Baibul a cikin shekara guda Maris 9Ƙidaya 15:1-411. Ubangiji ya ce wa Musa,2. “Ka yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Bayan kun shiga ƙasar da nake ba ku a matsayin gida,3. kuka yi hadayar da akan yi da wuta ga Ubangiji, daga cikin shanu, ko tumaki, abin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji, ko hadaya ta ƙonawa, ko hadayu don alkawura na musamman, ko hadayar yardar rai, ko kuma hadaya ta biki,4. sai shi wanda ya kawo hadayar yă miƙa wa Ubangiji hadaya ta gari mai laushi mai kyau, kashi ɗaya bisa goma na efa wanda aka kwaɓa da kwalaba ɗaya na mai.5. Da kowane ɗan rago don hadaya ta ƙonawa, a shirya kwalaba ɗaya na ruwan inabi, a matsayin hadaya ta sha.6. “ ‘In da rago ne za a miƙa, to, sai a shirya hadaya ta gari mai laushi, garin yă zama kashi biyu bisa goma na efa. A kwaɓa shi da kashi ɗaya bisa uku na garwan mai,7. da kashi ɗaya bisa uku na garwan ruwan inabi, a matsayin hadaya ta sha. A miƙa ta abin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.8. “ ‘Sa’ad da kuka shirya rago don hadaya ta ƙonawa saboda alkawari na musamman, ko hadaya ta salama ga Ubangiji,9. sai ku kawo hadaya ta gari tare da bijimi, kashi ɗaya bisa uku na gari mai laushi kwaɓaɓɓe da rabin garwan mai.10. A kuma kawo rabin garwan ruwan inabi na hadaya ta sha. Za tă zama hadayar da aka yi da wuta mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.11. Haka za a yi da kowane bijimi, ko rago, ko ɗan rago, ko bunsuru.12. Haka za a yi da kowannensu bisa ga abin da aka shirya.13. “ ‘Duk wanda yake ɗan ƙasa, ta haka ne dole zai aikata waɗannan abubuwa sa’ad da ya kawo hadaya da akan yi da wuta mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.14. Idan baƙon da yake baƙunci a cikinku, ko kowane ne da yake tare da ku a dukan zamananku, yana so yă ba da hadayar da akan yi da wuta don a yi ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji, dole yă yi kamar yadda kuke yi.15. Ƙa’ida ɗaya ce ga jama’a da kuma baƙin da suke zama a cikinku, wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a dukan tsararraki masu zuwa. Da ku, da baƙi, za ku zama ɗaya a gaban Ubangiji.16. Doka ɗaya da ƙa’ida ɗaya za a yi aiki da ita a kan ku da kuma baƙin da suke zama a cikinku.’ ”17. Ubangiji ya ce wa Musa,18. “Ka yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar da ina kai ku,19. kuka ci abincin ƙasar, ku miƙa wani sashe na amfanin ƙasar a matsayin hadaya ga Ubangiji.20. Ku kawo waina daga nunan fari na ɓarzajjen hatsinku, ku kuma miƙa shi a matsayin hadaya daga masussuka.21. A duk tsararraki masu zuwa, za ku miƙa wannan hadaya daga nunan fari na ɓarzajjen hatsinku ga Ubangiji.22. “ ‘To, in ku a matsayin jama’a, da gangan kuka ƙi kiyaye waɗannan ƙa’idodi da Ubangiji ya ba wa Musa ba,23. ko wani daga cikin umarnan da Ubangiji ya ba ku ta wurinsa, daga ranar da Ubangiji ya ba da su, har zuwa tsararraki masu zuwa,24. in kuwa aka yi haka ba da gangan ba, kuma da rashin sani, sai duk jama’a su miƙa ɗan bijimi don hadaya ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, tare da ƙayyadadden hadaya ta gari, da hadaya ta sha, da kuma bunsuru na hadaya don zunubi.25. Firist kuwa zai yi kafara domin dukan jama’ar Isra’ilawa, za a kuma gafarta musu, gama ba da gangan ba ne suka aikata, kuma