Baibul a cikin shekara guda Maris 18Ƙidaya 33:1-561. Ga wuraren da Isra’ilawa suka yi sansani sa’ad da suka fito runduna-runduna a ƙarƙashin Musa da Haruna daga Masar.2. Bisa ga umarnin Ubangiji, Musa ya rubuta wuraren tafiye-tafiyensu da sansaninsu. Ga yadda tafiye-tafiyen suka kasance.3. Isra’ilawa sun tashi daga Rameses a rana ta goma sha biyar, ga watan fari, kashegarin Bikin Ƙetarewa. Suka fita gabagadi a gaban dukan Masarawa,4. waɗanda suke binne gawawwakin ’ya’yan farinsu da Ubangiji ya karkashe; gama Ubangiji ya hukunta allolinsu.5. Isra’ilawa suka tashi daga Rameses, suka yi sansani a Sukkot.6. Suka tashi daga Sukkot, suka yi sansani a Etam, a gefen hamada.7. Suka tashi daga Etam, suka koma baya zuwa Fi Hahirot, wajen gabashin Ba’al-Zafon, suka yi sansani kusa da Migdol.8. Suka tashi daga Fi Hahirot, suka ratsa cikin teku zuwa hamada, bayan sun yi tafiya kwana uku a cikin Hamadan Etam, sai suka yi sansani a Mara.9. Suka tashi daga Mara, suka tafi Elim, inda akwai maɓulɓulan ruwa goma sha biyu, da itatuwan dabino guda saba’in, suka yi sansani a can.10. Suka tashi daga Elim, suka yi sansani kusa da Jan Teku.11. Suka tashi daga Jan Teku, suka yi sansani a Hamadan Sin.12. Suka tashi daga Hamadan Sin, suka yi sansani a Dofka.13. Suka tashi daga Dofka, suka yi sansani a Alush.14. Suka tashi daga Alush, suka yi sansani a Refidim, inda babu ruwan da mutane za su sha.15. Suka tashi daga Refidim, suka yi sansani a Hamadan Sinai.16. Suka tashi daga Hamadan Sinai, suka yi sansani a Kibrot Hatta’awa.17. Suka tashi daga Kibrot Hatta’awa, suka yi sansani a Hazerot.18. Suka tashi daga Hazerot, suka yi sansani a Ritma.19. Suka tashi daga Ritma, suka yi sansani a Rimmon Ferez.20. Suka tashi daga Rimmon Ferez, suka yi sansani a Libna.21. Suka tashi daga Libna, suka yi sansani a Rissa.22. Suka tashi daga Rissa, suka yi sansani a Kehelata.23. Suka tashi daga Kehelata, suka yi sansani a Dutsen Shefer.24. Suka tashi daga Dutsen Shefer, suka yi sansani a Harada.25. Suka tashi daga Harada, suka yi sansani a Makhelot.26. Suka tashi daga Makhelot, suka yi sansani a Tahat.27. Suka tashi daga Tahat, suka yi sansani a Tera.28. Suka tashi daga Tera, suka yi sansani a Mitka.29. Suka tashi daga Mitka, suka yi sansani a Hashmona.30. Suka tashi daga Hashmona, suka yi sansani a Moserot.31. Suka tashi daga Moserot, suka yi sansani a Bene Ya’akan.32. Suka tashi daga Bene Ya’akan, suka yi sansani a Hor Haggidgad.33. Suka tashi daga Hor Haggidgad, suka yi sansani a Yotbata.34. Suka tashi daga Yotbata, suka yi sansani a Abrona.35. Suka tashi daga Abrona, suka yi sansani a Eziyon Geber.36. Suka tashi daga Eziyon Geber, suka yi sansani a Kadesh, cikin Hamadan Zin.37. Suka tashi daga Kadesh, suka yi sansani a Dutsen Hor, a iyakar Edom.38. Bisa ga umarni Ubangiji, Haruna firist, ya hau Dutsen Hor, inda ya mutu a rana ta fari ga watan biyar, a shekara ta arba’in, bayan Isra’ilawa suka fito daga Masar.39. Haruna yana da shekara ɗari da ashirin da uku, sa’ad da ya mutu a Dutsen Hor.40. Sarki Arad Bakan’ane, wanda yake zaune a Negeb na Kan’ana, ya ji labari cewa Isra’ilawa suna zuwa.41. Suka tashi daga Dutsen Hor, suka yi sansani a Zalmona.42. Suka tashi daga Zalmona, suka yi sansani a Funon.43. Suka tashi daga Funon, suka yi sansani a Obot.44. Suka tashi daga Obot, suka yi sansani a Iye Abarim, a iyakar Mowab.45. Suka tashi daga Iyim, suka yi sansani a Dibon Gad.46. Suka tashi daga Dibon Gad, suka yi sansani a Almon Dibilatayim.47. Suka tashi daga Almon Dibilatayim, suka yi sansani a duwatsun