Baibul a cikin shekara guda Afrilu 10Yoshuwa 9:1-271. To, sa’ad da dukan sarakunan yammancin Urdun suka ji waɗannan abubuwa, sai waɗanda suke kan tudu, da na cikin kwari a yammanci, da dukan waɗanda suke gefen Bahar Rum har zuwa Lebanon (sarakunan Hittiyawa, Amoriyawa, Kan’aniyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa)2. suka haɗa kansu don su yaƙi Yoshuwa da Isra’ila.3. Amma da mutanen Gibeyon suka ji abin da Yoshuwa ya yi wa Yeriko da Ai,4. sai suka shirya wata dabara ta ruɗu, suka shirya ɗan abinci don tafiya, suka ɗauki tsofaffin buhuna a kan jakunansu da tsofaffin salkuna na ruwan inabi, yagaggu da suka sha ɗinki.5. Suka sa tsofaffin takalman da suka sha gyara, suka sa tsofaffin tufafi. Dukan abincinsu na tafiya ya bushe ya yi fumfuna.6. Sai suka je wurin Yoshuwa a sansanin Gilgal suka ce masa da mutanen Isra’ila, “Daga ƙasa mai nisa muka fito, yanzu fa, sai ku yi alkawari da mu.”7. Mutanen Isra’ila kuwa suka ce wa Hiwiyawa, “Wataƙila kuna kusa da mu, ta yaya za mu yi alkawari da ku?”8. Suka ce wa Yoshuwa, “Mu bayinku ne.” Amma Yoshuwa ya tambaye su ya ce, “Ku wane ne, kuma daga ina kuka zo?”9. Suka amsa suka ce, “Bayinka sun zo ne daga ƙasa mai nisa gama Ubangiji Allahnka ya yi suna sosai. Gama mun ji labarin abubuwan da ya yi. Dukan abubuwan da ya yi a Masar10. da kuma duk abubuwan da ya yi wa sarakuna biyu na Amoriyawa gabas da Urdun, Sihon sarkin Heshbon, da Og sarkin Bashan wanda ya yi mulki a Ashtarot.11. Dattawanmu da duk mazaunan ƙasar, suka ce mana, ‘Ku ɗauki abincin tafiyar da za ku riƙe; ku je ku same su ku ce musu, “Mu bayinku ne, ku yi alkawari da mu.” ’12. Abincin tafiyan nan namu yana da ɗumi lokacin da muka kintsa tashi daga gida a ranar da za mu kama hanya zuwa wurinku. Amma yanzu duba yadda ya bushe, ya yi fumfuna.13. Waɗannan salkuna kuma da muka cika ruwan inabi, sababbi ne amma duba yadda suka yayyage. Tufafinmu da takalmanmu duk sun yayyage don doguwar tafiya.”14. Mutanen Isra’ila suka ɗiba daga cikin abincin tafiyar amma ba su nemi nufin Ubangiji ba.15. Sa’an nan Yoshuwa ya yi alkawari zaman salama da su, cewa ba zai kashe su ba, sai shugabannin mutanen Isra’ila kuwa suka tabbatar musu da haka ta wurin yin rantsuwa.16. Kwana uku bayan sun yi alkawari da Gibeyonawa, sai Isra’ilawa suka ji cewa Gibeyonawa maƙwabtansu ne, waɗanda suke zaune kurkusa da su.17. Saboda haka Isra’ilawa suka tashi a rana ta uku suke je biranen mutanen, wato, Gibeyon, Kefira, Beyerot da Kiriyat Yeyarim.18. Amma Isra’ilawa ba su kai musu hari ba domin shugabanninsu sun rantse musu da sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila. Mutane Isra’ila duka kuwa suka yi gunaguni a kan shugabannin.19. Amma shugabanni suka amsa musu suka ce, “Mun rantse musu da sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila, saboda haka ba za mu taɓa su ba yanzu.20. Ga abin da za mu yi musu, za mu bar su da rai don kada fushin Allah yă sauka a kanmu gama mun riga mun rantse musu.”21. Suka ƙara da cewa, “Mu bar su da rai, amma bari su zama masu yankan itace da masu ɗibo mana ruwa.” Haka shugabannin suka cika alkawarinsu.22. Yoshuwa kuwa ya aika aka kira Gibeyonawa ya ce musu, “Don me kuka ruɗe mu kuka ce, ‘Mun zo ne daga wuri mai nisa,’ bayan kuwa kuna nan kurkusa da mu?23. Yanzu ku la’anannu ne. Ba za ku daina zama mana masu yankan itace da kuma masu ɗebo ruwa domin haikalin Allahnmu ba.”24. Suka amsa wa Yoshuwa suka ce, “An gaya wa bayinka dalla-dalla yadda