sun kawo wa Ubangiji hadayar da akan yi da wuta da kuma hadaya don zunubi saboda laifinsu.26. Za a gafarta wa dukan jama’ar Isra’ilawa, da baƙin da suke zama a cikinsu, gama duk laifin da aka yi da rashin sani, yakan shafi dukan mutane.27. “ ‘Amma in mutum ɗaya ne kaɗai ya yi laifi ba da gangan ba, dole yă kawo akuya domin hadaya don zunubi.28. Firist zai yi kafara a gaban Ubangiji saboda mutumin nan da ya aikata laifi ba da gangan ba, in kuwa an yi kafara saboda shi, za a gafarta masa.29. Ƙa’ida dai za tă zama ɗaya ga duk wanda ya yi laifi ba da gangan ba, ko shi ɗan ƙasa ne, ko kuma baƙon da yake zama a cikinku.30. “ ‘Amma duk wanda ya yi zunubi da gangan, ko shi ɗan ƙasa ne, ko baƙo, ya saɓi Ubangiji, dole a ware wannan mutum daga mutanensa,31. gama ya rena maganar Ubangiji, ya kuma karya umarninsa. Tabbatacce za a kashe wannan mutum, alhakinsa laifinsa kuwa yana wuyansa.’ ”32. Yayinda Isra’ilawa suke ciki hamada, sai aka sami wani mutum yana tattara itace a ranar Asabbaci.33. Waɗanda suka gan shi, suka kawo shi wurin Musa da Haruna da dukan taro,34. sai suka sa shi a gidan waƙafi don ba su riga sun san abin da za a yi da shi ba tukuna.35. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Dole mutumin yă mutu. Dole dukan taron su jajjefe shi a bayan sansani.”36. Saboda haka taron suka ɗauke shi zuwa bayan sansani, suka kuma jajjefe shi har ya mutu, yadda Ubangiji ya umarci Musa.37. Ubangiji ya ce wa Musa,38. “Ka yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘A dukan tsararraki masu zuwa, za ku sa tuntaye a gefen rigunarku, su sa zare mai ruwan shuɗi a bisan kowane tuntu.39. Tuntayen za su zama muku abin dubawa don ku riƙa tunawa da dukan umarnan Ubangiji, don kada ku bi son zuciyarku, da sha’awar idanunku yadda kuka taɓa yi.40. Sa’an nan za ku riƙa tuna, ku kuma aikata dukan umarnaina ku zama tsarkaka ga Allahnku.41. Ni ne Ubangiji Allahnku, da ya fitar da ku daga Masar, don in zama Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.’ ”Ƙidaya 16:1-351. Kora ɗan Izhar, wanda yake Balawe ne daga dangin Kohatawa, wata rana ya nemi Datan da Abiram ’ya’yan Eliyab, da On ɗan Felet dukansu daga kabilar Ruben, suka haɗa kai2. suka tayar wa Musa. Sai suka nemi goyon bayan sanannun shugabannin Isra’ilawa da aka naɗa a majalisa su guda 250,3. tare kuwa suka zo wurin Musa da Haruna, suka ce musu, “Kun wuce gona da iri! Dukan jama’an nan masu tsarki ne, kowannensu, Ubangiji kuma yana tare da su. Me ya sa kuke ɗaukan kanku fiye da taron jama’ar Ubangiji?”4. Da Musa ya ji haka, sai ya fāɗi rubda ciki ya yi addu’a5. Sai ya ce wa Kora da dukan waɗannan da suke tare shi, “Da safe, Ubangiji zai nuna wane ne yake nasa, da kuma wane ne yake da tsarki. Zai kuma sa mutumin yă zo kusa da shi. Mutumin da ya zaɓa kuwa zai sa yă zo kusa da shi.6. Kai Kora da ƙungiyarka, gobe, za ku ɗauki farantai,7. ku zuba wuta a ciki, ku kuma zuba musu turaren wuta a gaban Ubangiji. Sa’an nan wanda Ubangiji ya zaɓa a tsakaninmu sh ne mai tsarki. Ku Lawiyawa ku ne kuka wuce gona da iri!”8. Musa ya kuma ce wa Kora, “Yanzu ku saurara, ku Lawiyawa!9. Ashe, bai ishe ku ba, cewa Allah na Isra’ila, ya keɓe ku daga sauran jama’ar Isra’ilawa, ya kuma kawo ku kusa da shi don ku yi aiki a tabanakul na Ubangiji, ku kuma