Baibul a cikin shekara guda Maris 28Maimaitawar Shariʼa 17:1-201. Kada ku miƙa wa Ubangiji Allahnku, saniya ko tunkiyar da take da wani lahani, ko naƙasa a cikinta, gama wannan zai zama abar ƙyama gare shi.2. In an sami wani namiji ko ta mace mai zama a cikinku, a ɗaya daga biranen da Ubangiji ya ba ku yana aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnku ta wurin karya alkawarinsa,3. wanda ya saba wa umarnina, har ya yi sujada ga waɗansu alloli, yana rusuna musu, ko ga rana, ko ga wata, ko kuwa ga taurarin sama,4. in kuwa aka faɗa muku wannan, to, dole a bincika sosai. In kuwa gaskiya ne, aka kuma tabbatar cewa wannan abin ƙyama ya faru a cikin Isra’ila,5. sai a ɗauki namijin, ko ta mace wanda ya aikata wannan mugun abu zuwa ƙofar birni, a jajjefe wannan mutum sai ya mutu.6. Bisa ga shaidar mutum biyu ko uku, za a iya kashe mutum, amma ba za a iya kashe mutum bisa ga shaida mutum guda ba.7. Hannuwan shaidun ne za su zama na farko a kisan wanda ake zargin, sa’an nan hannuwan dukan mutane. Dole ku fid da mugu daga cikinku.8. In aka kawo ƙarar da yake da wuya sosai ga alƙali a kotunanku, ko wadda aka zub da jini ne, ko ta faɗa ce, ko kuwa ta wadda aka ci mutunci ce, ku kai su wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa.9. Ku je wurin firistoci, waɗanda suke Lawiyawa, ga kuma alƙalin wanda yake mulki a lokacin. Ku bincika daga gare su, za su kuwa ba da hukunci.10. Dole ku aikata hukuncin da suka yi a wurin da Ubangiji zai zaɓa. Ku lura fa, ku aikata kome da suka faɗa muku.11. Ku yi bisa ga dokar da suka koyar muku da kuma hukuncin da suka yi muku. Kada ku juya daga abin da suka faɗa muku, ko zuwa dama, ko zuwa hagu.12. Duk mutumin da ya yi rashin hankali wa alƙali, ko ga firist wanda yake aiki a nan wa Ubangiji Allahnku, dole a kashe shi. Dole ku fid da mugu daga Isra’ila.13. Dukan mutane kuwa za su ji, su kuma ji tsoro, ba kuwa za su ƙara yin rashin hankali kuma ba.14. Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, kuka mallake ta, kuka kuma zauna a cikinta, sai kuka ce, “Bari mu naɗa sarki a kanmu kamar sauran al’umman da suke kewaye da mu,”15. ku tabbata kun naɗa sarki a kanku wanda Ubangiji Allahnku ya zaɓa ne. Dole yă zama daga cikin ’yan’uwanku. Kada ku sa baƙo a kanku, wanda ba mutumin Isra’ila ɗan’uwanku ba.16. Sarkin, ba zai nemi dawakai da yawa wa kansa ba, ko yă sa mutane su koma Masar don su sami ƙarin dawakai ba, gama Ubangiji ya faɗa muku, “Ba za ku ƙara koma wancan hanya kuma ba.”17. Sarkin ba zai auri mata masu yawa ba, in ba haka ba zuciyarsa za tă karkata. Ba zai tara azurfa da zinariya da yawa ba.18. Sa’ad da ya hau kursiyin mulkinsa, sai yă rubuta wa kansa a littafin kofin wannan doka da aka ɗauka daga na firistoci, waɗanda suke Lawiyawa.19. Zai kasance tare da shi, zai kuma karanta shi dukan kwanakin ransa, saboda yă koyi girmama Ubangiji Allahnsa, yă kuma bi dukan kalmomin wannan doka da kuma waɗannan ƙa’idodi a hankali20. don kada yă ɗauki kansa ya fi ’yan’uwansa, yă kuma juya daga dokar zuwa dama, ko zuwa hagu. Sa’an nan shi da kuma zuriyarsa za su daɗe suna mulki a Isra’ila.Maimaitawar Shariʼa 18:1-221. Firistocin da suke Lawiyawa, tabbatacce dukan kabilar Lawi, ba za su sami rabo ko gādo tare da Isra’ila ba. Za su yi rayuwa a kan hadayun da aka kawo wa Ubangiji da wuta ne, gama wannan ne gādonsu.2. Ba