Baibul a cikin shekara guda Afrilu 12Yoshuwa 13:1-331. Sa’ad da Yoshuwa ya tsufa, Ubangiji ya ce masa, “Ka tsufa ƙwarai, ga shi kuma akwai sauran ƙasa mai fāɗi da ba ku riga kun mallaka ba.2. “Ga ƙasar da ta rage, “dukan yankunan Filistiyawa da na Geshurawa.3. Daga Kogin Shihor a gabashin Masar zuwa sashen Ekron a arewa, dukan wannan ƙasa ana lissafta ta a cikin ƙasar Kan’aniyawa, ko da yake tana a sashen da sarakuna biyar na Filistiyawa na Gaza, Ashdod, Ashkeloniyawa, Gat da Ekron; na Awwiyawa.4. Daga wajen kudu kuma, dukan ƙasar Kan’aniyawa ce. Iyakarta a arewa ta fara daga Ara ta Sidoniyawa har zuwa Afek, ta zarce har zuwa iyakar Amoriyawa;5. da ƙasar Gebaliyawa; da dukan Lebanon wajen gabas daga Ba’al-Gad a gindin Dutsen Hermon zuwa Lebo Hamat.6. “Dukan mazauna kan yankunan tuddai daga Lebanon zuwa Misrefot Mayim, wato, dukan Sidoniyawa, ni da kaina zan kore su a gaban Isra’ilawa. Ka tabbata ka raba wa Isra’ilawa ƙasar ta zama gādonsu kamar yadda na umarce ka,7. ka raba ta tă zama gādo wa kabilu tara da kuma rabin kabilar Manasse.”8. Rabin kabilar Manasse, mutanen Ruben da mutanen Gad suka karɓi rabonsu na gādo wanda Musa ya ba su a gabashin Urdun. Abin da Musa bawan Ubangiji ya ba su ke nan.9. Wannan ya tashi daga Arower a gefen kwarin Arnon, da kuma daga garin da yake tsakiyar kwarin, ya kuma haɗa da ƙasar da take tudun Medeba har zuwa Dibon,10. da dukan garuruwan Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulkin Heshbon, har zuwa iyakar Ammonawa.11. Haɗe da Gileyad, inda mutanen Geshur da Ma’aka suke. Dukan Dutsen Hermon, da dukan Bashan har zuwa Saleka,12. wato, dukan masarautar Og a Bashan, wanda ya yi mulkin Ashtarot da Edireyi, yana cikin waɗanda suke na ƙarshe da ba a kashe ba a cikin Refahiyawa. Musa ya ci su da yaƙi, ya ƙwace ƙasarsu.13. Amma Isra’ilawa ba su kori mutanen Geshur da Ma’aka ba, saboda haka suka ci gaba da zama cikin Isra’ilawa har wa yau.14. Kabilar Lawiyawa ne kaɗai Musa bai ba ta gādo ba, gama hadayun ƙonawa da ake miƙa wa Ubangiji, Allah na Isra’ila ne gādonsu, kamar yadda ya yi musu alkawari.15. Ga abin da Musa ya ba kabilar Ruben bisa ga iyalansu.16. Abin da ya kama daga Arower a gefen kwarin Arnon, da kuma daga garin da yake tsakiyar kwarin, da dukan ƙasar tudu kusa da Medeba17. zuwa Heshbon, da dukan garuruwan kan tudu, haɗe da Dibon, Bamot Ba’al, Bet-Ba’al-Meyon,18. Yahza, Kedemot, Mefa’at,19. Kiriyatayim, Sibma, Zeret Shahar kan tudu cikin kwari,20. Bet-Feyor, gangaren Fisga da Bet-Yeshimot,21. dukan garuruwan da suke kan tudu da dukan masarautar Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon. Musa ya yi nasara da shi, da shugabannin Midiyawa, wato, Ewi, Rekem, Zur, Hur, da Reba, sarakunan Sihon, waɗanda suka zauna a ƙasar.22. Ƙari a kan waɗanda aka kashe a yaƙi, Isra’ilawa suka kashe Bala’am ɗan Beyor da takobi don yana duba.23. Gefen Urdun shi ne iyakar mutanen Ruben. Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne gādon mutanen Ruben, bisa ga iyalansu.24. Ga abin da Musa ya ba kabilar Gad, bisa ga iyalansu.25. Yankin ƙasarsu ya ƙunshi Yazer, da dukan garuruwan Gileyad, da rabin ƙasar Ammonawa har zuwa Arower kusa da Rabba,26. da kuma daga Heshbon zuwa Ramat Mizfa da Betonim, da kuma daga Mahanayim zuwa sashen Debir,27. kuma a cikin kwari, Bet-Haram, Bet-Nimra, Sukkot da Zafon da kuma sauran masarautar Sihon sarkin Heshbon (gabashin Urdun, abin da ya kama har zuwa ƙarshen Tekun Kinneret).28. Waɗannan garuruwan da ƙauyukansu duka, gādon mutanen Gad ne, bisa ga iyalansu.29. Ga abin da Musa ya ba rabin kabilar