tsaya a gaba jama’a don ku yi musu aiki?10. Ya kawo ku da kuma dukan ’yan’uwanku Lawiyawa kusa da shi, amma yanzu kuna ƙoƙari ku karɓi aikin firist.11. Kai da ƙungiyarka kun haɗa kai kuna yi wa Haruna gunaguni, amma wane ne Haruna? A zahiri tawaye ne kuke wa Ubangiji.”12. Sai Musa ya aika a kira Datan da Abiram, ’ya’yan Eliyab maza, amma suka ce, “Ba za mu zo ba!13. Bai isa ba ne da ka fitar da mu daga ƙasar mai zub da madara da zuma, ka kawo mu nan hamada don ka kashe mu? Yanzu kuma so kake ka mai da kanka sarki a bisanmu?14. Ban da haka ma, ai, ba ka riga ka kai mu ƙasar mai zub da madara da zuma ba, ba ka ba mu gādon filaye da gonakin annabi ba, yanzu kuma kana so ka ruɗe mu. Mun ƙi, ba za mun zo ba!”15. Sai Musa ya husata ƙwarai, ya ce wa Ubangiji, “Kada ka karɓi hadayarsu. Ban ƙwace wani jakinsu ba, ban kuwa cuce waninsu ba.”16. Musa ya ce wa Kora, “Da kai da kuma dukan ƙungiyarka za ku bayyana a gaban Ubangiji gobe, kai da su. Haruna ma zai kasance a can.17. Kowannenku zai ɗauki faranti yă zuba turare a ciki. Wato, farantai 250 ke nan, a kuma miƙa su a gaban Ubangiji. Kai da Haruna za ku miƙa farantanku, ku ma.”18. Sai kowane mutum ya ɗauki farantinsa, ya sa wuta da kuma turare a ciki, suka tsaya da Musa da Haruna a ƙofar Tentin Sujada.19. Sa’ad da Kora ya tara mabiyansa don su yi hamayya da Musa da Haruna a ƙofar Tentin Sujada, sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana ga dukan taron.20. Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,21. “Ku ware kanku daga taron nan don in gama da su nan take.”22. Amma Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki suka tā da murya suka ce, “Ya Allah, Allahn ruhohin dukan ’yan adam, za ka husata da dukan taron ne, bayan mutum ɗaya ne ya yi zunubi?”23. Sai Ubangiji ya ce wa Musa,24. “Faɗa wa taron cewa, ‘Ku nisanci tentin Kora, da na Datan, da na Abiram.’ ”25. Musa ya tashi ya tafi wurin Datan da Abiram, dattawan Isra’ilawa kuwa suka bi shi.26. Ya gargaɗe taron ya ce, “Ku ƙaurace wa tentin waɗannan mugayen mutane! Kada ku taɓa kome da yake nasu, domin kada a shafe ku saboda zunubansu.”27. Sai suka tashi daga inda tentin Kora, da Datan, da Abiram suke. Datan da Abiram kuwa suka fita suna tsaye tare da matansu da ’ya’yansu da ’yan ƙananansu a ƙofar tentinsu.28. Sai Musa ya ce musu, “Da haka za ku san cewa Ubangiji ne ya aiko ni, in yi dukan waɗannan abubuwa, ba da nufin kaina na yi su ba.29. In waɗannan mutane sun mutu kamar yadda mutane suke mutuwa, in abin da yakan sami kowa shi ne ya same su, to, ba Ubangiji ne ya aiko ni ba.30. Amma in Ubangiji ya kawo wani abu sabo, ya sa ƙasa ta buɗe bakinta, ta haɗiye su da dukan abin da suke da shi, suka gangara cikin kabari a raye, ta haka za ku sani mutanen nan sun rena Ubangiji.”31. Nan da nan da ya gama faɗi wannan, sai ƙasa ta tsage inda Datan da Abiram suke tsaye,32. ta kuma buɗe bakinta, ta haɗiye su tare da mutanen gidansu da dukan mutanen Kora da dukan abin da yake mallakarsu.33. Suka gangara cikin kabari da rai, tare dukan mallakarsu; ƙasa ta rufe su, suka hallaka, suka rabu da jama’ar.34. Da jin kukansu, dukan Isra’ilawa da suke kewaye da su suka gudu, suna ihu, “Ƙasa za tă haɗiye mu, mu ma!”35. Sai wuta ta fito daga wurin Ubangiji ta cinye mutane 250 da suke miƙa