Baibul a cikin shekara guda Afrilu 5Maimaitawar Shariʼa 33:1-291. Wannan ita ce albarkar da Musa mutumin Allah ya furta a kan Isra’ilawa, kafin yă rasu.2. Ya ce, “ Ubangiji ya zo daga Sinai ya haskaka a bisansu daga Seyir; ya haskaka daga Dutsen Faran. Ya zo tare da dubban tsarkakansa daga kudu, daga gangara dutsensa.3. Tabbatacce kai ne wanda yake ƙaunar mutane; dukan tsarkaka suna a hannunka. A ƙafafunka, duk suka rusuna, daga wurinka kuma suka karɓi umarni,4. dokar Musa ta ba mu dokoki, mallakar taron Yaƙub.5. Shi ne sarki a bisa Yeshurun sa’ad da shugabannin mutane suka taru, tare da kabilan Isra’ila.6. “Bari Ruben yă rayu, kada yă mutu, kada mutanensa su zama kaɗan.”7. Ya kuma faɗa wannan game da Yahuda, “Ka ji, ya Ubangiji, kukan Yahuda; ka kawo shi wurin mutanensa. Da hannuwansa ya kāre kansa. Ka taimake shi a kan maƙiyansa!”8. Game da Lawi ya ce, “Tummim da Urim na mutumin da ka nuna masa tagomashi ne. Ka gwada shi a Massa; ka yi faɗa da shi a ruwan Meriba.9. Ya yi zancen mahaifinsa da mahaifiyarsa ya ce, ‘Ban kula da su ba.’ Bai gane da ’yan’uwansa ba, ko yă yarda da ’ya’yansa, amma ya kiyaye maganarka ya tsare alkawarinka.10. Ya koyar da farillanka ga Yaƙub, dokarka kuma ga Isra’ila. Ya miƙa turare a gabanka da kuma hadaya ta ƙonawa ɗungum a kan bagadenka.11. Ka albarkaci ɗaukan dabarunsa, ya Ubangiji, ka kuma ji daɗin aikin hannuwansa. Ka murƙushe kwankwaso waɗanda suka tayar masa; ka bugi abokan gābansa har sai ba su ƙara tashi ba.”12. Game da Benyamin ya ce, “Bari ƙaunataccen Ubangiji yă zauna lafiya kusa da shi, gama yana tsare shi dukan yini, wanda kuma Ubangiji yake ƙauna yana zama a tsakanin kafaɗunsa.”13. Game da Yusuf ya ce, “Bari Ubangiji yă albarkaci ƙasarsa da raɓa mai daraja daga sama a bisa da kuma zurfin ruwan da suke kwance a ƙarƙashi;14. da abubuwa masu kyau da rana take kawo, da kuma abubuwa mafi kyau da wata zai iya haifar;15. da zaɓaɓɓun kyautai na daɗaɗɗun duwatsu, da kyawawan amfani na madawwaman tuddai.16. Tare da kyautai mafi kyau na duniya da cikarta, da tagomashi na wanda yake zama a ƙaramin itace mai ƙonewa. Bari duk waɗannan su zauna a kan Yusuf, a goshin sarki a cikin ’yan’uwansa.17. Cikin daraja yana yi kamar ɗan fari na bijimi; ƙahoninsa ƙahonin ɓauna ne. Tare da su zai tukwiyi al’ummai, har ma da waɗanda suke ƙarshen duniya. Haka dubu dubban Efraim suke; haka dubban Manasse suke.”18. Game da Zebulun ya ce, “Ka yi farin ciki, Zebulun, a fitowarka, kai kuma Issakar, a cikin tentunanka.19. Za su kira mutane zuwa dutse, a can za su miƙa hadayun adalci; za su yi biki a yalwan tekuna, a dukiyoyin da aka ɓoye a cikin yashi.”20. Game da Gad ya ce, “Mai albarka ne wanda ya fadada mazaunin Gad! Gad yana zama a can kamar zaki, yana yayyage a hannu da kai.21. Ya zaɓi ƙasa mafi kyau wa kansa; aka ajiye masa rabon shugaba. Sa’ad da shugabannin mutane suka taru, ya aikata adalcin Ubangiji da kuma hukuncinsa game da Isra’ila.”22. Game da Dan ya ce, “Dan ɗan zaki ne, yana tsalle daga Bashan.”23. Game da Naftali ya ce, “Naftali ƙosasshe ne da tagomashin Ubangiji, ya kuma cika albarkarsa; zai gāji gefen kudu zuwa tafki.”24. Game da Asher ya ce, “Mafi albarka na ’ya’yan, shi ne Asher; bari yă sami tagomashi daga ’yan’uwansa, bari kuma yă wanke ƙafafunsa a cikin mai.25. Madogaran ƙofofinka za su zama ƙarfe da tagulla, ƙarfinka kuma