Abarim, kusa da Nebo.48. Suka tashi daga duwatsun Abarim, suka yi sansani a filayen Mowab kusa da Urdun, ɗaura da Yeriko.49. A can filayen Mowab, suka yi sansani kusa da Urdun ɗaura da Bet-Yeshimot har zuwa Abel-Shittim.50. A filayen Mowab kusa da Urdun ɗaura da Yeriko ne Ubangiji ya ce wa Musa,51. “Ka gaya wa Isra’ilawa cewa, ‘Sa’ad da kuka haye Urdun zuwa Kan’ana,52. ku kori dukan mazaunan ƙasar a gabanku. Ku rurrushe sassaƙaƙƙun duwatsu, da siffofinsu na zubi, ku kuma rurrushe dukan masujadansu na kan tudu.53. Ku mallaki ƙasar, ku kuma zauna a ciki, gama na ba ku ƙasar, ku mallake ta.54. Ku rarraba ƙasar ta wurin jefan ƙuri’a, bisa ga kabilanku. Kabilar da take babba, a ba ta babban gādo, ƙarami kabila kuwa, a ba ta ƙaramin gādo. Duk abin da ƙuri’a ta ba su, shi zai zama nasu. Ku rarraba wannan bisa zuriyar kakanninku.55. “ ‘Amma in ba ku kori mazaunan ƙasar ba, waɗanda kuka bari su ci gaba da zama, za su zama muku hakki a idanunku, da kuma ƙayayyuwa a bayanku. Za su ba ku wahala a ƙasar da kuke zama.56. Sa’an nan kuwa zan yi muku abin da na shirya yin musu.’ ”Ƙidaya 34:1-291. Ubangiji ya ce wa Musa,2. “Ka umarci Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka shiga Kan’ana, ƙasar da aka ba ku gādo za tă kasance da waɗannan iyakoki.3. “ ‘Gefenku na kudu zai haɗa da wani sashin Hamadan Zin ta iyakar Edom. A gabas, iyakarku ta kudu za tă fara daga ƙarshen Tekun Gishiri,4. tă ƙetare Mashigin Kunama a kudu, tă ci gaba zuwa Zin, sa’an nan tă nufi kudu da Kadesh Barneya. Sa’an nan za tă zarce zuwa Hazar Addar, tă nausa zuwa Azmon,5. inda za tă juya tă haɗu da Rafin Masar, tă kuma ƙarasa a Bahar Rum.6. “ ‘Iyakarku a yammanci, za tă kasance bakin Bahar Rum. Wannan ce za tă zama iyakarku a yamma.7. “ ‘Iyakarku a arewanci kuwa za tă tashi daga Bahar Rum zuwa Dutsen Hor,8. za tă kuma tashi daga Dutsen Hor, zuwa Lebo Hamat. Sa’an nan tă miƙe zuwa Zedad,9. tă ci gaba zuwa Zifron, sa’an nan tă ƙarasa a Hazar-Enan. Wannan ce za tă zama iyakarku a arewa.10. “ ‘Iyakarku a gabashi, za tă tashi daga Hazar-Enan zuwa Shefam.11. Iyakar za tă gangara daga Shefam zuwa Ribla a gefen gabashin Ayin, sa’an nan tă ci gaba a gangaren gabashin Tekun Kinneret.12. Sa’an nan tă gangara ta Urdun, tă ƙarasa a Tekun Gishiri. “ ‘Wannan za tă zama ƙasarku, tare da iyakokinta a kowane gefe.’ ”13. Sai Musa ya umarci Isra’ilawa ya ce, “Ku raba wannan ƙasa da za ku gāda ta hanyar jefa ƙuri’a. Ubangiji ya umarta cewa a ba da ita ga kabilu tara da rabi,14. saboda iyalan kabilar Ruben, kabilar Gad da rabin kabilar Manasse sun riga sun sami gādonsu.15. Waɗannan kabilu biyu da rabi, sun sami gādonsu a wancan hayin Urdun a gabashin Yeriko wajen fitowar rana.”16. Ubangiji ya ce wa Musa,17. “Waɗannan su ne sunayen mutanen da za su raba muku ƙasar gādo. Eleyazar firist, da Yoshuwa ɗan Nun.18. Ka kuma naɗa shugaba guda ɗaya daga kowace kabila domin yă taimaka a rabon ƙasar.19. “Ga sunayensu. “Kaleb ɗan Yefunne, daga kabilar Yahuda;20. Shemuyel ɗan Ammihud, daga kabilar Simeyon21. Elidad ɗan Kislon, daga kabilar Benyamin;22. Bukki ɗan Yogli, shugaba daga kabilar Dan;23. Hanniyel ɗan Efod, shugaba daga kabilar Manasse ɗan Yusuf;24. Kemuwel ɗan Shiftan, shugaba daga kabilar Efraim ɗan Yusuf;25. Elizafan ɗan Farnak, shugaba daga kabilar Zebulun;26. Faltiyel ɗan Azzan, shugaba daga kabilar Issakar;27. Ahihud ɗan Shelomi, shugaba daga kabilar Asher;28. Fedahel ɗan Ammihud, shugaba daga kabilar Naftali.”29. Waɗannan su ne mutanen da Ubangiji ya umarta su raba gādo ga Isra’ilawa a ƙasar Kan’ana.Zabura 35:9-169. Sa’an