Baibul a cikin shekara guda Maris 2Ƙidaya 1:1-541. Ubangiji ya yi magana da Musa a Tentin Sujada a cikin Hamadar Sinai, a rana ta fari na watan biyu a shekara ta biyu, bayan Isra’ilawa suka fito Masar ya ce,2. “Ka yi ƙidayan dukan al’umman Isra’ilawa bisa ga iyalansu da kabilarsu, ka rubuta kowa da sunansa bi da bi.3. Da kai da Haruna za ku lissafta dukan mazan Isra’ila bisa ga sashensu, waɗanda suka kai shekaru ashirin ko fiye, da za su iya shiga soja.4. Mutum ɗaya daga kowace kabila wanda yake shugaban danginsa, zai taimake ku.5. “Ga sunayen da za su taimake ku. “Daga kabilar Ruben, Elizur ɗan Shedeyur;6. daga kabilar Simeyon, Shelumiyel ɗan Zurishaddai;7. daga kabilar Yahuda, Nashon ɗan Amminadab;8. daga kabilar Issakar, Netanel ɗan Zuwar;9. daga kabilar Zebulun, Eliyab ɗan Helon;10. daga kabilar ’ya’yan Yusuf, daga Efraim, Elishama ɗan Ammihud; daga Manasse, Gamaliyel ɗan Fedazur;11. daga kabilar Benyamin, Abidan ɗan Gideyoni;12. daga kabilar Dan, Ahiyezer ɗan Ammishaddai;13. daga kabilar Asher, Fagiyel ɗan Okran;14. daga kabilar Gad, Eliyasaf ɗan Deyuwel;15. daga kabilar Naftali, Ahira ɗan Enan.”16. Waɗannan su ne mutanen da aka naɗa daga cikin jama’a, shugabannin asalin kabilu. Su ne kuma shugabannin dangogin Isra’ila.17. Sai Musa da Haruna suka ɗauki sunayen mutanen nan da aka ba su,18. suka kira dukan al’umma wuri ɗaya a rana ta fari ga wata na biyu. Aka kuwa rubuta mutanen bisa ga asalin kabilansu da iyalansu. Aka kuma rubuta sunayen maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekaru ashirin ko fiye,19. yadda Ubangiji ya umarci Musa. Da haka ya ƙidaya su a Hamadar Sinai.20. Daga zuriyar Ruben ɗan fari na Isra’ila. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.21. Jimillar maza daga mutanen Ruben 46,500 ne.22. Daga zuriyar Simeyon. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.23. Jimillar maza daga mutanen Simeyon 59,300 ne.24. Daga zuriyar Gad. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.25. Jimillar maza daga mutanen Gad 45,650 ne.26. Daga zuriyar Yahuda. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.27. Jimillar maza daga mutanen Yahuda 74,600 ne.28. Daga zuriyar Issakar. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.29. Jimillar maza daga mutanen Issakar 54,400 ne.30. Daga zuriyar Zebulun. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.31. Jimillar maza daga mutanen Zebulun 57,400 ne.32. Daga ’ya’yan Yusuf. Daga zuriyar Efraim. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.33. Jimillar maza daga mutanen Efraim 40,500 ne.34. Daga zuriyar Manasse. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.35. Jimillar maza daga mutanen Manasse 32,200 ne.36. Daga zuriyar Benyamin. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.37. Jimillar maza daga mutanen Benyamin 35,400 ne.38. Daga zuriyar Dan. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.39. Jimillar maza daga mutanen Dan 62,700 ne.40. Daga zuriyar Asher. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.41. Jimillar maza daga mutanen Asher 41,500 ne.42. Daga zuriyar Naftali. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.43. Jimillar maza daga mutanen Naftali kuwa 53,400 ne.44. Waɗannan su ne mazan da Musa da Haruna, tare da shugabanni goma sha biyun nan na Isra’ila suka ƙidaya, kowa a madadin iyalinsa.45. Dukan Isra’ilawan da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, an ƙidaya su bisa ga iyalansu.46. Jimillar kuwa ita ce mutum 603,550.47. Ba a dai ƙidaya zuriyar Lawi tare da saura kabilan ba.48. Ubangiji ya riga ya gaya wa Musa cewa,49. “Ka tabbatar ba ka ƙidaya mutanen Lawi ko kuma ka haɗe su tare a ƙidayan sauran Isra’ilawa ba.50. A maimakon haka sai ka naɗa Lawiyawa su lura da tabanakul Shaida, wato, kan dukan kayayyaki da kuma kome da yake na wuri mai tsarki. Za su ɗauko tabanakul da dukan kayayyakinsa; za su lura da shi, su kasance kewaye da shi.51. Duk sa’ad da za a gusar da tabanakul, Lawiyawa ne za su saukar da shi; kuma duk sa’ad da za a kafa shi, Lawiyawa ne za su yi haka. Duk wani dabam da ya je kusa da shi za a kashe shi.52. Sauran Isra’ilawa za su zauna ƙungiya-ƙungiya, kowane mutum a ƙungiyarsa daidai bisa ga ƙa’idarsa.53. Amma Lawiyawa za su kafa sansaninsu kewaye da tabanakul na Shaida. Don kada fushi yă fāɗo a kan al’ummar Isra’ilawa. Hakkin Lawiyawa ne su kula da tabanakul na Shaida.”54. Isra’ilawa suka yi duk waɗannan kamar dai yadda Ubangiji ya umarci Musa.