Ubangiji Allahnka ya umarci bawansa Musa yă ba ka ƙasar duka, ka kuma kashe duk masu zama a cikinta, muka ji tsoro cewa za ka kashe mu shi ya sa muka yi haka.25. Yanzu, a hannunka muke, ka yi duk abin da ka ga ya yi maka kyau.”26. Yoshuwa kuwa ya cece su daga hannun Isra’ilawa, har ba su kashe su ba.27. A ranar Yoshuwa ya sa Gibeyonawa suka zama masu yankan itace da ɗebo ruwa wa jama’ar Isra’ila da kuma domin haikalin Ubangiji a inda Ubangiji zai zaɓa. Abin da suke ke nan har wa yau.Yoshuwa 10:1-431. Adoni-Zedek sarkin Urushalima ya ji cewa Yoshuwa ya ci Ai da yaƙi ya kuma hallaka ta sarai, ya yi wa Ai da sarkinta abin da ya yi wa Yeriko da sarkinta, mutanen Gibeyon kuwa sun yi yarjejjeniya ta salama da Isra’ilawa, suna kuma zama kusa da su.2. Shi da mutanensa suka ji tsoron wannan sosai, gama Gibeyon muhimmiyar birni ce, har ma kamar ɗaya daga cikin biranen sarauta, ya ma fi Ai girma, mazanta duka kuwa mayaƙa ne na ƙwarai.3. Saboda haka sai Adoni-Zedek sarkin Urushalima ya roƙi Hoham sarkin Hebron, Firam sarkin Yarmut, Yafiya sarkin Lakish da Debir sarki Eglon ya ce,4. “Ku zo ku taimake ni in kai wa Gibeyon hari. Domin sun yi yarjejjeniya ta salama da Yoshuwa da Isra’ilawa.”5. Sai sarakunan nan biyar na Amoriyawa, sarakunan Urushalima, Hebron, Yarmut, Lakish da Eglon suka haɗa sojojinsu. Suka je dukansu suka yi shirin kai wa Gibeyon hari.6. Sai mutanen Gibeyon suka aika zuwa wurin Yoshuwa a sansani a Gilgal, “Kada ka juya wa bayinka baya, ka zo da sauri ka cece mu! Ka taimake mu domin sarakunan Amoriyawa duka daga kan tudu sun haɗa ƙarfinsu tare za su tasar mana.”7. Saboda haka Yoshuwa ya tashi da rundunarsa duka, tare da dukan jarumawansa.8. Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Kada ka ji tsoronsu; na ba ka su a hannunka. Ba waninsu da zai iya tsayayya da kai.”9. Bayan sun yi tafiya dukan dare daga Gilgal, Yoshuwa ya auko musu ba labari.10. Ubangiji ya sa suka ruɗe a gaban Isra’ilawa, Isra’ilawa kuwa suka yi babbar nasara a kansu a Gibeyon. Isra’ilawa suka fafare su a kan hanyar zuwa Bet-Horon suka karkashe su duka har zuwa Azeka da Makkeda.11. Suna guje wa Isra’ilawa suna gangarawa a kan hanyar Bet-Horon har zuwa Azeka, sai Ubangiji ya turo manyan duwatsu daga sararin sama suka karkashe su, waɗanda manyan duwatsun suka kashe sun fi waɗanda Isra’ilawa suka kashe da takobi.12. A ranar da Ubangiji ya ba da Amoriyawa a hannun Isra’ilawa, Yoshuwa ya ce wa Ubangiji a gaban Isra’ilawa, “Ke rana, ki tsaya cik a Gibeyon Kai wata, ka je Kwarin Aiyalon.”13. Sai rana ta tsaya cik, wata kuma ya tsaya, har sai da al’ummar ta ɗauki fansa a kan abokan gābanta, kamar yadda aka rubuta a cikin littafin Yashar. Rana ta tsaya a sararin sama, ba tă fāɗi ba har kusan yini guda.14. Ba a taɓa ganin abu haka ba ko dā can, ranar da Ubangiji ya saurari mutum. Ba shakka Ubangiji yana yaƙi domin Isra’ilawa.15. Sai Yoshuwa ya koma sansanin Gilgal tare da dukan Isra’ilawa.16. Sarakunan guda biyar suka gudu, suka ɓuya a cikin kogo a Makkeda.17. Lokacin da aka gaya wa Yoshuwa cewa an sami sarakunan nan biyar a ɓoye a cikin kogo a Makkeda.18. Sai ya ce, “Ku mirgina manyan duwatsu ku rufe bakin kogon, sai ku sa waɗannan mutane su yi tsaron kogon.19. Amma kada ku tsaya a can! Ku fafari abokan gābanku, ku kai musu hari ta baya, kada ku bari su kai biranensu, gama Ubangiji Allahnku ya ba da su a hannunku.”20. Saboda haka Yoshuwa da Isra’ilawa suka hallaka su da yawa ƙwarai, amma ’yan kaɗan ɗin