Baibul a cikin shekara guda Maris 17Ƙidaya 31:1-541. Ubangiji ya ce wa Musa,2. “Ka ɗaukar wa Isra’ilawa fansa, a kan Midiyawa. Bayan wannan za ka mutu, a kuwa tara ka ga mutanenka.”3. Saboda haka Musa ya ce wa mutane, “Ku shirya waɗansu daga cikin mazanku, su tafi su yi yaƙi da Midiyawa don su ɗaukar wa Ubangiji fansa a kansu.”4. Ku aiki maza dubu ɗaya daga kowace kabilar Isra’ila.5. Saboda haka aka samo mayaƙa dubu goma sha biyu shiryayyu don yaƙi, maza dubu ɗaya daga kowace kabilar Isra’ila.6. Musa ya aike su zuwa yaƙi, dubu ɗaya daga kowace kabila, tare da Finehas ɗan Eleyazar, firist, wanda ya ɗauki kayayyaki daga wuri mai tsarki da ƙahoni don kiran yaƙi.7. Suka yi yaƙi da Midiyawa, suka kashe kowane mutum yadda Ubangiji ya umarci Musa.8. A cikin waɗanda aka kashe kuwa akwai Ewi, Rekem, Zur, Hur da Reba; sarakuna biyar na Mediyawa. Suka kuma kashe Bala’am ɗan Beyor da takobi.9. Isra’ilawa suka kwashe mata da yaran Midiyawa, a matsayin bayi. Suka kwashe shanunsu da tumakinsu da kuma dukan dukiyarsu, a matsayin ganima.10. Suka ƙone dukan garuruwan da Midiyawa suke zama, da dukan sansaninsu.11. Suka kwashe dukan ganima haɗe da mutane da dabbobi,12. suka kawo bayi da ganiman nan, wurin Musa da Eleyazar firist, da kuma jama’ar Isra’ilawa, a sansaninsu a filayen Mowab kusa da Urdun daga ƙetaren Yeriko.13. Musa, da Eleyazar firist da dukan shugabannin jama’a, suka fito suka tarye su a bayan sansani.14. Musa kuwa ya husata da shugabannin sojojin da suke shugabannin dubbai da shugabannin ɗari-ɗarin da suka dawo daga yaƙi.15. Ya tambaye su ya ce, “Kun bar dukan mata da rai?16. Su ne waɗanda suka bi shawarar Bala’am suka kuma zama sanadin sa Isra’ilawa suka juya wa Ubangiji baya, har ya kawo abin da ya faru da Feyor, har annoba ya kashe dukan mutanen Ubangiji.17. Yanzu ku kashe dukan yara maza, ku kuma kashe kowace macen da ta yi lalata da namiji,18. amma ku bar kowace yarinyar da ba tă taɓa yin lalata da namiji ba.19. “Dukanku da kuka kashe mutum, ko kuka taɓa wani da aka kashe, dole ku kasance a bayan sansani har kwana bakwai. A rana ta uku da rana ta bakwai dole ku tsabtacce kanku da kuma bayinku.20. Ku tsarkake kowace taguwa da kuma kome da aka yi da fata, da gashin akuya, ko kuwa itace.”21. Sa’an nan Eleyazar firist, ya ce wa sojojin da suka je yaƙi, “Wannan ita ce ƙa’idar da Ubangiji ya ba wa Musa.22. Zinariya, azurfa, tagulla, baƙin ƙarfe, kuza, darma23. da dukan abin da wuta ba ta iya ci, dole yă shiga wuta sa’an nan zai zama da tsabta. Amma dole a kuma tsarkake ta da ruwan tsarkakewa. Duk abin da wuta za tă iya ci, dole a shigar da ita a ruwan tsarkakewa.24. A rana ta bakwai za ku wanke tufafinku, sa’an nan za ku tsarkaka, bayan haka ku shigo sansani.”25. Ubangiji ya yi magana da Musa ya ce,26. “Da kai da Eleyazar firist, da shugabannin jama’a, ku ƙidaya dukan mutane da dabbobin da aka ci da yaƙi.27. Ku kasa ganimar kashi biyu, ku ba sojojin da suka tafi yaƙi kashi ɗaya, kashi ɗaya kuma ku ba wa jama’a.28. Daga sojojin da suka je yaƙin kuwa, ka ware ganima wa Ubangiji, ka ɗauki ɗaya daga cikin mutum ɗari biyar, da shanu ɗari biyar, da jakuna ɗari biyar, da tumaki ɗari biyar.29. Ka ɗauki wannan sashe daga rabin rabonsu ka ba wa Eleyazar firist, a matsayin sashe na Ubangiji.30. Daga cikin rabin rabon Isra’ilawa, ka zaɓi ɗaya daga kowane hamsin na