Baibul a cikin shekara guda Afrilu 21Mahukunta 7:1-251. Kashegari da sassafe, Yerub-Ba’al (wato, Gideyon) da dukan mutanensa suka kafa sansani a maɓulɓulan Harod. Sansanin Midiyawa kuma yana arewa da su a kwari kusa da tudu na More.2. Sai Ubangiji ya ce wa Gideyon, “Mutanen da kake da su sun yi mini yawa da zan ba da Midiyawa a hannunsu. Don kada Isra’ila tă yi mini fahariya cewa ƙarfinta ne ya cece su,3. ka yi shela ga mutane yanzu cewa, ‘Duk wanda ya yi rawan jiki don tsoro, sai yă juya yă bar Dutsen Gileyad.’ ” Saboda haka mutum dubu ashirin da biyu suka koma, sai mutum dubu goma suka rage.4. Amma Ubangiji ya ce wa Gideyon, “Har yanzu mutanen sun yi yawa. Ka kai cikin ruwa, in kuma tankaɗe maka su a can. In na ce, ‘Wannan zai tafi da kai,’ to, zai tafi; amma in na ce, ‘Wannan ba zai tafi da kai ba,’ to, ba zai tafi ba.”5. Saboda haka Gideyon ya kai mutanen cikin ruwa. A can Ubangiji ya ce masa, “Ka ware waɗanda suka tanɗi ruwa kamar kare daga waɗanda suka durƙusa suka sha ruwan.”6. Mutum ɗari uku sun tanɗi ruwa, dukan sauran kuwa suka durƙusa suka sha ruwan.7. Sai Ubangiji ya ce wa Gideyon, “Da mutum ɗari uku ɗin nan da suka tanɗi ruwa, zan cece ka in kuma ba da Midiyawa a hannuwanku. Ka bar sauran mutane su tafi kowa zuwa wurinsa.”8. Saboda haka Gideyon ya mai da sauran Isra’ilawa zuwa tentinsu amma ya riƙe mutum ɗari uku waɗanda suka karɓi guzuri da ƙahonin sauran. To, sansanin Midiyawa yana ƙasa da su a kwarin.9. A daren nan Ubangiji ya ce wa Gideyon, “Tashi ka tafi sansaninsu domin zan ba da su a hannuwanka.10. In kana tsoron fāɗa musu, sai ka tafi da bawanka Fura11. ka kuma saurari abin da suke faɗi. Bayan haka za ka sami ƙarfin hali ka auka musu.” Saboda haka sai ya tafi tare da Fura bawansa zuwa sansanin.12. Midiyawa, Amalekawa da dukan sauran mutane gabashi suka yi sansani a kwari, kamar fāra. Raƙumansu kuma kamar yashi a bakin teku don sun wuce ƙirge.13. Gideyon ya iso daidai wani yana faɗa wa wani aboki mafarkinsa, yana cewa, “Na yi mafarki, na ga dunƙule burodin sha’ir ya fāɗo a tsakiyar sansanin Midiyawa. Ya bugi tentin da ƙarfin da ya sa tenti ta kife a ƙasa.”14. Abokinsa ya ce, “Ai wannan ba wani abu ba ne fiye da takobin Gideyon ɗan Yowash, mutumin Isra’ila. Allah ya ba da Midiyawa da dukan sansani a hannuwansa.”15. Da Gideyon ya ji mafarkin da fassararsa, sai ya yi wa Allah sujada. Ya koma sansanin Isra’ila ya yi kira da ƙarfi ya ce, “Ku tashi! Ubangiji ya ba da sansanin Midiyawa a hannuwanku.”16. Ya raba mutum ɗari uku ɗin kashi uku, ya ba kowannensu ƙaho da tulu da acibalbal a ciki.17. Ya ce musu, “Ku dube ni, ku bi abin da na yi. Sa’ad da na kai sansanin, ku yi daidai abin da na yi.18. Sa’ad da ni da dukan waɗanda suke tare da ni muka busa ƙahoninmu, to, ko’ina a kewayen sansanin sai ku busa naku ku kuma yi ihu, ku ce, ‘Don Ubangiji da kuma domin Gideyon.’ ”19. Gideyon da mutum ɗari da suke tare da shi suka kai sansanin da tsakar dare bayan an sauya matsara. Suka busa ƙahoninsu, suka farfashe tulunansu da suke hannuwansu.20. Ƙungiyoyi uku ɗin nan suka busa ƙahonin, suka fasa tuluna. Suka ɗauki acibalbal a hannuwansu na hagu da ƙahonin busawa a hannuwansu na dama, sai suka yi ihu, “Takobi don Ubangiji da kuma don Gideyon!”21. Yayinda kowannensu ya tsaya a inda yake kewaye da sansanin, dukan Midiyawa suka fito da gudu, suna kuka yayinda suke gudu.22. Sa’ad da aka busa ƙahonin nan ɗari uku sai Ubangiji ya sa Midiyawa suka yi ta saran juna. Mayaƙan suka gudu zuwa Bet-Shitta wajen Zerera har zuwa yankin Abel-Mehola kusa da Tabbat.23. Aka kira dukan Isra’ilawa daga Naftali, Asher da dukan Manasse, suka kuwa fatattaki Midiyawa.24. Gideyon ya aiki manzanni zuwa dukan ƙasar tudu ta Efraim cewa, “Ku gangaro ku yaƙi Midiyawa ku ƙwace ruwan Urdun gaba da su har zuwa Bet-Bara.” Saboda haka aka kira dukan mutanen Efraim suka ƙwace ruwan Urdun har zuwa Bet-Bara.25. Suka kuma kama shugabannin biyu na Midiyawa, Oreb da Zeyib suka kashe Oreb a dutsen Oreb, Zeyib kuma a wurin matsin ruwa inabin Zeyib. Suka fatattaki Midiyawa suka kawo kawunan Oreb da Zeba wurin Gideyon, wanda yake kusa da Urdun.Mahukunta 8:1-351. To, mutanen Efraim suka ce wa Gideyon, “Me ya sa ka yi mana haka? Me ya sa ba ka kira mu lokacin da ka tafi yaƙi da Midiyawa ba?” Suka zarge shi sosai.2. Amma ya ce musu, “Me na yi da za a iya kwatanta da abin da kuka yi? Ashe, kalar inabin da Efraim ta yi bai fi dukan girbin inabin da Abiyezer suka yi ba?3. Allah ya ba da Oreb da Zeyib, shugabannin Midiyawa a hannuwanku. Me na yi da ya fi naku? Da ya faɗi haka sai hankalinsu ya kwanta.”4. Gideyon da mutanensa ɗari uku, sun gaji, duk da haka suka yi ta fafarar, suka zo Urdun suka haye shi.5. Ya ce wa mutanen Sukkot, “Ku ba wa mutanena burodi; sun gaji, har yanzu ina fafarar Zeba da Zalmunna, sarakunan Midiyawa.”6. Amma shugabannin Sukkot suka ce, “Ka kama Zeba da Zalmunna ko ne? Don me za mu ba wa mayaƙanka burodi?”7. Sai Gideyon ya ce, “Haka ko? To, sa’ad da Ubangiji ya ba da Zeba da Zalmunna a hannuna, zan tsattsaga jikinku da ƙayayyuwan jeji.”8. Daga nan ya wuce zuwa Fenuwel ya yi irin roƙon nan, amma suka amsa yadda mutanen Sukkot suka yi.9. Saboda haka sai ya ce wa mutanen Fenuwel, “Sa’ad da na dawo da nasara zan rushe wannan hasumiya.”10. To, Zeba da Zalmunna suna a Karkor da mayaƙa wajen dubu goma sha biyar, abin da ya rage ke nan na mayaƙan gabashi; mayaƙa masu takobi dubu ɗari da ashirin ne suka mutu.11. Gideyon ya haura ta hanyar makiyaya, gabas da Noba, da kuma Yogbeha, ya fāɗa wa mayaƙan ta yadda ba su zata ba.12. Zeba da Zalmunna, sarakunan biyu na Midiyawa suka tsere, amma ya bi su ya kama, ya fatattaki dukan mayaƙansu.13. Sa’an nan Gideyon ɗan Yowash ya komo daga yaƙi ta Hanyar Heres.14. Ya kama wani saurayin Sukkot ya tambaye shi, saurayin kuwa ya rubuta masa dukan sunayen shugabanni saba’in da bakwai na Sukkot, da dattawan garin.15. Sa’an nan Gideyon ya zo ya ce wa mutanen Sukkot, “To, ga Zeba da Zalmunna, waɗanda kuka yi mini ba’a kuna cewa, ‘Ka kama Zeba da Zalmunna ko ne? Me zai sa mu ba mutanenka da suka gaji burodi?’ ”16. Ya kwashe dattawan garin ya koya wa mutanen Sukkot hankali ta wurin hukunta su da ƙayayyuwan hamada.17. Ya rushe hasumiyar Fenuwel ya kuma karkashe mutanen garin.18. Sa’an nan ya ce wa Zeba da Zalmunna, “Waɗanne irin mutane ne kuka karkashe a Tabor.” Suka ce, “Mutane kamar ka ne kowane kamar ɗan sarki.”19. Gideyon ya ce, “Waɗannan ’yan’uwana ne, ’ya’yan mahaifiyata. Muddin Ubangiji yana a raye, da a ce kun bar su da rai, da ba zan kashe ku ba.”20. Da ya juya wajen Yeter, ɗan farinsa, sai ya ce, “Ka kashe su!” Amma Yeter bai zāre takobinsa ba, domin shi yaro ne kawai kuma yana tsoro.21. Zeba da Zalmunna suka ce masa, “Zo, ka yi da kanka. ‘Yadda mutum yake haka ƙarfinsa.’ ” Ta haka Gideyon ya matso gaba ya kashe su, ya ɗauki kayan ado daga wuyar raƙumansu.22. Isra’ilawa suka ce wa Gideyon, “Ka yi mulkinmu, kai, ɗanka da jikanka, domin ka cece mu daga hannun Midiyawa.”23. Amma Gideyon ya ce musu, “Ni, ko ɗana, ba za mu yi mulkinku ba. Ubangiji ne zai yi mulkinku.”24. Kuma ya ce, “Ina da roƙo guda ɗaya, cewa kowannenku ya ba ni ’yan kunne daga rabon ganima.” (Al’adar mutanen Ishmayel ce su sa ’yan kunnen zinariya.)25. Suka ce, “Za mu yi farin cikin ba ka su.” Saboda haka suka shimfiɗa mayafi, kowanne ya sa ɗan kunne ɗaya daga ganimar.26. Nauyin ’yan kunnen zinariyar ya kai shekel ɗari goma sha bakwai, ban da kayan ado, abin wuya da tufafin shunayya waɗanda sarakuna Midiyawa suke sawa ko sarƙoƙin da suke wuyar raƙumansu.27. Gideyon ya efod da zinariyar, wanda ya ajiye a Ofra, garinsa. Dukan Isra’ila suka shiga yin karuwanci ta wurin yin sujada a can, ya kuwa zama wa Gideyon da dukan iyalinsa tarko.28. Da haka Isra’ilawa suka mallaki Midiyawa ba su kuma sāke tā da kai ba. A zamanin Gideyon ƙasar ta sami zaman lafiya har shekara arba’in.29. Yerub-Ba’al ɗan Yowash ya koma gida don yă zauna.30. Yana da ’ya’ya saba’in maza da ya haifa, gama yana da mata da yawa.31. Yana kuma da ƙwarƙwara wadda take Shekem, ita ma ta haifa masa ɗa wanda ya ba shi suna Abimelek.32. Gideyon ɗan Yowash ya rasu da kyakkyawan tsufa aka kuma binne shi a kabarin Yowash mahaifinsa a Ofra na mutanen Abiyezer.33. Ba a daɗe da rasuwar Gideyon ba, sai Isra’ila ta sāke shiga karuwanci suna bauta wa Ba’al. Suka kafa Ba’al-Berit yă zama musu allahnsu ba kuma34. tuna da Ubangiji Allahnsu, wanda ya cece su daga hannuwan abokan gābansu a kowane gefe ba.35. Suka kāsa nuna alheri ga gidan Yerub-Ba’al (wato, Gideyon) saboda abubuwa masu alherin da ya yi musu.Zabura 49:10-2010. Gama kowa na iya ganin masu hikima na mutuwa; wawaye da marasa azanci su ma kan hallaka su bar wa waɗansu arzikinsu.11. Kaburburansu za su ci gaba da zama gidajensu har abada, Can za su kasance har zamanai marasa ƙarewa, ko da yake sun ba wa filaye sunayen kansu.12. Amma mutum, kome arzikinsa, ba ya dawwama; shi kamar dabbobi ne da suke mutuwa.13. Wannan ne ƙaddarar waɗanda suke dogara a kansu, da kuma ta mabiyansu, waɗanda suka tabbatar da faɗinsu.14. Kamar tumaki an ƙaddara su ga kabari; za su kuwa zama abincin mutuwa amma masu gaskiya za su yi mulki a kansu da safe. Kamanninsu za su ruɓe a cikin kabari, nesa da gidajensu masu tsada.15. Amma Allah zai ceci raina daga kabari; tabbatacce zai ɗauke ni zuwa wurinsa.16. Kada ka razana da yawa sa’ad da mutum ya yi arziki sa’ad da darajar gidansa ta ƙaru;17. gama ba zai ɗauki kome tare da shi sa’ad da ya mutu ba, darajarsa ba za tă gangara tare da shi ba.18. Ko da yake yayinda yake a raye ya ɗauka kansa mai albarka ne, mutane