Baibul a cikin shekara guda Afrilu 17Yoshuwa 23:1-161. An daɗe bayan da Ubangiji ya ba Isra’ilawa hutu daga dukan abokan gāban da suke kewaye da su. Yoshuwa kuwa ya tsufa, shekarunsa sun yi yawa,2. sai ya aika a kira Isra’ilawa duka, dattawansu, shugabanninsu, alƙalansu, da manyan ma’aikatansu, ya ce musu, “Na tsufa, shekaruna kuwa sun yi yawa,3. ku kanku kun ga dukan abubuwan da Ubangiji Allahnku ya yi da idanunku wa dukan ƙasashen nan, Ubangiji Allahnku shi ne wanda ya yi yaƙi dominku.4. Ku tuna yadda na rarraba wa kabilanku ƙasashen nan su zama naku na gādo, dukan ƙasashen da suka rage, ƙasashen da na ci da yaƙi, tsakanin Urdun da Bahar Rum a yamma.5. Ubangiji Allahnku kansa zai kore su a madadinku. Zai fafare su a gabanku, za ku kuwa mallaki ƙasarsu, yadda Ubangiji Allah ya yi muku alkawari.6. “Ku yi ƙarfin hali, ku yi hankali, ku yi biyayya da dukan abin da aka rubuta a cikin Littafin Dokoki na Musa, ba tare da kun juya hagu ko dama ba.7. Kada ku haɗa kai da mutanen nan da suke zama cikinku; ba ruwanku da sunayen allolinsu, kada ku rantse da su. Kada kuwa ku bauta musu ko kuwa ku rusuna musu.8. Sai dai ku riƙe Ubangiji Allahnku da kyau, yadda kuka yi har zuwa yanzu.9. “ Ubangiji ya kori manyan ƙasashe masu ƙarfi; har wa yau ba wanda ya iya cin ku da yaƙi.10. Mutum ɗaya a cikinku ya isa yă sa mutane dubu nasu su gudu, domin Ubangiji Allahnku yana yaƙi dominku, kamar yadda ya yi alkawari.11. Saboda haka sai ku kula da kanku sosai, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku.12. “Amma in kuka juya baya kuka zama abokai ga waɗanda suka ragu suke zama a cikinku a ƙasashen nan, har kuka yi auratayya da su, kuka haɗa kai da su,13. ku tabbata cewa Ubangiji Allahnku ba zai kore muku mutanen ƙasashen nan ba, sai ma su zama muku dutsen tuntuɓe da tarko, za su zama bulala a bayanku, ƙayayyuwa a idanunku, har sai kun hallaka daga wannan ƙasa mai kyau wadda Ubangiji Allahnku ya ba ku.14. “Yanzu na kusa barin fuskar duniyan nan. Kun sani da dukan zuciyarku, da dukan ranku cewa, Ba ko ɗaya daga cikin alkawuran da Ubangiji Allahnku ya yi, da bai cika ba. Kowane alkawari ya cika; ba ko ɗaya da bai cika ba.15. Kamar yadda Ubangiji Allahnku kuwa ya cika kowane alkawari mai kyau, haka ma ba zai fasa kawo muku bala’in da ya faɗi ba, sai ya hallaka ku daga wannan ƙasa mai kyau da ya ba ku.16. In kuka karya alkawarin Ubangiji Allahnku wanda ya umarce ku, in kuka je kuka bauta wa waɗansu alloli, kuka rusuna musu, fushin Ubangiji zai sauko a kanku, za ku kuwa hallaka da sauri daga ƙasan nan mai kyau da ya ba ku.”Yoshuwa 24:1-331. Yoshuwa ya tattara dukan kabilan Isra’ila a Shekem. Ya aika a kira dattawa, shugabanni, alƙalai da manyan ma’aikatan Isra’ila, suka kai kansu gaban Allah.2. Yoshuwa ya ce wa dukan mutanen, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Dā can, kakanninku, Tera mahaifin Ibrahim, da Nahor sun zauna a hayin Kogin Yuferites suka yi wa waɗansu alloli sujada.3. Amma na ɗauki mahaifinku Ibrahim, daga ƙasar da take can a hayin Kogin Yuferites, na kawo shi ƙasar Kan’ana, na kuma ba shi ’ya’ya masu yawa. Na ba shi Ishaku,4. ga Ishaku kuwa na ba shi Yaƙub da Isuwa. Na ba Isuwa ƙasar kan tudu ta Seyir, amma Yaƙub da ’ya’yansa maza suka gangara zuwa Masar.5. “ ‘Sai na aiki Musa da Haruna, na aukar wa Masarawa annobai, ta wurin abin da na yi ne na fitar da ku.6. Lokacin da na fitar da iyayenku daga Masar, suka zo teku, sai Masarawa suka fafare su da kekunan yaƙi da dawakai har