Baibul a cikin shekara guda Afrilu 19Mahukunta 3:1-311. Waɗannan su ne al’umman da Ubangiji ya bari don yă gwada duk waɗannan Isra’ilawan da ba su san yaƙi a Kan’ana ba2. (ya yi haka ne domin yă koya wa zuriyar Isra’ilawa waɗanda ba su taɓa yin yaƙi a dā ba),3. sarakuna biyar na Filistiyawa, dukan Kan’aniyawa, Sidoniyawa, da kuma Hiwiyawan da suke zaune a duwatsun Lebanon daga Dutsen Ba’al-Hermon zuwa Lebo Hamat.4. An bar su domin su gwada Isra’ilawa a ga ko za su yi biyayya da umarnin Ubangiji, wanda ya ba wa kakanninsu ta wurin Musa.5. Isra’ilawa suka zauna tare da Kan’aniyawa da Hittiyawa, Amoriyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da kuma Yebusiyawa.6. Suka auri ’ya’yansu mata, su ma suka bar ’ya’yansu maza suka auri ’ya’yansu mata, suka kuma yi wa gumakansu sujada.7. Isra’ilawa suka aikata mugunta a gaban Ubangiji; suka manta da Ubangiji Allahnsu suka kuma bauta wa Ba’al da Ashera.8. Fushin Ubangiji kuwa ya yi ƙuna a kan Isra’ila har ya sayar da su ga Kushan-Rishatayim sarkin Aram-Naharayim, a wurinsa ne Isra’ilawa suka zama bayi shekara takwas.9. Amma da suka yi kuka ga Ubangiji, sai ya tad musu da mai ceto, Otniyel ɗan Kenaz, ƙanen Kaleb wanda ya cece su.10. Ruhun Ubangiji ya sauko masa, domin yă zama mahukuncin Isra’ila yă kuma je yaƙi. Ubangiji ya bayar da Kushan-Rishatayim sarkin Aram a hannun Otniyel, ya kuwa sha ƙarfinsa.11. Saboda haka ƙasar ta zauna da lafiya shekara arba’in har sai da Otniyel ɗan Kenaz ya rasu.12. Isra’ilawa suka sāke aikata mugayen ayyuka a gaban Ubangiji, saboda sun aikata wannan mugunta sai Ubangiji ya ba wa Eglon sarkin Mowab ƙarfi a kan Isra’ila.13. Da ya sami Ammonawa da Amalekawa suka haɗa hannu tare, sai Eglon ya tafi ya auka wa Isra’ila, suka ƙwace Birnin Dabino.14. Isra’ilawa suka zama bayin Eglon sarkin Mowab shekara goma sha takwas.15. Isra’ilawa suka sāke yin kuka ga Ubangiji, ya kuwa ba su mai ceto, Ehud, wani bahago, ɗan Gera daga kabilar Benyamin. Isra’ilawa suka aike shi da haraji wurin Eglon sarkin Mowab.16. To, Ehud ya riga ya ƙera takobi mai kaifi biyu mai tsawo wajen kamu ɗaya da rabi, wanda ya yi ɗamara da shi a cinyarsa ta dama ƙarƙashin rigarsa.17. Ya kai wa Eglon sarkin Mowab harajin, wanda yake mai ƙiba ne.18. Bayan Ehud ya ba da harajin, sai ya sallame mutanen da suka ɗauko harajin.19. A wajen gumaka kusa da Gilgal, shi kansa ya juya ya koma ya ce, “Ranka yă daɗe, ina da saƙo na asiri dominka.” Sarkin ya ce, “Ku ba mu wuri!” Sai dukan fadawansa suka fita.20. Sai Ehud ya matso yayinda shi kuwa yake zaune shi kaɗai a ɗakin sama mai sanyi a fadansa ya ce, “Ina da saƙo daga wurin Allah dominka.” Sarki ya tashi daga kujerarsa,21. Ehud ya kai hannun hagunsa, ya zaro takobi daga cinyar ƙafar damansa ya soki sarki a ciki.22. Har ƙotar ma ta shige ciki, takobin kuma ya fito ta bayansa. Ehud bai zare takobin ba, kitse kuwa ya rufe shi.23. Sa’an nan Ehud ya fita daga shirayin; ya rufe ƙofar ɗakin saman, ya kuma kulle su.24. Bayan da ya tafi, bayin sarki suka zo suka tarar duk ƙofofin ɗakin sama suna kulle, suka ce, “Wataƙila yana bayan gari ne a ɗakin ciki.”25. Suka yi ta jira har suka gaji. Da suka ga dai bai buɗe ƙofar ba, sai suka ɗauki