mutane, shanu, jakuna, tumaki, awaki ko kuma sauran dabbobi. Ka ba wa Lawiyawan da suke lura da tabanakul na Ubangiji.”31. Saboda haka Musa da Eleyazar suka aikata yadda Ubangiji ya umarci Musa.32. Yawan ganimar da sojoji suka kawo ita ce tumaki 675,00033. shanu 72,00034. da jakuna 61,000.35. Akwai kuma mata 32,000 da ba su yi lalata ba da namiji ba.36. Kashin da aka ba sojoji waɗanda suka tafi yaƙi shi ne, tumaki 337,500,37. tumakin da aka ware wa Ubangiji kuwa 657 ne;38. shanu 36,000, shanun da aka ware wa Ubangiji kuwa 72 ne;39. jakuna 30,500, jakunan da aka ware wa Ubangiji kuwa 61 ne;40. mutane 16,000, mutanen da aka ware wa Ubangiji kuwa 32 ne.41. Musa ya ba wa Eleyazar abin da aka ware wa Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.42. Kashin da aka ba wa Isra’ilawa, wanda Musa ya ware daga cikin na waɗanda suka tafi yaƙi,43. kashin da aka ba wa jama’a kuwa tumaki 337,500 ne,44. shanu 36,000,45. jakuna 30,50046. da mutane 16,000.47. Daga rabin kashi na Isra’ilawa, Musa ya ɗauki ɗaya daga cikin hamsin na mutane da na dabbobi, yadda Ubangiji ya umarce shi, ya ba wa Lawiyawan da suke lura da tabanakul na Ubangiji.48. Sai shugabannin da suka shugabancin rundunar yaƙin, shugabanni na dubu-dubu da shugabanni na ɗari-ɗari, suka zo wurin Musa49. suka ce masa, “Barorinka sun ƙidaya mayaƙan da suke ƙarƙashinmu, babu ko ɗayan ya ɓace.50. Saboda haka mun kawo wa Ubangiji hadaya na kayan zinariya da kowannenmu ya samu, mundaye, ƙawane, ’yan kunne da duwatsun wuya, don yin wa kanmu kafara a gaban Ubangiji.”51. Musa da Eleyazar firist, suka karɓi zinariya da kayan adon duka daga gare su.52. Dukan zinariya da shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, waɗanda Musa da Eleyazar suka karɓa, suka kuma miƙa hadaya ga Ubangiji, nauyinta ta kai shekel 16,750.53. Kowane soja, ya kwashi ganima wa kansa.54. Musa da Eleyazar firist, suka karɓi zinariya daga shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, suka kawo cikin Tentin Sujada, don su zama abin tuni ga Isra’ilawa a gaban Ubangiji.Ƙidaya 32:1-421. Mutanen Ruben da mutanen Gad, da suke da garken shanu da kuma garke tumaki masu yawa, suka ga cewa ƙasashen Yazer da Gileyad wurare ne masu kyau don kiwon shanu da tumaki.2. Saboda haka suka zo wurin Musa da Eleyazar da kuma shugabannin jama’a, suka ce,3. “Atarot, Dibon, Yazer, Nimra, Heshbon, Eleyale, Sebam, Nebo da Beyon,4. ƙasar da Ubangiji ya ci da yaƙi a gaban mutane Isra’ila, suna da kyau don dabbobi, bayinku kuma suna da dabbobi.”5. Suka ce, “In mun sami tagomashi daga gare ka bari a ba da wannan ƙasa ga bayinka, tă zama mallakanmu. Kada ka sa mu haye Urdun.”6. Musa ya ce wa mutanen Gad da mutanen Ruben, “Wato, sai ’yan’uwanku su yi ta yaƙi ku kuwa ku zauna nan?7. Don me za ku karya zuciya Isra’ilawa daga hayewa zuwa ƙasar da Ubangiji ya ba su?8. Haka iyayenku suka yi sa’ad da na aike su daga Kadesh Barneya don su dubo ƙasar.9. Gama bayan suka haura Kwarin Eshkol suka hangi ƙasar, sai suka karya zuciyar Isra’ilawa daga shigar ƙasar da Ubangiji ya ba su.10. A ranar kuwa Ubangiji ya husata har ya yi wannan rantsuwa cewa,11. ‘Tabbatacce ba wani daga cikin mutanen da suka fito daga Masar, tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba, da zai ga ƙasar da na rantse zan ba Ibrahim, da Ishaku, da Yaƙub, domin ba su bi ni sosai ba,12. ba ko ɗaya sai dai