Manasse, wato, wa rabin zuriyar Manasse, bisa ga iyalansu.30. Abin da ya miƙe daga Mahanayim haɗe da dukan Bashan, da gefen masarautar Og sarkin Bashan, da dukan garuruwan Yayir guda sittin da suke a Bashan,31. da rabin Gileyad, da Ashtarot, Edireyi (biranen sarki Og a Bashan). Wannan shi ne rabon da zuriyar Makir ɗan Manasse suka samu, domin rabin ’ya’yan Makir maza, bisa ga iyalansu.32. Waɗannan su ne rabon gādon da Musa ya yi lokacin da suke cikin filayen Mowab a hayin gabashin Urdun kusa da Yeriko.33. Amma Musa bai ba kabilar Lawiyawa gādo ba; Ubangiji, Allah na Isra’ila, shi ne gādonsu kamar yadda ya yi musu alkawari.Yoshuwa 14:1-151. Ga wuraren da Isra’ilawa suka sami gādo a ƙasar Kan’ana waɗanda Eleyazar firist, Yoshuwa ɗan Nun da kuma shugabannin iyalai kabila-kabila na Isra’ila suka raba musu.2. Ta wurin yin ƙuri’a aka raba wa kabilan nan tara da rabi, yadda Ubangiji ya umarta ta wurin Musa.3. Musa ya ba wa kabilan biyu da rabin nan gādonsu gabashin Urdun, amma bai ba wa Lawiyawa gādo a cikin sauran ba,4. gama ’ya’yan Yusuf sun zama kabilu biyu, Manasse da Efraim. Ba a ba Lawiyawa gādon ba sai dai garuruwan da aka ba su su zauna a ciki, da wurin kiwo mai kyau domin dabbobinsu.5. Haka Isra’ilawa suka raba ƙasar, yadda Ubangiji ya umarci Musa.6. Mutanen Yahuda kuma suka je wurin Yoshuwa a Gilgal, sai Kaleb ɗan Yefunne Bakenizze ya ce wa Yoshuwa, “Ka san abin da Ubangiji ya gaya wa Musa, mutumin Allah a Kadesh Barneya game da kai da ni.7. Ina da shekara arba’in lokacin da Musa bawan Ubangiji ya aike ni zuwa Kadesh Barneya in leƙi asirin ƙasar. Na kuwa kawo masa rahoto daidai yadda na ga ƙasar,8. amma ’yan’uwana waɗanda muka je tare su suka ba da rahoton da ya sa zukatan mutane suka narke don tsoro. Ni kam na bi Ubangiji Allah da dukan zuciyata.9. Saboda haka a ranan nan Musa ya rantse mini cewa, ‘Ƙasar da ka taka za tă zama ƙasarka ta gādo kai da ’ya’yanka har abada, domin ka bi Ubangiji Allahna da dukan zuciyarka.’10. “Ga shi, kamar yadda Ubangiji ya yi alkawari, ya bar ni da rai har na ƙara shekaru arba’in da biyar tun daga lokacin da ya gaya wa Musa wannan, a lokacin da Isra’ilawa suke yawo a cikin jeji. Ga ni nan yau shekaruna tamanin da biyar!11. Ina nan da ƙarfina kamar yadda nake da ƙarfi a lokacin da Musa ya aike ni; zan iya fita zuwa yaƙi da ƙwazo yanzu kamar yadda nake zuwa a dā.12. Yanzu sai ka ba ni wannan ƙasar da take kan tudu wadda Ubangiji ya yi alkawari zai ba ni a ranan nan. Kai ma ka ji a lokacin, yadda Anakawa suke a can, biranensu manya ne kuma sun kewaye su sosai, amma na sani Ubangiji zai taimake ni, zan kore su kamar yadda ya faɗa.”13. Sai Yoshuwa ya sa wa Kaleb ɗan Yefunne albarka, ya ba shi Hebron.14. Saboda haka Hebron ta zama ƙasar Kaleb ɗan Yefunne Bakenizze tun daga lokacin nan, domin ya bi Ubangiji, Allah na Isra’ila da dukan zuciyarsa.15. (Dā a kan kira wannan Hebron, Kiriyat Arba. Wannan Arba kuwa shi ne wani katon mutum a cikin Anakawa.) Sa’an nan ƙasar ta huta daga yaƙi.Zabura 44:20-2620. Da a ce mun manta da sunan Allahnmu ko mun miƙa hannuwanmu ga baƙin alloli,21. da Allah bai gane ba, da yake ya san asiran zuciya?22. Duk da haka saboda kai mun fuskanci mutuwa dukan yini; aka ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka.23. Ka farka, ya Ubangiji! Don me kake barci? Ta da kanka! Kada ka ƙi mu har abada.24. Me ya sa ka ɓoye fuskarka ka manta da azabanmu da kuma danniyar da ake mana?25. An kai mu ƙasa zuwa ƙura; jikunanmu sun manne da ƙasa.26. Ka tashi ka taimake mu; ka cece mu saboda ƙaunarka marar ƙarewa.Karin Magana 