hadaya da turare.Zabura 32:1-51. Mai farin ciki ne shi wanda aka gafarta masa laifofinsa, wanda aka shafe zunubansa.2. Mai farin ciki ne mutumin da Ubangiji ba ya lissafin zunubinsa a kansa wanda kuma babu ruɗu a ruhunsa.3. Sa’ad da na yi shiru, ƙasusuwana sun yi ta mutuwa cikin nishina dukan yini.4. Gama dare da rana hannunka yana da nauyi a kaina; an shanye ƙarfina ƙaf sai ka ce a zafin bazara.5. Sa’an nan na furta zunubina a gare ka ban kuwa ɓoye laifina ba. Na ce, “Zan furta laifofina ga Ubangiji.” Ka kuwa gafarta laifin zunubina.Karin Magana 11:16-1816. Mace mai hankali na samu bangirma, amma azzalumai za su sami dukiya.17. Mutumin kirki kan ribance kansa, amma mugu kan kawo wa kansa wahala.18. Mugun mutum kan sami albashin ƙarya amma shi da ya shuka adalci zai girbe lada tabbatacce.Markus 11:1-191. Sa’ad da suka yi kusa da Urushalima, suka zo Betfaji da Betani wajen Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki biyu daga cikin almajiransa,2. ya ce musu, “Ku je ƙauyen da yake gaba da ku, da shigarku, za ku tarar da wani ɗan jaki a daure a can, wanda ba wanda ya taɓa hawa. Ku kunce shi ku kawo nan.3. In wani ya tambaye ku, ‘Don me kuke yin haka?’ Ku gaya masa cewa, ‘Ubangiji yana bukatarsa, zai kuma dawo da shi ba da jimawa ba.’ ”4. Suka tafi, suka kuwa tarar da wani ɗan jaki a waje, a titi, daure a ƙofar gida. Suna cikin kunce shi ke nan,5. sai waɗansu mutane da suke tsattsaye a wurin suka ce musu, “Me kuke yi da kuke kunce ɗan jakin nan?”6. Suka amsa kamar yadda Yesu ya ce su yi. Mutanen kuwa suka ƙyale su.7. Da suka kawo shi wajen Yesu, sai suka shimfiɗa rigunarsu a bayansa. Yesu kuwa ya hau ya zauna bisansa.8. Mutane da yawa suka shimfiɗa rigunarsu a kan hanya, waɗansu kuma suka baza rassan itatuwan da suka sara daga gonaki.9. Waɗanda suka yi gaba, da kuma waɗanda suke biye, duk suka ɗaga murya, suna cewa, “Hosanna! ” “Mai albarka ne wanda yake zuwa a cikin sunan Ubangiji!”10. “Mai albarka ne mulkin nan mai zuwa na mahaifinmu Dawuda!” “Hosanna a can cikin samaniya!”11. Yesu ya shiga Urushalima ya kuma tafi filin haikali. Ya dudduba kome duka, amma da yake yamma ta yi, sai ya tafi Betani tare da Sha Biyun.12. Kashegari, da suke barin Betani, Yesu kuwa ya ji yunwa.13. Da ya hangi wani itacen ɓaure mai ganye, sai ya je domin yă ga ko yana da ’ya’ya. Amma da ya kai can, bai tarar da kome ba sai ganye, domin ba lokacin ’ya’yan ɓaure ba ne.14. Sai ya ce wa itacen, “Kada kowa yă ƙara cin ’ya’yanka.” Almajiransa kuwa suka ji ya faɗi haka.15. Da suka kai Urushalima, sai Yesu ya shiga filin haikalin, ya fara korar waɗanda suke saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur na masu musayar kuɗi, da kujerun masu sayar da tattabaru,16. ya kuma hana kowa yă ratsa da a filin haikali ɗauke da kayan ciniki.17. Da yake koya musu, sai ya ce, “Ashe, ba a rubuce yake ba cewa, ‘Za a kira gidana, gidan addu’a na dukan al’ummai ba’? Amma ga shi kun mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’ ”18. Manyan firistoci da malaman dokoki suka ji wannan, sai suka fara neman hanyar da za su kashe shi, gama suna jin tsoronsa, saboda dukan taron suna mamakin koyarwarsa.19. Da yamma ta yi, sai Yesu da almajiransa suka bar garin. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.