Kaleb ɗan Yefunne Bakenizze da Yoshuwa ɗan Nun, don su ne kaɗai suka bi Ubangiji da zuciya ɗaya.’13. Ubangiji ya husata da Isra’ila har ya sa suka yi ta yawo a hamada shekara arba’in, sai da dukan tsaran da suka aikata wannan mugunta a gabansa, suka mutu.14. “Ga shi ku kuma, tarin masu zunubi, kuna tsaya a matsayin kakanninku, kuna sa Ubangiji yă sāke husata da Isra’ila.15. In kun juye daga binsa, zai sāke barin dukan wannan mutane a hamada, ku ne kuwa za ku zama sanadin hallakarsu.”16. Sai suka zo wurin Musa, suka ce, “Muna so mu gina katangar dutse don dabbobinmu, da kuma birane don matanmu da ’ya’yanmu a nan.17. Matanmu da ’ya’yanmu za su zauna a biranen da suke da katanga, don kāriya daga mazaunan ƙasar, amma mu, za mu ɗauki makamai mu tafi tare da sauran Isra’ilawa, har mu kai su wuraren zamansu.18. Ba za mu koma gidajenmu ba sai kowane mutumin Isra’ila ya sami gādonsa.19. Ba za mu ci gādo tare da su a wancan hayin Urdun ba, domin mun sami gādonmu a wannan hayin gabashin Urdun.”20. Sai Musa ya ce musu, “In za ku yi haka, in za ku sha ɗamara da makamai a gaban Ubangiji, ku tafi yaƙi,21. in kuma dukanku za ku yi ɗamara, ku ɗauki makaman yaƙi a hayin Urdun a gaban Ubangiji har lokacin da ya kori abokan gābansa daga gabansa,22. to, sa’ad da aka ci ƙasar a gaban Ubangiji, kwa kuɓuta daga alhakinku ga Ubangiji da kuma Isra’ila. Ƙasan nan kuwa za tă zama mallakarku a gaban Ubangiji.23. “Amma in ba ku yi haka ba, kun yi zunubi ke nan ga Ubangiji; kuma ku san cewa zunubinku zai tone ku.24. Ku gina birane domin matanku da ’ya’yanku, ku gina katanga kuma domin dabbobinku, amma fa ku cika abin da kuka yi alkawari.”25. Mutanen Gad da mutanen Ruben, suka ce wa Musa, “Mu bayinka za mu yi yadda ranka yă daɗe ya umarta.26. ’Ya’yanmu da matanmu, garkunan shanunmu da na tumakinmu, za su kasance a nan biranen Gileyad.27. Amma bayinka, kowane mutum a cikinmu zai haye a gaban Ubangiji, zuwa yaƙi kamar yadda ranka yă daɗe ya faɗa.”28. Sai Musa ya yi wa Eleyazar firist, da Yoshuwa ɗan Nun, da shugabannin gidajen kakannin kabilan mutanen Isra’ila kashedi a kansu,29. ya ce, “In kowane sojan mutanen Gad da na mutanen Ruben, ya ɗauki makaman yaƙi, ya haye Urdun tare da ku a gaban Ubangiji, to, sa’ad da a ci ƙasar a gabanku, ku ba da ƙasar Gileyad tă zama mallakarsu.30. Amma in ba su haye tare da ku da shirin yaƙi ba, to, sai ku ba su gādo a wancan haye kamar sauran kabilun a Kan’ana.”31. Mutanen Gad da mutanen Ruben suka amsa, suka ce, “Barorinka za su yi abin da Ubangiji ya faɗa.32. Za mu haye a gaban Ubangiji zuwa Kan’ana, amma mallakarmu ta gādo, za tă kasance a wannan hayi na Urdun.”33. Sai Musa ya ba wa mutanen Gad, mutanen Ruben, da rabin mutanen Manasse ɗan Yusuf, masarautar Sihon, sarkin Amoriyawa, da masarautar Og na Bashan, dukan ƙasar, tare da biranenta da kuma yankunan da suke kewaye.34. Mutanen Gad suka gina Dibon, Atarot, Arower,35. Atrot Shofan, Yazer, Yogbeha,36. Bet-Nimra, da Bet-Haran a matsayin birane masu katanga, suka kuma gina katanga don dabbobinsu.37. Mutanen Ruben suka sāke gina Heshbon, Eleyale, da Kiriyatayim,38. haka kuma suka gina Nebo da Ba’al-Meyon (an canja waɗannan sunaye) suka kuma gina Sibma. Suka ba wa biranen da suka sāke ginawa sunaye.39. Zuriyar Makir ɗan Manasse suka tafi Gileyad, suka ci ta da yaƙi, suka kori mutanen Amoriyawa da suke can.40. Saboda