Baibul a cikin shekara guda Maris 26Maimaitawar Shariʼa 13:1-181. In wani annabi ko mai mafarkai, ya bayyana a cikinku, ya kuma yi muku shelar wata alama mai banmamaki ko al’ajabi,2. in kuwa alamar, ko al’ajabin da annabin ya yi faɗin ya faru, ya kuma ce, “Bari mu bi waɗansu alloli (allolin da ba ku sani ba) mu kuma yi musu sujada,”3. kada ku saurari kalmomin wannan annabi ko mai mafarki. Ubangiji Allahnku yana gwada ku ne don yă sani ko kuna ƙaunarsa da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku.4. Ubangiji Allahnku ne za ku bi, shi ne kuma za ku girmama. Ku kiyaye umarnansa, ku kuma yi masa biyayya; ku bauta masa, ku kuma manne masa.5. Dole a kashe wannan annabi ko mai mafarki, domin ya yi wa’azin tawaye ga Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, ya fanshe ku daga ƙasar bauta; gama annabin nan ya yi ƙoƙari yă juye daga hanyar da Ubangiji Allahnku ya umarce ku, ku bi. Dole ku fid da mugu daga cikinku.6. In ɗan’uwanka, ko ɗanka, ko ’yarka, ko matar da kake ƙauna, ko abokinka na kusa, a ɓoye ya ruɗe ka, yana cewa, “Mu je mu yi wa waɗansu alloli sujada” (allolin da ko kai, ko kakanninka ba su sani ba,7. allolin mutanen kewayenku, ko na kusa, ko na nisa, daga wannan ƙarshen ƙasar zuwa wancan),8. kada ka yarda da shi, kada ma ka saurare shi. Kada ka ji tausayinsa. Kada ka haƙura da shi, ko ka tsare shi.9. Dole ka kashe shi. Dole hannunka yă zama na farko a kisansa, sa’an nan hannuwan sauran dukan mutane.10. Ku jajjefe shi da duwatsu har sai ya mutu, domin ya yi ƙoƙari yă juye ku daga Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta kuma.11. Sa’an nan dukan Isra’ila za su ji su kuma tsorata, babu kuma wani a cikinku da zai ƙara yin irin wannan mugun abu.12. In kuka ji an yi magana a kan wani daga cikin biranen da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku zauna a ciki13. cewa mugaye sun taso a cikinku, suna rikitar da mutane a birni, suna cewa, “Mu je mu yi wa waɗansu alloli sujada” (allolin da ba ku sani ba),14. to, sai ku bincike labarin sosai a hankali. In kuwa gaskiya ne, an kuma tabbatar wannan abin ƙyama ya faru a cikinku,15. dole a karkashe dukan waɗanda suke zama a wannan birni da takobi. Ku hallaka su ƙaƙaf, ku karkashe mutanen birnin da kuma dabbobinsa.16. Ku tattara dukan ganimar birnin a tsakiyar gari, ku ƙone birnin da kuma ganimar ƙurmus a matsayin hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji Allahnku. Birnin zai kasance kufai har abada, kada a sāke gina shi.17. Ba za a iske wani daga cikin abubuwan nan da aka haramta a hannuwanku ba, saboda Ubangiji yă juya daga fushinsa mai ƙuna, yă nuna jinƙai, yă ji tausayinku, yă kuma ƙara yawanku, kamar yadda ya alkawarta da rantsuwa ga kakanninku,18. domin kun yi biyayya da Ubangiji Allahnku, kuna kiyaye dukan umarnan da nake ba ku a yau, kuna kuma aikata abin da yake daidai a idanunsa.Maimaitawar Shariʼa 14:1-291. Ku ’ya’yan Ubangiji Allahnku ne. Kada ku yi wa kanku zāne, ko ku yi wa kanku aski irin da akan bar sanƙo, saboda wanda ya mutu,2. gama ku jama’a ce mai tsarki ga Ubangiji Allahnku. Daga dukan mutane a fuskar duniya, Ubangiji ya zaɓe ku, ku zama abin mallakarsa.3. Kada ku ci wani haramtaccen abu.4. Waɗannan su ne dabbobin da za ku iya ci, saniya, tunkiya, akuya,5. mariri, barewa, mariya, makwarna, mazo, gada da kuma tunkiyar dutse.6. Za ku iya cin duk dabbar