14:3-33. Maganar wawa kan kawo sanda a bayansa, amma leɓunan masu hikima kan tsare su.Luka 11:1-281. Wata rana Yesu yana addu’a a wani wuri. Da ya gama, sai ɗaya daga cikin almajiransa ya ce masa, “Ubangiji, ka koya mana yin addu’a, kamar yadda Yohanna ya koya wa almajiransa.”2. Sai ya ce musu, “Sa’ad da kuke yin addu’a ku ce, “ ‘Ya Uba, sunanka mai tsarki ne mulkinka ya zo.3. Ka ba mu kowace rana abincin yini.4. Ka gafarta mana zunubanmu, kamar yadda mu ma ke gafarta wa duk wanda ya yi mana laifi. Kada ka bari a kai mu cikin jarraba.’ ”5. Sa’an nan ya ce musu, “Da a ce ɗayanku yana da aboki, sa’an nan ya je wurinsa da tsakar dare ya ce, ‘Aboki, ranta mini burodi guda uku,6. domin wani abokina da yake tafiya ya sauka a wurina. Ga shi, ba ni da abinci da zan ba shi.’7. Sai wanda yake cikin ɗaki ya amsa ya ce, ‘Kada ka dame ni. An riga an kulle ƙofa, da ni da yarana kuwa mun kwanta, ba zan iya tashi in ba ka kome ba.’8. Ina gaya muku, ko da yake ba zai so ya tashi ya ba shi burodin don shi abokinsa ne ba, duk da haka, zai tashi ya ba shi yawan abin da yake bukata, saboda nacewarsa.9. “Don haka ina faɗa muku, ku roƙa, za a ba ku, ku nema za ku samu, ku ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa.10. Gama duk wanda ya roƙa, yana karɓa, mai nema yana samu, wanda ya ƙwanƙwasa kuma, za a buɗe masa ƙofa.11. “Wane mahaifi ne a cikinku, in ɗansa ya roƙe shi kifi, zai ba shi maciji a maimakon,12. ko kuma in ya roƙi ƙwai, ya ba shi kunama?13. In fa haka ne, ko da yake ku mugaye ne, kun san ba ’ya’yanku kyautai masu kyau, balle fa Ubanku na sama, zai yi fiye da haka, ta wurin ba da Ruhu Mai Tsarki, ga masu roƙonsa!”14. Sa’ad da Yesu yake fitar da wani beben aljani daga wani mutum, da aljanin ya fita, sai mutumin wanda da bebe ne, ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki.15. Amma waɗansunsu suka ce, “Ai, da ikon Be’elzebub, sarkin aljanu ne, yake fitar da aljanu.”16. Waɗansu kuma suka gwada shi, ta wurin neman yă nuna musu wata alama daga sama.17. Yesu kuwa ya san tunaninsu, sai ya ce musu, “Duk mulkin da yake gāba da kansa, zai lalace, kuma gidan da yake gaba da kansa zai rushe.18. In Shaiɗan yana gāba da kansa, yaya mulkinsa zai tsaya? Ina faɗin haka domin kun ce, da ikon Be’elzebub nake fitar da aljanu.19. In da ikon Be’elzebub nake fitar da su, to, da ikon wa masu binku suke fitar da su? Saboda haka, za su zama alƙalanku ke nan.20. Amma in da ikon Allah ne ni nake fitar da aljanu, ashe, mulkin Allah ya zo muku ke nan.21. “Sa’ad da mutum mai ƙarfi, wanda yake da makamai yana gadin gidan kansa, an tsare lafiyar dukiyarsa ke nan.22. Amma in wani wanda ya fi shi ƙarfi, ya faɗa masa ya kuma sha ƙarfinsa, yakan ƙwace makaman da mutumin ke dogara da su, ya kuma rarraba ganima.23. “Wanda ba ya tare da ni, yana gāba da ni, wanda kuma ba ya tarawa da ni, watsarwa yake yi.24. “Lokacin da mugun ruhu ya fita daga mutum, sai ya bi ta wuraren da ba mutane, yana neman hutu, amma ya kāsa samu, sai ya ce, ‘Zan koma gidan da na bari.’25. Sa’ad da ya koma, ya tarar da gidan a share da tsabta, kuma a shirye.26. Sai ya je ya ɗebo waɗansu ruhohi bakwai da suka fi shi mugunta, sai su shiga su zauna a wurin. Ƙarshen wannan mutum kuwa zai fi farkonsa muni.”27. Da Yesu yake cikin faɗin waɗannan abubuwa, sai wata mace daga cikin taron ta ɗaga murya ta ce masa, “Mai albarka ce uwar da ta haife ka, wadda ka sha mamanta.”28. Yesu ya amsa ya ce, “A maimakon, masu albarka ne waɗanda suke jin maganar Allah, suna kuma biyayya da ita.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.