kuma sun yabe ka sa’ad da kake cin nasara,19. zai gamu da tsarar kakanninsa, waɗanda ba za su taɓa ganin hasken rayuwa ba.20. Mutumin da yake da arziki ba tare da ganewa ba shi kamar dabbobi ne da suke mutuwa.Karin Magana 14:22-2422. Ba waɗanda suke ƙulla mugunta sukan kauce ba? Amma waɗanda suke ƙulla abin da yake mai kyau sukan sami ƙauna da aminci.23. Duk aiki tuƙuru yakan kawo riba, amma zama kana surutu kan kai ga talauci kawai.24. Dukiyar masu hikima ita ce rawaninsu, amma wautar wawaye kan haifar da wauta ne kawai.Luka 15:11-3211. Yesu ya ci gaba da cewa, “Akwai wani mutum wanda yake da ’ya’ya biyu maza.12. Ƙaramin ya ce wa mahaifinsu, ‘Baba, ba ni rabon gādona.’ Sai mahaifin ya raba musu dukiyarsa.13. “Bayan ’yan kwanaki, sai ƙaramin ɗan ya tattara kayansa duk, ya tashi ya tafi wata ƙasa mai nisa. A can, ya ɓatar da dukiyarsa duka a rayuwar banza.14. Bayan ya ɓatar da kome, sai ga muguwar yunwa a dukan ƙasar, har ya shiga rashi.15. Sai ya je ya sami aiki a wurin wani mutumin ƙasar, wanda ya aike shi a gonakinsa, ya yi kiwon aladu.16. Ya yi marmarin cin dusan da aladun suke ci, amma ba wanda ya ba shi wani abu.17. “Da hankalinsa ya dawo, sai ya ce, ‘Kai, bayin mahaifina guda nawa ne, da suke da abinci fiye da isashe, ni kuma ina nan, zan mutu don yunwa!18. Zan tashi in koma wurin mahaifina, in ce masa, “Baba, na yi wa sama, na kuma yi maka zunubi.19. Ni ban isa a ƙara kira na ɗanka ba. Ka mai da ni kamar ɗaya daga cikin bayinka.” ’20. Sai ya tashi ya kama hanya ya koma wurin mahaifinsa. “Amma tun yana nesa, mahaifinsa ya hange shi. Tausayi kuma ya kama shi, sai ya tashi ya ruga da gudu wurinsa, ya rungume shi, ya yi masa sumba.21. “Sai ɗan ya ce masa, ‘Baba, na yi wa sama, na kuma yi maka zunubi. Ni ban isa a ƙara kira na ɗanka ba.’22. “Amma mahaifin ya ce wa bayinsa, ‘Maza! Ku kawo riga mafi kyau ku sa masa. Ku sa zobe a yatsarsa, da takalma kuma a ƙafafunsa.23. Ku kawo ɗan saniya mai ƙiba ku yanka. Bari mu yi biki mu yi shagali.24. Gama ɗan nan nawa, da ya mutu, amma yanzu yana da rai kuma. Da ya ɓata, amma yanzu an same shi.’ Sai suka fara shagali.25. “Yayinda ake haka, babban ɗan yana gona. Da ya zo kusa da gida, sai ya ji ana kiɗi ana rawa.26. Sai ya kira ɗaya daga cikin bayin, ya tambaye shi abin da yake faruwa.27. Bawan ya ce, ‘Ai, ɗan’uwanka ne ya dawo, shi ne mahaifinka ya yanka ɗan saniya mai ƙiba, gama ya yi murna ya karɓi ɗansa da ya dawo gida lafiyayye, ba abin da ya same shi.’28. “Sai yayan ya yi fushi, ya ƙi shiga gida. Sai mahaifinsa ya fita ya roƙe shi.29. Amma ya amsa wa mahaifinsa ya ce, ‘Duba! Duk waɗannan shekaru, ina yin maka aiki kamar bawa, ban taɓa maka rashin biyayya ba. Duk da haka, ba ka taɓa ba ni ko ɗan akuya domin in yi shagali da abokaina ba.30. Amma da wannan ɗan naka, wanda ya ɓatar da dukiyarka a kan karuwai ya dawo, ka yanka masa ɗan saniya mai ƙiba!’31. “Sai mahaifin ya ce masa, ‘Ɗana, kullum kana nan tare da ni, kuma duk abin da nake da shi, naka ne.32. Amma ya zama mana dole, mu yi shagali, mu yi murna, domin ɗan’uwan nan naka, da ya mutu, yanzu kuwa yana da rai, da ya ɓata, amma yanzu an same shi.’ ” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.