Baibul a cikin shekara guda Maris 5Ƙidaya 7:1-891. Sa’ad da Musa ya gama kafa tabanakul, sai ya shafe shi da mai, ya tsarkake shi tare da dukan kayayyakinsa, ya kuma shafe bagaden da mai, ya tsarkake shi da dukan kayayyakinsa.2. Sa’an nan shugabannin Isra’ila, wato, shugabannin iyalai waɗanda suke shugabancin kabilan da aka ƙidaya, suka miƙa hadayu.3. Suka kawo kyautansu a gaban Ubangiji. Kyautayin kuwa su ne, kekunan yaƙi shida da aka rufe, da shanu goma sha biyu, saniya guda daga kowane shugaba, da kuma keken yaƙi guda daga shugabanni biyu. Suka miƙa waɗannan a gaban tabanakul.4. Ubangiji ya ce wa Musa,5. “Ka karɓi abubuwan nan daga gare su, domin a yi amfani da su a aikin Tentin Sujada. Ka ba da su ga Lawiyawa, a ba kowane mutum bisa ga aikinsa.”6. Haka fa Musa ya ɗauki kekunan yaƙi da shanun ya ba wa Lawiyawa.7. Ya ba wa Gershonawa, kekunan yaƙi biyu da shanu huɗu bisa ga aikinsu,8. ya kuma ya ba wa kabilar Merari kekunan yaƙi huɗu da shanu takwas bisa ga aikinsu. Aka ba da su duka a ƙarƙashin ikon Itamar ɗan Haruna, firist.9. Amma Musa bai ba wa Kohatawa kome ba, gama aikinsu shi ne lura da kayayyaki masu tsarki waɗanda ake ɗauka a kafaɗa.10. Sa’ad da aka shafe bagaden da mai, sai shugabannin suka kawo hadayunsu saboda keɓewarsa, suka miƙa su a bagaden.11. Gama Ubangiji ya riga ya gaya wa Musa cewa, “Kowace rana, shugaba guda zai kawo hadayarsa saboda keɓewar bagade.”12. Wanda ya kawo hadayarsa a rana ta farko shi ne Nashon ɗan Amminadab, shugaban mutanen Yahuda.13. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri ne, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;14. ya kawo kwanon zinariya ɗaya, mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;15. da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;16. ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;17. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Nashon ɗan Amminadab.18. A rana ta biyu, Netanel ɗan Zuwar, shugaban mutanen Issakar, ya kawo hadayarsa.19. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;20. ya kuma kawo kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel, goma cike da turaren hayaƙi;21. da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;22. ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;23. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Netanel ɗan Zuwar.24. A rana ta uku, Eliyab ɗan Helon, shugaban mutanen Zebulun, ya kawo hadayarsa.25. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;26. ya kuma kawo kwanon zinariya ɗaya, mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;27. da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;28. ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;29. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Eliyab ɗan Helon.30. A ranan ta huɗu, Elizur ɗan Shedeyur, shugaban mutanen Ruben, ya kawo hadayarsa.31. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;32. ya kuma kawo kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;33. da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;34. ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;35. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Elizur ɗan Shedeyur.36. A rana ta biyar, Shelumiyel ɗan Zurishaddai, shugaban mutanen Simeyon, ya kawo hadayarsa.37. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;38. ya kuma kawo kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;39. da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;40. ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;41. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Shelumiyel ɗan Zurishaddai.42. A rana ta shida, Eliyasaf ɗan Deyuwel, shugaban mutanen Gad, ya kawo hadayarsa.43. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;44. ya kuma kawo kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;45. da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;46. ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;47. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Eliyasaf ɗan Deyuwel.48. A rana ta bakwai, Elishama ɗan Ammihud, shugaban mutanen Efraim, ya kawo hadayarsa.49. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;50. kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;51. da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;52. ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;53. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Elishama ɗan Ammihud.54. A rana ta takwas, Gamaliyel ɗan Fedazur, shugaban mutanen Manasse, ya kawo hadayarsa.55. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;56. kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;57. da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;58. ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;59. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Gamaliyel ɗan Fedazur.60. A rana ta tara, Abidan ɗan Gideyoni, shugaban mutanen Benyamin, ya kawo hadayarsa.61. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;62. kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;63. da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;64. ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;65. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Abidan ɗan Gideyoni.66. A rana ta goma, Ahiyezer ɗan Ammishaddai, shugaban mutanen Dan, ya kawo hadayarsa.67. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;68. kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;69. da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;70. ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;71. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Ahiyezer ɗan Ammishaddai.72. A rana ta goma sha ɗaya, Fagiyel ɗan Okran, shugaban mutanen Asher, ya kawo hadayarsa.73. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;74. kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;75. da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;76. ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;77. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Fagiyel ɗan Okran.78. A rana ta goma sha biyu, Ahira ɗan Enan, shugaban mutanen Naftali, ya kawo hadayarsa.79. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;80. kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;81. da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;82. ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;83. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Ahira ɗan Enan.84. Waɗannan su ne hadayun shugabannin Isra’ilawa saboda keɓewar bagade sa’ad da aka shafe shi, an kawo faranta goma sha biyu na azurfa, darunan goma sha biyu na azurfa don yayyafawa, da kuma kwanonin zinariya goma sha biyu.85. Kowane faranti na azurfa yana da nauyin shekel ɗari da talatin, kuma kowane daro na azurfa don yayyafawa yana da nauyin shekel saba’in. Duka-duka dai, nauyin kwanonin azurfa, shekel dubu biyu ne da ɗari huɗu, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri.86. Kwanonin zinariya goma sha biyu da aka cika da turaren hayaƙi kuwa, nauyinsu shekel goma ne kowanne, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri. Duka-duka dai, nauyin kwanonin zinariya, shekel ɗari ɗaya ne da ashirin.87. Jimillar dabbobi don hadaya ta ƙonawa, ta kai ƙanana bijimai goma sha biyu, raguna goma sha biyu da ’yan raguna goma sha biyu, dukansu bana ɗaya-ɗaya, tare da hadayarsu ta hatsi. Aka yi amfani da bunsurai goma sha biyu domin hadaya don zunubi.88. Jimillar dabbobi don hadaya ta salama, ta kai shanu ashirin huɗu, raguna sittin, bunsurai sittin da kuma ’yan raguna sittin, dukansu bana ɗaya-ɗaya. Waɗannan su ne hadayu saboda keɓewar bagade, bayan an shafe shi.89. Sa’ad da Musa ya shiga Tentin Sujada don yă yi magana da Ubangiji, sai ya ji murya tana magana da shi daga tsakanin kerubobi biyu a bisa murfin akwatin Alkawari. A ta haka Ubangiji ya yi masa magana.