Ƙidaya 2:1-341. Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,2. “Duk sa’ad da Isra’ilawa suka yi sansani, kowane mutum zai sauka a inda tutar ƙungiyar kabilarsa take. Sansanin zai kasance a kewaye da Tentin Sujada.”3. Kabilar Yahuda za su yi sansani bisa ga ƙa’idarsu a gabas, wajen fitowar rana. Shugaban mutanen Yahuda kuwa shi ne Nashon ɗan Amminadab.4. Yawan mutanen sashensa 74,600 ne.5. Kabilar Issakar za su yi sansani biye da su. Shugabansu shi ne Netanel ɗan Zuwar.6. Yawan mutanen sashensa 54,400 ne.7. Kabilar Zebulun za su yi sansani biye da su. Shugabansu shi ne Eliyab ɗan Helon.8. Yawan mutanen sashensa 57,400 ne.9. Dukan mazan da aka ba su aiki a sansanin Yahuda bisa ga sashensu sun kai 186,400. Su ne za su ja gaba.10. A kudu, a nan ne sashe sansanin mutanen Ruben a ƙarƙashin ƙa’idarsu, za su yi sansani. Shugaban mutanen Ruben shi ne Elizur ɗan Shedeyur.11. Yawan mutanen sashensa 46,500 ne.12. Kabilar Simeyon za su yi sansani biye da su. Shugaban mutanensa shi ne Shelumiyel ɗan Zurishaddai.13. Yawan mutanen sashensa 59,300 ne.14. Kabilar Gad za su zama na biye. Shugaban mutanensa shi ne Eliyasaf ɗan Reyuwel.15. Yawan mutanen sashensa 45,650 ne.16. Dukan mazan da aka ba su aiki a sansanin Ruben, bisa ga sashensu sun kai 151,450. Su ne za su zama na biyu in za a tashi.17. Sa’an nan Lawiyawa ɗauke da Tentin Sujada za su kasance a tsakiyar sansani sa’ad da aka tashi tafiya. Za su kama hanya kamar yadda aka dokace su su zauna a sansani, kowa a wurinsa a ƙarƙashin ƙa’idarsu.18. Ta wajen yamma kuma sashen Efraim za su yi sansani a ƙarƙashin ƙa’idarsu. Shugaban mutanensa, shi ne Elishama ɗan Ammihud.19. Yawan mutanen sashensa 40,500 ne.20. Kabilar Manasse ce za tă zama ta biye. Shugabansu shi ne Gamaliyel ɗan Fedazur.21. Yawan mutanen sashensa 32,200 ne.22. Na biye da su su ne mutanen Benyamin. Shugaban mutanensu kuwa Abidan ɗan Gideyoni.23. Yawan mutanen sashensa 35,400 ne.24. Dukan mazan da aka ba su aiki a sansanin Efraim, bisa ga sashensu su kai 108,100 ne. Su ne za su zama na uku sa’ad da za a tashi.25. A arewa za a sami sashen sansanin Dan, a ƙarƙashin ƙa’idarsu. Shugabansu shi ne Ahiyezer ɗan Ammishaddai.26. Yawan mutanen sashensa 62,700 ne.27. Kabilar Asher ce za tă zama ta biye. Shugabansu shi ne Fagiyel ɗan Okran.28. Yawan mutanen sashensa 41,500 ne.29. Kabilar Naftali za su zama na biye da su. Shugaban mutanen kuwa shi ne Ahira ɗan Enan.30. Yawan mutanen sashensa 53,400 ne31. Dukan mazan da aka ba su aiki a sansanin Efraim, bisa ga sashensu su kai 157,600. Su ne za su zama na ƙarshe, ƙarƙashin ƙa’idarsu.32. Waɗannan su ne Isra’ilawan da aka a ƙidaya bisa ga iyalansu. Dukansu da suke a sansani, mutane 603,550 ne.33. Ba a dai ƙidaya Lawiyawa tare da sauran Isra’ilawa ba yadda Ubangiji ya umarci Musa.34. Saboda haka Isra’ilawa suka yi duk ko mene ne da Ubangiji ya umarci Musa. Ta haka ne suka yi sansani a ƙarƙashin ƙa’idarsu kowanne tare da kabilarsa da danginsa.Zabura 29:7-117. Muryar Ubangiji ta buga da walƙatar walƙiya.8. Muryar Ubangiji ta girgiza hamada Ubangiji ya girgiza Hamadan Kadesh.9. Muryar Ubangiji ta murɗa itatuwan oak ya kakkaɓe itatuwan kurmi. Kuma a cikin haikalinsa kowa ya ce, “Ɗaukaka!”10. Ubangiji na zaune yana sarauta a bisa rigyawa; Ubangiji yana sarauta kamar Sarki har abada.11. Ubangiji kan ba da ƙarfi ga mutanensa; Ubangiji kan albarkace mutanensa da salama.Karin Magana 10:26-2926. Kamar yadda ruwan tsami yake ga haƙora hayaƙi kuma ga idanu, haka malalaci yake ga wanda ya aike shi.27. Tsoron Ubangiji kan ƙara tsawon rai, amma akan gajartar da shekarun mugaye.28. Abin da adali yake sa rai yakan kai ga farin ciki, amma sa zuciyar mugu ba ya haifar da kome.29. Hanyar Ubangiji mafaka ce ga adalai amma lalaci ne ga waɗanda suke aikata mugunta.Markus 7:14-3714. Sai Yesu ya sāke kiran taron wurinsa ya ce, “Ku saurare ni dukanku, ku kuma fahimci wannan.15. Ba abin da yake shiga mutum daga waje ba ne yake ƙazantar da shi. Sai dai abin da ya fita daga cikin mutum ne, yake ƙazantar da shi.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.