da suka rage suka tsere zuwa cikin biranensu masu kāriya.21. Dukan rundunar kuma suka dawo sansanin Makkeda tare da Yoshuwa, ba abin da ya same su. Ba wanda ya sāke tsokanar Isra’ilawa.22. Yoshuwa ya ce, “Ku buɗe bakin kogon ku kawo mini sarakunan nan guda biyar.”23. Sai suka kawo sarakunan biyar daga cikin kogo; sarakunan Urushalima, Hebron, Yarmut, Lakish da Eglon.24. Sa’ad da aka kawo sarakunan nan wurin Yoshuwa, ya kira dukan Isra’ilawa ya ce wa shugabannin rundunoni waɗanda suke tare da shi, “Ku zo nan ku taka wuyan sarakunan nan.” Sai suka zo suka taka wuyansu.25. Yoshuwa ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ko kuwa ku razana, amma ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Haka Ubangiji zai yi da duk abokan gāban da za ku yi yaƙi da su.”26. Sai Yoshuwa ya karkashe waɗannan sarakuna guda biyar, ya kuma rataye kowannensu a bisa itace inda jikunansu suka kasance har yamma.27. Da yamma Yoshuwa ya ba da umarni a sauko da su daga itatuwan a jefa su cikin kogon da suka ɓuya. Aka sa manyan duwatsu aka rufe bakin kogon, suna a can har wa yau.28. A ranan nan Yoshuwa ya ci Makkeda da yaƙi. Ya karkashe mutanen tare da sarkinta. Bai bar wani da rai ba. Ya yi wa sarkin Makkeda yadda ya yi wa sarkin Yeriko.29. Sai Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka tashi daga Makkeda zuwa Libna, suka kai mata hari.30. Ubangiji kuma ya ba da ƙasar da sarkinta a hannun Yoshuwa. Yoshuwa ya karkashe kowa ya hallaka birnin, bai bar wani da rai ba. Ya kuma yi wa sarkin yadda ya yi wa sarkin Yeriko.31. Sai Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka tashi daga Libna zuwa Lakish; suka yi shiri suka kai mata hari.32. Ubangiji ya ba da Lakish a hannun Isra’ilawa, a rana ta biyu kuwa Yoshuwa ya ci nasara a kansu. Ya karkashe duk mutanen birnin ya kuma hallaka birnin, kamar yadda ya yi a Libna.33. Horam sarkin Gezer kuwa ya zo don yă taimaki Lakish, amma Yoshuwa ya haɗa duk da shi da rundunarsa ya ci su da yaƙi, har bai bar waninsu da rai ba.34. Yoshuwa kuwa da dukan Isra’ilawa suka tashi daga Lakish zuwa Eglon; suka yi shiri suka kai mata hari.35. A ranan nan suka ci ƙasar da yaƙi, suka buge ta, suka karkashe kowa da takobi kamar dai yadda suka yi a Lakish.36. Sai Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka tashi daga Eglon zuwa Hebron suka kai hari a can.37. Suka ci birnin da yaƙi, suka karkashe mazaunanta, da sarkin, har da ƙauyukan, ba wanda ya tsira kamar yadda ya yi wa Eglon. Ya hallakar da ita sarai duk da kowane mutum da yake cikinta.38. Yoshuwa da Isra’ilawa duka suka juya suka kai wa Debir hari,39. suka hallaka birnin, da sarkinta da ƙauyukanta, suka karkashe dukan mazaunan wurin, ba su bar wani da rai ba. Suka yi wa Debir da sarkinta yadda suka yi wa Libna da sarkinta da kuma Hebron.40. Yoshuwa ya cinye yankin duka da yaƙi, haɗe da na kan tudu, da Negeb, da kwarin yamma, da filayen cikin duwatsu tare da sarakunansu duka. Bai bar wani da rai ba, ya kashe duk wani mai numfashi, yadda Ubangiji, Allah na Isra’ilawa ya umarta.41. Yoshuwa ya ci su da yaƙi daga Kadesh Barneya zuwa Gaza, da kuma daga dukan yankin Goshen zuwa Gibeyon.42. Yoshuwa kuwa ya cinye sarakunan nan duka da ƙasashensu gaba ɗaya gama Ubangiji, Allah na Isra’ila ne ya yi yaƙi domin Isra’ilawa.43. Yoshuwa kuwa ya dawo da dukan Isra’ilawa zuwa sansani a Gilgal.Zabura 44:1-31. Mun ji da kunnuwanmu, ya Allah; kakanninmu sun faɗa mana abin da ka aikata a kwanakinsu, tun dā