da take da rababben kofato, wadda kuma take sāke tona abin da suka riga suka haɗiye.7. Amma, cikin waɗanda suke sāke tona abin da suka riga suka haɗiye ɗin, ko suke da rababben kofato, ba za ku ci raƙumi, zomo ko rema ba. Ko da yake suna sāke tona abin da suka riga suka haɗiye, suna kuma da rababben kofato, su ɗin marar tsarki ne gare ku.8. Alade ma marar tsarki ne; ko da yake yana da rababben kofato, shi ba ya sāke tona abin da ya riga ya haɗiye. Ba za ku ci namansu ko ku taɓa gawarsu ba.9. Cikin dukan halittun da suke cikin ruwa, za ku iya cin duk wani da yake da ƙege da ɓamɓaroki.10. Amma duk wani abin da ba shi da ƙege da ɓamɓaroki, ba za ku ci ba; gama marar tsarki ne gare ku.11. Za ku iya cin kowane tsuntsu mai tsabta.12. Amma waɗannan ba za ku ci ba, gaggafa, ungulu, ungulun kwakwa,13. duki, buga zaɓi, kowace irin shirwa,14. kowane irin hankaka,15. jimina, ƙururu, bubuƙuwa, kowane irin shaho,16. da mujiya, da babbar mujiya, ɗuskwi,17. kwasakwasa, ungulu, da babba da jaka,18. zalɓe, kowane irin jinjimi, katutu, da kuma jamage.19. Dukan ’yan ƙwari masu fikafikai masu rarrafe, haram ne a gare ku, kada ku ci su.20. Amma duk wata halitta mai fikafikai mai tsabta ce, za ku iya ci.21. Kada ku ci abin da kun samu ya riga ya mutu. Za ku iya ba wa baren da yake zama a cikin wani daga biranenku, zai kuwa iya cinsa, ko kuwa za ku iya sayar da shi wa baƙo. Amma ku jama’a ce mai tsarki ga Ubangiji Allahnku. Kada ku dafa ɗan akuya a cikin madara mamansa.22. Ku tabbata kun keɓe kashi ɗaya bisa goma na amfanin gonakinku kowace shekara.23. Ku ci zakkar hatsinku, da na sabon ruwan inabinku, da na manku, da kuma na ’ya’yan fari na garkunanku na shanu da na tumaki a gaban Ubangiji Allahnku, a wurin da ya zaɓa a matsayin mazauni don Sunansa, don ku koyi girmama Ubangiji Allahnku kullum.24. Amma in wurin nan yana da nisa sosai, Ubangiji Allahnku kuma ya albarkace ku, ba za ku kuwa iya riƙe zakkarku ba (Saboda wurin da Ubangiji ya zaɓa yă sa Sunansa ya yi nisa sosai),25. to, sai ku sayar da zakkar, ku tafi da kuɗin wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa.26. Yi amfani da kuɗin ku saya duk abin da kuke so, ko shanu, ko tumaki, ko ruwan inabi, ko dai wani abin shan da ya yi tsami, ko kuwa duk abin da kuke so. Sai ku da gidanku, ku ci a can, a gaban Ubangiji Allahnku, ku kuma yi farin ciki.27. Kada dai ku manta da Lawiyawan da suke zama a biranenku, gama ba su da rabo, ko gādo na kansu.28. A ƙarshen kowace shekara uku, ku kawo dukan zakkarku na amfanin gona na wannan shekara, ku ajiye su a cikin birane,29. saboda Lawiyawa (waɗanda ba su da rabo ko gādo na kansu) da baƙo, da marayu, da kuma gwauraye, waɗanda suke zama a biranenku, su zo su ci su ƙoshi, ta haka Ubangiji Allahnku zai albarkace ku cikin dukan ayyukan hannuwanku.Zabura 37:23-2923. In Ubangiji ya ji daɗin hanyar da mutum yake bi, zai sa sawu su kahu;24. ko ya yi tuntuɓe, ba zai fāɗi ba, gama Ubangiji yakan riƙe shi da hannunsa.25. Dā ni yaro ne amma yanzu na tsufa, duk da haka ban taɓa ganin an yashe masu adalci ba ko a ce ’ya’yansu suna roƙon burodi.26. Kullum suna bayar hannu sake suna kuma ba da bashi ba da wahala ba, za a yi wa ’ya’yansu albarka.27. Ku juyo daga mugunta ku yi alheri; sa’an nan za ku zauna a ƙasar har abada.28. Gama Ubangiji yana ƙaunar masu aikata daidai kuma ba zai yashe amintattunsa ba. Za