutanensa.’ ”34. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ɗauki kayan yaji mai ƙanshi, resin na gum, da onika, da galbanum, da kuma zallan lubban, duk nauyinsu yă zama daidai.35. Ka yi turare mai ƙanshi yadda mai yin turare yake yi. A sa masa gishiri, yă zama tsabtatacce, tsarkakakke.36. Ka ɗiba kaɗan daga ciki, ka niƙa, ka ajiye a gaban akwatin alkawari a cikin Tentin Sujada, inda zan sadu da kai. Zai zama mafi tsarki a gare ku.37. Kada ku yi wani turare irinsa wa kanku; ku ɗauke shi a matsayi mai tsarki ga Ubangiji.38. Duk wanda ya yi irinsa don jin daɗin ƙanshinsa, dole a ware shi daga mutanensa.”Zabura 20:6-96. Yanzu na san cewa, Ubangiji yakan cece shafaffensa. Yakan amsa masa daga samansa mai tsarki da ikon ceto na hannun damansa.7. Waɗansu sun dogara a kekunan yaƙi waɗansu kuma a dawakai, amma mu, mun dogara a cikin sunan Ubangiji Allahnmu.8. Za a durƙusar da su, su kuma fāɗi, amma mu za mu tashi mu tsaya daram.9. Ya Ubangiji, ka ba da nasara ga sarki! Ka amsa mana sa’ad da muka yi kira!Karin Magana 6:6-236. Ku tafi wurin kyashi, ku ragwaye; ku lura da hanyoyinsa ku zama masu hikima!7. Ba shi da jagora ba shugaba ko mai mulki,8. duk da haka yakan yi tanade-tanadensa da rani ya kuma tattara abincinsa a lokacin girbi.9. Har yaushe za ku kwanta a can, ku ragwaye? Yaushe za ku farka daga barcinku?10. Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi, ɗan naɗin hannuwa don a huta,11. talauci kuwa zai zo kamar ’yan hari rashi kuma kamar ɗan fashi.12. Sakare da mutumin banza wanda yana yawo da magana banza a baki,13. wanda yake ƙyifce da ido, yana yi alama da ƙafafunsa yana kuma nuni da yatsotsinsa,14. wanda yake ƙulla mugunta da ruɗu a cikin zuciyarsa, kullum yana tā-da-na-zaune-tsaye15. Saboda haka masifa za tă fāɗa farat ɗaya; za a hallaka shi nan da nan, ba makawa.16. Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi, abubuwa bakwai da suke abin ƙyama gare shi,17. duban reni, harshe mai ƙarya, hannuwa masu zub da jinin marar laifi,18. zuciyar da take ƙulla mugayen dabaru, ƙafafun da suke sauri zuwa aikata mugunta,19. mai shaidar ƙarya wanda yake zuba ƙarairayi, da kuma mutumin da yake tā-da-na-zaune-tsaye a cikin ’yan’uwa.20. Ɗana, ka kiyaye umarnan mahaifinka kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.21. Ka ɗaura su a zuciyarka har abada; ka ɗaura su kewaye da wuyanka.22. Sa’ad da kake tafiya, za su bishe ka; sa’ad da kake barci, za su lura da kai; sa’ad da ka farka, za su yi maka magana.23. Gama waɗannan umarnai fitila ne, wannan koyarwa haske ne, kuma gyare-gyaren horo hanyar rayuwa ce,Mattiyu 25:1-301. “A lokacin mulkin sama zai zama kamar budurwai goma waɗanda suka ɗauki fitilunsu suka fita don su taryi ango.2. Biyar daga cikinsu wawaye ne, biyar kuma masu hikima.3. Wawayen sun ɗauki fitilunsu, sai dai ba su riƙe mai ba.4. Masu hikimar kuwa suka riƙo tulunan mai da fitilunsu.5. Ango ya yi jinkirin zuwa, sai duk suka shiga gyangyaɗi har barci ya kwashe su.6. “Can tsakar dare, sai aka ji kira, ana cewa, ‘Ga ango nan! Ku fito, ku tarye shi!’7. “Sai dukan budurwan nan suka farka suka kuna fitilunsu.8. Sai wawayen suka ce wa masu hikimar, ‘Ku ɗan sassam mana manku; fitilunmu suna mutuwa.’9. “Su kuwa suka amsa, suka ce, ‘A’a, wataƙila ba zai ishe mu da ku ba. Gara ku je wurin masu sayarwa ku sayo.’10. “Amma yayinda suke kan tafiya garin sayen mai, sai ango ya iso. Budurwai da suke a shirye, suka shiga wajen bikin auren tare da shi. Aka kuma kulle ƙofa.11. “An jima can, sai ga sauran sun iso. Suka ce, ‘Ranka yă daɗe! Ranka yă daɗe! Ka buɗe mana ƙofa!’12. “Amma ya amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, ban san ku ba.’13. “Saboda haka sai ku zauna a faɗake, don ba ku san ranar ko sa’ar ba.14. “Har wa yau, za a kwatanta shi da mutumin da zai yi tafiya, wanda ya kira bayinsa ya kuma danƙa musu mallakarsa.15. Ga guda, ya ba shi talenti biyar na kuɗi, ga wani talenti biyu, ga wani kuma talenti ɗaya, kowa bisa ga azancinsa. Sa’an nan ya yi tafiyarsa.16. Mutumin da ya karɓi talenti biyar, nan da nan ya tafi ya yi kasuwanci da su har ya sami ribar talenti biyar.17. Haka ma, wannan mai talenti biyu, shi ma ya yi riba biyu.18. Amma mutumin da ya karɓi talenti ɗaya ɗin, ya tafi, ya tona rami, ya ɓoye kuɗin maigidansa.19. “Bayan an daɗe, sai maigidan bayin nan ya dawo, ya kuma daidaita lissafi da su.20. Mutumin da ya karɓi talenti biyar, ya kawo ƙarin talenti biyar. Ya ce, ‘Maigida, ka danƙa mini talenti biyar. Ga shi, na yi ribar biyar.’21. “Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’22. “Mutumin da yake da talenti biyu, shi ma ya zo ya ce, ‘Maigida, ka danƙa mini talenti biyu; ga shi, na yi ribar biyu.’23. “Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’24. “Sa’an nan mutumin da ya karɓi talenti ɗaya ya zo. Ya ce, ‘Maigida, na san cewa kai mutum ne mai wuyan sha’ani, kana girbi inda ba ka shuka ba, kana kuma tara inda ba ka yafa iri ba.25. Saboda haka na ji tsoro, na je na ɓoye talentinka a ƙasa. Ga abinka.’26. “Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Kai mugun bawa, mai ƙyuya! Ashe, ka san cewa ina girbi inda ban yi shuka ba, ina kuma tarawa inda ban yafa iri ba?27. To, in haka ne, ai, da ka sa kuɗina a banki, don sa’ad da na dawo da na karɓi abina da riba.28. “ ‘Karɓi talentin daga hannunsa ku ba wanda yake da talenti goma.29. Gama duk mai abu za a ƙara masa, zai kuma same shi a yawalce. Duk wanda ba shi da shi kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa.30. Ku jefar da banzan bawan nan waje, cikin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.’ Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.