can.2. Da hannunka ka kori al’ummai ka kuma dasa kakanninmu; ka ragargaza mutanen ka kuma sa kakanninmu suka haɓaka.3. Ba da takobinsu ba ne suka ci ƙasar, ba kuwa ƙarfin hannunsu ne ya ba su nasara ba; hannun damanka ne, ƙarfin hannunka, da kuma hasken fuskarka, gama ka ƙaunace su.Karin Magana 13:24-2524. Duk wanda ba ya horon ɗansa ba ƙaunarsa yake yi ba, amma duk mai ƙaunarsa yakan kula ya hore shi.25. Masu adalci sukan ci isashen abinci, amma cikin mugaye na fama da yunwa.Luka 10:1-241. Bayan haka, Ubangiji ya naɗa waɗansu mutum saba’in da biyu, ya aike su biyu-biyu, su riga shi yin gaba zuwa kowane gari da kowane wuri da zai shiga.2. Ya ce musu, “Girbi na da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne. Saboda haka, ku roƙi Ubangijin girbi ya aikar da ma’aikata zuwa gonarsa.3. Ku tafi! Ina aikan ku kamar tumaki cikin kyarketai.4. Kada ku ɗauki jakar kuɗi, ko jaka, ko takalma. Kada ma ku gai da kowa a kan hanya.5. “Sa’ad da kuka shiga wani gida, ku fara da cewa, ‘Salama a gare ku mutanen gida.’6. In akwai mutum mai salama a gidan, salamarku za tă kasance tare da shi, in kuwa babu, salamarku za tă koma muku.7. Ku zauna a wannan gidan, kuna ci kuna shan duk abin da suka ba ku, gama ma’aikaci ya cancanci albashinsa. Kada ku yi yawan sāke masauƙi, daga gida zuwa gida.8. “Sa’ad da kuka shiga garin, kuma aka karɓe ku, ku ci ko mene ne da aka ajiye a gabanku.9. Ku warkar da marasa lafiya da suke wurin. Ku kuma faɗa musu cewa, ‘Mulkin Allah yana kusa da ku.’10. Amma sa’ad da kuka shiga garin, kuma ba a karɓe ku ba, ku bi titi-titi ku ce,11. ‘Ko ƙurar garinku da kuke manne a ƙafafunmu, mun karkaɗe muku. Duk da haka, ku tabbatar da wannan, “Mulkin Allah yana kusa.” ’12. Ina dai faɗa muku, a ranan nan, za a fi jin tausayin Sodom fiye da wannan garin.13. “ ‘Kaitonki, Korazin! Kaitonki, Betsaida!’ Ai, da a ce a Taya da Sidon ne aka yi ayyukan banmamaki da aka yi a cikinku, da tuni sun tuba, suna zama cikin rigar makoki da toka.14. A ranar shari’a, za a fi jin tausayin Taya da Sidon fiye da ku.15. Ke kuma Kafarnahum, kina tsammani za ki sami ɗaukaka ne? A’a, za a hallaka ki.16. “Wanda ya saurare ku, ni yake saurara. Wanda ya ƙi ku, ni yake ƙi. Amma wanda ya ƙi ni kuwa, ya ƙi wanda ya aiko ni ne.”17. Mutum saba’in da biyun nan suka dawo da murna, suka ce, “Ubangiji, har mun sha ƙarfin aljanu ma a cikin sunanka.”18. Sai ya amsa ya ce, “Na ga Shaiɗan ya fāɗi daga sama kamar walƙiya.19. Na ba ku iko da za ku tattaka macizai, da kunamai, ku kuma shawo kan dukan ikon abokin gāba, kuma ba wani lahani da zai same ku.20. Duk da haka, kada ku yi farin ciki da cewa, kun sha ƙarfin ruhohi, amma ku yi farin ciki, domin an rubuta sunayenku a sama.”21. A wannan lokaci, Yesu, cike da murna ta wurin Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Na yabe ka, ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan abubuwa ga masu hikima, da masu ilimi, ka kuma bayyana su ga ƙananan yara. I, ya Uba, gama wannan shi ne nufinka mai kyau.22. “Ubana ya danƙa mini dukan kome. Ba wanda ya san Ɗan sai Uban, kuma ba wanda ya san Uban, sai Ɗan, da kuma waɗanda Ɗan ya zaɓa ya bayyana musu shi.”23. Sai ya juya wajen almajiransa, ya ce musu a ɓoye, “Albarka ga idanun da suka ga abin da kuke gani.24. Ina faɗa muku, annabawa da sarakuna da yawa sun so su ga abin nan da kuke gani, amma ba su gani ba. Sun so su ji abin da kuke ji, amma ba su ji ba.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.