Baibul a cikin shekara guda Afrilu 13Yoshuwa 15:1-631. An raba wa kabilar Yahuda gādonsu ta wurin yin ƙuri’a, bisa ga iyalansu, rabon ya kai har zuwa sashen Edom, zuwa Jejin Zin can kurewar kudu.2. Iyakarsu a kudanci ta tashi tun daga kurewar kudu na Tekun Gishiri,3. zuwa kudancin Hanyar Kunama, ta ci gaba har zuwa Zin, zuwa kudancin Kadesh Barneya. Sa’an nan ta kurɗa zuwa Hezron har zuwa Addar, ta kuma karkata zuwa Karka.4. Sai ta wuce zuwa Azmon ta haɗu da Rafin Masar, ta ƙarasa a Bahar Rum. Wannan shi ne iyakarsu ta kudu.5. Iyakarsu ta gabas kuwa ita ce Tekun Gishiri wadda ta zarce har zuwa gaɓar Urdun. Iyakarsu ta arewa ta fara ne daga Tekun Gishiri a bakin Urdun,6. wajen Bet-Hogla ta wuce har zuwa arewancin Bet-Araba, zuwa Dutsen Bohan ɗan Ruben.7. Sai iyakar ta haura zuwa Debir daga Kwarin Akor ta juya arewa da Gilgal, wadda take fuskantar hawan Adummim a kudancin kwari, ta ci gaba zuwa ruwan En Shemesh, ta ɓullo ta En Rogel.8. Sai kuma ta gangara zuwa Kwarin Ben Hinnom a gangaren kudancin birnin Yebusiyawa (wato, Urushalima). Daga can ta haura zuwa kan tudun a yammancin Kwarin Hinnom, a arewancin ƙarshen Kwarin Refayim.9. Daga kan tudun, iyakar ta nufi maɓulɓular ruwa na Neftowa, ta ɓullo a garuruwan da suke a Dutsen Efron, ta gangara zuwa Ba’ala (wato, Kiriyat Yeyarim).10. Sa’an nan ta karkata yamma daga Ba’ala zuwa Dutsen Seyir, ta wuce ta gangaren Dutsen Yeyarim (wato, Kesalon), ta ci gaba zuwa Bet-Shemesh, ta bi zuwa Timna.11. Ta wuce zuwa gangaren arewancin Ekron, ta juya zuwa Shikkeron, ta wuce zuwa Dutsen Ba’ala, ta kai Yabneyel, iyakarta ta ƙare a teku.12. Bakin Bahar Rum nan ne iyakar yammanci. Wannan ita ce iyakar da ta kewaye jama’ar Yahuda bisa ga iyalansu.13. Yoshuwa ya ba Kaleb ɗan Yefunne wuri a Yahuda, Kiriyat Arba, wato, Hebron, bisa ga umarnin Ubangiji. (Arba shi ne mahaifin Anak.)14. Daga can sai Kaleb ya kori ’ya’yan Anak, maza su uku daga Hebron, wato, Sheshai, Ahiman da Talmai.15. Daga can ya nufi Debir ya yi yaƙi da mutanen da suke zama a can (Dā sunan Debir, Kiriyat Sefer ne).16. Kaleb ya ce, “Zan ba da ’yata Aksa aure ga wanda zai ci Kiriyat Sefer da yaƙi.”17. Otniyel ɗan Kenaz, ɗan’uwan Kaleb, ya ci Kiriyat Sefer da yaƙi; saboda haka Kaleb ya ba wa Aksa ’yarsa, ya kuwa aure ta.18. Wata rana da ta zo wurin Otniyel, sai ya zuga ta ta roƙi mahaifinta fili. Da ta sauka daga kan jakinta sai Kaleb ya tambaye ta ya ce, “Me kike so in yi miki?”19. Ta amsa ta ce, “Ka yi mini alheri na musamman, tun da ka ba ni wuri a Negeb, ina roƙonka, ka ba ni maɓulɓulan ruwa.” Kaleb kuwa ya ba ta maɓulɓulan ruwa na tuddai da na kwari.20. Wannan shi ne