zuwa Jan Teku.7. Amma suka yi kuka ga Ubangiji don taimako, ya kuwa sa duhu ya raba tsakaninsu da Masarawa; ya sa teku ya rufe Masarawa. Kun gani da idanunku abin da na yi wa Masarawa, sa’an nan kuka zauna a jeji na tsawon lokaci.8. “ ‘Na kawo ku ƙasar Amoriyawa waɗanda suke gabas da Urdun. Suka yi yaƙi da ku, amma na ba da su a hannunku, na hallaka su a gabanku, kuka kuma mallaki ƙasarsu.9. Lokacin da Balak ɗan Ziffor, sarkin Mowab, ya yi shiri yă yaƙi Isra’ila, ya aiki Bala’am ɗan Beyor don yă la’anta ku.10. Amma ban saurari Bala’am ba, saboda haka sai ya ma sa muku albarka, na kuɓutar da ku daga hannunsa.11. “ ‘Sai kuka ƙetare Urdun kuka isa Yeriko. Mutanen Yeriko suka yi faɗa da ku, kamar yadda Amoriyawa, Ferizziyawa, Kan’aniyawa, Hittiyawa, Girgashiyawa, Hiwiyawa, da Yebusiyawa suka yi, amma na ba da su a hannunku.12. Na aika rina ta kore su a idonku, haka kuma sarakunan Amoriyawan nan. Ba da takobinku ko bakanku ne kuka yi haka ba.13. Na ba ku ƙasar da ba ku yi wata wahala kafin ku samu ba, na ba ku kuma biranen da ba ku gina ba; kuka kuma zauna a cikinsu, kuka ci daga ’ya’yan itacensu da ’ya’yan zaitun da ba ku ne kuka shuka ba.’14. “Yanzu, sai ku ji tsoron Ubangiji, ku bauta masa da dukan aminci. Ku zubar da allolin da kakanninku suka yi musu sujada a hayin Kogin Yuferites da kuma a Masar, ku bauta wa Ubangiji.15. Amma in kuka ga ba za ku iya bauta wa Ubangiji ba, sai ku zaɓa yau wanda za ku bauta masa, ko allolin da kakanninku suka bauta musu a hayin Kogin Yuferites, ko kuma allolin Amoriyawa, waɗanda kuke zama a cikin ƙasarsu. Amma da ni da gidana, Ubangiji ne za mu bauta wa.”16. Sai mutanen suka amsa suka ce, “Allah ya kiyashe mu da rabuwa da Ubangiji Allahnmu, har a ce mu bauta wa waɗansu alloli!17. Ubangiji Allahnmu ne da kansa ya fitar da iyayenmu daga Masar, daga ƙasar bauta, ya yi manyan abubuwan al’ajabi, a idanunmu. Ya kiyaye mu cikin dukan hanyar da muka bi, da cikin ƙasashen da muka ratsa;18. Ubangiji kuwa ya kore mana dukan Amoriyawa, waɗanda suke zaune a ƙasar. Don haka mu ma za mu bauta wa Ubangiji, gama shi ne Allahnmu.”19. Yoshuwa ya ce wa mutanen, “Ba za ku iya bauta wa Ubangiji ba gama shi Allah mai tsarki ne; mai kishi kuma. Ba zai gafarta muku zunubin tawaye ba.20. In kuka juya wa Ubangiji baya, kuka bauta wa waɗansu alloli, zai juya yă kawo muku bala’i, yă hallaka ku, yă kawo ƙarshenku.”21. Amma mutanen suka ce wa Yoshuwa, “Mu dai! Za mu bauta wa Ubangiji.”22. Yoshuwa kuwa ya ce musu, “Ku ne shaidun kanku cewa kun zaɓi ku bauta wa Ubangiji.” Suka amsa suka ce, “I, mu ne shaidun kanmu.”23. Yoshuwa ya ce musu, “Yanzu sai ku zubar da allolin da suke cikinku, ku miƙa wa Ubangiji, Allah na Isra’ila zuciyarku.”24. Mutanen kuma suka ce, “Za mu bauta wa Ubangiji Allahnmu, mu kuma yi masa biyayya.”25. A wannan rana Yoshuwa ya yi alkawari saboda mutanen, kuma a can Shekem ya tsara musu ƙa’idodi da dokoki.26. Yoshuwa kuwa ya rubuta abubuwan nan a cikin Littafin Dokoki na Allah. Sa’an nan ya ɗauki babban dutse ya ajiye a ƙarƙashin itacen oak kusa da tsattsarkan wuri na Ubangiji.27. Ya ce wa duka mutanen, “Ku gani! Wannan dutse zai zama mana shaida, ya ji duk maganar da Ubangiji ya yi mana, zai zama muku shaida in ba ku yi wa Allahnku gaskiya ba.”28. Sai Yoshuwa ya sallami mutane, kowa ya tafi ƙasar da aka ba shi gādo.29. Bayan waɗannan abubuwa, Yoshuwa ɗan Nun, bawan Ubangiji, ya mutu yana da shekaru ɗari da goma.30. Suka kuma binne shi a ƙasarsa ta gādo, a Timnat Sera