mabuɗi, suka buɗe. Sai ga shugabansu a ƙasa matacce.26. Yayinda suke fama jira, Ehud ya riga ya yi gaba. Ya bi ta wajen gumaka zuwa Seyira.27. Da ya iso can, sai ya busa ƙaho a ƙasar tudu ta Efraim, Isra’ilawa kuma suka gangaro tare da shi daga tuddai, shi kuwa yana jagorarsu.28. Ya umarce su ya ce, “Ku bi ni, gama Ubangiji ya ba Mowab abokin gābanku a hannunku.” Haka suka gangaro tare da shi suna mallaki mashigin Urdun da ta shiga zuwa Mowab, ba su yarda wani ya haye ba.29. A lokacin sun kashe mutanen Mowab dubu goma, dukansu jarumawa da masu ji da ƙarfi; ba ko ɗaya da ya tsira.30. A wannan rana aka mai da Mowab bayin Isra’ila, ƙasar kuwa ta sami zaman lafiya shekara takwas.31. Bayan Ehud, sai Shamgar ɗan Anat, wanda ya karkashe Filistiyawa ɗari shida da sandar korar shanun noma, shi ma ya ceci Isra’ila.Mahukunta 4:1-241. Bayan rasuwar Ehud, Isra’ilawa suka sāke aikata mugayen ayyuka a gaban Ubangiji.2. Saboda haka Ubangiji ya sayar da su ga Yabin sarkin Kan’ana wanda yake mulki a Hazor. Shugaban mayaƙansa shi ne Sisera, wanda yake zaune a Haroshet Haggoyim.3. Domin Yabin sarkin Kan’ana yana da kekunan yaƙin ƙarfe ɗari tara, ya ji wa Isra’ilawa ƙwarai har shekara ashirin, sai suka yi kuka ga Ubangiji, don taimako.4. A lokacin Debora annabiya, matar Laffidot ce take bi da Isra’ila.5. Takan yi zaman shari’a a ƙarƙashin Dabinon Debora tsakanin Rama da Betel, a ƙasar tudu ta Efraim, Isra’ilawa kuwa sukan zo wurinta don tă yi musu shari’a.6. Sai ta aika a kira mata Barak ɗan Abinowam daga Kedesh a Naftali, ta ce masa, “ Ubangiji, Allah na Isra’ila ya umarce ka, ‘Je ka, ka ɗauki mutane Naftali da na Zebulun dubu goma tare da kai, ka yi jagoransu zuwa Dutse Tabor.7. Zan jawo Sisera, shugaban mayaƙan Yabin, da keken yaƙinsa da mayaƙansa zuwa Kogin Kishon in ba da su a hannunku.’ ”8. Barak ya ce, “In kika tafi tare da ni, zan tafi; amma in ba ki zo tare da ni ba, ba zan tafi ba.”9. Debora ta ce, “To, shi ke nan, zan tafi tare da kai. Amma saboda yadda ka ɗauki wannan batun, darajar ba za tă zama taka ba, gama Ubangiji zai ba da Sisera a hannun mace.” Saboda haka Debora ta tafi tare da Barak zuwa Kedesh,10. a can Barak ya kira Zebulun da Naftali. Mutum dubu goma suka kuma bi shi, Debora kuma tana tare da shi.11. To, Heber Bakene ya riga ya bar Keniyawa, zuriyar Hobab, ɗan’uwan matar Musa, ya kafa tentinsa wajen babban itace a Za’anannim kusa da Kedesh.12. Sa’ad da aka gaya wa Sisera cewa Barak ɗan Abinowam ya haura zuwa dutsen Tabor,13. sai Sisera ya tattara keken yaƙinsa na ƙarfe ɗari tara wuri ɗaya da dukan mutanen da suke tare da shi daga Haroshet Haggoyim zuwa Kogin Kishon.14. Sa’an nan Debora ta ce wa Barak, “Je ka! Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya ba da Sisera a hannunka. Ba Ubangiji ya riga ya sha gabanka?” Saboda haka Barak ya gangara zuwa Dutsen Tabor, da mutum dubu goma biye da shi.15. Da matsowar Barak, Ubangiji ya murƙushe Sisera da dukan sarakunansa da mayaƙansa da takobi, Sisera kuwa ya gudu da ƙafa ya bar keken yaƙinsa.16. Amma Barak ya bi keken yaƙin da mayaƙan har Haroshet Haggoyim. Aka karkashe dukan mayaƙan Sisera ba ko ɗayan da ya tsira.17. Amma Sisera, ya tsere da ƙafa