Baibul a cikin shekara guda Maris 24Maimaitawar Shariʼa 9:1-291. Ku ji, ya Isra’ila. Kuna gab da haye Urdun, ku shiga, ku kuma kori al’ummai da suka fi ku yawa, suka kuma fi ku ƙarfi, masu manyan biranen da suke da katangar da suka yi tsaye zuwa sama.2. Mutane ne masu ƙarfi, kuma dogaye, zuriyar Anakawa! Ai, kun ji akan ce, “Wa zai iya tsayayya da Anakawa?”3. Amma ku zauna da sani a yau, cewa Ubangiji Allahnku, shi ne wanda ya ƙetare ya sha gabanku kamar wuta mai cinyewa. Zai hallaka su, zai rinjaye su a gabanku. Za ku kore su, ku kuma hallaka su nan da nan, yadda Ubangiji ya yi muku alkawari.4. Bayan Ubangiji Allahnku ya kore su a gabanku, kada ku faɗa a zuciyarku, “Ubangiji ya kawo mu a nan, mu mallaki wannan ƙasa saboda adalcinmu ne.” A’a, saboda muguntar waɗannan al’umma ne ya sa Ubangiji ya kore su a gabanku.5. Ba domin adalci ko mutuncinku ba ne ya sa za ku mallaki ƙasarsu; sai dai saboda muguntar al’umman nan ne ya sa Ubangiji Allahnku yana korinsu a gabanku don yă cika abin da ya rantse wa kakanninku, wato, Ibrahim, Ishaku da Yaƙub.6. Ku gane wannan, cewa ba domin adalcinku ba ne ya sa Ubangiji Allahnku yana ba ku wannan ƙasa mai kyau, ku mallaki, gama ku mutane masu taurinkai ne.7. Ku tuna da wannan, kada kuma ku manta yadda kuka tsokane Ubangiji Allahnku, har ya yi fushi a hamada. Daga ranar da kuka bar Masar har sai da kuka isa nan, kuna ta tawaye wa Ubangiji.8. A Horeb, kun tayar wa Ubangiji har ya yi fushin da ya isa yă hallaka ku.9. Sa’ad da na hau kan dutse don in karɓi allunan dutse, allunan alkawarin da Ubangiji ya yi da ku, na zauna a kan dutse yini arba’in da dare arba’in; ban ci abinci ba, ban sha ruwa ba.10. Ubangiji ya ba ni alluna biyu wanda shi kansa ya yi rubutu da yatsarsa. A kansu akwai dukan umarnan Ubangiji da an furta muku a kan dutse a tsakiyar wuta, a ranar taron jama’a.11. A ƙarshen yini arba’in da dare arba’in ɗin, Ubangiji ya ba ni alluna biyu na dutse, allunan alkawari.12. Sa’an nan Ubangiji ya faɗa mini, “Sauka daga nan da sauri, domin mutanenka waɗanda ka fitar da su daga Masar sun lalace. Sun juye da sauri daga abin da na umarce su, suka kuma yi zubin gunki wa kansu.”13. Sai Ubangiji ya ce mini, “Na ga mutanen nan, su masu taurinkai ne sosai!14. Bar ni kawai, in hallaka su, in kuma shafe sunansu daga ƙarƙashin sama. Zan kuwa yi maka wata al’umma mafi ƙarfi da kuma masu yawa fiye da su.”15. Saboda haka na juya, na sauko daga dutsen yayinda yake cin wuta. Allunan biyu na alkawarin kuma suna a hannuwana.16. Sa’ad da na duba, sai na ga cewa kun yi zunubi wa Ubangiji Allahnku; kun yi wa kanku gunkin da kuka yi zubi a siffar ɗan maraƙi. Kun kauce da sauri daga hanyar da Ubangiji ya umarce ku.17. Saboda haka na ɗauko alluna biyun na jefar da su daga hannuwana, na farfashe su a idanunku.18. Sai nan da nan kuma na fāɗi rubda ciki a gaban Ubangiji, yini arba’in da dare arba’in; ban ci ba, ban sha ba, kamar yadda dā na yi, duka saboda zunubin da kuka aikata a gaban Ubangiji. Ta haka kuka tsokane shi don yă yi fushi.19. Na ji tsoron fushi da hasalar Ubangiji, gama ya yi fushin da ku da ya isa yă hallaka ku. Amma na yi roƙo a lokacin, Ubangiji kuwa ya saurare ni.20. Ubangiji ya yi fushi sosai da Haruna, har ya yi niyya yă hallaka shi, amma a wannan lokaci, na yi addu’a saboda Haruna shi ma.21. Sa’an nan na ɗauki kayan zunubin da kuka yi, wato, gunkin ɗan bijimi, na ƙone shi da wuta, na farfashe shi, na niƙa shi liɓis, sai da ya zama kamar ƙura mai laushi, na zubar da ƙurar a cikin ruwan