Baibul a cikin shekara guda Maris 27Maimaitawar Shariʼa 15:1-231. A ƙarshen kowace shekara ta bakwai, dole ku yafe basusuwan da kuke bi.2. Ga yadda za ku yafe basusuwan, kowane mai bin bashi, yă yafe bashin da yake bin ɗan’uwansa mutumin Isra’ila. Ba zai bukaci mutumin Isra’ila wanda yake ɗan’uwa yă biya shi bashi ba, gama an yi shelar lokacin da Ubangiji ya ajiye na yafe bashi.3. Za ku iya nemi baƙo yă biya ku bashin da kuke binsa, amma dole ku yafe duk wani bashin da kuke bin ɗan’uwa.4. Amma bai kamata a sami matalauci a cikinku ba, gama Ubangiji Allahnku zai albarkace ku a ƙasar da yake ba ku, ku mallaka a matsayin gādo,5. in dai kun yi cikakken biyayya ga Ubangiji Allahnku, kuka kuma lura, kuna kiyaye dukan waɗannan umarnan da nake ba ku yau.6. Gama Ubangiji Allahnku zai albarkace ku kamar yadda ya yi alkawari, za ku kuma ba al’ummai masu yawa bashi, amma ba za ku karɓa bashi daga wurin wani ba. Za ku yi mulkin al’ummai masu yawa, babu wata kuwa da za tă yi mulkinku.7. In akwai matalauci a cikin ’yan’uwanku, a duk wani daga cikin biranen da Ubangiji Allahnku yake ba ku, kada ku taurara zuciya, ko ku ƙi saki hannu ga ɗan’uwanku matalauci.8. A maimakon haka ku bayar hannu sake, ku kuma ba shi bashi gwargwadon abin da yake bukata a sauƙaƙe.9. Ku yi hankali kada ku riƙe wannan mugun tunani cewa, “Shekara ta bakwai, shekarar yafewar basusuwa, ta yi kusa,” har ku nuna mugun nufi ga ɗan’uwa mabukaci, ku ƙi ba shi wani abu. Zai yi kuka ga Ubangiji a kanku, abin kuwa zai zama laifi a kanku.10. Ku bayar hannu sake gare shi, ku kuma yi haka ba tare da gunaguni ba; saboda wannan fa Ubangiji Allahnku zai albarkace ku a cikin dukan aikinku, da kuma kome da kuka sa hannunku a kai.11. Kullum za ku kasance da matalauta a ƙasar. Saboda haka na umarce ku ku bayar hannu sake ga ’yan’uwa da kuma matalauta, da masu bukata a ƙasarku.12. In ɗan’uwa mutumin Ibraniyawa, namiji ko ta mace, ya sayar da kansa gare ka, ya kuma bauta maka shekaru shida, a shekara ta bakwai dole ka ’yantar da shi.13. Sa’ad da kuka sake shi, kada ku bar shi yă tafi hannu wofi.14. Ku ba shi kyautai hannu sake daga tumakinku, daga masussukarku, da kuma daga wurin matsewar inabinku. Ku ba shi yadda Ubangiji Allahnku ya albarkace ku.15. Ku tuna, dā ku bayi ne a Masar, Ubangiji Allahnku kuma ya fisshe ku. Shi ya sa nake ba ku wannan umarni a yau.16. Amma in bawanka ya ce maka, “Ba na so in bar ka,” saboda yana ƙaunarka da iyalinka, ya kuma fiye masa yă zauna da kai,17. sai ka ɗauki basilla ka huda kunnensa a bakin ƙofa, zai kuwa zama bawanka dukan rayuwarsa. Ka yi haka ma wa baiwarka.18. Sa’ad da kuka ’yantar da shi kada ku damu, gama shekara shida ya yi muku bauta wadda ta ninka ta ɗan ƙodago. Ubangiji Allahnku kuwa zai albarkace ku a kome da kuke yi.19. Ku keɓe wa Ubangiji Allahnku kowane ɗan fari na garkenku na shanu, da na tumaki. Kada ku sa ɗan fari na shanunku aiki, kada kuma ku aske gashin