zai zama daidai da kwanakinka.26. “Babu wani kamar Allah na Yeshurun, wanda yake hawa a bisa sammai don yă taimake ka a kan gizagizai kuma a cikin darajarsa.27. Allah madawwami shi ne mafakarka, a ƙarƙashina kuma madawwamin hannuwa ne. Zai kore abokin gābanka a gabanka, yana cewa, ‘Ka hallaka shi!’28. Haka Isra’ila zai zauna lafiya shi kaɗai; zuriyar Yaƙub a tsare a ƙasar hatsi da sabon ruwan inabi, inda sammai za su zuba raɓa.29. Kai mai albarka ne, ya Isra’ila! Wane ne yake kamar ka, mutanen da Ubangiji ya ceta? Shi ne mafakarka da mai taimakonka da kuma takobinka mai ɗaukaka. Abokan gābanka za su zo neman jinƙai a gabanka, za ka kuwa tattake masujadansu.”Maimaitawar Shariʼa 34:1-121. Sai Musa ya hau Dutsen Nebo daga filayen Mowab, zuwa ƙwanƙolin Fisga, wanda yake ƙetare Yeriko. A can Ubangiji ya nuna masa dukan ƙasar, daga Gileyad zuwa Dan,2. da ta dukan Naftali, da yankin Efraim da na Manasse, dukan ƙasar Yahuda har zuwa Bahar Rum,3. da Negeb da dukan yankin Kwarin Yeriko, Birnin Dabino, har zuwa Zowar.4. Sa’an nan Ubangiji ya ce masa, “Wannan ce ƙasar da na yi alkawari da rantsuwa wa Ibrahim, Ishaku da Yaƙub, sa’ad da na ce, ‘Zan ba da ita ga zuriyarku.’ Na bar ka ka gani da idanunka, amma ba za ka haye zuwa cikinta ba.”5. Nan fa, a ƙasar Mowab Musa bawan Ubangiji ya mutu, yadda Ubangiji ya faɗa.6. Aka binne shi a Mowab, a kwarin kusa da Bet-Feyor, amma har wa yau babu wanda ya san inda kabarinsa yake.7. Musa yana da shekara ɗari da ashirin sa’ad da ya mutu, duk da haka idanunsa ba su dushe ba, ƙarfinsa kuwa bai ragu ba.8. Isra’ilawa suka yi makoki domin Musa a filayen Mowab kwana talatin, sai da lokacin kuka, da na makoki suka ƙare.9. To, Yoshuwa ɗan Nun ya cika da ruhun hikima, gama Musa ya ɗibiya hannuwansa a kansa. Saboda haka Isra’ilawa suka saurare shi, suka kuma aikata abin da Ubangiji ya umarci Musa.10. Tun daga nan ba a sāke yin wani annabi a Isra’ila kamar Musa ba, wanda Ubangiji ya san shi fuska da fuska,11. wanda kuma ya yi dukan waɗannan alamu banmamaki da al’ajaban da Ubangiji ya aike shi yă yi a Masar, da a kan Fir’auna, da a kan dukan shugabanninsa, da kuma a kan dukan ƙasarsa.12. Gama babu wani wanda ya taɓa nuna iko mai ƙarfi, ko yă aikata ayyukan banrazana waɗanda Musa ya yi a gaban dukan Isra’ila.Zabura 40:13-1713. Ka ji daɗin cetona, ya Ubangiji; Ya Ubangiji, ka zo da sauri ka taimake ni.14. Bari masu neman raina su sha kunya su kuma rikice; bari dukan waɗanda suke neman lalacewata su koma baya da kunya.15. Bari masu ce mini, “Allah yă ƙara!” Su sha mamaki saboda kunyar da za su sha.16. Amma bari dukan masu nemanka su yi farin ciki su kuma yi murna a cikinka; bari waɗanda suke ƙaunar cetonka kullum su ce, “ Ubangiji mai girma ne!”17. Ni dai matalauci ne da mai bukata; bari Ubangiji yă tuna da ni. Kai ne taimakona da mai cetona; Ya Allahna, kada ka jinkirta.Karin Magana 13:13-1413. Duk wanda ya rena umarni zai ɗanɗana ƙodarsa, amma duk wanda ya yi biyayya da umarni zai sami lada.14. Koyarwar mai hikima maɓulɓulan rai ne, mai juyar da mutum daga tarkon mutuwa.Luka 8:1-251. Bayan wannan sai Yesu ya zazzaga gari da ƙauye, yana wa’azin bisharar mulkin Allah. Sha Biyun nan kuwa suna tare da shi,2. da kuma waɗansu mata waɗanda aka warkar da su daga cututtukansu, da kuma mugayen ruhohi. Cikinsu akwai Maryamu (wadda ake kira Magdalin) wadda