Ƙidaya 8:1-261. Ubangiji ya ce wa Musa,2. “Yi magana da Haruna, ka ce masa, ‘Sa’ad da za ka shisshirya fitilun nan bakwai, ka shirya su yadda za su fuskanci gaba domin haskensu yă haskaka ta gaba.’ ”3. Haka kuwa Haruna ya yi; ya shisshirya fitilun yadda za su fuskanci gaba a kan wurin ajiye fitilan, kamar dai yadda Ubangiji ya umarci Musa.4. Ga yadda aka yi wurin ajiye fitilan. An ƙera shi da zinariya daga gindinsa har zuwa sama inda ya buɗu. Aka ƙera wurin ajiye fitilan yadda Ubangiji ya nuna wa Musa.5. Ubangiji ya ce wa Musa,6. “Keɓe Lawiyawa daga sauran Isra’ilawa, ka tsarkake su.7. Ga yadda za ka tsarkake su, ka yayyafa musu ruwan tsarkakewa; ka sa su aske jikunansu duka su kuma wanke tufafinsu, ta haka za su tsarkake kansu.8. Ka sa su ɗauki ɗan bijimi tare da lallausan garin hadaya, kwaɓaɓɓe da mai; sa’an nan, kai kuma ka ɗauki ɗan bijimi na biyu na hadaya don zunubi.9. Ka kawo Lawiyawa a gaban Tentin Sujada, ka kuma kira taron Isra’ilawa duka.10. Za ka kawo Lawiyawa a gaban Ubangiji, Isra’ilawa kuma za su ɗibiya musu hannuwansu.11. Haruna zai miƙa Lawiyawa a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa daga Isra’ilawa, saboda a shirya su domin aikin Ubangiji.12. “Bayan Lawiyawa sun ɗibiya hannuwansu a kan bijiman, sai ka yi amfani da ɗaya a matsayin hadaya don zunubi ga Ubangiji, ɗayan kuma domin hadaya ta ƙonawa, don yin kafara saboda Lawiyawa.13. Ka kuma sa Lawiyawa su tsaya a gaban Haruna da ’ya’yansa, sai ka miƙa su kamar hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji.14. Da haka za ka keɓe Lawiyawa daga sauran Isra’ilawa, Lawiyawa za su zama nawa.15. “Bayan ka tsarkake Lawiyawa, ka kuma miƙa su kamar hadaya ta kaɗawa, sai su zo su yi aikinsu a Tentin Sujada.16. Gama dukansu an ba ni su daga cikin Isra’ilawa a maimakon dukan waɗanda suka fara buɗe mahaifa, wato, dukan ’ya’yan farin Isra’ilawa. Na karɓi Lawiyawa su zama nawa.17. Kowane ɗan farin haihuwa, ko mutum, ko dabba a Isra’ila, nawa ne. Sa’ad da na kashe ’ya’yan fari a Masar, na keɓe ’ya’yan fari na Isra’ilawa wa kaina.18. Na kuma ɗauki Lawiyawa a maimakon dukan ’ya’yan fari maza a Isra’ila.19. Cikin dukan Isra’ilawa, na ba da Lawiyawa kyauta ga Haruna da ’ya’yansa, su yi hidima a Tentin Sujada a madadin Isra’ilawa, su kuma yi kafara dominsu saboda kada annoba ta bugi Isra’ilawa sa’ad da suka je kusa da wuri mai tsarki.”20. Musa, Haruna da kuma dukan taron Isra’ilawa, suka yi da Lawiyawa yadda Ubangiji ya umarci Musa.21. Lawiyawa suka tsarkake kansu, suka kuma wanke tufafinsu. Sai Haruna ya miƙa su kamar hadaya ta kaɗawa a gaban Ubangiji, ya kuma yi kafara saboda su don yă tsarkake su.22. Bayan haka, sai Lawiyawa suka zo don su yi aikinsu a Tentin Sujada, a ƙarƙashin Haruna da ’ya’yansa. Suka yi da Lawiyawa kamar dai yadda Ubangiji ya umarci Musa.23. Ubangiji ya ce wa Musa,24. “Wannan ya shafi Lawiyawa ne, wato, mazan da suka kai shekara ashirin da biyar, ko fiye, za su zo su yi aiki a Tentin Sujada,25. amma in suka kai shekaru hamsin da haihuwa, dole su huta daga wannan aiki na yau da kullum, su kuma daina aiki.26. Za su iya taimakon ’yan’uwansu cikin tafiyar da ayyuka a Tentin Sujada, amma su kansu ba za su yi aikin ba. Haka fa za ka ba wa Lawiyawa aikinsu.”Zabura 31:1-51. A gare ka, ya Ubangiji, na nemi mafaka; kada ka bari in taɓa shan kunya; ka cece ni cikin rahamarka.2. Ka juye kunnenka gare ni, ka zo da sauri ka cece ni; ka zama dutsen mafakata, mafaka mai ƙarfi na cetona.3. Da yake kai ne dutsena da kuma kagarata, saboda sunanka ka bi da ni ka kuma jagorance ni.4. Ka ’yantar da ni daga tarkon da aka sa mini, gama kai ne mafakata.5. Cikin hannuwanka na miƙa ruhuna; ka cece ni, ya Ubangiji