haka Musa ya ba da Gileyad ga mutanen Makir, zuriyar Manasse, suka kuma zauna a can.41. Yayir, wani ɗan Manasse, ya ci ƙauyukansu da yaƙi, ya kuma ba su sunan Hawwot Yayir.42. Noba kuma ya ci Kenat da ƙauyukanta da yaƙi, ya kuma ba ta suna Noba, bisa ga sunansa.Zabura 35:1-81. Yi hamayya, ya Ubangiji, da waɗanda suke hamayya da ni; yi faɗa da waɗanda suke faɗa da ni.2. Ka ɗauki garkuwa da kuma makami; ka tashi ka taimake ni.3. Ka ɗaga māshi da kuma abin da ake jefa a kan waɗanda suke fafarata. Ka ce wa raina, “Ni ne cetonka.”4. Bari waɗanda suke neman raina su sha kunya a kuma kunyatar da su; bari waɗanda suke shirya lalacewata su juya da baya su ruɗe.5. Bari su zama kamar yayi a gaban iska, mala’ikan Ubangiji kuma yana korarsu;6. bari hanyarsu tă yi duhu ta kuma yi santsi, mala’ikan Ubangiji kuma yana fafararsu.7. Da yake sun ɓoye tarko domina ba dalili kuma babu dalili suka haƙa mini rami,8. bari lalaci yă kama su ba zato, bari tarkon da suka ɓoye yă kama su, bari su fāɗa cikin ramin, yă kai ga lalacinsu.Karin Magana 12:1-11. Duk mai ƙaunar horo yana ƙaunar sani, amma duk mai ƙin gyara wawa ne.Markus 14:55-7255. Manyan firistoci da dukan ’yan Majalisa, suka shiga neman shaidar laifin da za a tabbatar a kan Yesu, domin su kashe shi. Amma ba su sami ko ɗaya ba.56. Da yawa suka ba da shaidar ƙarya a kansa, amma shaidarsu ba tă zo ɗaya ba.57. Sai waɗansu suka miƙe tsaye, suka ba da wannan shaida ƙarya a kansa, suka ce,58. “Mun ji shi ya ce, ‘Zan rushe wannan haikali da mutum ya gina, cikin kwana uku, in sāke gina wani wanda ba ginin mutum ba.’ ”59. Duk da haka ma, shaidarsu ba tă zo ɗaya ba.60. Sai babban firist ya tashi a gabansu, ya tambayi Yesu ya ce, “Ba za ka amsa ba? Wane shaida ke nan waɗannan mutane suke kawowa a kanka?”61. Amma Yesu ya yi shiru, bai kuwa amsa ba. Babban firist ya sāke tambayarsa ya ce, “Kai ne Kiristi, Ɗan Mai Albarka?”62. Yesu ya ce, “Ni ne. Za ku kuwa ga Ɗan Mutum yana zaune a hannun dama na Mai Iko, yana kuma zuwa a cikin gizagizan sama.”63. Babban firist ya yage tufafinsa, ya yi ce, “Ina dalilin neman waɗansu shaidu kuma?64. Kun dai ji saɓon. Me kuka gani?” Duka suka yanke masa hukuncin kisa.65. Sai waɗansu suka fara tattofa masa miyau, suka rufe masa idanu, suka bubbuge shi da hannuwansu, suka ce, “Yi annabci!” Masu gadin kuma suka ɗauke shi, suka yi masa duka.66. Yayinda Bitrus yake ƙasa a filin gidan, sai wata yarinya, baiwa, ɗaya daga cikin ma’aikatan babban firist, ta zo can.67. Da ta ga Bitrus yana jin ɗumi, sai ta dube shi da kyau. Ta ce, “Kai ma kana tare da Yesu, Banazare.”68. Amma ya yi mūsu ya ce, “Ban san abin da kike magana ba, balle ma in fahimce ki.” Sai ya fita zuwa zaure.69. Da baiwar ta gan shi a can, sai ta sāke gaya wa waɗanda suke tsattsaye a wurin, ta ce, “Wannan mutum yana ɗaya daga cikinsu.”70. Sai ya sāke yin musu. Bayan ɗan lokaci kaɗan, sai waɗanda suke tsattsaye kusa suka ce wa Bitrus, “Lalle, kana ɗaya daga cikinsu, gama kai mutumin Galili ne.”71. Sai ya fara la’antar kansa, yana rantsuwa musu, yana cewa, “Ban san wannan mutumin da kuke magana a kai ba.”72. Nan da nan zakara ya yi cara sau na biyu. Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi masa cewa, “Kafin zakara yă yi cara sau biyu, za ka yi mūsun sanina sau uku.” Sai ya fashe da kuka. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.