ɗan fari na tumakinku.20. Kowace shekara, kai da iyalinka za ku ci su a gaban Ubangiji Allahnku, a wurin da ya zaɓa.21. In dabbar tana da lahani, gurguntaka ko makantaka, ko kuwa tana da wani mugun lahani, kada ku miƙa ta ga Ubangiji Allahnku.22. Sai ku ci a cikin biranenku. Mutum marar tsabta da mai tsabta zai iya ci kamar yadda ake yi da barewa ko mariri.23. Amma kada fa ku ci jinin, ku zubar da shi a ƙasa kamar ruwa.Maimaitawar Shariʼa 16:1-221. Ku kiyaye watan Abib, ku kuma yi shagalin Bikin Ƙetarewar Ubangiji Allahnku, domin a watan Abib ne ya fitar da ku daga Masar da dad dare.2. Ku miƙa ’yar dabba daga cikin garkenku na tumaki, ko na shanu a matsayin Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji Allahnku a wurin da Ubangiji zai zaɓa a matsayin mazauni don Sunansa.3. Kada ku ci shi da burodin da aka yi da yisti, kwana bakwai za ku ci burodi marar yisti, burodi ne na wahala, gama kun bar Masar da gaggawa, saboda haka dukan kwanakin rayuwarku za ku tuna da lokacin da kuka fita daga Masar.4. Kada a iske yisti a cikin mallakarku a dukan ƙasarku har kwana bakwai. Kada ku bar wani nama na hadayar da kuka yi a yammancin ranar farko, yă kwana har safe.5. Kada ku miƙa hadayar Bikin Ƙetarewa a wani garin da Ubangiji Allahnku yake ba ku,6. sai dai a wurin da ya zaɓa yă zama mazauni don Sunansa. A can za ku miƙa hadayar Bikin Ƙetarewa da yamma, sa’ad da rana tana fāɗuwa, a ranar tunawa da fitowarku daga Masar.7. Ku gasa shi, ku kuma ci a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa. Sa’an nan da safe, ku dawo cikin tentunanku.8. Kwana shida za ku ci burodi marar yisti, a rana ta bakwai kuma sai ku yi taro ga Ubangiji Allahnku, a cikin wannan rana ba za ku yi kowane irin aiki ba.9. Ku ƙirga makoni bakwai, wato, ku fara ƙirga mako bakwai ɗin daga lokacin da kuka sa lauje don ku yanke hatsinku da suke tsaye.10. Sa’an nan ku yi shagalin Bikin Makoni ga Ubangiji Allahnku, ta wurin ba da hadaya ta yardar rai daidai da albarkun da Ubangiji Allahnku ya yi muku.11. Ku kuma yi farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku a wurin da ya zaɓa a matsayin mazauni don Sunansa, da ku da ’ya’yanku maza da mata, da bayinku maza da mata, da Lawiyawan cikin biranenku, har ma da baƙi, da marayu, da kuma gwaurayen da suke zama a cikinku.12. Ku tuna fa, dā ku bayi ne a Masar, sai ku lura, ku bi waɗannan ƙa’idodi.13. Ku yi shagalin Bikin Tabanakul har kwana bakwai, bayan kuka gama tattara amfanin gona daga masussukarku da kuma daga wuraren matsin inabinku.14. Ku yi farin ciki a Bikinku, da ku da ’ya’yanku maza da mata, da bayinku maza da mata, da Lawiyawa, da baƙi, da marayu, da kuma gwaurayen da suke zama a cikin biranenku.15. Kwana bakwai za ku yi shagalin Bikin ga Ubangiji Allahnku a wurin da ya zaɓa. Gama Ubangiji Allahnku zai albarkace ku a cikin dukan girbinku da kuma cikin dukan aikin hannuwanku, farin cikinku kuwa zai cika.16. Sau uku a