aljanu bakwai suka fito daga cikinta.3. Da Yowanna matar Kuza, manajan iyalin Hiridus; da Suzana; da waɗansu mata da yawa. Waɗannan mata suna taimaka musu cikin hidima, daga cikin abin da suke da shi na zaman gari.4. Yayinda taron mai girma na taruwa, mutane kuma daga garuruwa dabam-dabam suna zuwa wurin Yesu, sai ya ba da wannan misali ya ce,5. “Wani manomi ya fita domin ya shuka irinsa. Da yana watsa irin, sai waɗansu suka fāɗi a kan hanya, aka tattaka su, tsuntsayen sararin sama kuma suka cinye su.6. Waɗansu suka fāɗi a kan dutse, da suka tsira sai suka yanƙwane don babu ruwa a wurin.7. Waɗansu kuma suka fāɗi a cikin ƙaya. Da suka yi girma tare, sai ƙayan suka shaƙe su.8. Waɗansu kuma har yanzu, suka fāɗi a ƙasa mai kyau, suka yi girma, suka ba da amfani riɓi ɗari-ɗari, fiye da abin da aka shuka.” Da faɗin haka sai ya ce, “Duk mai kunnen ji, yă ji.”9. Almajiransa suka tambaye shi ma’anar wannan misali.10. Sai ya ce, “Ku ne aka ba sanin asirin mulkin Allah, amma ga sauran mutane kam, ina magana da misalai, saboda, “ ‘ko da yake suna kallo, ba za su gani ba, ko da yake suna ji, ba za su gane ba.’11. “Ga ma’anar misalin, irin, shi ne maganar Allah.12. Waɗanda suka fāɗi a kan hanya su ne mutanen da suka ji, amma Iblis, yakan zo ya ɗauke maganar daga zuciyarsu, don kada su gaskata, su sami ceto.13. Na kan dutse kuwa, su ne da jin maganar, sukan karɓa da murna, amma ba su da saiwa. Sukan gaskata na ɗan lokaci, amma lokacin gwaji, sai su ja da baya.14. Irin da suka fāɗi a cikin ƙaya kuwa, su ne mutanen da suka ji, amma a kwana a tashi, tunanin kayan duniya, da neman arziki, da son jin daɗi, sukan hana su ba da ’ya’ya.15. Amma irin da suka fāɗi a ƙasa mai kyau kuwa, su ne mutane masu kyakkyawar zuciya, mai kyau, da suka ji, suka riƙe, suka kuma jimre har suka ba da ’ya’ya.”16. “Ba mai ƙuna fitila sa’an nan ya ɓoye ta a cikin tulu, ko kuma ya sa ta a ƙarƙashin gado ba. A maimakon haka, yakan sa ta a kan wurin ajiye fitila, saboda mutane masu shigowa su ga haske.17. Ba abin da yake ɓoye da ba za a fallasa ba. Kuma ba abin da yake rufe, da ba za a sani ba, ko a fitar da shi a fili ba.18. Saboda haka, ku yi tunani da kyau yadda kuke saurara. Duk wanda yake da shi, za a ƙara masa, duk wanda ba shi da shi kuma, abin da yake tsammani yana da shi ma, za a karɓe daga gare shi.”19. Sai uwar Yesu da ’yan’uwansa suka zo, domin su gan shi, amma ba su iya zuwa kusa da shi ba, saboda taron.20. Sai wani ya faɗa masa cewa, “Ga uwarka da ’yan’uwanka suna tsaye a waje suna so su gan ka.”21. Ya amsa ya ce, “Mahaifiyata da ’yan’uwana, su ne waɗanda suke jin maganar Allah, suna kuma aikata ta.”22. Wata rana Yesu ya ce wa almajiransa, “Mu haye zuwa wancan gefen tafkin.” Sai suka shiga jirgin ruwa suka fara tafiya.23. Da suna cikin tafiya, sai barci ya kwashe shi. Sai wata babban iska ta taso kan tafkin, har ruwa ya fara shiga cikin jirgin. Suka shiga babban hatsari.24. Almajiran suka je suka tashe shi daga barci, suka ce, “Ubangiji, Ubangiji, za mu nutse!” Ya tashi ya kwaɓe iskar da kuma haukar ruwan. Sai ruwan da iskar suka natsu. Kome ya yi tsit.25. Sai ya tambayi almajiransa, “Ina bangaskiyarku?” A cikin tsoro da mamaki, suka ce wa junansu, “Wane ne wannan? Yana ba da umarni ga iska da ruwa ma, kuma suna biyayya da shi?” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.