Baibul a cikin shekara guda Afrilu 11Yoshuwa 11:1-231. Sa’ad da Yabin sarkin Hazor ya ji wannan, sai ya aika saƙo zuwa wurin Yobab sarkin Madon, da sarkin Shimron, da Akshaf,2. ya kuma aika zuwa ga sarakunan arewa waɗanda suke kan tuddai da kuma waɗanda suke cikin Araba a kudancin Kinneret da cikin filayen kwari, da cikin Nafot Dor a yamma;3. ya kuma aika zuwa ga Kan’aniyawa a gabas da yamma; da kuma zuwa ga Amoriyawa, Hittiyawa da Ferizziyawa, da Yebusiyawa da suke kan tuddai; da kuma Hiwiyawa masu zama a gindin dutsen Hermon a yankin Mizfa.4. Suka fito da dukan rundunansu da keken yaƙi masu yawan gaske, babbar runduna, yawansu ya yi kamar yashin bakin teku.5. Duk sarakunan nan suka haɗa mayaƙansu tare, suka kafa sansani a bakin Ruwayen Meron don su yi yaƙi da Isra’ilawa.6. Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Kada ka ji tsoronsu, domin war haka gobe zan ba da dukansu a hannun Isra’ilawa, za su kuwa karkashe su. Za ku gurgunta dawakansu, ku kuma ƙone keken yaƙinsu.”7. Sai Yoshuwa da dukan mayaƙan suka auka musu a bakin Ruwayen Meron.8. Ubangiji kuwa ya ba Isra’ilawa nasara a kan su, suka ci su da yaƙi, suka fafare su har zuwa Sidon Babba, zuwa Misrefot Mayim, har zuwa Kwarin Mizfa a gabas, ba wanda suka bari da rai.9. Yoshuwa ya yi musu yadda Ubangiji ya umarta, ya gurgunta dawakansu, ya kuma ƙone keken yaƙinsu.10. A lokacin nan Yoshuwa ya koma da baya ya ci Hazor da yaƙi, ya kuma kashe sarkinta da takobi. (Hazor ce babbar masarautan ƙasashen nan.)11. Suka karkashe duk mazaunan ƙasar da takobi, ba su bar wani mai numfashi ba, suka kuma ƙona Hazor.12. Yoshuwa ya ƙwace masarautun nan duka ya kuma kashe sarakunansu da takobi, ya hallakar da su ƙaƙaf kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya umarta.13. Duk da haka Isra’ilawa ba su ƙone biranen da suke kan tuddai ba, sai Hazor kaɗai Yoshuwa ya ƙone.14. Isra’ilawa suka kwashi ganima da dabbobi na waɗannan birane, amma suka karkashe mutanen duka da takobi, ba su bar wani mai numfashi ba.15. Yadda Ubangiji ya umarci bawansa Musa, haka Musa ya umarci Yoshuwa, shi kuwa ya yi duk abin da Ubangiji ya umarci Musa.16. Saboda haka Yoshuwa ya cinye ƙasar duka da yaƙi, dukan Negeb, duka yankin Goshen, filayen kwari na yamma, Araba da tuddai na Isra’ila da kwarinta.17. Daga Dutsen Halak wanda ya miƙe zuwa wajajen Seyir, zuwa Ba’al-Gad a Kwarin Lebanon ƙasa da Dutsen Hermon. Ya kama sarakunansu ya karkashe su.18. Yoshuwa ya daɗe yana yaƙi da dukan waɗannan sarakuna.19. Sai Hiwiyawa kaɗai waɗanda suke zama a Gibeyon, sauran ba ko birni ɗaya da ta yi yarjejjeniya ta salama da Isra’ilawa, Isra’ilawa kuwa suka ci dukansu da yaƙi.20. Gama Ubangiji ne ya taurare zukatansu waɗannan sarakuna suka yi yaƙi da Isra’ilawa don yă hallaka su gaba ɗaya, yă gamar da su ba jinƙai, yadda Ubangiji ya umarci Musa.21. A lokacin nan Yoshuwa ya je ya hallaka Anakawa daga ƙasar tudu. Daga Hebron, Debir da Anab. Daga dukan ƙasar tuddai na Yahuda, da kuma dukan ƙasar tudu ta Isra’ila, Yoshuwa ya hallaka su duka da garuruwansu.22. Ba a bar waɗansu Anakawa a harabar Isra’ila ba; sai dai a Gaza, Gat da Ashdod ne aka samu waɗanda suka ragu da rai.23. Yoshuwa kuwa ya ƙwace dukan ƙasar yadda Ubangiji ya umarci Musa, ya ba da ita ta zama ƙasar gādo ga Isra’ilawa, kabila-kabila. Ta haka ƙasar ta huta daga yaƙi.Yoshuwa 12:1-241. Waɗannan su ne sarakunan ƙasashen da Isra’ilawa suka ci da yaƙi, suka kuma mallaki ƙasarsu a gabashin Urdun, daga kwarin Arnon zuwa Dutsen Hermon haɗe da dukan gefen gabas na Araba.2. Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon. Ya yi mulki daga Arower wadda take iyakar kwarin Arnon, daga tsakiyar kwarin har zuwa, Kogin Yabbok, wanda yake iyakar Ammonawa. Wannan ya haɗa da rabin Gileyad.3. Ya kuma yi mulki a kan gabashin Araba daga tekun Kinneret zuwa Tekun Araba (wato, Tekun Gishiri), zuwa Bet-Yeshimot da kuma kudu zuwa gangaren dutsen Fisga.4. Haka ma suka ci sashen Og sarkin Bashan, ɗaya daga cikin Refahiyawa na ƙarshe da ya yi mulki a Ashtarot da Edireyi.5. Mulkinsa ya taso daga Dutsen Hermon, da Saleka, da dukan Bashan har zuwa iyakar Geshurawa da Ma’akatiyawa haɗe da rabin Gileyad, zuwa kan iyakar Heshbon ta sarki Sihon.6. Sai Musa, bawan Ubangiji da Isra’ilawa suka ci Sihon da Og da yaƙi. Musa bawan Ubangiji kuwa ya ba da ƙasarsu ga mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse.7. Waɗannan su ne sarakuna da kuma ƙasashen da Yoshuwa da Isra’ilawa suka ci da yaƙi a yammancin Urdun, daga Ba’al-Gad a Kwarin Lebanon zuwa Dutsen Halak wanda ya miƙe zuwa Seyir. Yoshuwa ya raba ƙasarsu ta zama gādo ga Isra’ilawa bisa ga yadda aka raba su kabila-kabila.8. Ƙasar ta haɗa da ƙasar kan tudu, filayen arewanci, Araba, gangaren Dutse, da jejin, da kuma Negeb, wato, ƙasashen Hittiyawa, Amoriyawa, Kan’aniyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa, da Yebusiyawa.9. Sarkin Yeriko, ɗaya sarkin Ai (kusa da Betel), ɗaya10. sarkin Urushalima, ɗaya sarkin Hebron, ɗaya11. sarkin Yarmut, ɗaya sarkin Lakish, ɗaya12. sarkin Eglon, ɗaya sarkin Gezer, ɗaya13. sarkin Debir, ɗaya sarkin Bet-Gader, ɗaya14. sarkin Horma, ɗaya sarkin Arad, ɗaya15. sarkin Libna, ɗaya sarkin Adullam, ɗaya16. sarkin Makkeda, ɗaya sarkin Betel, ɗaya17. sarkin Taffuwa, ɗaya sarkin Hefer, ɗaya18. sarkin Afek, ɗaya sarkin Sharon, ɗaya19. sarkin Madon, ɗaya sarkin Hazor, ɗaya20. sarkin Shimron Meron, ɗaya sarkin Akshaf, ɗaya21. sarkin Ta’anak, ɗaya sarkin Megiddo, ɗaya22. sarkin Kedesh, ɗaya sarkin Yokneyam a Karmel, ɗaya23. sarkin Dor (A Nafot Dor), ɗaya sarkin Goyim a Gilgal, ɗaya24. sarki Tirza, ɗaya. Duka-duka dai sarakuna talatin da ɗaya ne.Zabura 44:4-194. Kai ne Sarkina da kuma Allahna, wanda ya ba da nasarori wa Yaƙub.5. Ta wurinka mun tura abokan gābanmu baya; ta wurin sunanka muka tattake maƙiyanmu.6. Ba na dogara ga bakana, takobina ba ya kawo nasara;7. amma kana ba mu nasara a kan abokan gābanmu, ka sa abokan gābanmu suka sha kunya.8. A cikin Allah muke fariyarmu dukan yini, kuma za mu yabi sunanka har abada.9. Amma yanzu ka ƙi mu ka kuma ƙasƙantar da mu; ba ka ƙara fita tare da mayaƙanmu.10. Ka sa muka gudu a gaban abokin gāba, kuma abokan gābanmu suka washe mu.11. Ka ba da mu a cinye kamar tumaki ka kuma watsar da mu a cikin al’ummai.12. Ka sayar da mutanenka a kuɗin da bai taka ƙara ya karye ba babu wata riba daga sayar da su