shekara dukan maza su bayyana a gaban Ubangiji Allahnku a wurin da ya zaɓa; a Bikin Burodi Marar Yisti, da a Bikin Makoni, da kuma a Bikin Tabanakul. Babu wani da zai bayyana a gaban Ubangiji hannu wofi.17. Dole kowannenku yă kawo kyauta daidai yadda Ubangiji Allahnku ya albarkace shi.18. Ku naɗa alƙalai da shugabanni don kowace kabila, a kowane birnin da Ubangiji Allahnku yake ba ku, za su kuma shari’anta mutane ba nuna bambanci.19. Kada ku ɓata shari’a, ko ku nuna bambanci. Kada ku karɓi cin hanci, gama cin hanci yakan makanta idanu mai hikima, yă murɗe maganar mai gaskiya.20. Gaskiya ce kaɗai za ku bi don ku rayu, ku kuma mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.21. Kada ku kafa wani ginshiƙin itacen Ashera kusa da bagaden da kuka gina wa Ubangiji Allahnku,22. kada kuma ku tayar da dutse mai tsarki, gama waɗannan ne Ubangiji Allahnku yana ƙi.Zabura 37:30-3630. Bakin mutum mai adalci yakan yi magana da hikima, harshensa kuwa yakan yi maganar abin da yake daidai.31. Dokar Allahnsa tana a cikin zuciyarsa; ƙafafunsa ba sa santsi.32. Mugaye suna fako suna jira masu adalci, suna ƙoƙari neman ransu;33. amma Ubangiji ba zai bar su a ikonsu ba ko ya bari a hukunta su sa’ad da aka kawo su shari’a ba.34. Ku sa zuciya ga Ubangiji ku kuma kiyaye hanyarsa. Zai ɗaukaka ku ku ci gādon ƙasar, sa’ad da aka kawar da mugaye, za ka gani.35. Na ga wani mugu, azzalumi, yana yaɗuwa kamar ɗanyen itace a asalin ƙasarsa,36. amma yakan mutu nan da nan kuma ba ya ƙara kasancewa; ko an neme shi, ba za a same shi ba.Karin Magana 12:17-1917. Mashaidin gaskiya kan ba da shaidar gaskiya, amma mashaidin ƙarya yana baza ƙarairayi ne.18. Maganganun rashin tunani sukan soki mutum kamar takobi, amma harshen mai hikima kan kawo warkarwa.19. Leɓunan gaskiya kan dawwama har abada, amma harshen ƙarya yakan dawwama na ɗan lokaci ne kawai.Luka 3:1-381. A shekara ta goma sha biyar ta mulkin Kaisar Tiberiyus, a lokacin Buntus Bilatus ne gwamnar Yahudiya, Hiridus kuma yana sarautar Galili, ɗan’uwansa Filibus yana sarautar Ituriya da Tarakunitis, Lisaniyas kuma yana sarautar Abiline. 2. A lokacin ne Annas da Kayifas suke manyan firistoci. Sai maganar Allah ta zo wa Yohanna, ɗan Zakariya a hamada.3. Ya zaga dukan ƙasar da take kewaye da Urdun, yana wa’azin baftismar tuba don gafarar zunubai.4. Kamar yadda yake a rubuce a littafin annabi Ishaya. “Muryar mai kira a hamada, ‘Ku shirya wa Ubangiji hanya, ku miƙe hanyoyi dominsa.5. Za a cike kowane kwari, a farfashe kowane dutse da kowane tudu. Za a miƙe hanyoyin da suka karkace, a gyaggyara hanyoyi masu gargaɗa su zama sumul.6. Dukan ’yan Adam kuwa za su ga ceton Allah!’ ”7. Yohanna ya ce wa taron da suke zuwa domin yă yi musu baftisma, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku, ku guje wa fushin nan mai zuwa?8. Ku yi ayyukan da suka dace da tuba. Kada ma ku yi tunani za ku iya ce wa kanku, ‘Ai, muna da mahaifinmu Ibrahim.’ Ina gaya muku cewa daga cikin duwatsun nan Allah zai iya tā da ’ya’ya wa Ibrahim.9. An riga an sa bakin gatari a gindin itatuwa, kuma duk itacen da bai ba da ’ya’ya masu kyau ba, za a sare shi a jefa cikin wuta.”10. Sai taron suka tambaye shi, suka ce “Me za mu yi ke nan?”11. Ya amsa ya ce, “Ya kamata, mutumin da yake da riguna biyu, yă raba da wanda ba shi da riga, mai abinci kuma yă yi haka.”12. Masu karɓar haraji ma suka zo, domin a yi musu baftisma. Suka yi tambaya, suka ce “Malam, me ya kamata mu yi?”13. Ya ce musu, “Kada ku karɓa fiye da abin da aka ce a karɓa.”14. Sai waɗansu sojoji suka tambaye shi, “Mu fa? Me ya kamata mu yi?” Sai ya amsa ya ce, “Kada ku ƙwace kuɗin mutane, kada kuma ku yi shaidar ƙarya. Ku yi haƙuri da abin da ake biyanku.”15. Mutane suka zuba ido, suna kuma tunani a zuciyarsu, ko Yohanna ne Kiristi wanda ake sauraron zuwansa.16. Yohanna ya amsa musu duka ya ce, “Ina muku baftisma da ruwa. Amma wani wanda ya fi ni iko yana zuwa, ban ma isa in kunce igiyar takalmansa ba. Shi zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da wuta kuma.17. Matankaɗinsa yana a hannunsa don yă tankaɗe sussukarsa ya kuma tattara alkama cikin rumbunsa, amma zai ƙone yayin da wutar da ba a iya kashewa.”18. Da kalmomi masu yawa Yohanna ya yi wa mutane gargaɗi, ya kuma yi musu wa’azin bishara.19. Amma da Yohanna ya tsawata wa Hiridus mai mulki saboda Hiridiyas, matar ɗan’uwansa, da kuma dukan sauran mugayen abubuwan da ya yi,20. Hiridus dai ya ƙara ɓata al’amarin. Ya sa a kulle Yohanna a kurkuku.21. Sa’ad da ake wa dukan mutane baftisma, sai aka yi wa Yesu shi ma. Da yana cikin addu’a, sai sama ya buɗe,22. Ruhu Mai Tsarki kuma ya sauko masa a wata siffa, kamar kurciya. Sai murya ta fito daga sama, ta ce, “Kai ne Ɗana, wanda nake ƙauna, kai ne kuma kana faranta mini zuciya ƙwarai.”23. To, Yesu kansa yana da shekaru kusan talatin da haihuwa sa’ad da ya fara aikinsa. An ɗauka shi ɗan Yusuf ne, ɗan Heli,24. ɗan Mattat, ɗan Lawi, ɗan Melki, ɗan Yannai, ɗan Yusuf,25. ɗan Mattatiyas, ɗan Amos, ɗan Nahum, ɗan Esli, ɗan Naggai,26. ɗan Ma’at, ɗan Mattatiyas, ɗan Semeyin, ɗan Yosek, ɗan Yoda,27. ɗan Yowanan, ɗan Resa, ɗan Zerubbabel, ɗan Sheyaltiyel, ɗan Neri,28. ɗan Melki, ɗan Addi, ɗan Kosam, ɗan Elmadam, ɗan Er,29. ɗan Yoshuwa, ɗan Eliyezer, ɗan Yorim, ɗan Mattat, ɗan Lawi,30. ɗan Simeyon, ɗan Yahuda, ɗan Yusuf, ɗan Yonam, ɗan Eliyakim,31. ɗan Meleya, ɗan Menna, ɗan Mattata, ɗan Natan, ɗan Dawuda,32. ɗan Yesse, ɗan Obed, ɗan Bowaz, ɗan Salmon, ɗan Nashon,33. ɗan Amminadab, ɗan Ram, ɗan Hezron, ɗan Ferez, ɗan Yahuda,34. ɗan Yaƙub, ɗan Ishaku, ɗan Ibrahim, ɗan Tera, ɗan Nahor,35. ɗan Serug, ɗan Reyu, ɗan Feleg, ɗan Eber, ɗan Sala,36. ɗan Kainan, ɗan Arfakshad, ɗan Shem, ɗan Nuhu, ɗan Lamek,37. ɗan Metusela, ɗan Enok, ɗan Yared, ɗan Mahalalel, ɗan Kainan,38. ɗan Enosh, ɗan Shitu, ɗan Adamu, ɗan Allah. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.