gādon kabilar Yahuda bisa ga iyalansu.21. Garuruwan kabilar Yahuda da suke kudu cikin Negeb zuwa iyakar Edom su ne. Kabzeyel, Eder, Yagur,22. Kina, Dimona, Adada,23. Kedesh, Hazor, Itnan,24. Zif, Telem, Beyalot,25. Hazor-Hadatta, Keriyot Hezron (wato, Hazor),26. Amam, Shema, Molada,27. Hazar Gadda, Heshmon, Bet-Felet,28. Hazar Shuwal, Beyersheba, Biziyotiya,29. Ba’ala, Iyim, Ezem,30. Eltolad, Kesil, Horma,31. Ziklag, Madmanna, Sansanna,32. Lebayot, Shilhim, Ayin, Rimmon, jimillarsu, garuruwa da ƙauyukansu duka ashirin da tara ne.33. Biranen da suke a filayen kwari su ne, Eshtawol, Zora; Ashna,34. Zanowa, En Gannim, Taffuwa, Enam,35. Yarmut, Adullam, Soko, Azeka,36. Sha’arayim, Aditayim, Gedera (Gederotayim ke nan). Garuruwa goma sha huɗu ke nan da ƙauyukansu.37. Zenan, Hadasha, Migdal Gad,38. Dileyan, Mizfa, Yokteyel,39. Lakish, Bozkat, Eglon,40. Kabbon, Lahman, Kitlish,41. Gederot, Bet-Dagon, Na’ama, Makkeda, garuruwa goma sha shida ke nan da ƙauyukansu.42. Libna, Eter, Ashan,43. Yefta, Ashna, Nezib,44. Keyila, Akzib, Maresha, garuruwa tara ke nan da ƙauyukansu.45. Ekron da ƙauyukan da suke kewaye da ita;46. yammancin Ekron da dukan garuruwa da ƙauyukan da suke kusa da Ashdod.47. Ashdod da garuruwa da kuma ƙauyukan da suke kewaye da ita, Gaza da garuruwanta da ƙauyukanta har zuwa Rafin Masar da kuma Bahar Rum.48. Birane na cikin ƙasar tuddai kuwa, su ne, Shamir, Yattir, Soko,49. Danna, Kiriyat Sanna (wato, Debir),50. Anab, Eshtemo, Anim,51. Goshen, Holon, Gilo, garuruwa goma sha ɗaya ke nan da ƙauyukansu.52. Arab, Duma, Eshan,53. Yanum, Bet-Taffuwa, Afeka,54. Humta, Kiriyat Arba (wato, Hebron) da Ziyor, garuruwa tara ke nan da ƙauyukansu.55. Mawon, Karmel, Zif, Yutta56. Yezireyel, Yokdeyam, Zanowa,57. Kayin, Gibeya, Timna, garuruwa goma ke nan da ƙauyukansu.58. Halhul, Bet-Zur, Gedor,59. Ma’arat, Bet-Anot, Eltekon, garuruwa shida ke nan da ƙauyukansu.60. Kiriyat Ba’al (wato, Kiriyat Yeyarim) da Rabba, garuruwa biyu ke nan da ƙauyukansu.61. Biranen da suke a jeji kuwa su ne, Bet-Araba, Middin, Sekaka,62. Nibshan, Birnin gishiri da En Gedi, garuruwa shida ke nan da ƙauyukansu.63. Kabilar Yahuda kuwa ba su iya korar Yebusiyawa waɗanda suke zama cikin Urushalima ba; har wa yau Yebusiyawa suna nan zaune tare da mutanen Yahuda.Yoshuwa 16:1-101. Rabon da aka ba wa Yusuf ya fara tun daga Urdun kusa da Yeriko, gabas da ruwan Yeriko, sai ya miƙe zuwa jeji, ya haura har zuwa cikin ƙasar tudu na Betel.2. Ya ci gaba daga Betel (wato, Luz), ya zarce zuwa sashen Arkitawa na Atarot,3. ya sauka zuwa yammancin bakin iyakar Yalfetiyawa har zuwa yankin Bet-Horon wanda yake cikin