a hallaka masu aikata mugunta gaba ɗaya, ’ya’yan mugaye za su hallaka.29. Masu adalci za su gāji ƙasar su kuma zauna a cikinta har abada.Karin Magana 12:15-1615. Hanyar wawa daidai take a gare shi, amma mai hikima kan saurari shawara.16. Wawa kan nuna fushinsa nan take, amma mai la’akari kan ƙyale zargi.Luka 2:25-5225. To, akwai wani mutum a Urushalima mai suna Siman, shi mai adalci da kuma mai ibada. Yana jiran fansar Isra’ila, Ruhu Mai Tsarki kuwa yana tare da shi.26. An bayyana masa ta wurin Ruhu Mai Tsarki cewa ba zai mutu ba sai ya ga Kiristi na Ubangiji.27. Da Ruhu ya iza shi, sai ya shiga cikin filin haikali. Sa’ad da iyayen suka kawo jaririn nan Yesu don su yi masa abin da al’adar Doka ta bukaci,28. sai Siman ya karɓi yaron a hannuwansa ya yabi Allah, yana cewa,29. “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kamar yadda ka yi alkawari, yanzu ka sallami bawanka lafiya.30. Gama idanuna sun ga cetonka,31. wanda ka shirya a gaban dukan mutane,32. haske don bayyanawa ga Al’ummai da kuma ɗaukaka ga mutanenka Isra’ila.”33. Mahaifin yaron da kuma mahaifiyarsa suka yi mamaki abin da aka faɗa game da shi.34. Sa’an nan Siman ya sa musu albarka ya ce wa Maryamu mahaifiyarsa, “An ƙaddara yaron nan yă zama sanadin fāɗuwa da tashin mutane da yawa a Isra’ila, zai kuma zama alamar da mutane ba za su so ba,35. ta haka za a fallasa tunanin zukatan mutane da yawa. Ke ma, takobi zai soki zuciyarki.”36. Akwai wata annabiya ma, mai suna Anna, diyar Fanuwel, na kabilar Asher. Ta tsufa kutuf; ta yi zama da mijinta shekaru bakwai bayan sun yi aure,37. ta kuwa zama gwauruwa sai da ta kai shekaru tamanin da huɗu. Ba ta taɓa barin haikali ba, tana sujada dare da rana, tana kuma azumi da addu’a.38. Tana haurawa wurinsu ke nan a wannan lokaci, sai ta yi wa Allah godiya ta kuma yi magana game da yaron nan ga dukan waɗanda suke sauraron fansar Urushalima.39. Bayan da Yusuf da Maryamu suka gama yin dukan abubuwan da Dokar Ubangiji ta bukaci, sai suka koma Galili suka tafi Nazaret garinsu.40. Yaron kuwa ya yi girma ya yi ƙarfi; ya cika da hikima, alherin Allah kuwa yana bisansa.41. Kowace shekara, iyayen Yesu sukan je Urushalima don Bikin Ƙetarewa.42. Da Yesu ya cika shekaru goma sha biyu, sai suka tafi Bikin bisa ga al’ada.43. Bayan Bikin, da iyayen suka kama hanya don su koma gida, sai Yesu, yaron nan, ya tsaya a Urushalima, ba da saninsu ba.44. Su kuwa sun ɗauka yana tare da su, saboda haka, suka yi ta tafiya har na yini guda. Sa’an nan suka fara nemansa cikin ’yan’uwansu da abokansu.45. Da ba su gan shi ba, sai suka koma Urushalima nemansa.46. Bayan kwana uku, sai suka same shi a filin haikali zaune a tsakiyar malamai, yana sauraronsu yana kuma yi musu tambayoyi.47. Dukan waɗanda suka ji shi, suka yi mamakin fahimtarsa, da amsoshinsa.48. Da iyayensa suka gan shi sai suka yi mamaki. Mahaifiyarsa ta ce masa, “Ɗana, don me ka yi mana haka? Ni da mahaifinka duk mun damu muna nemanka.”49. Sai ya ce, “Don me kuke nemana? Ba ku san cewa, dole in kasance a gidan Ubana ba?”50. Amma ba su fahimci abin da yake faɗin musu ba.51. Sai ya koma Nazaret tare da su, yana yi musu biyayya. Mahaifiyarsa kuma ta riƙe dukan waɗannan abubuwa a zuciyarta.52. Yesu kuwa ya yi girma, ya kuma ƙaru cikin hikima, ya kuma sami tagomashi a wurin Allah da mutane. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.