zuwa tentin Yayel, matar Heber Bakene, domin suna da abokantaka da Yabin sarkin Hazor da kuma kabilar Heber Bakene.18. Yayel ta fito ta taryi Sisera ta ce masa, “Ranka yă daɗe, ka shigo, ka shigo ciki. Kada ka ji tsoro.” Saboda haka ya shiga cikin tentinta, sai ta rufe shi da bargo.19. Sai ya ce, “Ina roƙonki, ki ba ni ruwa in sha, ina jin ƙishirwa.” Sai ta buɗe salkar madara, ta ba shi ya sha, sai ta kuma rufe shi.20. Ya ce mata, “Ki tsaya a ƙofar tenti, in wani ya zo ya tambaye ki, ‘Akwai wani a nan?’ Ki ce masa ‘a’a.’ ”21. Amma Yayel, matar Heber, ta ɗauki turken tenti da guduma ta tafi wurinsa da sauri sa’ad da yake barci saboda gajiya. Ta kafa masa turken a gindin kunnensa ta haɗa shi da ƙasa, har ya mutu.22. Sai ga Barak mai bin sawun Sisera, Yayel kuwa ta fito don marabtarsa, ta ce, “Shigo, zan nuna maka mutumin da kake nema.” Saboda haka ya shiga ciki tare da ita, sai ga Sisera kwance da turken a gindin kunnensa, matacce.23. A ranar Allah ya yi kaca-kaca da Yabin, sarkin Kan’ana a gaban Isra’ila.24. Isra’ilawa kuwa suka ƙara ƙarfi gāba da Yabin, sarkin Kan’aniyawa, har suka hallaka shi.Zabura 48:9-149. Cikin haikalinka, ya Allah, mun yi tunani a kan ƙaunarka marar ƙarewa.10. Kamar sunanka, ya Allah, yabonka ya kai iyakokin duniya; hannunka na dama ya cika da adalci.11. Dutsen Sihiyona ya yi farin ciki, ƙauyukan Yahuda suna murna saboda hukuntanka.12. Yi tafiya cikin Sihiyona, ku kewaye ta, ku ƙirga hasumiyoyinta,13. ku lura da katangarta da kyau, ku dubi fadodinta, don ku faɗe su ga tsara mai zuwa.14. Gama wannan Allah shi ne Allahnmu har abada abadin; zai zama jagorarmu har zuwa ƙarshe.Karin Magana 14:18-1918. Marar azanci kan gāji wauta, amma mai la’akari kan sami rawanin sani.19. Masu mugunta za su rusuna a gaban masu kirki, mugaye kuma za su yi haka a ƙofofin adalai.Luka 14:25-3525. Taron mutane mai yawa suna tafiya tare da Yesu, sai ya juya ya ce musu,26. “Duk wanda yakan zo wurina, amma bai ƙi mahaifinsa da mahaifiyarsa, da matarsa da ’ya’yansa, da ’yan’uwansa mata da maza, kai, har ma ransa ba, ba zai iya zama almajirina ba.27. Kuma duk wanda ba yakan ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, ba zai iya zama almajirina ba.28. “In wani daga cikinku yana so ya gina gidan sama, ai, yakan fara zama ne, ya yi lissafin abin da ginin zai ci tukuna, don yă ga ko yana da isashen kuɗi da zai gama ginin.29. Gama in ya sa tushen gini, amma bai iya gamawa ba, duk wanda ya gani zai yi masa ba’a,30. yana cewa, ‘Wannan mutum ya fara gini, amma bai iya gamawa ba.’31. “Ko kuma, wane sarki ne, in zai je yaƙi da wani sarki, ai, yakan fara zama ne, ya duba ya ga, ko da mutane dubu goma, shi zai iya ƙarawa da mai zuwa da dubu ashirin?32. In ba zai iya ba, to, tun suna nesa, zai aika da wakilai, su je neman sharuɗan salama.33. Haka nan fa, kowane ne a cikinku, da ba ya rabu da abin da yake da shi ba, ba zai iya zama almajirina ba.34. “Gishiri fa yana da kyau, amma in gishiri ya rabu da daɗin ɗanɗanonsa, ta yaya za a sāke mai da daɗin ɗanɗanonsa?35. Ba shi da wani amfani, ko ga ƙasa, ko ga juji, sai dai a zubar da shi. “Duk mai kunnen ji, yă ji.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.