kwari. Ya zarce kuma zuwa Gezer, ya gangara ya yi ƙarshe a Bahar Rum.4. Wannan ne yankin da aka ba wa Manasse da Efraim zuriyar Yusuf gādonsu.5. Yankin Efraim ke nan bisa ga iyalansu. Iyakar ƙasarsu ta gādo ta kama daga Atarot Addar a gabas zuwa Bet-Horon,6. ta wuce zuwa Bahar Rum. Daga Mikmetat a arewa kuwa iyakar ta karkata gabas zuwa Ta’anat Shilo, ta wuce zuwa Yanowa a gabas.7. Sai ta gangara daga Yanowa zuwa Atarot da Na’ara, ta bi ta Yeriko, ta kuma fito ta Urdun.8. Daga Taffuwa kuma iyakar ta bi yamma zuwa kwazazzaban Kana, ta ƙarasa a Bahar Rum. Wannan shi ne gādon mutanen Efraim bisa ga iyalansu.9. Gādon ya kuma haɗa da dukan garuruwa da ƙauyuka waɗanda aka keɓe wa mutanen Efraim daga cikin gādon mutanen Manasse.10. Ba su kori Kan’aniyawan da suke zama a Gezer ba, don haka Kan’aniyawa suna zama tare da mutanen Efraim har wa yau; amma Kan’aniyawa suka zama masu yin aikin dole.Zabura 45:1-51. Zuciyata ta cika da kyakkyawan kan magana yayinda nake rera ayoyina wa sarki; harshena ne alƙalamin ƙwararren marubuci.2. Kai ne mafi kyau cikin mutane an kuma shafe leɓunanka da alheri, da yake Allah ya albarkace ka har abada.3. Ka ɗaura takobinka a gefenka, ya jarumi; ka rufe kanka da ɗaukaka da kuma daraja.4. Cikin darajarka ka hau zuwa nasara a madadin gaskiya, tawali’u da adalci; bari hannunka na dama yă nuna ayyukan banmamaki.5. Bari kibiyoyinka masu tsini su huda zukatan abokan gāban sarki; bari al’ummai su fāɗi ƙarƙashin ƙafafunka.Karin Magana 14:4-54. Inda ba shanu, wurin sa wa dabbobi abinci zai kasance ba kome, amma daga ƙarfin saniya ce yalwar girbi kan fito.5. Mashaidi na gaskiya ba ya ruɗu, amma mashaidin ƙarya kan baza ƙarairayi.Luka 11:29-5429. Da taron mutane suka ƙaru, sai Yesu ya ce, “Wannan mugun zamani ne. Tana neman wani abin banmamaki, amma ba ko ɗaya da za a ba ta, sai dai ta Yunana.30. Kamar yadda Yunana ya zama alama ga mutanen Ninebe, haka ma Ɗan Mutum zai zama ga zamanin nan.31. A ranar shari’a, Sarauniyar Kudu za tă tashi tsaye tare da wannan zamani, ta yanke wa wannan zamani hukunci, domin ta zo daga ƙarshen duniya ta saurari hikimar Solomon, ga shi kuwa, shi wanda ya fi Solomon girma, na nan.32. A ranar shari’a, mutanen Ninebe za su tashi tsaye tare da wannan zamani, su yanke wa wannan zamani hukunci. Gama sun tuba sa’ad da Yunana ya yi musu wa’azi. Ga shi yanzu, shi wanda ya fi Yunana girma, na nan.33. “Babu wanda yakan ƙuna fitila sa’an nan ya ɓoye ta, ko ya rufe ta da murfi ba. A maimako, yakan ajiye ta a kan wurin ajiye fitila, don masu shiga su ga haske.34. Idonka shi ne fitilar jikinka. Sa’ad da idanunka suna da lafiya, dukan jikinka ma