rafin da yake gangarowa daga dutse.22. Kun kuma sa Ubangiji ya yi fushi a Tabera, a Massa da kuma a Kibrot Hatta’awa.23. Sa’ad da Ubangiji ya aike ku daga Kadesh Barneya ya ce, “Ku haura ku mallaki ƙasar da na ba ku.” Amma kuka yi tawaye ga umarnin Ubangiji Allahnku. Ba ku amince da shi, ko ku yi masa biyayya ba.24. Kun yi ta tawaye wa Ubangiji tun ran da na san ku.25. Na kwanta rubda ciki a gaban Ubangiji waɗannan yini arba’in da dare arba’in domin Ubangiji ya ce zai hallaka ku.26. Na yi addu’a ga Ubangiji na ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kada ka hallaka mutanenka, gādon kanka, da ka fansa ta wurin ikonka mai girma, ka kuma fitar da su daga Masar da hannu mai ƙarfi.27. Ka tuna da bayinka Ibrahim, Ishaku da Yaƙub. Kada ka kula da taurinkan, mugunta da kuma zunubin wannan mutane.28. In ba haka ba, ƙasar da ka fitar da mu, za tă ce, ‘Domin Ubangiji bai iya kai su cikin ƙasar da ya yi musu alkawari ba ne, kuma domin ya ƙi su, shi ya sa ya fitar da su ya kashe su a hamada.’29. Amma su mutanenka ne, gādonka da ka fitar ta wurin ikonka mai girma, da kuma hannunka mai ƙarfi.”Maimaitawar Shariʼa 10:1-221. A lokacin Ubangiji ya ce mini, “Ka sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko, ka haura wurina a kan dutse. Ka kuma yi akwatin katako.2. Ni kuwa zan yi rubutu a kan allunan nan biyu, kalmomin da suke a alluna na farko, waɗanda ka farfashe. Za a ajiye su a cikin akwatin.”3. Sai na yi akwatin da itacen ƙirya, na kuma sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko, sai na haura dutse da alluna biyun a hannuwana.4. Ubangiji kuwa ya sāke yin rubutu a waɗannan alluna abin da ya rubuta a allunan farko, wato, Dokoki Goma da ya furta a kan dutse a tsakiyar wuta, a ranar da mutane suka taru. Sai Ubangiji ya ba ni su.5. Sa’an nan na sauko daga dutsen, na kuma ajiye allunan a cikin akwatin da na yi, yadda Ubangiji ya umarce ni, kuma suna can a yanzu.6. (Isra’ilawa suka kama hanya daga rijiyoyin Beyerot Bene Ya’akan zuwa Mosera. A can Haruna ya rasu, aka kuma binne shi. Sai Eleyazar ɗansa ya gāje shi a matsayin firist.7. Daga can suka tashi zuwa Gudgoda, daga Gudgoda kuma suka tafi Yotbata, ƙasa mai rafuffukan ruwa.8. A lokacin Ubangiji ya keɓe kabilar Lawi don su riƙa ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, su tsaya a gaban Ubangiji, su riƙa yin masa hidima, su kuma sa albarka a cikin sunansa, yadda suke yi har wa yau.9. Shi ya sa Lawiyawa ba su da rabo, ko gādo a cikin ’yan’uwansu; Ubangiji ne gādonsu yadda Ubangiji Allahnku ya faɗa musu.)10. To, na kasance a kan dutse yini arba’in da dare arba’in kamar yadda dā na yi da farko. Ubangiji kuwa ya saurare ni a wannan lokaci kuma. Ba nufinsa ba ne yă hallaka ku.11. Ubangiji ya ce mini, “Ka sauka, ka jagoranci mutanen a hanyarsu, domin su shiga, su kuma mallaki ƙasar da na rantse wa kakanninsu, zan ba su.”12. Yanzu fa, ya Isra’ila, mene ne Ubangiji Allahnku yake so a gare ku, in ba ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin hanyoyinsa, ku ƙaunace shi, ku bauta wa Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku,13. ku kuma kiyaye umarnan Ubangiji da kuma ƙa’idodinsa da nake ba ku a yau don amfaninku ba?14. Sammai, har da sama sammai, da duniya, da kome da yake cikinta na Ubangiji Allahnku ne.15. Duk da haka Ubangiji ya ƙaunaci kakanninku, ya kuma zaɓe ku, ku zuriyarsu, a bisa dukan al’ummai, yadda yake a yau.16. Saboda haka sai ku kame zukatanku, kada ku ƙara yin taurinkai.17. Gama Ubangiji Allahnku ne Allahn alloli da Ubangijin iyayengiji, Allah mai girma, mai ƙarfi da kuma mai banrazana, wanda ba ya sonkai, ba ya cin hanci.18. Yakan tsare marayu da gwauraye, yana ƙaunar baƙon da yake zama a cikinku, yana ba su abinci da tufafi.19. Sai ku ƙaunaci baƙi, gama dā ku ma baƙi ne a ƙasar Masar.20. Ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku kuma bauta masa. Ku manne masa, ku kuma yi rantsuwarku da sunansa.21. Shi ne abin yabonku; shi ne Allahnku, wanda ya aikata muku waɗancan manya abubuwa banmamaki masu banrazanar da kuka gani da idanunku.22. Kakanninku da suka gangara zuwa Masar, su saba’in ne, yanzu kuwa Ubangiji Allahnku ya sa kuka ƙaru, kuka zama kamar taurari a sama.Zabura 37:12-1712. Mugaye sukan shirya wa adalai maƙarƙashiya su ciji baki a kansu;13. amma Ubangiji yakan yi dariyar mugaye, gama ya sani ranarsu tana zuwa.14. Mugaye sukan zare takobi su ja baka don su kashe matalauta da masu bukata, don su kashe waɗanda hanyoyinsu daidai suke.15. Amma takubansu za su soki zukatansu, kuma bakkunansu za su kakkarye.16. Ƙanƙanen abin da mai adalci yake da shi ya fi arzikin mugaye yawa;17. gama za a kakkarya ikon mugaye, amma Ubangiji zai riƙe mai adalci.Karin Magana 12:11-1111. Duk wanda ya nome gonarsa zai sami abinci a yalwace, amma shi da yake naushin iska marar azanci ne.Luka 1:57-8057. Sa’ad da kwanaki suka yi don Elizabet ta haihu, sai ta haifi ɗa.58. Maƙwabtanta da ’yan’uwanta suka ji cewa Ubangiji ya nuna mata jinƙai mai yawa, suka kuma taya ta farin ciki.59. A rana ta takwas, sai suka zo don a yi wa yaron kaciya, dā za su sa masa sunan mahaifinsa Zakariya ne,60. amma mahaifiyar yaron ta ce, “A’a! Za a ce da shi Yohanna.”61. Sai suka ce mata, “Ba wani a cikin danginku mai wannan suna.”62. Sai suka yi alamu wa mahaifinsa, don su san sunan da zai su a kira yaron.63. Ya yi alama a kawo masa allo, a gaban kowa sai ya rubuta, “Sunansa Yohanna.” Dukan mutane kuwa suka yi mamaki.64. Nan da nan bakinsa ya buɗe harshensa kuma ya saku, sai ya fara magana yana yabon Allah.65. Maƙwabta duk suka cika da tsoro, mutane kuwa suka yi ta yin magana game da dukan waɗannan abubuwa a ko’ina a cikin ƙasar tudu ta Yahudiya.66. Duk waɗanda suka ji wannan kuwa sun yi mamaki suna cewa, “To, me yaron nan zai zama?” Gama hannun Ubangiji yana tare da shi.67. Mahaifinsa Zakariya ya cika da Ruhu Mai Tsarki sai ya yi annabci ya ce,68. “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, domin ya zo ya kuma fanshe mutanensa.69. Ya tā mana ƙahon ceto a gidan bawansa Dawuda70. (yadda ya yi magana tun tuni ta wurin annabawansa masu tsarki),71. cewa zai cece mu daga abokan gābanmu daga kuma hannun dukan waɗanda suke ƙinmu72. don yă nuna jinƙai ga kakanninmu, yă kuma tuna da alkawarinsa mai tsarki,73. rantsuwar da ya yi wa mahaifinmu Ibrahim,74. don yă kuɓutar da mu daga hannun abokan gābanmu, yă kuma sa mu iya yin masa hidima babu tsoro,75. cikin tsarki da adalci a gabansa dukan kwanakinmu.76. “Kai kuma, ɗana, za a ce da kai annabin Maɗaukaki; gama za ka sha gaban Ubangiji don ka shirya masa hanya,77. don ka sanar da mutanensa ceto, ta wurin gafarar zunubansu,78. saboda jinƙai na Allahnmu mai ƙauna, hasken nan na ceto zai ɓullo mana daga sama,79. don yă haskaka a kan waɗanda suke zama cikin duhu, da kuma cikin inuwar mutuwa, don yă bi da ƙafafunmu a hanyar salama.”80. Yaron kuwa ya yi girma ya kuma ƙarfafa a ruhu; ya zauna a hamada sai lokacin da ya fito a fili ga mutanen Isra’ila. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.