za su sami gādo a cikin ’yan’uwansu ba; Ubangiji ne gādonsu, kamar yadda ya yi musu alkawari.3. To, ga rabon da jama’a za su ba firistoci daga hadayun da suka miƙa ta bijimi ne, ko ta tunkiya ce; sai su ba firistoci kafaɗar, kumatun, da kuma kayan cikin.4. Za ku ba su nunan fari na hatsinku, da sabon ruwan inabinku, da manku, da kuma gashi na fari daga askin da kuka yi na tumakinku.5. Gama Ubangiji Allahnku ya zaɓe su da zuriyarsu daga cikin dukan kabilanku don su tsaya su yi hidima a cikin sunan Ubangiji har abada.6. Idan Balawe ya tashi daga wani garinku, wurin da yake da zama a Isra’ila, ya tafi a wurin da Ubangiji ya zaɓa, zai iya dawo a duk lokacin da ya ga dama.7. Zai iya yin hidima a cikin sunan Ubangiji Allahnsa kamar dukan sauran ’yan’uwansa Lawiyawa waɗanda suke hidima a can, a gaban Ubangiji.8. Zai sami rabo daidai da sauran, ko da yake ya karɓi kuɗin mallaka na iyali da ya sayar.9. Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, kada ku kwaikwayi hanyoyin banƙyama na al’ummai da suke can.10. Kada a sami wani a cikinku da ya miƙa ɗansa, ko ’yarsa a wuta, ko a sami mai duba, ko mai maita, ko mai fassara gaibi, ko mai sihiri,11. ko boka, ko mabiya, ko maye, ko mai sha’ani da matattu.12. Duk wanda yake yin waɗannan abubuwa, shi abin ƙyama ne ga Ubangiji, saboda waɗannan abubuwa banƙyama ne kuwa Ubangiji Allahnku ya kori waɗancan al’ummai kafin ku.13. Dole ku zama marasa zargi a gaban Ubangiji Allahnku.14. Al’ummai da za ku kora sukan saurari waɗannan masu maita, ko masu duba. Amma ku, Ubangiji Allahnku bai yarda muku ku yi haka ba.15. Ubangiji Allahnku zai tayar muku da wani annabi kamar ni daga cikin ’yan’uwanku. Dole ku saurare shi.16. Gama abin da kuka nema daga Ubangiji Allahnku ke nan a Horeb, a ranar taro, sa’ad da kuka ce, “Kada ka bari mu ji muryar Ubangiji Allahnmu, ko mu ƙara ganin wuta mai girma, in ba haka ba, za mu mutu.”17. Sai Ubangiji ya ce mini, “Abin da suka faɗa yana da kyau.18. Zan tayar musu da wani annabi kamar ka daga cikin ’yan’uwansu; zan sa kalmomina a cikin bakinsa, zai kuma faɗa musu kome da na umarce shi.19. Duk wanda bai saurari kalmomina da annabin nan yake magana da sunana ba, ni kaina zan nemi hakki a kan mutumin.20. Amma duk annabin da ya ɗauka cewa yana magana da sunana a kan wani abin da ban umarce shi ya faɗa ba, ko kuwa wani annabin da ya yi magana da sunan waɗansu alloli, dole a kashe shi.”21. Mai yiwuwa ku ce wa kanku, “Yaya za mu san cewa wannan saƙo ba Ubangiji ne ya faɗa ba?”22. In abin da annabin ya furta da sunan Ubangiji bai faru ba, ko bai zama gaskiya ba, saƙo ne da Ubangiji bai faɗa ba ke nan. Wannan annabi ya yi rashin hankali ne kawai. Kada ku ji tsoronsa.Zabura 37:37-4037. Ka dubi marasa zargi, ka lura da adali; akwai sa zuciya domin mutum mai salama.38. Amma za a hallaka dukan masu zunubi; za a yanke sa zuciya ta mugaye.39. Ceton adalai kan zo daga Ubangiji; shi ne mafaka a lokacin wahala.40. Ubangiji yakan taimake su yă kuma cece su; yakan kuɓutar da su daga mugaye yă kuma cece su, domin sukan nemi mafaka daga gare shi.Karin Magana 12:20-2220. Akwai ruɗu a zukatan waɗanda suke ƙulla mugunta, amma waɗanda suke aikata alheri za su yi farin ciki.21. Ba wani lahanin da zai sami masu adalci, amma mugaye suna da nasu cike da wahala.22. Ubangiji yana ƙyamar leɓunan masu ƙarya, amma yana jin daɗin mutanen da suke masu gaskiya.Luka 4:1-301. Yesu kuwa cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dawo daga Urdun, Ruhu kuma ya kai shi cikin hamada,2. inda kwana arba’in, Iblis ya gwada shi. Bai ci kome ba a cikin kwanakin nan, a ƙarshensu kuwa ya ji yunwa.3. Iblis ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, ka faɗa wa wannan dutse yă zama burodi.”4. Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba.’ ”5. Iblis ya kai shi can kan wani wuri mai tsawo, ya nunnuna masa a ƙyiftawar ido dukan mulkokin duniya.6. Ya ce masa, “Zan ba ka dukan ikonsu da darajarsu, gama ni aka danƙa wa, kuma zan bai wa duk wanda na ga dama.7. Saboda haka in ka yi mini sujada, dukan wannan zai zama naka.”8. Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, kuma shi kaɗai za ka bauta wa.’ ”9. Sai Iblis, ya kai shi Urushalima ya sa ya tsaya a kan wuri mafi tsayi na haikali ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka yi tsalle daga nan zuwa ƙasa.10. Gama a rubuce yake, “ ‘Zai umarci mala’ikunsa game da kai, su kiyaye ka da kyau;11. za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’ ”12. Yesu ya amsa ya ce, “An ce, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ”13. Da Iblis ya gama dukan wannan gwajin, ya bar shi sai lokacin da wata dama ta samu.14. Yesu ya koma Galili cikin ikon Ruhu. Labarinsa kuwa ya bazu ko’ina a ƙauyuka.15. Ya yi ta koyarwa a majami’unsu, kowa kuwa ya yabe shi.16. Ya tafi Nazaret, inda aka yi renonsa. A ranar Asabbaci kuma, ya shiga majami’a kamar yadda ya saba. Sai ya miƙe don yă yi karatu.17. Aka kuwa ba shi naɗaɗɗen littafin annabi Ishaya. Da ya buɗe, sai ya sami wurin da aka rubuta,18. “Ruhun Ubangiji yana kaina, domin ya shafe ni, in yi wa matalauta wa’azin bishara. Ya aiko ni in yi shelar ’yanci ga ’yan kurkuku, in kuma buɗe idanun makafi, in ba da ’yanci ga waɗanda aka danne.19. In yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji.”20. Sai ya naɗe naɗaɗɗen littafin ya mayar wa mai hidimar, ya kuma zauna. Dukan idanun waɗanda suke a majami’ar, suka koma a kansa.21. Sai ya fara ce musu, “A yau, Nassin nan, ya cika a kunnenku.”22. Duk suka yabe shi, suka yi mamakin kalmomin alheri da suke fitowa daga bakinsa. Suka yi tambaya, suna cewa, “Anya, wannan ba ɗan Yusuf ba ne?”23. Yesu ya ce musu, “Tabbatacce, na san za ku faɗa mini karin maganan nan, ‘Likita, warkar da kanka! Ka kuma yi abin da muka ji ka yi a Kafarnahum, a nan garinka.’ ”24. Ya ci gaba, da ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, babu annabin da ake yarda da shi a garinsa.25. Ina tabbatar muku a zamanin Iliya, akwai gwauraye da yawa a Isra’ila, sa’ad da aka rufe sararin sama har shekara uku da rabi, aka kuma yi yunwa mai tsanani ko’ina a ƙasar.26. Duk da haka, ba a aiki Iliya ga ko ɗaya a cikinsu ba. Sai dai zuwa ga wata gwauruwa da take a Zarefat, a yankin Sidon.27. Akwai kuma mutane da yawa a Isra’ila masu kuturta a zamanin annabi Elisha, amma ba ko ɗayansu da aka tsarkake sai Na’aman mutumin Suriyan nan kaɗai.”28. Dukan mutanen da suke cikin majami’a suka fusata ƙwarai da jin wannan.29. Suka tashi, suka fitar da Yesu bayan gari, suka kai shi goshin tudun da aka gina garin, don su ture shi ƙasa,30. amma sai ya bi ta tsakiyar taron ya yi tafiyarsa. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.