a ƙasar kan tudu ta Efraim, arewa da Dutsen Ga’ash.31. Isra’ilawa kuwa sun bauta wa Ubangiji dukan kwanakin Yoshuwa, da kuma kwanakin dattawan da ya bari, da waɗanda suka ga duk abin da Ubangiji ya yi wa Isra’ila.32. Aka kuma binne ƙasusuwan Yusuf da aka kawo daga Masar, a Shekem a wurin da Yaƙub ya saya da azurfa ɗari daga ’ya’yan Hamor, babban Shekem. Wurin ya zama gādon zuriyar Yusuf.33. Eleyazar ɗan Haruna, ya mutu aka binne shi a Gibeya, wurin da aka ba ɗansa Finehas a ƙasar kan tudu ta Efraim.Zabura 47:1-91. Ku tafa hannuwanku, dukanku al’ummai; ku yi sowa ga Allah da muryoyin farin ciki.2. Ubangiji Mafi Ɗaukaka mai banmamaki ne, Sarki ne mai girma a bisa dukan duniya!3. Ya rinjayi al’ummai a ƙarƙashinmu, mutane kuma a ƙarƙashin ƙafafunmu.4. Ya zaɓar mana gādonmu, abar taƙamar Yaƙub, wanda yake ƙauna.5. Allah ya haura a cikin sowa ta farin ciki, Ubangiji ya haura a cikin ƙarar ƙahoni.6. Ku rera yabai ga Allah, ku rera yabai; ku rera yabai ga Sarkinmu, ku rera yabai.7. Gama Allah shi ne Sarkin dukan duniya; ku rera zabura ta yabo gare shi.8. Allah yana mulki a bisa al’ummai; Allah yana zama a kan kursiyinsa mai tsarki.9. Manyan mutanen al’ummai sun taru a matsayin mutanen Allah na Ibrahim, gama sarkunan duniya na Allah ne; ana ɗaukaka shi ƙwarai.Karin Magana 14:14-1414. Marasa bangaskiya za su sami sakamako cikakke saboda hanyoyinsu, kuma mutumin kirki zai sami lada saboda nasa.Luka 13:23-3523. Sai wani ya tambaye shi ya ce, “Ya Ubangiji, shin, wai mutane kima ne kawai za su sami ceto?” Ya ce musu,24. “Ku yi matuƙar ƙoƙari ku shiga ta matsattsiyar ƙofa, domin ina faɗa muku, mutane da yawa za su yi ƙoƙarin shiga, amma ba za su iya ba.25. Da zaran maigidan ya tashi ya rufe ƙofar, za ku tsaya a waje kuna ƙwanƙwasawa, kuna roƙo cewa, ‘Ranka yă daɗe, buɗe mana ƙofa.’ “Amma shi zai amma ya ce, ‘Ni ban san ku, ko inda kuka fito ba.’26. “Sa’an nan za ku ce, ‘Haba, mu da muka ci, muka sha tare da kai, har ka yi koyarwa a cikin titi-titi namu.’27. “Amma shi zai amma ya ce, ‘Ban san ku, ko inda kuka fito ba. Ku rabu da ni, dukan ku masu aikata mugunta!’28. “Za a yi kuka a can, da cizon haƙora, sa’ad da kuka ga Ibrahim, da Ishaku, da Yaƙub, da dukan annabawa a mulkin Allah, amma ku kuwa, za a jefar da ku a waje.29. Mutane za su zo daga gabas, da yamma, da kudu, da arewa, su ɗauki wuraren zamansu a bikin, a cikin mulkin Allah.30. Tabbatacce, akwai waɗansu da suke na ƙarshe, da za su zama na farko, na farko kuma, da za su zama na ƙarshe.”31. A wannan lokaci, waɗansu Farisiyawa suka zo suka ce wa Yesu, “Ka bar nan ka tafi wani wuri dabam. Hiridus yana so ya kashe ka.”32. Ya amsa ya ce, “Ku je ku gaya wa dilan nan, wato, mai makirci cewa, ‘Da yau da kuma gobe, zan fitar da aljanu, in kuma warkar da mutane, sa’an nan a rana ta uku in cika burin aikina.33. Duk da haka, dole in ci gaba da aikin a yau, da kuma gobe, sa’an nan in ci gaba da yin haka kashegari kuma, gama tabbatacce, ba annabi da yakan mutu a bayan birnin Urushalima!’34. “Urushalima, ayya Urushalima, ke da kika kashe annabawa, kuma kika jefa wa waɗanda aka aika gare ki da duwatsu. Sau da yawa na yi kewan in tattara ’ya’yanki wuri ɗaya, kamar yadda kaza takan tattara ’ya’yanta cikin fikafikanta, amma ba ki yarda ba!35. Duba, an bar muku gidanku fanko. Ina kuwa faɗa muku, ba za ku sāke ganina ba, sai kun ce, ‘Mai albarka ne shi wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji.’ ” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.