na cike da haske, amma sa’ad da idanunka suna da lahani, dukan jikinka ma na cike da duhu.35. Ka lura fa, kada hasken da yake cikinka ya zamana duhu ne.36. Saboda haka, in dukan jikinka yana cike da haske, ba inda ke da duhu, jikinka kuwa zai kasance da haske gaba ɗaya, kamar yadda hasken fitila yake haskaka ka.”37. Da Yesu ya gama magana, sai wani Bafarisiye ya gayyace shi cin abinci tare da shi. Sai kuwa ya shiga ya zauna a tebur.38. Amma Bafarisiyen ya lura cewa, Yesu bai wanke hannu kafin ya ci abinci ba, sai mamaki ya kama shi.39. Sai Ubangiji ya ce masa, “Ku Farisiyawa, kukan wanke bayan kwano da kwaf, amma a ciki kuna cike da kwaɗayi da mugunta.40. Ku wawayen mutane! Ashe, wanda ya yi bayan, ba shi ne kuma ya yi cikin ba?41. Ku ba matalauta abin da yake cikin kwano, kuma kome zai zama muku da tsabta.42. “Kaitonku, Farisiyawa, domin kuna ba wa Allah zakka na na’ana’arku, da ƙarƙashinku, da kuma sauran ganyen lambunku iri-iri, amma kun ƙyale adalci da ƙaunar Allah. Ya kamata da kun kiyaye na ƙarshen, ban ba barin na farkon.43. “Kaitonku, Farisiyawa, domin kun cika son wuraren zama masu daraja a majami’u, da kuma yawan gaisuwa a wuraren kasuwanci.44. “Kaitonku, domin ku kamar kaburbura ne da ba a sa musu alama ba, waɗanda mutane suke takawa don rashin sani.”45. Sai ɗaya daga cikin masanan dokoki ya ce wa Yesu, “Malam, in ka faɗi waɗannan abubuwa haka, kai kuma ka zage mu ke nan.”46. Yesu ya amsa ya ce, “Ku masanan dokoki ma, kaitonku, domin kun ɗora wa mutane kaya masu nauyi waɗanda da ƙyar suke ɗaukawa, amma ku da kanku ba za ku sa ko yatsa ɗaya, don ku taimake su ba.47. “Kaitonku, domin kun gina kaburbura saboda annabawa, nan kuwa kakannin-kakanninku ne suka kashe su.48. Wannan ya shaida cewa kun amince da abin da kakannin-kakanninku suka yi. Sun karkashe annabawa, ku kuma kun gina kaburburansu.49. Saboda haka, Allah a cikin hikimarsa ya ce, ‘Zan aika musu da annabawa da manzanni. Za su kashe waɗansu, su kuma tsananta wa waɗansu.’50. Saboda haka, alhakin jinin dukan annabawa da aka kashe, tun farkon duniya, yana kan wannan zamani,51. wato, tun daga jinin Habila, har zuwa jinin Zakariya, wanda aka kashe tsakanin bagade da mazauni. I, ina gaya muku, alhakinsu duka yana kan wannan zamani.52. “Kaitonku, masanan dokoki, domin kun ɗauke mabuɗin ilimi. Ku kanku ba ku shiga ba, kuma kun hana wa waɗanda suke shiga, su shiga.”53. Da Yesu ya bar wurin, sai Farisiyawa da malaman dokoki suka fara gaba mai tsanani da shi, kuma suna tsokanansa da tambayoyi.54. Suna fakonsa, don su kama shi a kan wata magana da zai faɗa. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.