da ka yi.13. Ka mai da mu abin dariya ga maƙwabtanmu, abin dariya da reni ga waɗanda suke kewaye da mu.14. Ka sa muka zama abin ba’a a cikin al’ummai; mutanen suna kaɗa mana kai.15. Dukan yini ina cikin wulaƙanci, fuskata kuma ta rufu da kunya16. saboda ba’ar waɗanda suke zagi suke kuma ƙina, saboda abokan gābana, waɗanda suka sha alwashi sai sun yi ramuwa.17. Dukan wannan ya faru da mu, ko da yake ba mu manta da kai ba ko mu kasance masu ƙarya ga alkawarinka.18. Zukatanmu ba su juya baya; ƙafafunmu ba su kauce daga hanyarka ba.19. Amma ka ragargaza mu ka kuma maishe mu abin farautar karnukan jeji ka kuma rufe mu cikin duhu baƙi ƙirin.Karin Magana 14:1-21. Mace mai hikima kan gina gidanta, amma da hannunta wawiya takan rushe shi ƙasa.2. Wanda tafiyarsa ta aikata gaskiya ce kan ji tsoron Ubangiji, amma wanda hanyoyinsa ba a kan gaskiya ba ne yakan rena shi.Luka 10:25-4225. Wata rana, sai wani masanin dokoki ya miƙe tsaye don yă gwada Yesu. Ya tambaya ya ce, “Malam, me zan yi don in gāji rai madawwami?”26. Yesu ya amsa ya ce, “Me aka rubuta a cikin Doka? Yaya kake karanta ta?”27. Sai ya amsa ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan ƙarfinka, da kuma dukan hankalinka’; kuma, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ ”28. Yesu ya ce, “Ka amsa daidai. Ka yi haka, kuma za ka rayu.”29. Amma domin ya kāre kansa, sai ya tambayi Yesu ya ce, “Shin, wane ne maƙwabcina?”30. Yesu ya amsa ya ce, “Wani mutum ya tashi daga Urushalima za shi Yeriko, sai ya fāɗi a hannun mafasa, wato, ’yan fashi. Suka ƙwace tufafinsa, suka yi masa dūka, suka bar shi nan bakin rai da mutuwa.31. Ya zamana wani firist ya bi kan wannan hanya. Da ya ga mutumin, sai ya bi gefe ya wuce abinsa.32. Haka ma wani daga kabilar Lawi, mai hidima cikin haikali, da ya zo wurin, ya gan shi, sai shi ma ya bi gefe ɗaya, ya wuce abinsa.33. Amma wani mutumin Samariya da yake kan tafiya, da ya kai inda mutumin yake, ya gan shi, sai ya ji tausayinsa.34. Ya je wurinsa, ya daddaure masa raunukansa, sa’an nan ya zuba mai, da ruwan inabi. Ya ɗauki mutumin ya sa a kan jakinsa, ya kai shi wani masauƙi, ya yi jinyarsa.35. Kashegari, sai ya ɗauki dinari biyu, ya ba wa mai masauƙin ya ce, ‘Ka lura da shi, bayan na dawo, zan biya ka duk abin da ka ƙara kashewa a kansa.’36. “A ganinka, a cikin waɗannan mutane uku, wane ne maƙwabcin mutumin da ya fāɗi a hannun mafasa?”37. Masanin dokoki ya amsa ya ce, “Wanda ya nuna masa jinƙai.” Yesu ya ce masa, “Je ka, ka yi haka nan.”38. Yayinda Yesu da almajiransa suna cikin tafiya, sai ya kai wani ƙauye inda wata mace mai suna Marta ta marabce shi a gidanta.39. Tana da ’yar’uwa mai suna Maryamu, wadda ta zauna a gaban Ubangiji tana jin maganarsa.40. Marta kuwa, aikin hidima da ya kamata a yi, ya ɗauke mata hankali, sai ta zo wurin Yesu, ta ce, “Ubangiji, ba ka damu da yadda ’yar’uwata ta bar mini aiki ni kaɗai ba? Gaya mata ta taimake ni!”41. Amma Ubangiji ya amsa ya ce, “Marta, Marta, hankalinki ya tashi, kuma kina damuwa a kan abubuwa da yawa.42. Amma abu ɗaya tak ake bukata, Maryamu ta zaɓi abin da ya fi kyau, kuma ba za a raba ta da shi ba.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.