nan raina zai cika da farin ciki a cikin Ubangiji in yi kuma murna a cikin cetonsa.10. Dukan raina zai ce, “Wane ne kamar ka, ya Ubangiji? Ka kuɓutar da matalauta daga waɗanda suka fi ƙarfinsu, matalauta da masu bukata daga waɗanda suke musu fashi.”11. Shaidu marasa imani sun fito; suna mini tambaya a kan abubuwan da ban san kome a kai ba.12. Suna sāka alherin da na yi musu da mugunta suka bar raina da nadama.13. Duk da haka sa’ad da suke ciwo, na sanya rigar makoki na ƙasƙantar da kaina da azumi. Sa’ad da aka mayar mini da addu’o’i babu amsa,14. nakan yi ta yawo ina makoki sai ka ce yadda nake yi wa abokina ko ɗan’uwana. Nakan sunkuyar da kaina cikin baƙin ciki sai ka ce ina kuka domin mahaifiyata.15. Amma sa’ad da na yi tuntuɓe, sukan taru suna murna; masu kai hari sun taru a kaina sa’ad da ban sani ba. Suna ɓata mini suna ba tsagaitawa.16. Kamar marasa sani Allah suna mini riyar ba’a; Suna hararata da ƙiyayya.Karin Magana 12:2-22. Mutumin kirki kan sami tagomashi daga Ubangiji, amma Ubangiji yakan hukunta mai son yin wayo.Markus 15:1-241. Da sassafe, sai manyan firistoci da dattawa, da malaman dokoki, da dukan Majalisa, suka yanke shawara. Suka daure Yesu, suka kai shi, suka miƙa shi ga Bilatus.2. Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa ya ce, “I, haka yake, kamar yadda ka faɗa.”3. Manyan firistoci suka zarge shi a kan abubuwa da yawa.4. Don haka Bilatus ya sāke tambayarsa ya ce, “Ba za ka amsa ba? Dubi abubuwa da yawa da suke zarginka da su.”5. Amma har yanzu, Yesu bai ba da amsa ba, Bilatus ya yi mamaki.6. Yanzu fa, al’ada ce a lokacin Bikin, a saki ɗan kurkuku guda wanda mutane suka roƙa.7. Wani mutumin da ake kira Barabbas, yana a kurkuku, tare da waɗansu ’yan tawaye da suka yi kisankai a lokacin wani hargitsi.8. Taron suka matso, suka ce roƙi Bilatus yă yi musu abin da ya saba yi.9. Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Kuna so in sakar muku Sarkin Yahudawa?”10. Don ya san saboda sonkai ne manyan firistoci suka ba da Yesu a gare shi.11. Amma manyan firistoci suka zuga taron su sa a saki Barabbas, a maimakon Yesu.12. Bilatus ya tambaye su ya ce, “To, me zan yi da wanda kuke ce da shi, sarkin Yahudawa?”13. Suka yi ihu, suka ce, “A gicciye shi!”14. Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Don me? Wane laifi ya yi?” Amma suka ƙara yin ihu suna cewa, “A gicciye shi!”15. Don son yă faranta wa taron rai, sai Bilatus ya sakar musu Barabbas. Ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye.16. Sojojin suka tafi da Yesu cikin fadar gwamna (wato, Firetoriyum), suka kira dukan kamfanin sojoji wuri ɗaya.17. Suka sa masa wata riga mai ruwan shunayya, suka kuma tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa.18. Sai suka fara ce masa, “Ranka yă daɗe sarkin Yahudawa!”19. Suka dinga bugunsa a kā da sanda, suka tattofa masa miyau. Suka durƙusa suka yi masa bangirma na ba’a.20. Bayan da suka gama yin masa ba’a, suka tuɓe rigar mai ruwan shunayyar, suka sa masa nasa tufafi. Sai suka tafi da shi don a gicciye shi.21. Sai ga wani mutum daga Sairin da ake kira Siman, mahaifin Alekzanda da Rufus, yana wucewa kan hanyarsa daga ƙauye. Sai suka tilasta shi yă ɗauki gicciyen.22. Suka kawo Yesu a wurin da ake kira Golgota (wanda yake nufin Wurin Ƙoƙon Kai).23. Sai suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da mur, don yă rage zafi, amma bai sha ba.24. Sai suka gicciye shi. Suka rarraba tufafinsa, suka jefa ƙuri’a a kansu don su ga abin da kowa zai samu. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.