Allah na gaskiya.Karin Magana 11:4-64. Dukiya ba ta da amfani a ranar fushi, amma adalci kan yi ceto daga mutuwa.5. Adalcin marasa laifi kan miƙe hanyarsu, amma akan ƙasƙantar da mugaye ta wurin muguntarsu.6. Adalcin masu aikata gaskiya kan cece su, amma rashin aminci tarko ne ga mugayen sha’awace-sha’awace.Markus 9:1-291. Ya kuma ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, waɗansu da suke tsattsaye a nan ba za su mutu ba, sai sun ga mulkin Allah ya bayyana da iko.”2. Bayan kwana shida, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, Yaƙub da Yohanna tare da shi, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, suka kasance su kaɗai a wurin. A can aka sāke kamanninsa a gabansu.3. Tufafinsa suka zama fari suna ƙyalli, fiye da yadda wani a duniya zai iya yi su.4. Iliya da Musa suka bayyana a gabansu, suna magana da Yesu.5. Bitrus ya ce wa Yesu, “Rabbi, ya yi kyau da muke nan. Bari mu kafa bukkoki guda uku, ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Iliya.”6. (Bai san abin da zai faɗa ba ne, gama sun tsorata ƙwarai.)7. Sai wani girgije ya bayyana, ya rufe su, wata murya kuma ta fito daga girgijen, ta ce, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna, ku saurare shi!”8. Farat ɗaya, da suka waiwaya, ba su ƙara ganin kowa tare da su ba, sai dai Yesu.9. Da suna saukowa daga dutsen, Yesu ya umarce su kada su gaya wa kowa abin da suka gani, sai bayan Ɗan Mutum ya tashi daga matattu.10. Suka riƙe wannan zance a ɓoye tsakaninsu, suna tattaunawa ko mece ce ma’anar “tashi daga matattu.”11. Suka tambaye shi, suka ce, “Don me malaman dokoki suke cewa, sai Iliya ya fara zuwa?”12. Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya ne, Iliya zai zo da fari, yă kuma mayar da dukan abubuwa. Don me kuma aka rubuta cewa, dole Ɗan Mutum yă sha wahala sosai, kuma a ƙi shi?13. Amma ina faɗa muku, Iliya ya riga ya zo, kuma suka yi duk abin da suka ga dama da shi, kamar yadda aka rubuta game da shi.”14. Da suka dawo wurin sauran almajiran, sai suka ga babban taro kewaye da su, malaman dokoki suna gardama da su.15. Nan take da dukan mutanen suka ga Yesu, sai suka cika da mamaki, suka ruga da gudu don su gai da shi.16. Ya tambaye su ya ce, “Gardamar me kuke yi da su?”17. Wani mutum a cikin taron ya amsa ya ce, “Malam, na kawo maka ɗana mai wani ruhun da yake hana shi magana.18. Duk lokacin da mugun ruhun ya kama shi, yakan jefa shi a ƙasa. Bakinsa yakan yi kumfa, yă cije haƙorarsa, yakan sa jikinsa ya sandare, yă zama da ƙarfi. Na roƙi almajiranka su fitar da ruhun, amma ba su iya ba.”19. Yesu ya ce, “Ya ku zamani marar bangaskiya, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron.”20. Sai suka kawo shi. Da ruhun ya ga Yesu, nan da nan sai ya buge yaron da farfaɗiya. Ya fāɗi a ƙasa, yana birgima, bakinsa yana kumfa.21. Yesu ya tambayi mahaifin yaron ya ce, “Tun yaushe yake haka?” Ya ce, “Tun yana ƙarami.22. Ya sha jefa shi cikin wuta, ko ruwa don yă kashe shi. Amma in za ka iya yin wani abu, ka ji tausayinmu ka taimake mu.”23. Yesu ya ce, “ ‘In za ka iya’? Ai, kome mai yiwuwa ne ga wanda ya gaskata.”24. Nan da nan mahaifin yaron ya faɗa da ƙarfi ya ce, “Na gaskata, ka taimake ni in sha kan rashin bangaskiyata!”25. Da Yesu ya ga taron suna zuwa can a guje, sai ya tsawata wa mugun ruhun ya ce, “Kai ruhun kurma, da na bebe, na umarce ka, ka fita daga cikinsa, kada kuma ka ƙara shigarsa.”26. Sai ruhun ya yi ihu, ya buge shi da ƙarfi da farfaɗiya, ya fita. Yaron ya kwanta kamar matacce, har mutane da yawa suka ce, “Ai, ya mutu.”27. Amma Yesu ya kama shi a hannu ya ɗaga, ya kuwa tashi tsaye.28. Da Yesu ya shiga gida, almajiransa suka tambaye shi a ɓoye, suka ce, “Me ya sa ba mu iya fitar da shi ba?”29. Ya amsa ya ce, “Sai da addu’a kaɗai irin wannan yakan fita.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.